ZUCIYAR MUTUM

chapter 12

by @khairatup01

ZUCIYAR MUTUM

NA

Ummulkhair S Panisau.
(khairatup).

Karamci Writers Association.

Vote @wattpad khairi_mud.



                   12

Da misalin ƙarfe goma na dare Uwani ta fito don samun ruwan ɗumi. A lokacin Aisha na zauna ita kaɗai a falo tana kallon tangamemen hoton Habib da na jariran da aka ɗora a bango. Gani take yi Uwani na ɗauke da wani abu da ita ta rasa.Wannan karon a haushi kawai take ji ba tsoro ne. Tsoron rasa jariran da mijinta. 

Uwani ta wuce ta bata snni ba har ta je ta dafa ruwan ta dawo bata lura da ita ba. Sai taji ta kasa tafiya ko babu komai damuwar Aisha na da alaƙa da ita.  Sai dai kafin tayi magana ko taje inda take taji shigowar Habib sai tayi sauri ta laɓe a gefe.

"Yaya na gan ki a haka Shatu?" 

"Habib zauna ina son muyi magana."

Samun wurin yayi ya zauna yana fuskantar ta. Bai gamsu da yanayin da ya ganta ba hakan ya saka ya shafa fuskarta ya riƙo hannunta ɗaya cikin nasa.

"Ina jinki rigimatu."

Ta ɗan harare shi kamar yadda ta saba in ya kira ta da wannan sunan.

Kawai Uwani ji tayi tana son ta ji me zasu tattauna babu mamaki hakan ya shafe ta da rayuwarta.

"Habib ya kamata a gyara al'amarin nan da wuri" ta faɗa da muryar da ke cike da natsuwa amma da wani irin sauti na yanke hukunci.

Habib yayi mata ƙuri da ido ya na sauraronta har ta kai aya. "Me kike nufi?"

"Ban yarda da yarinyar nan ba. Akwai mugunta da ƙeta a tare da ita."

Koma meye ke kika zaɓe ta. Amma me yasa kika faɗi haka?"

"Na lura so take ta ɗaure zuciyar yaran nan gareta kawai. Ki kan ka na lura ka fara sonta yadda kake bin ta da kallo . Idan bamu ɗauki mataki tun yanzu ba ,wannan yaran ba zai gane wace asalin mahaifiyarsa ba."

Habib yayi shiru na ɗan lokaci kafin ya samu zarafin yin magana ta riga shi. "Na san me zaka ce cewa zaka yi shayarwa to sai dai  nemi wata uwar ta shayar da shi. Ka bar Uwani ta tafi ka ƙara mata kuɗi,amma ina son ta bar gidan nan na har abada." 

Dafe ƙirji Uwani tayi. Cike da fargaba bata son a rabata da yaran nan tana son su.

"Aisha wata nawa ya rage su cika wattani shidda? kiyi haƙuri ki bar ta.Ni ba sonta nake ba ke kin sani ke nake so ke kawai. Kin sani ba ajina bace ina tausayinta ne kawai. Daga wannan bani da wani haɗi da ita. Ki daina saka wa ranki zan yaudara ki na aureta shin tayi miki kama da kalata? Bata da ilimi,bata da wayewa ,bata magana ai kin ga babu haɗi. Ina son ki kwantar da hankalinki."

Jin haka sai Aisha taji sanyi a ranta ta kuma yarda ba son Uwani yake ba. Nan ya samu ya janyota jikinsa yana rarrashinta. Ya faɗi hakan ne don Uwani ta samu sauƙi daga Aisha.

Uwani tuni hawaye suka soma yi mata fareti a saman fuska. Ashe ita kaɗai ke haukanta baya sonta (uh'uhm to fa Uwani daman yace yana sonki ne?)

Salalaɓawa tayi ta hau sama tana kuka. A daren ta yankewa kanta hukuncin abinda zata yi ya zame musu masalaha dukaninsu.

Yaran ta ɗauka a karo na ƙarshe ta kwantar dasu kan kafafuwanta tana shafa kansu.A hankali ta sauke numfashi, idonta cike da ƙwalla.Da ƙaramar murya mai nauyin gaske tace "Zan tafi amma da soyayyarku a cikin raina. Ba zan manta daku ba...." 

Yaran suka kalleta kamar suna jin ta suka kama yatsanta ɗaya ya kama dama ɗayar ta kama hagu. Sakin yatsun suka yi suka kama haɓar rigarta gam kawai sai zuciyarta ta tsinke ta fashe da kuka. Ganin uwarsu tana kuka suma suka sa kukan gabaɗaya suka dinga kuka babu mai rarashin wani abin gwanin ban tausayi.

Aisha ta lura in tayi wa Uwani barazana zata saduda ta gudu saboda ta gane lagonta na son yaran da take yi haka ya saka ta yanke shawarar bi mata ta bayan gida. 

Ƙoƙarin shaƙo wuyan yaran take yi yayin da Uwani ke son hanata sai wafce hannun Aisha take amma bata da ƙarfi.

"In na gama dasu sai na dawo kan ki kuma na saka a birne min ku a neme ku a rasa sai dai ku zama tarihi daman babu wanda ya san ki sai shi uban gayar shi ma zan gaya masa kin gudu dasu ayi ta nemanki amma ko sahunki ba za a gani ba. 

Yara sai kuka suke yi Uwani nata kuka tana son ƙwatar yaran bakinta sai kai-kawo yake na son furta wani abu a wahale ta ƙara buɗe bakinta tace "Zan tafi don Allah ki rabu dasu kar ki musu komai zan tafi ina son su gudan jinina ne su...."

Ba Aisha ba kawai Uwanin ma da kanta sai da ta tsaya cak tana tunanin da gaske magana tayi? da gaske bakinta ya buɗe muryarta ta dawo? 

Aisha kuwa ta ƙaɗu da ta ji muryar Uwani. Murya mai sanyi da daɗi. "Dama kina magana duk tsahon wannan lokacin raina mana hankali kike yi?"

Da sauri ta girgiza kai ta share hawayenta tace "Aa yanzu ne, Alhamdullilahi,Allah na gode maka. Aunty Aisha kar kiyi musu komai zan tafi Wallahi. Ki tuna wahalar da kika sha kafin ki same su? Ni bana son mijinki ki daina ganin ko soyayya muke bana son shi. Zan tafi amma kiyi min alƙawarin kulawa dasu."

"Baki isa ki gaya mini abinda zanyi ba. Nima ai ina son nasu amma na fi son mijina dasu. Na yarda za ki tafi amma ki sani bana son a kai safiya baki tafi ba. Bana so na wayi gari na gan ki a cikin gidan nan. Ina son ki bar nan garin gabaɗaya ki tafi can wata duniyar ko ki koma garinku. Wallahi Uwani in na farka na ganki a gidan nan guba kawai zan zuba muku duk ku mutu kowa ya huta."

Uwani ta zaro idanuwanta waje cike da tashin hankali tunani take anya kuwa Aishar na da hankali kuwa? anya ta san me take yi kuwa? Babu dole zata tafi amma tana fatan wata rana Allah Ya haɗata da yaranta.

Bayan nan Aisha ta fice daga ɗakin. Ta bar Uwani cikin zullumi.

*
*

Tsakar dare ta buɗe ƙofar bayan ta gama haɗa kayanta tsaf. Misalin ƙarfe ɗaya ta ɗauki ledar kayanta ta kai ƙasa. 

Ta koma ta ɗauki yaran ta kai su falo haka ta ajiyesu ta shafa kumatunsu tayi ta fice tana kuka.

A hankali ta buɗe ƙaramar ƙofar ta fice tana yiwa gidan kallon ƙarshe. Ba zama ta gane unguwar ba saboda ba fita take ba kuma bata taɓa jin an ambaci sunan unguwar ba. Hawayen da suka zubo mata ta ɗauke ta juya a ranta tace "Sai wata rana."

Da ƙafa ta tafi tayi nisan tafiya kafin ta isa titi. Ga titin wayam a tsorace take yadda titin yayi tsit ko kukan karnuka babu. Jiki na ƙyarma ta tsaya a jikin wani symbol ta coge tana kalle-kallen manyan ginanuka. 

Ina zata?daga ina zata fara? wa zai tallafi rayuwarta? kawai sai ta saki kayan ƙasa ta tsugunna ta haɗe kai da guiwa ta saki kuka. 

Haka ta raƙube a jikin bishiya ta shimfiɗa zaninta ta kwanta a kai tana kallon taurari ta yi shiru. A tunaninta babu wata mai irin ƙaddararta da damuwarta a faɗin duniyar nan. Bata da iyaye, bata da ƙanne,bata da kawunai da gwagwanai bata da miji ,ba ɗa daga ita sai halinta ita kuwa wacce iriyar baƙinciki gare ta a duniya waye zai sota? waye zai ja ta a jiki da zuciya ɗaya?.... Haka tayi ta saƙe-saƙe har ɓarawon ya ɗauketa.

*

Washegari.
6:00am.

Dit,dit,dit.karaɗin motoci da hayaniyar tsirarun mutane ke tashi. Almajirai sun soma yin bara. Yayin da wasu ke takawa wasu kuma na wucewa wasu suna cikin mota. Gari bai gama washewa ba akwai lullumi a yanayin. Da alamu wasu yan makaranta ne ake hada-hadar kai su makaranta wasu kuma kawai gasu nan dai kowa dai sabgar gabasa yake yi. 

A hankali na gyara zamana na dinga bin ko ina da kallo na ɗaura ɗankwali a kaina. Daga nesa kaɗan na hango mai tuyar ƙosai. Aiko na tashi don yunwa nake ji. 

Na ɗauki ledar kayana na kuma goya ƙaramar jakar ƙuɗin a bayana. Ina ta kaf-kaf da jakata. 

  Me ƙosai na ƙoƙarin haɗa wutar tuya ɗayar kuma ta dama koko. Na gaishe ta ta amsa ba yabo ba fallasa ƙilla ta raina yanayina ne. Ban damu ba na daina damuwa burina kawai na samu na saka wani abin a cikina.

"Ƙosai nake so da koko."

Ta juyo ta ƙaren kallo sama da ƙasa sai kuma ta zumɓuri baki. "Amma dai kina da kuɗi ko? don ba na bada bashi kuma ba na bada sadaka."

"Da kuɗi na Hajiya ."

Ta zauna tace "Bara na soya sai a baki yanzu na fito sai kin jira."

Ina nan zaune tana ta kallon yadda take al'amuranta. Ana ta zuwa ana siya har ta dama kokon nan. Nima na sai ƙosan ɗari biyu kokon naira ɗari yunwa nake ji kun san dai cikin mai shayarwa. Haka na tashi kan abincin nan na biyata na kuma yi mata sallama. Ban san fa inda zani ba bafa ni da kowa a garin Kano shi ma Kanon yawan ambaton ta da Hamma ya dinga yi ya saa na haddace ta. 

Sai da nayi nisan tafiya naji duk na gaji fitsari nake ji ga ishi ruwa.

A gefe na hangi wani bawan Allah. Na isa kusa da shi nace "Don Allah bawan Allah ishi ruwa nake ji ina zan samu?"

Ya kalle ni kafin yace "ki tsallaka can sai ki siya a wancan shagon."

"To in zan yi fitsari fa?"

"Wai baƙuwa ce ke?"

"Eh ba san kowa ba ina ce tasha?"

Ya jima yana kallona ko tunanin me yake yi oho. Ya ɗan yi jim yace min "Zan taimaka miki muje na sai miki ruwan."

Kamar ba zan bi shi ba amma gangar jikina na bani umarnin na bi shin ƙila zan dace ya taimaka min tsakani da Allah.

Haka muka tsallaka ya sai min ruwa da biredi na ko ji daɗi na saki jiki na ci na sha ruwan nayi masa godiya. 

Yace dani "Tashi zan taimaka miki zan kai ki inda za a baki aiki ana biyanki."

"Ban iya aikin komai ba."

"Zasu koya miki."

"To na gode yayana, Allah Ya saka maka da alkairi."

Ya tasa ni a gaba da muka karya wata kwana ya tarar mana adaidaita sahu muka shiga na riƙe ledar kayana kam da jakata na rungume don na jima ina ji ana gaya min ana sata a birni akwai ɓarayi a birni sosai sai kana kula.Na yi hadar wannan karatun na riƙe gam a kaina ban manta ba. Musamaman lokacin da Baba yake shiga birni yake dawowa da labarai kala-kala na birni. In yana bawa matarsa labari ina saurara a faƙaice.
*

Kalle-kallen hanya kawai nake yi. Shi kuma sai faman waye-waye yake yi. Gabana na ta faɗuwa ban san me yake min daɗi ba yarana suna cikin raina soyayyarsu na nan ciki fal tana nuƙurƙusata. Mutanen birni basu da imani yanzu da shi kenan da gaske kashe su zata yi nima ta kashe ni kuma? Wata zuciyar tace"Zata iya tunda ta kusan kashe kanta ma waye ba zata kashe ba? Ya ALLAH ka kare mini ƴa'ƴana ,ka karesu daga sharrin wannan matar." Ta faɗa tana share hawayenta.

Basu wani jima suna tafiya ba taji mutumin yace "Ya isa a nan zamu sauka nawa kuɗin ka?"

Mai adaidaita sahu yace "Ɗari biyar zaka bani." 

Babu musu ya bashi. Wani madaidaicin gida ne bai kai kwatan nasu Alhaji ba. Ƴar ƙaramar ƙofa ce . Sau biyu ya ƙwanƙwasa a lokaci guda daga ciki aka kuma yin irin yadda yayi na salon ƙwanƙwasa ƙofar. Sai shi ma ya maimaita hakan amma ƙaramar ƙwaƙwalwata bata bani cewa wannan mutumin ba na Allah bane.

A hankali aka buɗe ƙofar wata matashiya ce ta fito tana taunar cingum kaya jikinta kuwa daidai suke da babu. Wani ɗan siket ne da shima. Ji kake tana ƙas,ƙas sai tayi kwai yace tushh ta ƙara yi tana girgiza jikinta.

"Ya dai hudu? Yau kuma wa ka samo?"

Ya ɗan kanne mata ido ɗaya alamar tayi shiru.

"Ah kace sabon kai ka jawo bata san dawar garin ba kenan lallai yau kayo wa magajiya kamu." 

Kaina ya ɗaure daga nan na soma jin tsoro. 

Shi kuma ya sa hannu ya rungumo ƙugun yarinyar. Ta ko yi taga-taga ta yi masa wata hanƙaɗa ya koma da baya zai faɗi. Dama ba wani ƙiba gare shi ba siriri ne sosai kamar wannan siririyar abin juyawar nan ta cikin agogo. Sai kace mariƙin lema. 

"Kai fa baka da hankali da wani ƙazamin hannunka zaka na wani taɓa ni..kar ka sake ina nufin bakin rijiya ba wurin wasan yaro bane." 

"Daɗina da ke wani zubin ba ki da mutunci muje ciki."

Ya juyo ya kalle ni yace "Shigo." Haka na ja jemammun ƙafafuwana da suka yi sanyi na bi shi muka shiga ciki.

Tun da muka shiga zaure na biyu nake ganin mata kala-kala cikin shiga mara kyau da tsari gasu nan duk mata ne yara da manya. Yawu na haɗiya nace da shi "Bawan Allah ina ne nan don Allah?" 

"A nan za ki zauna kar ki damu fa. Irin ku nan ne mafakar ku."

"Irin ku nan ne mafakar ku" na maimaita me kenan yake nufi?

Nan wata ta saki fito ,muka juya muka kalleta. 

Tayi tsalam kuwa tace "Kanbuuu shege matsiyaci Hudu zo ka bani kuɗi na da kayi min wayo. Na taimaka maka amma ka yi min haka bayan kowacce  nan gidan ba tsaranta bane kai na tallafa maka ka nuna min akuyanci."

"Ke reza me haka ne wannan ai yarfi ne baki ga baƙuwa bane?"

"Iyi baƙuwa ina ruwana da wannan dubu biyu ta zaka ƙirgo ka lalo ka bani kawai malam."

"Zan baki bara na gana da Magajiyar taku tukunna."

Ɗakuna goma sha biyu ne shidda a jere wuri guda shidda a jere wuri guda sai banɗaki guda ɗaya yana kallon hanyar waje. Mata sun kai ashirin a tsukun gidan. Kowacce da kalar tata shigar. Wasu karta ma suke yi wata kuwa ta ɗaura zani amma iya rigar mama ce a jikinta tana shan taba hayaƙi yana tashi sama.

Zuciyata ta tsinke kar dai nan ɗin gidan karuwai ne? Cogewa tayi a wuri guda tana kallonsu cike da tashin hankali. Ta kuma rungume jakar kayanta tana zazzare ido.

Daga bayanta taji magana "Eh Hudu yau kayi babban kamu. Na siya dubu talatin."

"Haba Magajiya kullum sai in samo miki daƙwalayen mata sai ki dinga biyana da arha bayan su kina samun dubbunai dasu yanzu ki kalli wannan yarinyar kina ganinta kin ga babu wanda ya san ta fes take fyalleliya gangariya Wallahi kaya zata ja miki a gidan nan dama gashi yaran naki sun fara tsufa sai shafa man kantuna . Ita kuwa wannan farar bafulatana ce jajir da ita ga gashi komai fa nata natural ne...."

"Kai naji kar ka cika ni da magana ka ce zaka zagi yarana bayan sun fiye mini kai. Zan baka hamsin."

"Ko ke fa Hajajju. Allah Ya biya ya ƙara miki nisan kwana.
"Ke ce wacce ko maye ya kalle ki, sai ya farka!
Magajiya mai dariyar da ke sa zuciya ta karaya,
Kamar ki babu mace mai hana maza kwanciyar hankali da dariya daya!"