Chapter 6
by @khairatup01
ZUCIYAR MUTUM
NA
Ummulkhair S Panisau.
(Khairatup)
Karamci Writers Association.
6.
Maganganu yake ji ƙasa-ƙasa a cikin madafar tsoro ma yaji Wallahi a zatonsa ɓarayi ne amma haka yayi shahada ya daure ya buɗe ƙofar a bazata suka ga haske a kicin ɗin da sauri Mari ta ja zaninta ta rufe jikinta shi kuma Nata'ala ya ari na kare. Da sauri Habib ya saki salati ya juya baya yana jin wani irin tashin hankali na sukarsa.
Mari jikinta ya soma rawa tuni ta saki kukan tashin hankali har ga Allah bata son barin gidan tana jindaɗin gidan matuƙa abinci mai kyau ga albashi ga suttura ana musu saboda Hajiya na son tafta yau gashi Alhaji ya kamata da kan sa.
Da ɓacin rai yace ki kira shi ki same ni a falo yanzu ki saka kayan mutunci kafin ki fito ya sa kai ya fita daga kicin ɗin ransa a dagule a cikin gidansa ake wannan abin.
Aisha tashi saka wani abin ki sauko ƙasa zamu yi maganar yan aikin ki.
Da sauri ta buɗe idanuwanta ta sauko ƙasa "Masoyi meya faru?"
"Ki sauko ke dai."
A gurguje ta sa hijab na Sallah ta sauka ganin Mari da Nata'ala sai da gabanta ya faɗi cikin ranta ko addu'a take yi Allah Ya sa ba wani shashancin suka ƙara yi ba.
Bayan sun zauna ya bisu da kallo ya kalli Aisha.
"Wannan ba shi ne wanda kika bawa aiki ba?"
"Shi ne amma me ya faru wai?"
"Kin san iskancin da suke yi min a gidana?"
"Wane irin iskanci kuma Masoyi."
"Irin wanda kika sani. A kicin na gansu suna aikata alfasha a gidana fa to ki sallamesu bana son sake ganinsu a gidan nan ki sallamesu su tafi."
Hankalin Aisha,Mari da Nata'ala yayi mugun tashi dukaninsu.
Am Habib kayi haƙuri ka yafe musu bazasu kuma ba wannan ma tsautsayi ne.
Ku bashi haƙuri mana ku gaya mai baza ku ƙara ba.
Da sauri suka soma magiya yayi haƙuri ba zasu ƙara ba.
Habib ya kallesu suka kuma guma mai wani taƙaici wai haƙuri Aisha na da kai kuwa?
Aisha in wani abu ya faru a gidan nan da mu za a kuka baki da hankali ne?
Habib me kake cewa ne?
Sarai kin ji ni.
Habib dama suna son junasu aure zasu yi kawai ayi musu auren yafi.
"What are you saying?" Wai Aisha ba kya sanin me za ki faɗa ne kafin kiyi magana uwarta ce ke ko ubansa ce ke da za ki ce na musu aure? to ki saurareni da kyau babu hannuna a ciki na faɗa ki sallame su.
Nata'al yayi tsalam ya shiga maganar.
"Alhaji ni maraya ne kayi min wallici kawai ka aura min Mari Wallahi ina sonta yanzun ma shaiɗan ne ya rinjaye mu amma ba halinmu bane. Alhaji ka duba lamarin nan aikin lada ne lada zaka samu in ka mana auren nan da muyi zina ai gwara muyi sunna."
Habib ma kasa magana yayi a wannan gaɓar. Tsaki ya saki kawai ya shige ya haura sama ya barsu a wurin.
Aisha cike da ɓacin rai ta sa hannu ta zabgawa Mari mari a fuska ta juya ta kuma sakarwa Nata'ala tana huci ta sa yatsanta tana nuna su.
"Wallahi baku isa ku shiga tsakanina da burina ba, ku wawayen ina ne? busuraye kawai ba kwa gajiya da dare ma na kama ku na kuma muku magana amma dake jahilai ne ku masu kunnen ƙashi shi ne kuka kuma kawo kan ku ga shi yanzu Habib ya gan ku. To ai shi kenan ku hada kayanku da safe ku ƙara mai shegu mayu." Ta barsu a gun a fusace.
"Mun shiga uku Nata'ala yaya kenan ina zamu?"
"Kiyi shiru babu abinda zai faru na kashe masa jiki. Ita kuma Hajiya akwai tamu da ita Wallahi muna nan bazata bari mu tafi ba kije kiyi baccinki da munshari."
"Allah Nata'ala?"
"Ni na gaya miki ba zamu tafi ba."
"To madalla muje zuwa."
To fa ana wata ga wata me zai faru ne?
Tana shiga ɗakin ta isa kusa da shi ya zauna jigum kan gadon hankalinsa ya tashi sosai akan abinda ya gani tsoro yake ji kar ayi abin kunya a gidansa yana da kwamasho.
"Bae kana ji kayi haƙuri ka bar maganar nan kayi musu auren Wallahi basa yi..."
"Meye haka ne Aisha baki da hankali ne? me kike nufi da ba zasu sake ba ko basa yi da ba sa yi amma yau na gansu kar ki sake gaya min maganar banza da wofi Aisha sai sun bar min gidana ko wai gidanki ne ban sani ba ko kuma da sa hannunki suke min hakan a gidana?"
Mamaki ya rufe bakin Aisha ta kasa ƙara cewa komai. Bata taɓa ganin wannan fuskar ta Habib ba saboda ya iya saisaita fushinsa.
Komawa tayi ta kwanta tare da ɗaura aniyar ƙara tunkararasa da safe don ba zata bari ayi mata sakiyar da ba ruwa ba.
*
Kwata-kwata Aisha bata iya bacci ba saboda firgici barin Nata'ala daga gidan babban giɓi ne gareta da tsarinta don kuwa shi kaɗai kwakwalwarta ke hasashen samun abokin wasa a tare dashi. Jigum tayi kawai tana tunanin abinda zata yi.
Cikin manyan kaya ya fito farare tas da su dake shi kalarsa kalar ba fara bace sosai sai kayan suka haska shi. Mutum ne mai haiba da son gayu. Sai ƙamshi yake yi kamar wata macen.
Ina zaka je a haka Habib?
Kallon ban gane ba ya bita da shi yana ɗaura agogon akan tsintsiyar hannunsa. Bai kula ta ba kasancewar miskilancin na kansa dama ba ma'abocin magana bane ba sosai yana da kamewa.
Habib fita zaka yi a haka?
Aisha ina ganin kin bawa kan ki amsa. Sai na dawo.
Aa tsaya-tsaya gaskiya kayi kyau da yawa ka sake kaya.
Dariya ma ta bashi. Ya sa hannunsa ya jawota jikinsa ya manna ta da ƙirjinsa yace "Haba Shatu na kin san daga ke ba ƙari ki kwantar da hankalinki ke kin sani kin gama da ruhina da gangar jikina ni ɗin naki ne ke ƙaɗai."
"Ina tsoro Habib ina tsoro in na rasa ka akwai matsla zuciyata da kwakwalwata na gaya mini akwai abinda yake zuwa akwai guguwar da zata zo ta shiga tskanina da kai ta rabamu. Habib in kayi mini kishiya Wallahi mutuwa zanyi." Ta ƙarsa faɗa tana fashewa da kuka.
Rungumeta yayi tsam a ƙirjinsa yace "Shhhhh! ya isa na miki alƙawarin babu wadda zata rabani da soyayyarki kece kaɗai a zuciyata sarauniyar mata.Tauraruwa mai haska Habibullahi Baban Abi Baban Hajiya."
Dariya suka yi a tare. Ya saka hannu yana share mata hawayen sannan ya sumbaci lebanta yace "Na tafi sai na dawo zan shiga asibitin nan na duba marar lafiyar nan in ta ji dama sai in saka a maida ta gida."
"To Allah Ya tsare. Amma ya batun su Mariya?"
Ajiyar zuciya ya sauke ya gyara tsyuwarsa tsahon minti biyu kamar bazai ce komai ba sai kuma ya bata amsa.
"Nayi tunani bazan rabasu da hanyar samun abincinsu ba amma ba zan bari su ƙara kaancewa a wuri ɗaya naga koda na koresu bazasu rabu da juna ba ɓarnar dai bata kau ba. Saboda haka na yanke shawarar anjima bayan san sauko daga massalaci za a ɗaura musu aure tunda duk marayu ne ko?"
Daɗi ya hau kan kaza wani irin sukuni ya saukar mata ta rungume shi sosai tana godiya sai ta bar Habin da mamakin dalilin farincikin Aisha haka sai kace wasu shaƙiƙanta. Wayarsa ta soma ƙara ya ɗauka ya kara a kunnensa ya fice yana magana "Hello Sani ka is..."
Tsalle Aisha tayi ta koma da baya ta faɗan kan gadonta tana hamdala ga Allah.
*
Asibiti.
Orthopedic Hospital.
11:30am.
Ɗakin da suke ya shiga da sallama Iya Talai ce ta amsa masa tana murmushi. Gefensu ya kalla yaga an kawo musu abinci.
Zaunawa yayi kan kujera ya gaida Iyar suka soma rahar su kamar yadda suka saba.
Iya ta farka ko?
Eh na wajena sai dai na lura kamar bata iya magana.
Bata magana kuma Iya?
Gaskiya bata magana sai dai ta bi mutum da ido ko tayi a aikace.
To fa bara na ga likitan naji. Don ni dai in dai ba kunnuwa na ne suka ji min ba daidai ba gaskiya kamar naji muryarta.
To ban sani ba amma ka kira likitan mu ji.
Fita yayi yaje ofishin likitan.
Bayan sun gaisa yake tambayarsa yanayin jikin yarinyar.
Likitan yace naga akwai wasu matsaloli amma ina shawartar ka da ka maida ta asibiti ayi mata gwajin kwakwalwa kamar ta samu matsala.
Innallillahi wa inna illahir rajun likita matsalar kwakwalwa daga accident a ƙafa?
Aa ban ce ba ai ba wani ciwo taji ba ai ka san abinda ake kira tashin hankali (trauma) ko?
Eh likita.
To shi ta samu. Ka sauya mata asibiti ka je kuyi mata gwajin za a gano kan matsalar.
Haka suka yi sallama ya bashi nambar wani likitan ya kuma basu sallama don babu matsala an gyara ƙafar.
Bayan sun shiga mota ya rasa inda zai saka ransa yaji daɗi shi bai san yarinya bare asalinta ba to ina ma zai kai ta a kula da ita? Sitiyari ɗin motar ya buga da ƙarfi har sai da Iya ta tambaye shi ko lafiya?
Iya zan ajiye ki a gida don Allah kar ki gaywa Hajiya komai zan mata bayani da kaina. Zan tafi da ita gidana saboda zamu dinga zuwa ganin likita bana son hankalin Hajiya ko na Abi ya tashi daman Abi ba daɗi yake ji ba.
To Baba babu komai Allah Ya bata lafiya ya sa kaffara.
Ameen.
*
Wajan ƙarfe uku ya isa gida da kansa ya buɗe mata ƙofa ta fito.
Sai dai bin ko ina ta soma yi da kallo a cikin ranta kuwa tana mamakin girman gidan da tsaruwarsa lallai akwai gidaje a birni duk da gidansu gidan gandu ne kuma babba ne bai kai wanan tsaruwa da kyau ba. Gidan ya burgeta sai taga kamar a aljanar duniya take kawai.
"Muje" taji ya faɗa .
Bin sa take a baya har suka shiga ainihin cikin gidan a nan ne Uwani ta gane ashe wajen ba komai bane ba nan abin yake. Turƙashi wannan abu ya burgeta ainun daman can da ƙauyancinta sai ta ƙara zama ƴar ƙauyen ta dinga shafa kujera tana jin laushi sai ta saki murmushi.
Daga sama taji wata muryar daban mai daɗi da aji amma akwai alamar tuhuma da faɗa a cikinta.
"Habib wacce ce wannan?"
"Ita ce marar lafiyar zan sauya mata asibiti ne."
"Amma a rasa mai riƙota sai kai?"
"Baki ga larura bace ba wa zan saka?"
"Ga maigadi ,ga Iliya ga Nata'ala ga Mari duk basu isa ka saka su ba sai ka taɓa wannan ƙazamar?"
"Nata'ala ! Nata'ala ! " Sunan da ta dinga nanatawa kenan a saman lebbanta ta kasa yin magana shin Nata'ala mijinta ake nufi ko wani ne? kai me zai kawo Nata'ala nan gidan gaskiya ba shi bane ba wani ne daban.
"To ban yi niya ba ki saka a buɗe wancan ɗakin na ƙasa ta zauna a ciki"
"Ta zauna kuma? a ina wai? wasa kake yi Habib wasa ne wannan."
"Dama ni abokin wasan ki ne? ko ki saka ko na saka."
Shiru tayi cike da ɓacin rai ta gama ƙuluwa gaskiya ba zata zauna da wannan yarinyar ƙazama ba mai kama da bararoji ba.
Da kansa ya zaunar da ita akan kujera one seater.Ya isa inda Mariya ke kwantawa ya ƙwanƙwasa mata ƙofa.
Da sauri ta fito don daman tana jikin ƙofar tana gulma. "Yallaɓai gani."
"Ki share wancan ɗakin ki gyara ga baƙuwa nan a koya mata komai a nuna mata komai kinga bata da lafiya ki kula sosai har sai ta warke ni na baki wannan umarnin.
An gama Yallaɓai zan kula in sha Allah. Allah Ya ƙara girma da arziƙzi.
"Amin"ya faɗa.
Cikin rabin awa ta kammala komai ta shigar da Uwani. Ta nuna mata banɗaki tace ta shiga. Uwani ta kalli ƙafarta ta kalli Mariya.
Mariya da mamaki take kallon Uwani duk da gabanta sai faɗuwa yake yi in ta kalleta da manyan idanuwanta ƙwarjini tayi mata gashi daman Alhaji ya bata amana kuma so take ta wanke kanta daga wurinshi kan laifin jiya da ya kamata da shi.
"Ba kya magana ne?"
Uwani ta gyaɗa mata kai kawai idanuwanta sun ciciko da ƙwalla.
'Allah sarki." Mariya ta faɗa cike da tausayi.
Komai sai da ta taya ta sannan ta fita ta kawo mata abinci taci.
Bayan la'asar aka ɗaura auren Mariya da Nata'ala.
A falon duk suka zauna harda Habib wanda yake yi musu nasiha da son barka na kasancewa ma'aurata.
Habib yaja kunnensu kuma ya umarci Mariya da ta koma can Bq inda Nata'ala yake in yaso ta dinga shigowa tana aikinta.
Nata'ala baki a washe yace "Na gode Alhaji Allah Ya jiƙan magabata Ya ƙara buɗi mun gode sosai da wanan abu da kayi mana bazamu taɓa mantawa da kai ba duniya da lahira Alhaji."
Gaban Uwani dai da ya faɗi jin murya sak ta Nata'ala ga sunan ma iri ɗaya. Ba dai kunnuwanta ne suke yi mata gizo ba suke jiyo mata ba daidai ba amma dai kai.... wannan muryar Nata'ala ce. Aure ? aure yayi a nan ya manta da ita a can ? hannunta a kan ƙirjinta gashi babu damar ta fita da kanta saboda ƙafarta wayyo Allah duniya gashi ta kasa yin magana tun bayan abinda ya faru da ita a can Chiroro tsakaninta da Sageer to wai me ke shirin faruwa da ita ne? wata sabuwar jarrabawar ce ta tunkarota? Bata amsa bata kuma da bai bata amsa kawai ta bar hawayenta suka ci gaba da yi mata ambaliya a saman fuskarta.