ZUCIYAR MUTUM

chapter 19

by @khairatup01

ZUCIYAR MUTUM

NA

KhairatUp

Karamci writers Association.

Vote@wattpad khairi_muhd.

TALLA! TALLA! TALLA!

❤️ *ƊANLARABAWA INVESTMENT! Kyau Da Ƙima A Hannunku!* ❤️

*Ku sauka lafiya zuwa masarautar ƙayatarwa!* 👑
  
*ƊANLARABAWA INVESTMENT* na kawo muku:

*Atamfofi masu kyau na zamani*  
*Shaddodi da Laces masu ɗaukar ido*
*Takalma & Jakunkuna masu ladabi da ƙima*
*Hijabai, mayafai da dogwayen riguna masu salon zamani*  
*Yari da sarƙa da kayan ado masu ban sha’awa*
*Akwatuna masu kyau don tafiya ko haɗa lefe*
*Turaruka masu ƙamshi da kayan kwalliya na garari*
*Nau'in kayan kicin na alfarma da kayan ɗaki*
*Zannuwan gado da labulaye na kashe kala*

*Da dai sauran su*

*Muna tura kayanmu ko'ina a fadin Nijeriya da ƙasashen ƙetare. Cikin mutuntaka da cika alƙawari in sha Allah*

*Location: Kano, Ƙofar Waika, Layin Malam Sani Shawus.* 
*Lambar waya domin tuntuɓa*: ***  

*Ko ku shiga zaurenmu na manhajar WatsApp ta wannan link kamar haka:*

***

*Za ku more da kallon kayayyaki na ƙawa bisa ingantaccen farashi da rahusa mai kama da kyauta. Sayen nagari, mayar da kuɗi gida.*

                   18.

Saffiya da Sa'adatu sun dawo misalin ƙarfe takwas na dare. A gajiye suke sosai basu tsaya ma neman kowa ba suka shige ɗakinsu. 

Saffiya ta kalli Sa'adatu tace "Kin ji tashin ta tashinan da yake wakana  a gidan nan ko. "

"Wai Hamma Haidar? "

"Uhm."

"Gaskiya kuna da son kan ku ƴan gidan nan. Komai aka yi sai ku bashi laifi ku ɗora masa kahon zuƙa ta fitina. Ita Afeeyar ina baku san ta bane? Ba ku san abubuwan da take yi bane? Kawai don kuna tsoron Umma shi kenan sai a dame shi."

"Ba haka bane Sa'ada, kin gane hakan Mami yake shafa kin sani bata iya tashin hankali ba."

"Mami fa ita ta so hakan,ko in ce ita ta ga dama zata bari kishiyar da ta zo da same ta tana mata mulki   a cikin gida. Ta mulki miji,ta mulki ƴa'ƴa ta kuma mulki jama'ar gidan. Ni da ba zan iya ba. Kinga a bar maganar nan bacci nake ji sosai da sosai kinga gobe za a fara biki akwai kuleran bamu je wankin kai ba don Allah ki kwanta ki daina tunanin komai tunanin ma zai saka ki ƙin kyau gobe don fuskar ki zata nuna rashin samun bacci."

"Yes Ma!" Ta faɗa suka sa dariya tare.

Asuba tagari.

*

Washegari Alhaji Baffa da kan sa ya kira Haidar da Mami ɗakinsa na saama.

Haidar bacci bai ishe shi ba ya fito daga ɓarinsa idanuwan nan jajir gashi ya cukurkuɗe saboda yadda ya tara shi yayi yawa sosai. Da gajeran wando da singileti ya fita wayarsa a hannu yana tafe yana haɗa hanya kamar dai baccin bai ishe shi ba ko ya sha wani abu.

Da sallama ya shiga ɗakin Baffan ya same shi a kan kujera me zaman mutum ɗaya daman ita kaɗai ce a ɗakin. 

"Barka da Asuba Baffa"

"Barkanmu dai Haidar. "

Ya juya ya gaida Mami ma amma kadaran kadahan haka ta amsa masa.

Baffa ya ɗora da ; 
"Haidar yanzu dube ka don Allah kalli kan ka kamar wata gonar bola ka tara tayi sama tayi tsiri ba dole a dinga maka kallon baka sauya hali ba fisabilillahi? Ka aske wannan kan kafin anjima kar na ƙara tozali da wannan dajin."

"An gama Baffa zan aske. Dama yau nake son askewar."

"Yayi."

Mami tayi tsaki kamar fa zata mari Haidar haka take ji.

Baffa yace "Ina wannan yarinyar ta kwana mun manta saboda waccar matsalar"

"Baffa na fa nutsu ,tana nan sama a ɗakin da yake kusa da su Saffiya."

"To Alhamdullilhi" Baffa ya faɗa yana dariyar Haidar da yace "Ya fa nutsu" da ace da ne lokacin da kansa yake hayaƙi yadda aka zabga wannan mahawarar a ɗakinsa zata kwana.

Mami tace "Baffa naga kana masa zancen wata yarinya kuma ,kamata yayi ka saka ya maida matarsa ɗakinta ko za a zauna lafiya."

Za ayi wannan maganar Fatima amma ba yanzu ba. Sai an gama bikin Saffiya. Ya juya ya kalli HAIDAR yace kirawo ta ina son nayi magana da ita.

To Baffa. Haka ya fita ya isa bakin ƙofar ya ƙwanƙwasa sau biyu ta buɗe masa.

Tayi wanka ta fito fes da ita. Ta saka doguwar rigar da ya kai mata da hula a kanta. 

"Ina kwana."

"Lafiya ƙalau ki zo Baffana yana son yin magana da ke."

"To. In taho a haka? na wanke hijabin ne."

Ta so ta ba shi dariya haka ya dake yace "Eh muje ai Baffana ne da Mami."

"Kamar muryar Bro nake ji haka?" Sa'a ta tambaya daga bakin ɗaya ƙofar.

"Ni ne sis ashe kun dawo." 

"Eh mun dawo.Bro wacece wannan".

"Uwani."

Dariya Sa'a tayi tace "Kaji wani sunan ƴan ƙauye. A wannan zamanin dama ana saka irin wannan sunan daman?

"Gashi nan dai kin ji yau."

"To yayi."

Ya tusa ƙeyarta a gaba har ɗakin Baffa.

Tsugunnawa tayi kamar zata kifa wurin gaishe su d sauri da sauri "Ina kwananku." 

"Lafiya"suka amsa a taƙaice.

Mami dai taɓe bakinta tayi. 

Baffa kuma yace "Yarinya yaya sunan ki?"

"Uwani. Uwanin chiroro."

Baffa yayi murmushi yace "Chiroro dai ta Minna?"

"Eh."

"Ina iyayenki da ƴan'uwanki?"

"Ban sani ba. Bani da kowa. Innata da Babana sun rasu. Ban taɓa ganin wani yaje a matsyain ƴan'uwansu ba sai aminin Baba shi ma yayi min aure yayi balaguro daga garin ban san inda yake ba." Ta ƙarasa faɗa muryarta na rawa kanta a ƙasa. 

Haidar ya san kuka take don yadda yaji muryar na rawa gashi tana gogewa da bayan hannunta.

Baffa ya jinjina kai yace "Ikon Allah! Ina mijin naki? yaya aka yi kika tsinci kan ki a Kano a irin wannan gidan?"

    "Sageeru ne ƙanin Nata'ala zai yi min fyaɗe shi ne na gudu kuma Inno ta gani amma sai ta ɗora mini laifi. Ganin Sageeru zai iya haike min a gaban Inno ma sai na gudu sai mota ta buge ni wanda ya buge ni ya taho dani Kano aka kai ni asibiti saboda na samu karaya a ƙafata. Daga nan sai na rasa murya ta saboda tsananin firgita na koma zama da HAMMA da matarsa. Sai naga Nata'ala a gidan yayi aure ya auri mai aikin gidan ni kuma ya saidani ga matar gidan..." ta kuma fashewa da kuka. 

Ɗakin ya yi tsit sai kukan ta ke tashi. An rasa mai rarrashinta saboda tausayi da jinjina cin amanar mijin da ta ɗauka a matsayin gatan ta.

Haidar ya rarrafa kusa da ita ya bata hankacif ta goge fuskarta. Ko Mami da yarinyar bata yi mata ba sai da ta tausaya mata.

A hankali Mami tace"Suka siye ki ki musu me?"

Tana shiɗewa tace "Wai zan haifa musu jariri sai na tafi na bar gidan." 

Haidar yace "Ki haifa musu jariri kuma ta yaya? aurar ki yayi?"

"Aa bai aure ni ba."

"Me ya miki to?" ya faɗa yana ƙara girman idanuwansa.

"Ganin bana iya magana kuma bani da gata bani da wurin zama ya saka na yarda zan haifa musu ɗan.Ban san me suka yi min ba asibiti muka je aka yi mana gwaje-gwaje na sha wuya likitan ya saka min wani abu a jikina daga nan da aka kwana biyu sai na samu ciki a ɗaki nake zama a sama komai Hamma yana yi mini ta kulawa har na haihu na haifi ƴan biyu a a asibiti. Sai Hajiyar tace na gama aikina in tafi saboda bata son kowa ya san sirrin jariranta da ƙyar ta yarda da mijinta na shayar da yaran na wata biyu sai ta kore ni bayan mijin yace ba zan tafi ba.Ta ce wai son Hamma nake yi shi ma Hamma sona yake yi,tace in ban tafi ba zata kashe min ƴarana shi ne na tafi cikin dare na kwana a titi saboda ban san kowa ba bam ma san garin ba ban taɓa fitowa ba sai in za a asibiti shi ma a mota da daddare. Da safe na haɗu da Hudu yace zai taimaka mini ashe shi ma mugun ne ya kai ni gidan mata masu zaman kansu magajiyar ta siye ni a dubu hamshin ya tafi ya bar ni."

"Innallilahi wa inna illahir raj'un. Tayaya muryar ki ta dawo?" Mami ta tambayeta cike da tausayi.

"Ban sani ba kawai naga tana son ɓalla ƙafar Hassan ne sai nayi ihu ashe maganar ta fito daga nan ne maganata ta dawo. A can gidan Magajiyar maza da yawa suna zuwa da daddare suna shigo mana ɗakuna ban taɓa yarda ba faɗa muke dasu sai suyi min duka ko a ƙoƙon min baya da sigari " ta faɗa tana son ɗaga rigarta. 

Mami tayi saurin riƙe mata hannu "Ba sai kin buɗe ba mun gani."

Hajiya guduwa nayi da ƙyar sai muka yi karo da wannan Hamma ɗin ya taimaka min ya ƙwace ni daga hannunsu. Don Allah kar ku kore ni in na girma nayi kuɗi zan nemo dangina duk da ban san ta ina zan fara ba.Zan dinga yi muku wanke-wanke da shara da wanki duk wani aiki in kuka saka ni zanyi amma don Allah kar ku kore ni. Mutanen cikin duniyar nan mugwaye ne suna da son kan su kowa amfani yake da wani saboda wani muradi nasu. Ni marainiya ce ku duba maraicina. Nata'ala ya auri ni ne don ya cimma burinsa na mallakar jikina da zama ƴar aiki ga ƴan gidansu ya tafi ya bar ni. Hajiya ta bar ni a gidanta saboda in haifa mata ɗa. Hamma ya biye mata saboda yana tsananin sonta ta kusan kashe kanta sabida ya ƙi yarda da ƙudirinta. Ta raba ni da ƴa'ƴana a lokacin da suke da buƙata ta a kusa da su. Ta bani kuɗaɗe wanda ban san yaya zanyi dasu ba suna cikin ƙullin kayana ban san ma nawa bane sabida ba su nake so ba ahali nake so Allah ne kaɗai ya san abinda yake a ciki zuciyata...." ta kasa ƙarasawa ta kife a gun tana kuka mai ratsa zuciya.

Mami ta kalli Baffa shi ma ita yake kallo.

Haidar kuwa daskarewa yayi a gun yana kallon ikon Allah. Ƴar ƙaramar yarinyar nan ta ga rayuwa ta haɗu da mugwayen mutane selfish people with black heart.

Baffa yace "Kiyi shiru yarinya.Ni nan zan tsaya miki ni ne mahaifinki yanzu. Ki daina kuka ba duka aka taru aka zama ɗaya ba." 

"Na gode Alhaji ina zuwa ."ta fita da gudu. Ɗakin da aka sauketa ta shiga ta kwance kayanta ta ɗauko jakar ƙudin ta koma ɗakin na Baffa.

"Alhaji gashi ka rike kuɗin ni dai kar ka koreni . Naga sai an biya ake taimakon mutum a duniya. Kuɗin da Hajiya ta bani ne."

"Aa zamu yi faɗa da ke ba zan karɓa ba.Bana do domin Allah zan taimaka miki ba don kuɗi ba. Nima fa ƴa'ƴa mata gare ni. Kar kiji tsoron komai. Ba duka aka haɗu aka zama ɗaya ba. Kinga waɗan nan yatsun hannun namu?" 

Ta gyaɗa masa kai tamkar ƙadangaruwa.

"Yadda kika gansu ba ɗaya ba ma'ana kansu ba ɗaya bane to haka mu ma mutane muke. Kowa da halinsa."

"Na gode Alhaji. Na gode Hajiya in sha Allahu ba zaku yi da na sanin barina a cikin gidan nan ba. Daga yau na zame muku tamkar baiwa kuyi yadda kuke so dani nayi ammana na sadakar ."

"Aa ki kira ni da Baffa kamar yadda kowa yake kirana."

"To Baffa."

Haidar a sama mata makaranta daga islamiya har boko bayan bikin nan. Mami ga amanar ƴata na baki daga yau komai nata a hannunki zai kasance ki kula. Naga tana da abubuwan gyara sosai ki sa ido. Ki dinga koya mata."

Mami tace "Na karɓa Alhaji. Allah Ya taya mu riƙo."

"Ameen."

Haidar ɗauki kuɗin nan ka juya mata su.Ƙirgasu nawa ne?

Haidar ya ƙirga kuɗi milliyan ɗaya da rabi.

"Wai fansar abinda tayi musu ne nan.Allah ka shirya ka sa mu fi ƙarfin zuciyoyinmu."

"Ameen Ya ALLAH."

"Baffa ina son kar kowa ya ji wannan labarin. Kawai ace mairainiya ce ka san husumar yan gidan nan sai a tsangwama mata".

"Da wannan kuma." Ya kalli Haidar yace "Jeka mana Aliyu."

Aliyu ya tashi ya fita ba don ya so ba.

"Maminsu gata nan ki haɗa ta da yaran ki kuma gaya musu amanata ce kar wanda ya ci mata zarafi."

"An gama Alhajin Allah." Ta faɗa sigar tsokana tana murmushi.

Shi ma murmushin yayi mata. Suka fita ita da Uwanin Inna ta chiroro.

Mami ta fita tare da Uwani. Nan ta nuna mata ko ina na ɓarin. Duk inda Mami ta sa ƙafa sai Uwani ta saka ta ta.

     A falo suka zauna. Mami ta kalli Uwani tace "Kin iya girki ne Uwani?"

"Aa na iya tuƙa tuwo dai. "

"To kin ce baki je makaranta ba ya batun sallah da karatun sallah?"

"Maminsu Haidar kawai naga ana alwala ana dungura goshi nima hakan nake yi ban san me ake cewa ba fa." 

Mami ta saki salati ta sanar da ubangiji cike da ta'ajubi da tashin hankali tace "Uwani babu abinda kika sani na ibada? "

"Uhm'uhm ba haka ake yi ba ko Mamin Haidar?"

"Tashi maza mu je ki yi alwala in gani ki nunan ma yadda kike sallar." 

Uwani ta shiga cikin damuwa ganin yadda ran Mami yake a ɓace da ita akan batun sallah. Da gaske fa ilimi haske ne ba mamaki yanzu wani kallo ake yi mata na jahila. Yo ai ba kamar bane jahilar ce ita. 

Daga sama Saffiya da Sa'adatu ke saukowa. 

"Mamita baƙuwa kika yi ne?" Saffiya ta tambayi Mami.

"Eh ƙanwa ce kuka samu. Zamu yi magana anjima. Ina zuwa." Ta wuce haɗe da jan hannun Uwani suka hau sama.

Saffiya ta kalli Sa'adatu tace "Na ga Mami a firgice. Me aka yi mata haka kuma wace wannan ɗin?"

"Ban sani ba. Ita yarinyar dai na ganta da safe da Hamma Haidar yace min sunanta Uwani wai."

"Kai su Mami akwai kwashe -kwashe fa. Yanzu wace haka wai Uwani? Kwana biyu rashin zamanmu ya sa bama samun kanun labarai." 

Suka sa dariya tare suka tafa. 

"Muje kar mu makara fa. Duk na fara gajiya."

"Bari ke dai biki budiri."

Ficewa suka yi dukaninsu su biyu abaya ce a jikinsu baƙaƙe. 

Sa'a ce ta buɗe motar da mukuli alamu ita ce zata yi tuƙin.

A cikin banɗaki kuwa Mami ta lura Uwani bata iya komai ba. Tabbas zata jajirce don ganin ta zamo cikakkiyar mutum abar koyi ga kowa,tunda ta umarce ta da ta ɗebi ruwa a buta ta tsugunna ta gabatar da alwala ta kafa mata idanuwanta,tsitsiyar hannu ta wanke,sannan ta wanke ƙafafu ,ta miƙe kurum. Haka suka fito daga banɗakin ta tsaya a tantagaryar ƙasa ta lura motsa baki take kurum ,daga bisani tayi tazarce kawai ta dungura goshinta a ƙasa ta sake miƙewa kusan raka'a shidda ta yi sallar tayi sallama da alamun ko tahiyar bata yi ba. 

"Uwani kin idar da sallar?"

Gyaɗa kai tayi a kunya ce.

"Kina da son ibada amma akwai sauran ki. Shekarunki nawa?"

"Sha shidda."

"Yaya aka yi kika iya wannan sallar?"

"Naga kawai ana yi ne shi ne nima nake yi."

"To in kina jinin al'ada yaya kike yi?"

Tayi dum alamar bata fahimci abinda take nufi ba. Hakan ya ƙara sanyaya guiwar Mami ta gane bata ma san meye al'adar ba. Zata sake tambayarta tace "Mami ina fitsarin jini amma. Yanzu haka ma shi nake yi."

Ras gaban Mami ya faɗi. Tace "Yana miki ciwo in kina yi?"

"Aa".

"Innalillahi,subahanallahi, Uwani wannan ai shi ake nufi da jinin al'adar. Tun yaushe kika fara ma'ana karo na nawa kenan da kika yi?"

"Tun ƙarshen waccar shekarar."

"Wa'iyazubillahi,Uwani kada ki jefani cikin kokwanto na sani ke musulma ce kuma kina cikin jinsin musulmai ko sa kike a ƙauye na sani akwai masu ilimi da marasa imili bare ma yanzu duk an waye ana wayar da kai a kan addini. Me yasa ba kya zuwa makarantar?"

Muna dasu. Lokacin da Abba ya saka ni matarsa ce ta hana ni zuwa dana yi aure kuma Inno bata bari na fita ko ina saboda ayyukan gidan gandu.

"To in kina yi yaya kike yi ki tare shi?"

"Kawai in naga baya daina zuwa sai na saka tsumma na toshe gun."

"Kuma Hajiyar da kika zauna a gidanta bata taɓa lura ba."

"Ban sani ba. Ba fita nake ba. A ɗakin kuma ba tashi nake yi ba."

"To in kika gama ba kya yin wanka kike yin sallah"?

"Yadda ake yin wanka haka nake yin abina."

Mami ta dafe goshinta ta sauke ajiyar zuciya dole a tausayawa Uwani a tallafi rayuwarta daga duhu zuwa haske.

"Uwani ki sani shi ubangiji baya yiwa bayinsa uzuri ga barin ibada domin bai ɗaukewa kowa ba. Ko a cikin jeji kike dole ki nemi ilimin da za ki bautawa ubangiji,Zan saka ki a islamiya za ki samu ilimi mai ɗorewa a cikinta. Ina mai burin kema wata ran ki koyar a cikinta kina so?

"Eh." Tayi murmushi ta sa tafin hannunta ta rufe fuskarta. 

Ki daina jin kunya. Kafin nan zamu magana akan imani;imani yana da kaso hawa-hawa,kamar yadda ki ka yi min bayanin cewar kin ga kawai ana sallah ke ma kina yi yarda da umarni na yi sallah shi ne dirkar farko da mutum zai tanada ba wai kawai kana yin sallah ne domin kaga ana yi ba ko kuma  kana sallah,domin ka da kaga baka yi a nan kin rusa tsayayyar sallar da aka ce sai ta samu sannan za'a rabaka da aikata alfasha sai mutum ya tarbiyantar da zuciyarsa cewa zai yi ne domin biyayya da umarni da Allah subahanahu wata'ala ya bayar sanan kuma yayi imani cewar wata ibada zai yi wacca Allah Ya wajabta masa yayi ta kuma yayi ta da kyakkyawar ikhlasi babu riya a cikinta ya kuma gamsu domin Allah zai yi."

Tuni Uwani hawaye ya gama wanke mata fuska. 

Na fahimci kina zurfin tunani kije kiyi nazari akan bayani na da an gama bikin Saffiya zan sa ki a makaranta.Yanzu ki zo muje ki ci abinci muyi aiki."

"Na gode Mamin Haidar. Wallahi na ƙaru kuma zan yi aiki da abinda kika ce ba zan baki kunya ba in sha Allahu."