ZUCIYAR MUTUM

chapter 17

by @khairatup01

ZUCIYAR MUTUM

NA

KHAIRATUP

Karamci Writers Association.

Vote@wattpad khairi_muhd.

                   

Hotel ya koma. Har a lokacin bata tashi. Ruwa ya samu ya buɗe ya ya yayyafa mata a kan fuska kamar zata shiɗe ta tashi ta  sa ihu. 
"Wayyo Allah na shiga uku ba ni bace ban yi komai ba na bar miki ƴa'ƴan kar ki....."

"Hello!"Ya faɗa da ƙarfi. 

Sai a lokacin ta dawo cikim hayyacinta. Ta koma gefe ta raƙube tana kuka. Da kewar yaranta ta tashi. 

"Ke ba kya gajiya da kuka? Komai kuka kullum kuka. Daga ina kike kuka ina za ki kuka? Haba mana." 

"Kayi haƙuri."

Sai aukin bada haƙuri kika iya. To yanzu ba wannan ba kin yi sallah?

Aa ban yi ba.

Me yasa ba ki lokaci ba?

Uhmuhm.

Tashi ki yo alwala kiyi slllah ki karya kiyi wanka mu tafi. Ai za ki bini garinmu ko?

Zan je.

Banɗakin ya nuna mata ta shiga. Bata sha wahalar amfani da kayan ciki ba saboda ta riga ta saba da wannan   gidan HAMMA.

Tuno Hamma da tayi kaɗai sai da idanuwanta suka ciko da hawaye. Tana kewar shi tana kewar ƴa'ƴanta ji tayi kamar ta haɗiyi zuciya haka take ji. A kowacce daƙiƙa ƙirjinta yana cika da kewar tagwayenta . Tana kewar Hamma da kulawarsa abida ya fi burgeta da shi sanyin sa da iya karram ɗan'adam. ...

Ƙofar banɗakin Haidar ya buga "Kiyi sauri muna makara bana son muyi tafiyar dare."

"Yanzu zan fito." 

Tana fitowa ta samu hijab ta zura ta soma dungura kai. Kawai kallon yadda take sallar yake yi kamar ba sallah take ba ko dai yarinar musulunci ta karɓa budurwa kamar haka bata iya sallah ba. 

Sai da iddar ya kalle ta da kyau yace "Yaya sunan ki ne?"

"Uwani". Ta ba shi amsa kaitsaye.

"Wanne irin suna ne haka? meye asalin sunanki?"

"Sunan kenan. Haka Innata take kirana kafin ta rasu ni ban taɓa jin an kira ni da wani sunan ba sai wannan har a garinmu ma kowa haka yake kiran  daga baya aka koma ce min Uwanin Nata'ala" ta faɗa cike da wauta.

Dariya ta ba shi. Ya juya kuwa yayi tayin ta har sai da ta ji babu daɗi.

Da yaga zata yi kuka yace "Tsaya yi haƙuri don Allah kada kiyi kukan nan. Amma waye Nata'alan ko shi ne ya saida ke?"

"Aa tsohon mijin  ne Nata'ala..."

Idanuwansa ya kwalalo waje yace "Miji? kina nufin kin taɓa aure?"

"Eh!."

"Yana ina,me ya raba ku?"

"Yaudarata yayi. Ya bar ni a garinmu. Yace zai nemi kuɗi mu dawo Kano tare. Su kuma ƴan gidansu basa sona sai ƙaninsa Sageeru ya yi ƙoƙarin yi min fyaɗe shi ne na gudu sai mota ta kaɗe ni....." Katse ta yayi saboda lokaci amma zai saurari labarinta.

Kinga ɗau kayan nan ki saka. Au fara yo wanka zamu tafi in muka je can za ki ƙarasa min labarin naki.

Kai ta gyaɗa masa. Har zata shiga banɗakin sai kuma ta juya ta kalle shi tace "Amma ka fita saboda zan shirya in na fito."

Ya ƙare mata kallo tun daga sama har ƙasa ya saki dariya yace "Na ji."

Wai ya fita sai kace zai mata wani abun ne. Yarinyar nan ta raina shi ma me a jikin nata ƴar ƙarama da ita ƴar mitsil. 

*

Tafiyar awa shidda suka yi zuwa garin Gombe kasancewar yanayin na gari da cunkoso. Ta Zaria suka tafi suka wuce Bauchi . Ta taga take kallon hanya dazuzuka da titi da ƴan tsirarun gidaje haka daga nesa. Tafiyar akawai gajiya amma taji daɗin tafiyar.

Har bacci sai da tayi. Bai tashe ta ba. Hasalima karatun qur'ani ya kunna yana bi wani bin kuma ya amsa waya har suka isa garin.

Cikin mintuna kalilan ya isa Jekadefari (Unguwa ce mai tarihi da Turawa suka zauna bayan sun ci nasara a kan Sarkin Gombe a shekarar 1903. Akwai gine-ginen tarihi da dama a nan,kuma unguwar na ɗauke da muhimman cibiyoyi.) Bai tashe ta ba har sai da suka shiga ainihin cikin gidan. 

Tuni labarin isowar Haidar ya isarwa Mami da Umma. Tuni Afeeya ta miƙe ta fito da saurinta a falo suka haɗu da Umman.

"Ina za ki je?"

"Wajan Haidar za ni na bashi haƙuri."

"Koma ciki shegiya marar hankali."

"UMMA so nake yi ya maida ni fa kiyi h."

Bata bari ta ƙarasa ba ta rarumi wata tukunyar fulawa da aka yi ado da ita a falon ta wulla mata shi. Da sauri ta sunkuya ta saki ihun firgici "Wayyo Umma."

"Kin wuce ko sai na yi gutsi-gutsi da ke."

Da gudu ta koma ciki. Amma tana shiga ta buɗe tagar ɗakin nata ta dirga. Ba zata iya barin Haidar ya kwana lafiya ba.

   Zulai zo nan Zulai.

Da sauri ta dawo da tsugunna "Gani Hajiya".

"Ina Haidar?"

"Yana ɓarayin Hajiya Mami." 

Gudu ta saka don kar ya tafi nasa ɓarin ta kasa ganinsa a ɓarin Mami ne za ayi ta ta ƙare kuma dole ya haƙura ya yi ammanna.

Kawai gani suka yi ta faɗo falon Mami tsalam kamar zata faɗa kansu.

Ƙafar Haidar ta kama tana kuka "Yaya Haidar don Allah kayi haƙuri ka yafe min ka maidani ɗakina Wallahi na san nayi kuskure laifina ne ba da gaske nake ba..."

"Tashi mana Afeeya. Meye haka?"

"Aa Mami bari na bashi haƙuri da gaske ni na nemi sakin amma ba da gaske nake ba kawai..."

Mami ta katse ta "Ya isa na ji tashi zo ki zauna a nan. Zamu yi maganar a tsanake."

Da ƙyar ta tashi jikinta sai rawa yake yi. Ba ma sosai take gani ba.

'Haidar ka kalli yarinyar nan tayi nadama ka maida ita ɗakinta haka."

"Mami ni fa na yarda ku aura min duk wacca kuke so amma ban da wannan yarinyar. Daƙiƙi ke maimaita aji."

"Innallillahi wa inna illahir raj'un ,Haidar ni kake gayawa haka?" Mami ta faɗa tana kuka hannunta a kan ƙirjinta.

"Mami ya kike haka? Ni fa ban miki komai ba. Ki daina min kuka Allah Yayi fushi dani a kan waccar abar matsiyaciyar yarinya mara kunya kune kuke son ta amma ban da ita muguwa ce..."

"Kul. Fitsararre ɗan iskan yaro mara kunya. Kai dai baka cika ɗan halak ba butulu. " Hajiya Umma ta faɗa tana huci cike da masifa da tashin hankali a kan fuskarta bata ƙi ta shimfiɗa masa mari ba a bisa fuska ba.

"Haba Umma abin duk bai kai haka ba . Ke da ɗan naki ai bai kyautu a ji kan ku ba. Za ayi masalaha Umma ai da Afeeya da Haidar duk naki ne rainonki ne."

"Yi min shiru munafuka.Ai na san daɗi kike ji ɗan ki ya maidan ƴa bazawara. Ran ki ƙal tamkar farar takarda to sai me don ya saki Afeeya? Ai shi yayi asara  wacce zata aure shin dama in ba Afeeyan ba na duba matsayin ubansa na bashi ƴa ya zo yayi min wannan sakayar . Tsiyar ɗan shaye-shaye kenan. Ba hankali bare nutsuwa."

"Me yake faruwa ne haka   Hajiya Zaliha?"Baffa ya tambaya yana shigowa. Gabaɗaya sun yi cirko-cirko kamar zakaru a falo.

"Meye kuwa ban da wannan yaron marar kunya ni zai yi wa fitsara uwarsa na ganinsa." 

"Ya haka kuma Hajiya Fatima. Haidar ba uwarka bace?"

"Baffa ban yi komai ba fa. Kawai na faɗa ba zan  maida ƴarta Afeeya ba shi ne take wannan masifar tana jifana da kalamai munana. Shin waye ya ɗorani a kan shaye-shayen in ba ita ba?"

Baffa ya sa hannu ya wanka mai mari. "kai maras kunya ai ko baka ji kunyar kowa ba ka ji tawa. A gabana kake wa iyayen ka rashin arziƙi ko dai ka shawo wani abun ne?"

Haidar bai iya cewa komai ba kawai ya juya ya fice.Baffa yayi ta kiransa amma bai tsaya ba ko juyowa ma bai yi ba.

"Innallillahi wa inna illahir raju'un.Wannan wacce iriyar masifa ce? Yau naga abinda ya ishe ni ni Fatima".

"Baki ga komai ba Fatima ni na gaya miki da sauran ki.Sai kunyi da  na sani a gaba.Ai idan ma Haidar ya maida Afeeya bai haihu fa."

Baffa ya daka musu tsawa "Wai kuma yaran zaku koma. Hajiya Zaliha ina nan a gabana kike faɗar irin wannan akan Haidar? "

Sai kawai makirar matar ta sa kuka ta zauna kan kujera.

"Ba zaku gane abinda nake ji ba a cikin zuciyata. Ni aka sakarwa ƴa. Aka maida ta ƙaramar bazawarar ƙarfi da yaji. Ni nake ganin ƙuncin da ƴata take ciki kawai don ita agola ce shi yasa ake yi mata bambamci....Ni kawai Alhaji ka bari na maida ta wurin ubanta. Na gaji, na gaji da irin cin zarafin da ake yi min ni da ƴa'ƴana don kawai Haidar shi ne namiji sai a bar shi ya dinga yin abinda ya ga dama?"

Falon yayi tsit aka rasa mai bakin magana.Alhajin ma zaunawa yayi baki gum. 

Can na hango Uwani a rakuɓe tana karkarwa taga kalar masifar da bata taɓa gani ba. Ita fa ba wuya ta firgita Haidar yana fita ta miƙe zata bi shi sai kuma ta kasa kamar an riƙe mata ƙafa a wurin haka taji. 

Shasheƙar kukan da suka dinga ji ya saka suka juya saitin inda kukan yake tashi.

Sai a lokacin Mami ta tuna da yarinyar da Haidar ya shigo da ita bayan ya dawo.

Baffa yace "Wacece wannan?"

"Haidar ne yazo da ita wadda yake gaya maka jiya."

"Au. A kai ta ɗaki ta huta. Kun zo kuna hayaniya a gaban baƙuwa. Bai kyautu ba babu tsari ina murna nima yanzu gidana lafiya kalau ashe da saura. Ga shi gida na biki an fara taruwa haba kun bani kunya."

Afeeya ta kafe Uwani da ido jin ance baƙuwar ta haidar ce.

Tuni ta ƙanƙance idanuwanta ta miƙe tsaye ta manta ma Baffa ya dawo yana falon.
Gaban Uwani ta ƙarasa ta cakumo hannunta ta miƙar da ita tsaye.

"Wacece ke? Meye haɗin ki da mijina Haidar?"

Uwani fa ta rikice sai zazare idanuwa kawai take. Daman idanuwan sun cika taf da hawaye ta rasa ma me zata ce. Daman ba wuya ta rikice.

A tsawace tace "Don uban ki wacece ke?"

"Uwani suna..na...Uwani. "

"Sai kuma aka yi yaya?"

Bata da amsa ta ga tsorata tace "Kiyi haƙuri zan tafi."

"Ai dolen ki ma ki tafi." 

"Ba ke kika kawo ta ba saboda haka baki isa ki koreta ba. Ina gidan ubana ne nan? Ina da damar da zan kawo ko da dabba ce kuma a zauna da ita." Haidar ya faɗa yana ƙarasawa ciki. Umma ta maka mai harara shi ma ya watsa mata. 

Afeeya ya kala yace "Babu ruwanki da ita. Ni na kawo ta."

"Da ruwana Haidar da ruwana har da tsaki na Wallahi. Baka isa ba Wallahi baka isa ba. Shi ya sa ka sake ni? Saboda wannan yarinyar ƴar ƙauye mai kama da bararoji ka sake ni? Ka ji kunya ka faɗi Wallahi."

"Na ji kunyar sai me?" Ya ja hannun Uwani suka bar falon.

Haka suka bisu da kallo zuuuu baki buɗe.

Mami ta ƙara daskarewa daga zaunen da take.

"Baffa Haidar yafi ƙarfina." 

"Hajiya Fatima baki ga komai ba sai ranar da wannan yaron mai kama da ɗan maraƙi ya kwaso miki abin kunya tukunna."  Ta juya ta kalli Afeeya tace "To ƴar mara zuciya mara hali baki dazu zuciya namiji kike wa haka ,to ki sani kin dinga kwasar kayan taƙaici kenan. Shegiya sai dai dama in halin ubanki kika gado. Wuce muje" ta finciki hannunta suka fice daga falon.

"Hajiya Fatima kar kisa damuwar Haidar a cikin zuciyarki kiyi tayi masa addu'a da bakinki irin na Uwa sai ki ga ya daidaita kukan ko fushin ba shi da amfani. Nafi so ku kwantar da hankalinku   a gama bikin nan lafiya in yaso sai a ga yadda za ayi."

Mami na kuka tace "Yaron nan baya son ya gan ni ina zaune lafiya. Kullum Haidar a gidan nan kowa Haidar haba wannan wacce kalar masifa ce?  Yanzu ga wata ya kawo. Gashi Umman ta su ma gani take yi ni na sa saka ya saki Afeeya Wallahi bani da matsala da auren Afeeya da Haidar bana bin ta da mugun nufi..."

"Ya isa babu komai. Ki tashi ki ji dani. Naga duk kun wani firgice saboda wannan shashan yaron."

Hum "Muje Baffa. Daman ina son na gaya maka ya kamata a ce gobe an tura mota Billiri a taho da su."

"Nayi wannan tunanin nima. Don na yi magana ma da Joɓe zai tafi da Isalle da safe su taho dasu in sha Allah."

"To Allahu Ya sha."

"Ameen."

*

"Ke baki da hankali? baki da bakin magana ana gaya miki maganganu kina ji?"

"Kayi haƙuri.."

"In kika ƙara ce min in yi haƙurin nan sai na make ki. Baki da wayo."

Kuka ta soma yi tana sharewa da bayan hannunta.

"Kukan me kuma kike yi? Ke baki da aiki sai na kuka daga nan sai bada haƙuri kika iya?" 

"Kayi haƙuri."

Hannu ya sa ya dafa goshinsa ya furzar da iska hannunsa ɗaya a kan ƙugunsa.Ba zai iya cewa komai ba.

"Za ki iya komawa ciki inda muka fito?"

"Aa ba zan gane ba.Don Allah ka maida ni kar wannan matar ta dake ni."

"Mtsw! Muje".

A baya ta dinga bin sa tana share hawaye.

Da ya koma bai ga kowa ba. Da kan sa ya haura sama ya buɗe ɗakinsu Sa'adatu duk da ya san ba zai same su ba sun fara shiga hada-hadar biki. Ɗaya ɗakin ya buɗe babu kowa a ciki akwai kayan alatu na zama a ciki.

Ta saman ya leƙa yace "Ke! Ke!" Ya manta sunan nata. Da ƙarfi yace "Ke ki hawo sama." 

A hankali ta haura saman. Ya nuna mata ɗakin. Ɗakin su Sa'a ya kuma komawa ya buɗe kayansu ya ɗebo wasu ya kai mata. 

"Ki yi wanka. Zan sa a kawo miki abinci. Ki ci ki yi sallah ki kwanta . Zan dawo da safe muyi magana da Mami da Baffa."

"To."