REINA

4

by @seemahwrites


04...."My T. Ina kwana" ta maida masa da gaisuwar. Tana ƙarawa da "kaga ƴar rigimar ka ta hana mu barci ko?"

Ya murmusa, kwana 5 kenan amma har yanzu wani ɓangare na jikin shi ya kasa gaskata cewa wanzuwar Reina cikin rayuwar su gaskiya ne ba mafarki ba.
"Duk wata Sarauniya ai da rigima aka santa Fauzah ta"

"Oh haka ma kace? To gobe wurin ka zan kawo ta ku kwana"

Saida ya dara kana yace "Da kuwa kinga yanda ake raino mai kyau ba Irin naku na ƴan koyo ba."

Zancen shi ya saka ta darawa itama "ai ko? To kuwa kada daga baya kazo kace ba haka ba"

"Ki gwada ni mana ki gani" yace yana miƙa hannu ya karɓi babyn Ganin ta cire bakin ta daga jikin Fauziyya.
"Zo nan ƴar albarka, baiwar Allah, Fauzah tana so tayi miki sharri ko?" Yace yana lakatar fuskar Reina ita kuwa ta shiga murmusawa.

"Masha Allah tabarakallah, Fauzah kaman kakin yarinyar nan kika yi" 

Leƙa fuskar Reina Hajiya Fauziyya tayi tace "ni kuwa banga kaman da ake ta cewan ba T. Haka hanci na yake a nane?"

"Toh ta girma ne kika ga bai tsiro ba?" ya amshe cikin salon karɓa ma ƴarshi faɗa.

"Oh ashe hancin ma shuka ne da zai tsiro"

Ciza laɓɓan shi yayi ya ɗan jijjiga kai. "Idanma bai fito ba zamu yanke naki ne mu dasa mata"

"Lala-lala, Sarauniyar babanta ne ba nawa ba, kuje can ku ƙarata da munin ku" tace tana taɓe baki.

"Munji mun gode kuma zaki maimaita" ya sumbaci kumatun Reina sannan ya maida ta ma Fauziyya yana faɗin "toh mun fita sai ayi mana addu'a"

"Allah ya kiyaye, ya tsare kuma yasa a samu abinda aka je nima"

Da ameen ya amsa yana juyawa baby ta callara ƙara. "Iyee, to ai sai kazo ku tafi tare, kaga tun yanzu an fara nuna min fifiko" 

Juyowa yayi ya dawo yana faɗin "Don kada ki wuni kuka ne amma da taren zamu tafi" ya sake manna ma Reina sumba kafin ya juya ya fice yana jin kukan ta a cikin zuciyar shi.

Ba'a ɗauki awa guda ba mai jego ta fito cikin rantsatstsiyar leshi da jaririyarta cikin shawul. Ƴan barka har sun fara sintiri, da wanda zuwan su na farko kenan da kuma wanda so da girmama abin duniya ya saka su dawowa a karo na barkatai.

A cikin baby basket aka saka Reina duk mai son kallon ta saidai yaje ya leƙa don kada a saka mata tsamin jiki a garin passing-passing.

Aka fara shigo da abin kari ma ƴan gaisuwa nan suka zauna suka baje shi tsaff, kafin a ɗaura abincin Rana shima suyi mishi illa.

Hira ta zauna suka sha da baƙin ta dama wanda bata wayi fuskokin su ba har zuwa jimawa da aka samu Reina ta maida barci sai ta nemi iznin ta koma ciki don basu samu isasshen barci ba daren jiya. 

Bata sake fitowa ba saida aka yi azahar nan tazo ta samu yawan mutane sun ninka na ɗazu kaman ma yaune suna, haka ta zauna aka sake sabon gaisuwa.

.....

"Yanzu sake komawa zaka yi?" Tace tana jingine da jikin wardrobe ɗinsu da ƙofofin sun ɓaɓɓalle amma gyara ya gagara saboda damuwowin su na yau da kullum yafi ƙarfin wannan.

"Inada zaɓin da ya wuce wannan ne Saudah? Kina gani dai sati ya kusan ƙarewa yaron nan yana zaune a gida, gashi kema EDDn ki ya kusa, ba zanso har ki haihu Yaseer bai koma makaranta ba" Kamal ya sanya rigan da ta ciro mishi ya shiga haɗa botir.
"Kema da kin shirya ne muka je kika yi musu barka, Hajiya Fauziyya ba zata ji daɗi ba idan baki je ba bayan ta roƙe ki ki dawo."

Taɓe baki Saudat tayi tace "tana zagaye da jama'a ina har zata wani lura da rashin zuwa na?"

"Kiyi haƙuri mu dai je ɗin"

Ta turo baki. "Nifa ba daɗi nake ji ba abban Yaseer."

Sauƙe murya yayi cikin lallashi yace "kiyi haƙuri."

Tana zunkuɗe-zunkuɗen baki ta shiga shiryawa. Shi da kanshi ya fita waje kiran Suhail a wurin wasa kasancewar yau Alhamis babu Islamiyya, shi kuwa sai murna yake ganin za'a je anguwa. Cikin zumuɗi ya shirya

Har sun fito ta jawo musu ƙofa Yaseer ya shigo da uniform ɗin hadda.
"Ina wuni Ummah, ina wuni Abba, fita zaku yi ne?"

"Gidan Alhaji Tahir zamu je yin barkan sabuwar jinjira" cewar Kamal.

"Toh sai kun dawo, Allah ya kiyaye" yace yana nufar hanyar ɗakin su da nufin ya ajiye jakar shi don ya ɗibo yunwa.

"Ai yanzu kam shiryawa zaka yi muje ka taya ni da wannan sarkin rikicin" Saudat ta nuna Suhail da ya washe ma Yaseer ɗin haƙwara baki ɗaya murna ya cika shi.

Sosa kai yayi "Umma zan shigar da hadda ne"

"Babu jimawa ai zamu dawo, sai mu siyo sabon batir ɗin toci ka shigar da haddan da daddare" 

Da toh ya amsa sannan ya shiga ɗaki ya sako T-shirt ɗin gwanjo navy blue da baƙin wando ya fito ya ɗauki buta sannan ya ƙarasa bakin rariya ya ɗauraye ƙuran ƙafar shi ya koma ya shafa mai a ƙafar da fuskan shi sai ƙyalli suke, bai manta da taje kanshi ba. 
kafin lokacin da ya gama Saudat ta gaji da tsayuwa ta samu kujera ta zauna amma kuma bata ƙosa da jiran nashi ba dukda ma bayi da sanyin jiki ko kaɗan.

"Muje umma" yace da ita yana kama hannun suhail, kamal ya riga da ya wuce nima musu napep, itama ta miƙe suka fita.

.

Zuwan Saudat gidan karo na biyu kenan, tun auren Alhaji Tahir da Hajiya Fauziyya shekaru biyu baya sai kuma yau da Allah ya azurta su da samun ƙaruwa, amma kuma gani take kaman an ƙara wa gidan girma da kyau. wai duk wannan gidan mace ce ƴar mace?- take tunani a ranta.

Shi kuwa Kamal ƙiyaste yawan miliyoyin da aka zubar wurin tada gini irin wannan kamar ba a ƙasar shi Nigeria inda miliyoyin mutane suke fama da yunwa bane.

Yanzu har mutane zasu iya rayuwa su kaɗai a irin wannan wargajejen gida suyi barci cikin kwanciyar hankali?- tunanin Yaseer Kenan.

Dakatar dasu da security yayi daga ƙofar shiga ne ya dawo da hankalin su zuwa gare shi, tun kan aje ko ina Saudat har ta fara shiga ɓacin rai bayan yanzu wasu suka shige a gaban su ba tare da an tuhume su ko an bincike su ba.

"Malam Ina zuwa?" Cewar security da ya toshe Idanu da baƙin gilashi.

Ba zuwar Kamal na farko ko biyun sa ba kenan don haka ya saki murmushi tare da cewa "officer Baka gane ni bane?"

"Ban gane ka ba kai wa?"

"Ɗan uwan me gidan ne fah! Sunana Kamal, mun haɗu shekaran jiya nazo gun me gidan ka manta?" Ya ƙarashe da sakin ƙaramin dariyan sanayya don yasan yanzu kam dole ya ɗago shi tunda zuwan shi na bayan ma hana shi shiga yayi sai cikin Sa'a Alhaji Tahir ɗin ya dawo a lokacin, yace masa yaje ya dawo saboda abinci ya dawo ci kuma ba daɗewa zaiyi ba ana jiran sa a office.

Yayi tsammanin yau idan ya dawo yana da direct pass na shiga gidan amma sai security ɗinnan ya ɗan zaro glasses ɗin idanun shi ya lanƙaye ta a karan ƙaton hancinsa ya ƙare musu kallo daga kan Kamal har Suhail a wulaƙance sannan ya maida glasses ɗinshi ya ƙwama.
"Toh idan haka ne ai muma ƴan uwan nashi ne, Please don't waste my time, ku bar wurin nan"

"Mu tafi" Saudat tace da Yaseer. Ya kuwa ja hannun ƙanin shi suka juya zasu bar wurin sai Kamal yayi saurin riƙo hannun ta, yasan idan ta tsaya shima Yaseer nata zai bi.

Kamal ya ƙara faɗaɗa murmushi kafin yace "wallahi ni ɗan uwan shi ne officer, mahaifin su da mahaifiyar mu uba ɗaya uwa kawai suka raba"

Yi yayi kaman bai jishi ba ya juya wurin wani mota da ya tunkaro gidan ya gaida su fuska a sake sannan ya bada izinin a wangale musu su shiga. 

"Abban Yaseer ko aljanna ake rabawa a gidan nan ya kamata mu haƙura haka nan" Saudat tace cikin ƙosawa da ɓacin rai. 

Juyawa yayi ya fuskance ta cikin faɗa-faɗa yace "Haba Saudatu, ki zamo mai hakuri mana, zai barmu mu shiga fah, ki barni muyi magana dashi"

Jinjina kai tayi "toh shikkenan, munyi gaba sai ka Iso" ta riƙo hannun yaranta da niyyar yanzu ko ya tsayar da ita ba tsayawa zata yi ba. 
Wannan wani irin wulaƙanci ne? Wasu sunzo a gaban su wasu sunzo a bayan su duk a keke napep an barsu sun shiga dake su sun sanya kaya masu kyau da tsada sun sha kwalliya kamar suna suka zo tun yau. 

Juyawa suka yi suka fara tafiya har sun kusan ƙure garun gidan shi kuwa Kamal yaji haushin ta don haka bai dakatar da ita ba kuma bai bi bayan ta ba, yaci gaba da roƙon mai gadi ya barshi ya shiga don yaje ya haɗu da Alhaji Tahir Idan yana ciki.

"Umman Yaseer!!" Aka ƙwala mata kira daga cikin adaidaita da ya wuce su, hakan ya saka ta saurin waigawa don ganin waye mai kiran. A ƙofar gidan da suka baro mai napep ya faka Inna larai ta fito tare da yafato Saudat da hannu.

Sakin fuska tayi suka nufi wurin ta, sauran ƴan aikin suna fito da kayayyakin da suka zo dashi. "Kardai mun sha saɓani umman Yaseer" cewar Inna larai domin a tunanin ta sun fito daga gidan ne zasu tafi.

"Wallahi Inna larai, Ina wuni yaya zafi" 

Miƙawa mai keke naira dubu tayi bayan sun gama cire kayan ya miƙo mata canjin ɗari biyu "Lafiya alhamdulillah, yaya mazaje na?"

Rage tsayi kaɗan Yaseer yayi ya gaidata ta amsa da "mai gida Irin wannan swagger haka! inafa jiran cefane" sai ya murmusa tare da sosa ƙeya a kunyace.

"Toh ku shiga wannan napep ɗin ya maida ku mana, kinga sauƙi yazo muku ba sai kun take ƙarshen titin nan da ba'a samun abun hawa cikin sauƙi ba"

Ta luma hannu cikin jakarta ta ciro wani  ɗari biyun ta haɗa da canjin hannun ta sannan ta danƙa wa Yaseer tana cewa "toh gashi na sayi wankar nan don yayi min"

Saurin jan baya yayi yana ƙoƙarin kwace hannun shi amma ba ƙaramin ruƙo tayi mishi ba don tasan halin shi sarai.
"Ki barshi kawai Inna don Allah" yace kaman zai saka ihu.

"Naƙi na barin, salon gobe ka kunce auren tunda kayi wanka naƙi yabawa?" Ta dunƙula masa kuɗin a hannu kafin ta sake shi sai ya shiga mata godiya. 

Kwatance tayi ma mai adaidaitan na unguwan da zasu je, kana  tayi musu ciniki. Saudat kuwa har ta shige ciki ganin Kamal ya tunkaro su, ta riga ta saka ma ranta ba zata shiga gidan nan ba kada ma ya ɓata lokacin shi, don haka tace ma su Yaseer suyi sauri su shiga su tafi.

"Inna Larai ba'a barmu mun shiga ba fah" cewar Suhail ganin da gaske komawa gida zasu yi.

Kallon Saudat a kaikaice Inna larai tayi don tabbatar da zancen Suhail, "wai haka Umman Yaseer?" 

"Babu komai wallahi Inna" shine abinda bakinta yace amma hannun ta duka ya kaiwa Suhail saidai ya riga ya gudu ya ɓoye a bayan Yaseer.

"Toh me yasa?!" Ta tambaya a fusace.

Shiru Saudat tayi ganin kamal ya Iso ta kawar da kai gefe shima kallo ɗaya yayi mata ya ɗauke kai ya gaida Inna Larai sannan ya amsa da. "Kinsan dake an canja masu tsaron gidan shiyasa nake ga wannan bai wayi fuska ta ba" 

Kaɗan ya rage Saudat ta saki tsaki amma ta matse.

Inna Larai ta ƙarasa wurin security "akan mene zaka hana ɗan uwan me gida shiga?" 

Saida ya sake cire madubin idanun shi ya kalli Kamal wannan karon a mamakance, daga rigan gwanjon dake wuyar shi, haɗe da wandon jeans din da duk sunji ruwa sun gama koɗewa gashi basu samu guga ba, har komai nashi baiyi kama da wanda ya haɗa sanayya da masu gidan da suke gadi ba balle haɗin jini.

"Oh wai dama ɗan uwan shin ne da gaske?"

Cike da takaici Inna Larai tace "Haba kai kuwa malam ɗan sanda? Aikin da aka ɗauke ku yi kenan saboda Allah? Idan tsare mutane za'a dinga yi ana musu tambayoyi kamata yayi ana tsare kowa da wanda yazo a mota da wanda yazo a ƙafa babu bambanci, amma wannan ba yi bane ko kaɗan. Wulaƙanta ɗan adam ba abin yi bane wallahi..." 

Taje ta jawo hannun Saudat, mai napep daman ya riga ya dire ta ganin za'a ɓata mishi lokaci. Har ta wuce dasu ciki tana balbali, Kamal ma yayi saurin bin bayan su, Suhail sai tsallen murna yake yi, Yaseer kuwa yunwar cikin shi ne ya dame shi.

Yawan Mutanen da suka tarar a parlourn Hajiya Fauziyya yaso bawa Saudat tsoro har ta fara tunanin ko dai sun ɓata ƙirge ne yaune suna?.
Yawanci baƙin fuska ne sai ta rasa gaida su ne zata yi ko ta share su? Saidai koma ta share sun bata ga ƙyallin Hajiya Fauziyya a parlourn ba.

"Zo muje kiga" cewar Inna larai bayan taje ta ajiye laidar hannun ta a kitchen ta dawo ta riski Saudat tana ta dibi-dibi don haka suka nufi ƙofar bedroom ɗin da hajiya Fauziyya take.

Knocking tayi saida aka ɗauki minti guda kafin kofar ta buɗu Aina'u ta leƙo.
"Ah-ah, Inna Larai kun Iso? Bismillah" ta buɗe mata ƙofar don ta shiga amma ganin su Saudat biye a bayan ta yasa tayi hanzarin riƙe ƙofar.
"Au Inna tare da baƙi kike ne? Da sun jira mu a parlourn ai" 

Kafin Inna Larai tayi Magana daga cikin ɗakin suka ji Muryar Hajiya Fauziyya tana tambayar "Aina'u wanene?" Rufe ƙofar tayi kafin ta juya cikin ladabi tace "Hajiya Saudatu ce, Matar Kamalun Jama'are"

Fuska ta saki sosai cikin jin daɗi tace "Ahh, Umman Yaseer zaki ce ba sai kin wahalar da kanki da wannan dogon bayanin ba. Buɗe musu su shigo" 

Bata da zaɓin da ya wuce tayi yanda aka ce ba tare da musu ba ta buɗe suka shigo sannan tayi saurin sake datse ƙofar kafin sauran ƴan parlourn su fara tuttuɗowa ciki.

"Ni nama yi fushi tunda sai yau uwa take zuwa ganin ƴarta" cewar Hajiya Fauziyya tana Gyara zama a kan gadon tare da sauƙe ƙafafuwan ta ƙasa, ga bakin Reina manne da ƙirjin ta tana aikin ci ba ji ba gani.

Shimfiɗar fuskar da Saudat ta samu ya saka ta sakin fuska itama cikin ɗan jin nauyi tace "kiyi haƙuri Aunty, jikin ne yaƙi daɗi." 
Kallo take ƙarewa makeken bedroom ɗin da take ayyana idan baiyi girman gidan su ba baki ɗaya toh tabbas zai iya fin rabi. 

Ga wani makeken gado da bata taɓa ganin mai kyau da girman shi ba, tsayin saman gadon kuwa ya doshi taɓa ceiling. Ɓangaren Kayan jarirai kuwa ga wardrobe girman shi kamar na wanda za'a kai ɗakin miji saidai anyi shi ne Musamman na jarirai abun sha'awa da cartoon ɗin Masha and the bear a jiki. Ga kuma set na drawers shima, haɗi da gadon jarirai shima pink a gefen gadon uwarta.

Cikin zuciyar Saudat tace "Allah ka azurta mu da mai albarka."

Sai muryar Hajiya Fauziyya ta jiyo Cikin tausayawa tana cewa "Allah sarki, Allah ya raba ku lafiya kema ki samu mai hana ki barci" ta ƙarashe cikin sigar zolaya.

"Bata barin ku kuyi barci ko?" Saudat ta Isa bakin gadon tana leƙa fuskar Reina dake tsotson mama idanun ta a rufe daga ɗan nesa.

Gefen ta Hajiya Fauziyya ta ɗan bubbuga mata alamun ta zauna, Saudat bata yi ƙasa a guiwa ba kuwa ta zauna sannan ta jawo Suhail jikin ta gudun kada yayi musu ɓarna, Yaseer kuma ta barshi a parlour.



*Saliha Ahmad Na'ibi ✨*