Chapter 15
by @khairatup01
ZUCIYAR MUTUM..
NA
KhairatUp
Karamci Writers Association.
Vote @ wattpad khairi_muhd.
15.
"Ina ne gidanku?"
"Bani da kowa ni marainiya ce."
"Hah! To yanzu a ina zan ajiye ki?"
"Ka kai ni tasha zan tafi koma wani gari ne ,amma ba zan iya ci gaba da zama a garin nan ba."
Haidar ya ƙare mata kallo tsaf tuni ya ji kan sa ya fara ɗaukar caji. Shi fa baya son irin wannan abin. Taimakonta kawai yayi niyar yi ba shi da wani burin kai ta wani gun ko ya shiga jikinta.
"Kin ga nima ba ɗan garin nan bane ba. Bikin abokina na zo kuma gobe nake son komawa garinmu ban san inda zan ajiye ki ba ko ke kina da wani wurin da kika sani?"
Da sauri ta girgiza masa kanta.Ta saka gefen hannu ta share hawayenta tace masa "Ban san kowa ba bani da kowa ka sauke ni a nan zan tambayi tasha.."
"Hey! hey! Ya isa bana son kuka Wallhi. Zan kai ki hotel ki kwana a can gobe in zan tafi Gombe zan zo na ɗauke ki."
"Ina ne haka? Ni ban san wani otel ba."
Be san me zai ce mata ba kawai sai ya faka motar a gefen titi ya ɗauki kwallin sigarin shi da lighter ya fita waje.
Tayi kwal a cikin mota zuciyarta na bugu dum-dum kar fa shi ma mugun ne kamar Hudu? Wata zuciyar tace da ita "Haba ai da mugu ne ba zai fanshe ki daga gun waɗanan matan ba." Saƙe-Saƙe ta dinga yi ita kaɗai.
Haidar kuwa sai da ya sha kara biyar kafin ya samu ya nutsu.Wayarsa ya zaro daga cikin aljihunsa ya nemi nambar Tareeq sai dai Tareeq bai ɗaga kiran ba har sau biyu sai da ya kalli agogon hannunsa ya ga ƙarfe goma sha ɗaya saura. Tsaki yayi cikin ransa yace "Bala'i dama ta ina Tareeq zai ɗaga masa waya an kai masa amarya."
Haka dole ƙanwar naƙi ya koma cikin motar ya shiga. Wani Hotel ya kai su Green Palace ya biya suka shiga. Ba kunya ba komai ya zare rigarsa daga shi sai singililetinsa tuni Uwani ta kurma ihu ta sa hannu ta kulle idanuwanta.
Tsorata yayi da ihun da ta yi ya tsaya cak hannu riƙe da ƙugu yana kallon ikon Allah.
"Ban gane ba? Uban meye yake saka ki ihu?"
"Kai ne ka cire riga bana so."
"Keee! Me.." maganar ma ya kasa yi ba shi da kalmomin da zai iya yi mata ruwansu.
Ji yayi kamar ya mamake ta ya shige banɗaki don ya watsa ruwa daman zafi yake ji.
Uwani ta gyara zamanta a kan gadon kan kace me sanyin Ac ya doke ta sai bacci daman ga gajiya.
Haidar yana fitowa yaga tayi bacci.Mamaki ya kama shi bata yi wanka ba bata yi sallah ba.
Sallar yayi. Ya zauna a kan kujera ya miƙe ƙafafunsa a kan teburin nan na tsakiya ya ɗauki wayarsa. Bai ji kira ba amma yaga wayar Hajiya da Mami da Afeeya da Baffajo har ma da kiran Habib.
Ji kira rututu kamar wani mai laifi ,to me zan musu ne wai?
Wayar ce ta soma ƙara "HAJIYA" ya gani. Ba tare da wani ɓata lokaci ba ya ɗaga kiran.
"Sweetheart yaya kike?"
"Ka ci gidanku Haidar kana ina ma tukunna?"
"Hajiya ina nan ina kewar ki amma kika baɗan ƙasa a ido wayyo Allah babu amanar ƙauna Dr."
"Babu wani daɗin bakin ka da zai shige ni yau. Haidar me kake so ka zama ne? Mamin ma ba zaka bar ta ta huta ba har yau hallayenka na nan adalci kenan Haidara?"
"Hajiya don Allah ki fahimce ni ki bari na gaya miki abinda ya faru ba laifia bane Wallahi."
"Laifin waye to?"
"Hajiya Afeeya ta raina ni, a gabanku ne take nunawa ita ta Allah ce. Ni take azabtarwa amma ba a gani saboda kawai ana mini kallon ɗan sholi sarkin rashin tunani."
"Haidar fisabilillilahi haka ya kamata ma kace? Gaya min ni zan saurare ka me tayi maka har ya sa ka sake ta?"
Hajiya....Ya kwashe komai tsab ya gaya mata bai rage mata komai ba.
Hajiya tayi shiru a wannan gaɓar. Daga bisani kuma tace "Ina son ka maida Afeeya ɗakinta. kayi haƙuri ka ji?"
"Hajiya Wallahi Allah ba zan maida Afeeya ba."
"Ban isa ba kennan?"
"Kin isa Hajiya ki bani ko wace ce na yi miki alƙawari zan ɗauka amman ban da Afeeya."
"Haidar anya baka koma ruwa ba?"
"Garau nake Hajiya,Wallahi duk na daina shan su,sigari ce kaɗai bata rabu dani ba."
"Innalillahi wa inna illajir raji"un Haidar me kake son ka zama ne? Shi kenan kai babu mai sa ka babu mai hana ka ? Abinda kake so shi zaka yi baka da na gaba kenan?"
"Wallahi kun isa kuyi ta min addu'a kawai Hajiya zan daina ɓata muku in sha Allah."
Yanzu kana ina?
Ina Kano.
A ina a Kano?
Hotel.
Shiru Hajiya tayi don ta san Haidar sarai baya ƙarya baya kwana-kwana kome zaka yi masa ba zai taɓa rissina ba musanmman ma in shi ne da gaskiya.
Me kake yi a Hotel ɗin?
Hajiya gobe in na zo zan gaya miki.
Ka tabbatar kazo. Na san halin ka zaka iya tafiya baka biyo ba.
Zan zo Hajiya ai ni na ce miki zan zo.
Naji. Ta ajiye waya. Shi ma ya sauke ajiyar zuciya.
Kallon Uwani ya sake yi yadda take bacci ba tare da wata damuwa ba, fuskarta tayi masa kyau. Gashinta ya bi da kallo ya gan shi a cike bai siɗik da sauri yace "A'uzubillahi." Ya tashi da saitin inda kujerar ta take. Tunanin rayuwarsa yake yi irin ƙalubalen da yake fuskanta tun yarintarsa har kawo yau babu wani abin alfahari da zai ɗauka a ciki. Ya sani iyayensa da ƴan'uwansa suna ƙoƙari kuma suna haƙuri da shi. Da kan sa ya san baya jin magana,yana da taurin kai,yana da saurin fushi da fusata ba fa komai ke burge shi ba. Duk wani abu da yayi matar mahaifinsa na da kwamasho a ciki. Yadda ta dulmiyar masa sa da rayuwa a harkar shaye-shaye,da bin mata addu'ar iyayye da kuma iko na ubangiji ya saka ya daina amma ya sha matuƙar wahala. Amma da yake makira ce sai ta saka aka aura masa Afeeya don ta maida shi ruwa sai dai ya gane su amma ya bar su da halinu ya dinga bin su yadda suke so amma da yake ba shi da hakkinta sai Allah Ya kawo ƙarshen zaman.... wayarsa ce tayi ƙara. Wannan karon ya san Mami ce. Amma yana ɗauko wayar sai ya ga nambar Baffajo ce.
Ajiyar zuciya ya sauke ya ɗaga haɗe da yin sallama." Assalamu alaikum. Barka da dare Baffa."
"Barka Aliyu Haidar
. Rigimar ka tayi maka yawa Haidar ina murna ka girma ka fara tunani irin na manya ashe ba haka bane?"
"Baffa ayi haƙuri da ni kamar yadda aka saba. Allah Ya shirye ni. "
"Ameen Haidar. Kana ina?"
"Ina kano gobe zan dawo Gombe."
"Amma ka kyauta?"
"Baffa na kyauta masalahar mu ce ni da Afeeya."
"Haidar a kunne na?"
"Afuwa Baffa.Amma ita ta nema. Tace bani da mafani bata jindadin zama da ni bana mata komai bani da zuciya sai kurin banza abubuwa kala-kala da zan gaya maka duka Baffa sai ka jinjina min irin zaman da nayi da ita tsahon lokutan nan."
Baffa yayi shiru. Can kuma yace "Haidar da ka ƙara haƙurin ai. Ka san shi namiji shi ne babba shi ne uba dole sai kana haƙuri da mata. Ba ka ganin iyayen ka Mami da Umma?.
"Ina gani Baffa. Ka ɗauka kawai kwanan auren ne ya ƙare."
Baffa yayi dariya irin wadda ya jima bai yi ba. Haidar ba shi da munafurci ko ɓoye-ɓoye kaitsaye yake faɗar maganar sa ba shakku babu ƙarya. Shi yasa in ya faɗi magana ba ya musawa don tun asali baya ƙarya.
Ka tabbatar ka dawo goben.
Baffa zan dawo amma Baffa zan taho da wata yarinya.
Da sauri Baffa yace "Yarinya Haidar me ne?"
Baffa abar a tausaya mata ce, ni kuma na ƙwato ta ne daga bakin kuraye ƙarama ce nan ya labarta masa komai....
Baffa ya sauke ajiyar zuciya yace "Allah Ya yi maka albarka Haidar. Zaka yi albarka in sha Allahu. Ka taho da ita ni zan riƙe ta a matsayin ƴa."
"Na gode Baffa.Allah Ya ƙara girma."
Suka ajiye waya tare.
Haidar na son mahaifinsa yadda mahaifin nasa shi ma yake son sa. Wannan soyayyar ce ta ja masa baƙin jini a gun Umma kishiyar Mami. Baffa yana fahimtar sa Mami kuwa sai yadda Umma tayi da ita.
*
"Ka same shi?"
"Da shi muka gama waya."
"Me ya sa ya saki yarinyar nan? Ya ga muna zaman lafiya da ƴar'uwata yake so ya ɓata mana zumunci."
"Aa. Ba laifi yayi muku ba kuma ban yarda ko waccen ku ta shiga rayuwarsa ba. Zai dawo gobe in ya zamu yi magana . Amma daga yau na hana wannan maganar. Ai na a alkalanci ta fuska ɗaya. Ku jira ya dawo a ji daga bakinsu duk su biyun sai a gane mai gaskiya."
Mami dai tayi shiru zuciyarta na duka biyu-biyu bata son ta ɓatawa abiyar zamanta rai saboda tana son ta.
*
Afeeya kwance kan gadon Umma sai kuka take yi .
"Umma ba zan rabuwa da Hamma Haidar ba. "
"A banza da ba za ki iya rabuwa da shi ba ai da ba za ki ce ya sake ki ba. Kwata-kwata baki da basira baki iya komai ba sam ba ki ɗauko halina ba. Ni da kika gan ni kishiyata ma a tafin hannuna take sai yadda nayi da ita ko baki gani ba? Maimakon ki ɗauko halina kiyi gadon nono na shi ne za ki wani sako auren? Aliyun nan fa da kike gani rainona ne a lokacin da na saka uwarsa ta bar gidan nan ni na koya masa duk wani banzan hali amma naga alama...."
Afeeya ta katse mata zancen tace "Umma.Wasa nake mai gwada shi nake yi. Jiya maganin da kika bani nayi amfani da shi so nake naga ko zan mallake shin. Ashe aikin bai yi ba."
"Gaggawa gare ki Afeeya.Haka ubanki ya sake ni saboda wata. Na taho dake gidan nan burina na aurar da ke ga Haidar shi ne magajin ubansa ni ban haifi namiji ba, sai mata suma guda biyu kawai. Gabaɗaya burina akan ki yake Afeeya amma kika ɗebi ƙasa kika watsan a idanuwa. Ai shi kenan sai ki zauna a haka."
Afeeya ta kuma saka kuka. "Na shiga uku Umma. Don Allah kiyi wani abun a kai Umma."
"Me zan yi Afeeya? Me kike so nayi miki? Ai kin kashe komai da hannunki. Yaron nan yanzu da kafi a jikinsa wannan muguwar ƙanwar uban nasa ta tashi tsaye ta ɓatan shirina a kan sa. Na kashe ƙuɗaɗe amma a banza sai ki zauna mu ci gaba da gogar ɗuwawu."
In dai na rasa Hamma Haidar tabbas na tafka asara. Na san ba shi da daɗin mu'amala ba mutum ne mai nuna kulawa ba amma ana cin ƙuɗinsa yadda ya kamata ko a siyan kwana da yake yi ba shi da hannun jarirai na yi wa kaina? Amma sai na nemo hanyar da zan koma gidan Hamma Haidar.
*
"Habib na lura tunda yarinyar nan ta tafi baka cikin yanayi na nutsuwa? Wai me yasa ka damu da ita ne?"
"Aisha yaya za ki tambaye ni irin wannan? Ai dole na damu bata da kowa a nan ,ni ta sani. Da kin yi haƙuri ma boarding zan kai ta gidan Hajiya zan maidata na san zata zauna da ita tamkar su Rukkaya.."
"Saboda asirinmu ya tonu ko me kake nufi? Ai zaman Uwani a cikin rayuwarmu barazana ce ga dukaninmu. Gara a hakan ta tafi mu muna nan babu wani abu da ya rage a tsakaninmu. Ƴaƴan nan namu ne bana kowa ba. Na bata hakkinta na san zata gina kanta."
"An gaya miki komai ƙuɗi ne Aisha? Mtsw ki je don Allah ki bani wuri na huta."
Aisha ta bar masa ɗakin yana wasa da yaran sa. Babu ruwanta da wan fushinsa tunda ita ta samu cikar burinta. Babban burinta a duniya ta samu ƴa'ƴa da Habib don ta rabu da samun kishiya kuma burin ya cika babu ruwanta da wata Uwani da zata mutu ma da tafi farinciki don babu wanda zai sirrin da ke tsakaninta da Uwani.