ZUCIYAR MUTUM

Chapter 8

by @khairatup01

ZUCIYAR MUTUM

NA

Ummulkhair S Panisau.
(Khairatup).

Karamci Writers Association.

Vote@Wattpad khairi_Muhd

No.8

Sai da Aisha ta tabbatar da Habib baya falon ta shigar da Nata'ala ɗakin Uwani.

Uwani tana kwance lamo sai kuka take yi ta rasa yaya zata yi da rayuwarta taji daɗi babu uwa babu uba bata san kowa nata ba mijin da take alfahari da samun shi gashi nan ya ci amanarta yazo birni ya waye yayi aure ya manta da batunta ma. Jin an buɗe ƙofar ɗakin yasa ta juya don ganin waye.

Aisha ce ta shigo a bayanta kuma Nata'ala ne biye da ita. 

Miƙewa tayi tsam ta gyara zamanta ta ɗau ɗankwalinta ta ɗaura.

Saida gaban Aisha ya faɗi da taga yarinyar kuma ta rasa dalilin hakan. 

Kallo kallo kawai ake yi tsakanin Uwani da Nata'ala yana mata kallon kiyi haƙuri tana yi masa kallon tuhuma.

Aisha ta sa mukulli ta ƙulle ƙofar ta ja kujera ta zauna. Shi kuma Nata'ala ya isa gaban Uwani ya zauna a gefenta yana son kama hannunta.

Matsar da hannun tayi ta juyar da kanta ta saka ɗan yatsanta ta ɗauke ƙwallar da ta zubo mata.

Aisha ta gaji da diramar da ake yi tayi gyaran murya ta fara magana.
"Na san ba kya iya buɗe baki kiyi magana amma na san kina jina kuma kina fahimta. Ba dogon turanci zanyi miki ba magana ce zamu yi da ke ta taimakon juna ma'ana zan taimake ki kema za ki taimakeni amma taimakon zai kasance a cikin sirri za ayi shi. Wannan mijinki ne na sani amma a halin yanzu zai sake ki saboda ni nafi buƙatar ki a sama da shi a taƙaice ma nayi fansar ki ta hanyar aura masa wata matar Mariya mai aikina. Ni kuma za ki yi mini wani aiki babu wahala aikin kawai Haihuwa za ki yi ki bani ɗan ke kuma zan biyaki da ƙuɗaɗɗe masu daraja ta matuƙar nauyi wanda za ki mora ki kuma bar wa ƴa'ƴa da jikokinki."

Wani irin gingirin-gin taji kanta yayi mata wai "Nata'ala ya sake ta kuma zata haifa mata ɗa ta bar mata tayaya kenan?" Katse mata tunani Aisha tayi ta hanyar ci gaba da yin magana kaitsaye.

"Abun babu wahala zamu je gun likita yayi miki gwaji in kin haye za ayi miki IVF (Haɗin ƙwayar hallita). Kin san yanzu kimiya yazo da abubuwa da dama ciki harda wannan haɗa ƙwayar hallita don samar da ɗa. Ina buƙatar ɗan ne kuma ba zan iya haihuwa ba in nayi sanya za ayi wa mijina aure ni kuma na tsani kishiya bana ƙaunarta ko kaɗan kinga kuwa maganar ma na zauna da ita haihu bai taso ba ni da Habib shekarar mu goma da aure kuma dani yayi arziƙin kinga kuwa ni kaɗai ce na cancanci na daddali arziƙinsa.Na biya mijinki kuma ya siyu ."

Hawaye basu daina yi mata fareti a bisa fuska ba ji take yi daman ta mutu ta huta. Wannan wacce iriyar ƙaddara ce ke bibiyarta. Ina zata je? Minna bata da kowa , chiroro Sageer da Inno bazasu barta ba Nata'alan da take tunƙaho da shi ya sake ta ya yaudareta yaci amanarta to in ta warke ta bar nan gidan ina zata je?.......

"Uwani ki yafe mini babu yadda zan yi ne, ke kin sani bani da arziƙi bani da hanyar samun su dole na zaɓi arziƙi a sama da ke ko dan rayuwarmu tayi kyau ta daidaita. Ki yarda da abinda take so ki saka hannu ki haifa musu ɗa in yaso sai mu maida aurenmu daga baya."

"So take ta buɗe baki ta zage shi wai su maida aurensu... wani abu mai ɗaci ya ziyarci maƙogwaronta da ƙyar ta haɗiyi yawu mai ɗaci da zafi a maƙoshi. Da zata iya magana da tace bata yarda ba. Ta tuna da kalaman Sageer akan Nata'ala bai yi ƙarya ba tabbas Nata'ala jininsu ɗaya da Sageer jinin Inno suke babu sannaya a rayuwarsu. Ta yarda gwara ta yardan ta samu mafaka a rayuwarta kafin ta samu yadda zata nemo ahalinta ko ta samu masu ƙaunarta."

"Kin amince?"

Kai ta gyaɗa mata a hankali haɗe da lumshe idanuwanta sauran hawayen suka ƙarasa zubo mata.

"Ma sha Allah! Bismillah Nata'ala zaka iya sakinta yanzu."

Nata'ala yace "Na sake ki Uwani saki ɗaya."

Gabanta sai da ya faɗi ta yi masa wani irin kallo ,tuni taji ya fita daga ranta taji babu abinda ta tsana sama da Nata'ala bata maida martani amma tabbas akwai ranar da zata ba shi amsa daidai da tambayarsa. Ɗauke kai tayi daga kallonsa.

Dafin kallon da tayi masa har tsakar kansa yaji kallon kuma yaji bai kyauta mata ba amma ya zai yi yafi son kuɗin fiye da ita.

Haka suka tashi suka tafi suka barta da ƙunar rai. Kuka ta fashe da shi gashi babu murya babu bangon da zata kwanta a kai babu wanda zaya gayawa damuwarta abu goma da ashirin. "Allah na gode maka na amshi wannan jarrabawar ma Allah ka dube ni ka shiga cikin lamurana Allah ka kawo mini ɗauki ka saka mini abinda wannan bawa naka yayi mini." Cikin ranta take ta yi masa addu'a a haka bacci ya sace ta ba don tana son yi ba.

*

"Erm! Dear ina son dama...uhm.muyi magana yanzu."

Juyowa yayi yana fuskantar ta sai dai kafin ta ƙara magana ya rigata "Aisha kin je gidan Adda kuwa?"

Ta soma soshe-soshen kai ta ɗan juyar masa da ƙeya baya sannan tace "Gobe nake shirin naje nayi odern kayan barka ne basu iso ba sai gobe."

"Hmm! Ina son ki gyara alaƙarki da ƴan'uwana bana son wannan wariyar da kike yi Aisha cikinku fa babu wanda zan ture dukaninku nawa ne."

"In sha Allah ai dama ba laifina bane sune suke nuna min wariya basa sona saboda kawai bana haihuwa."

"Aa ba wai basa son ki ba na halinki ne basa so."

Shiru tayi bata kuma yin magana ba. Sai da taga zai kwanta ta kuma lallabawa kamar zata koma cikin shi ta ce "Magana nake so fa muyi mai muhimmanci."

"Ina jin ki."

"Na samo mana mafita game da haihuwa Hubby an easy way."

"Tayaya?" Ya tambayeta kaitsaye.

"Uhm ta hanyar IVF".

"Aisha meye kuma Ivf?"

"Haɗa ƙwayar hallita."

"Ta wa da ta wa kenan?"

"Misali da kai da wata ayi gwaji a ga ko zata iya concieving babyn sai a saka mata...."

"Aisha na jima ina tunanin ko kin samu matsala a kwakwala ban yarda ba amma yau na yarda kije ki kwanta zamu ganin likita da safe this is not you."

Baki Aisha ta hangame ganin ya juya mata baya zai kwanta.Da zafin nama ta juyo da shi ta soma magana cikin kuka da kissa.

"Habib Wallahi na lura baka sona baka ƙaunata so kake yi kaga bayana so kake yi kayi auren nan dama don kaga bani da yadda zan yi nafi sonka na fi kishin ka Wallahi ko ka yarda Habib ko na daina ci da sha a gidan nan har sai na mutu kowa ma ya huta."

Ta daina ba shi mamaki tsoro ma ta fara ba shi. "Aisha! Aisha!" Sai ma ya kasa ƙarasa maganar saboda ba shi da abin cewa gabaɗaya ta soma ba shi tsoro ya kasa gane mata dole ya kwanta ya barta tana ta kuka har bacci ya ɗauke shi don bai san ma yadda aka yi ta kwanta ba.

Taga tsara yadda zata yaudare shi kuma dole ya bi abinda take so. Ko baya so sai Uwani ta zame musu sourrogate mum. Dole ta mallaki nata ɗan ko ƴar ko ta halin ƙaƙa. Juyawa ta kalle shi ji take kamar ta mangare masa kai.Tsaki ja ta kwanta.

*

Washegari ya riga ta tashi daga bacci ya shirya tsab ya saka kaya kampani za shi akwai aiki sosai za a sauke sabon kaya kuma dole ya kasance a wurin.

Bai bi ta kan Aisha ba don ta ɓata masa rai yayi tafiyarsa. Ita ma tana jin duk abinda yake yi kawai ta kyale shi ne saboda akwai gagarumin abinda ta shirya don kuwa babu gudu babu ja da baya a lamarin da ta shirya.

Aisha ta gama tsara abinda zata yi ta shirya saida ta daidaici lokacin dawowar Habib ta zauna a falo hannunta riƙe da wata ƴar ƙaramar leda fara. Sai jijjiga ƙafafuwanta take yi tana jiran shigowar Habib. Cikin ikon Allah bakwai daidai ya dawo bayan ya gama gaisawa da ma'aikatansa ya shigo ciki da sallama. A daƙile ta amsa babu rahama akan fuskarta. 

Ya so ya wuce ta amma sai ya kasa. Ya sauke ajiyar zuciya ya tsugunna a gabanta "Shatu, ba ki haƙura ba? ina son ki gane haihuwa lokaci ce ta Allah ce na san zamu haifa amma bata wannan hanyar ba. Kina gani wadda zata yarda ayi wannan da ita an mata adalci ne? ki fawallawa Allah khairan in sha Allahu Shatu ta ki basar don Allah bana son na gan ki a haka kefa tauraruwata ce mai haska mini ƙalbina ke zara ce daban a cikin mata,ke bugun zuciyata ce matsayinki daban yake bayan Abi da Hajiya kin sa kece ta uku a jeran waɗanda nake mutuwar so da ƙauna zan iya yin komai a kan ki."

"Ƙarya kake yi Habib baka sona ƙarya kake yi. Daɗin baki ne kawai wanda ka saba min ba sona kake yi ba saboda haka yau cikin biyu za ayi ɗaya ko ka yarda da buƙatata ko na ɗaukar wa kaina matakin da ya dace don da na zuba ido naga ka auri wata har ka tara da ita kuma ta haifa maka ƴa'ƴa Habib gwara na mutu ƙasa ta rufe min idona."

"Me kike nufi Aisha? Me kike shirin aikatawa?"

"Masalaha na nema mana ka zaɓa ko ni ko taurin kan ka?"

Ya rasa ma mai zai ce mamaki da tsoro yake ji yana ji a jikinsa Aisha na shirin aikata wani babban abu wanda zai yi kuka ita ma zata yi kuka a gaba.

"Habib ka gaya min me ka zaɓa?"

"Aisha zauna muyi magana zamu samu mafita...."

Tuni ta ciro wata ƴar ƙaramar kwalba ta buɗe tana baya tana magana "Shi kenan Habib ina son ka amma ba zan iya raba ka da wata ƴa mace a duniya ba. Habib kar ka manta dani kayi min takwara Habib." Tuni ta kafa kwalbar nan ta kwankwaɗe abin ciki cikin abinda bai fi sakan guda ba ta soma amayar da kumfa daga bakinta tayi luuu ta faɗa da baya hannu a makogwaro tana kakari. 

Kan Habib ya ƙulle ya ruɗe ya rikici ya gigice hularsa ya cire yayi jifa da ita . Ya isa ya ɗago kanta yana jijjiga ta "Aisha! Aisha! Tashi Aisha! Innallillahi wa inna illahir raju'un Aishaaaaaaa...." Saɓarta yayi a kafaɗarsa yayi waje da ita a gigice a baya ya saka ta ya taka kan mota yayi waje. Sauran masu aiki kowa yayi zuru-zuru an rasa me ke faruwa.

*

Asibiti.

Nan da nan aka ƙarbe ta aka soma bata taimakon gaggawa. Jikin Habib har wani rawa yake yi idanuwansa sun yi jajir saboda tashin hankali. Cikin ransa kuwa jinjina ɗanyen kai irin na Aisha yake da gaske zata iya kashe kanta aka kishi? Innallillahi wa inna illahir rajun ta kasa barin bakinsa ita kawai yake ta ambata yana cike da tashin hankali ya kasa tsaye ya kasa zaune so yake kawai likitan ya fito yace masa Aisha ta warke babu wata matsala koma meye zai yi mata.

*

BAYAN WASU AWWANI.

Habin zaune kan kujera daf da Aisha yana jin bugun numfashinta yadda yake fita da sauri da sauri lokaci guda ta zabge ta yi rama. A hankali ya kama hannunta ya soma magana "Aisha am sorry ,zanyi duk abinda kike so amma don Allah ki tashi kiyi mini magana ko faɗa ne kiyi min ni nafi son hakan amma don Allah ki tashi kiyi min magana."

A hankali ta buɗe idanuwanta dishi-dishi take gani amma haka ta buɗe idanuwanta tana kallon shi oxygen ɗin ta zame daga kan fuskarta tace "Da gaske Habib zaka yarda a haɗa ƙwayar hallitar ka da ta wata?"

"Na yarda Aisha na yarda amma don Allah kar ki ƙara yin irin wannan abin bana so bana so kin tsoratar dani. Kin san girman laifin abinda kika aikata kuwa? ƙoƙarin kashe kan ki fa kika yi haramun ne yin hakan. Aisha kar ki kuma yi min haka."

Da murya irin ta marasa lafiya tace "Kayi alƙawari?"

"Na ɗauka."

Luuuu idanuwanta suka rufe ta koma bacci dama allurar bata saketa ba.

Kallonta kawai ya dinga yi yana mamakin yadda Aisha zata iya yiwa kanta haka don ta saka shi yayi abinda take so lallai a gaida mata tabbas dole a ji tsoron mata da sharrinsu shi kam yau yaga bala da idanuwansa ra'ayil ayn."

Bayan kwana biyu suka koma gida ta warware.Basu kuma waccar maganar ba saida taji dama-dama babu wanda ya san tayi ciwo har ta kwanta a asibiti bai faɗawa kowa ba haka ita ma daman ba don kowa tayi ba don shi uban gayyar tayi kuma kwalliya ta biya kuɗin sabulu.

Sai da taga ta kwana biyu sannan ta same shi a ɗaki tace "Yanzu Hamma ka shirya mu samu muje asibitin ayi muku gwaji?"

"Aisha ai kece mai gayya mai aiki in kin shirya na shirya. Yadda kike so haka za ayi ni kin gama tsorata ni ne."

Murmushi tayi tace "Da wuri haka? Ai Wallahi Allah Hamma da baka yarda ba sai ka dinga ganin bala'i kala-kala don daman na saka a raina in na tsira a wannan ina da plan B. "

Idanuwansa ya ƙara wa girma ya gyara zamansa haɗe da saka hannunsa a kan wuyan ta "Aisha anya kuwa kin warke? ko dai kwanyarki ta samu matsala? Mu koma asibiti ko?"

Hararasa tayi tace "Ras nake kuma na fika ma tunani."

"Kai ina ƙarya kike yi Wallahi. Can dai ki nemo tunanin ki. "

Dariya tayi sosai ta tashi ta zauna akan ƙafar shi ta rungume shi ta sumbaci goshinsa tace "Ina son ka Hubbyna Wallahi kai kaɗai ne a birnin zuciyata son da nake yi maka bashi da adadi kuma bashi da geji zuciyata azalzala take yi in ka ambaci aure ko naga wata na kallon ka, Hamma Wallahi a kan ka zan iya kisa kuma in kashe kaina duk saboda kai. Da in raba ka da wata gwara na ƙone ku na kuma ƙone kaina kowa ma ya huta. Son da nake yi maka babu ƙarya a ciki ko algus. Hamma nima ina son naga mun haifi ƴa'ƴa wanda zasu kira ka da Daddy ni kuma Mummy. Kuma da yardar Allah burinmu zai cika. Da zan iya Habib da zan iya da na gaya maka yadda na ke ji sai dai kash zuciyar mutum birninsa."

A wannan gaɓar da gaske Habib Aisha tsoro take ba shi ya kasa cewa komai yana hango obsession a cikin idanuwanta wanda zai zame mata matsala a zamantakewarsu. Dole ƙanwar naƙi haka ya rungumeta yana shafa bayanta alamar rarrashi." 

"Aisha wacce ce zata iya wannan sadaukarwar?"

"Uwanin Chiroro."

"Wacce ce haka?"

"Mara lafiyarka." 

"What?"

"Yes ,ka ji daidai ita wannan yarinyar da take cikin gidana."

"Aisha....." 

"Hamma am serious ita kuma ta yarda. Ai yafi safe babu wanda ya santa bata da kowa zata zauna damu zamu kula da ita har ta sauka lafiya mu sallameta ta bamu ɗanmu ta ƙara mai mu kuma mu rufe bakin ƴan takura."

"Astagafirullah! Aisha yarinya ce ƙarama ba zata iya ba daga ganinta bata kai 18 ba ma ke ko 17 na san bata wuce ba Aisha ki nemo wata".

"Aa Hamma ita ƙaɗai ce zata iya , bata da wayo ba zata tona mana asiri ba gashi daman bata magana kai ko da tana magana zata mara mana baya saboda irin kuɗin da zamu bata har ta gama rayuwarta.Kaga mun tallafeta mu ma mun samu namu sanyin idaniyar."

"Aisha don Allah..."

"Kaga Habib muje kaji daga bakinta."

Wash zan ɗan ajiye alƙalamina don na huta mu haɗu a shafi na gaba."