ZUCIYAR MUTUM

chapter 20

by @khairatup01

ZUCIYAR MUTUM

NA

Khairatup

Karamci Writers Association.

    Vote@wattpad khairi_muhd.

  
              20.

Wuyan rigar Uwani ta ja da ƙarfi haɗe da miƙar da ita tsaye lokaci guda ta sauke mata mari a saman fuska ji kake ya bada sautin tau mai ƙarfi da gigitarwa. Bata gama dawowa daga hayyacinta ba ta soma dukanta ta ko ina duk inda ta samu babu ƙaƙutawa. 

Uwani kuwa ƙoƙarin ƙwatar kanta take yi amma bata da ƙarfi babu hali bata saba maida martani ba bata iya faɗa ba komai aka ce mata haka zata yi. 

A falon aka rasa mai taimakon Uwani sun yi cirko-cirko kawai suna ganin ikon Allah. Babu wanda hankalinsa ya kai ya fita neman taimako sun gama ɗauke wuta.

"Don ubanki ina kika je da mijina ɗazu,wacece ke ne?" 

Uwani ba zata iya yin magana ba saboda shaƙar da ta yi mata. Idanuwanta sun yi jajir saboda wahala ga shaƙar wuya. Afeeya ta wulwula ta juya ta maka mata naushi a gefen ido ai kuwa Uwani ta sa wani irin ihu tare da kiran "Wayyo Allahna." 

Tuni gefen idon Uwani ya tashi yayi jajir . Afeeya bata san imani ko tausayi ba ta kwantar da Uwani ƙasa ta zauna a kanta. Ta ci gaba da surutai.

"Sai na yi maganinki Wallahi sai kin gane Allah ɗaya ne mijina? mijina kike bibiya me kike taƙama da shi wanan surar ko me?" Kawai ta saka hannu ta ja rigar jikin Uwani daga sama har ƙasa sai da ta yaga rigar nan ya zama Uwani babu riga a jikinta daga ita sai rigar mama da underwear.

Uwani ta daina jin raɗaɗin wancan dukan ƙoƙarin kare kanta take yi kawai wanan wacece? wacce iriyar lukutar masifa ce wanan ba a taɓa ci mata mutunci irin haka ba. Kuka take babu sauti hawaye kawai ki bin kumatunta hawaye daga ƙasan rai ga wanda aka zalinta.

Meenali da gudu ta fita don neman agaji don in ba a kawo taimako ba Afeeya zata iya kashe Uwani yadda idanuwanta suka rufe.

Ƙofar Haidar ta dinga bugawa da ƙarfi aiko da masifa shi ma ya fito a fusace "Uban waye na ci wa ƙuɗi yake buga min ƙofa?"

"Zata kashe Uwani ku ceceta don Allah."

Ai tuni ya sa gudu ya nufi ɓarin Mami. 

Mami a can kuwa sama-sama ta dinga jin kamar hayaniya tashi tayi tace "Hajiya ba kya jin hayaniyar nan tafi kama da ta tashin hankali?"

"Muje mu gani kin san yaran nan ba kai garesu ba."

Uwani ta gama galaɓaita. Haidar yana shiga ya zare idanuwa ganin irin wanan tashin hankalin.

Karaf ya jiyo maganar Saffiya "Ai wai dama Hamma take ƙoƙarin janyewa hankali ya koma kanta? Lallai ki casa ƴar iska shegiya ni daman bata yi min ba..."

Afeeya ji tayi anyi sama da ita an maka da jikin garu tabar ruɗewa da zafi ta saki wani irin ihu da ya gigita mutanen wurin suka juya dan ganin waye.

"Hamma Hai...d.." 

"Afeeya! Innallillahi wa inna illahir rajun. Da ma mahaukaciya ce ke bamu sani ba? Me tayi miki?tun jiya na gaya miki baki da hurumi da yarinyar nan amma baki ji ba Wallahi hukuma ce zata rabani da ke sai kin gane baki da gata."

Afeeya ta tashi da ƙyar riƙe da goshi lokaci guda taji ciwon kai ya saukar mata me tsanani. Da ƙyar tace "Wallahi ina da gata, ina da asali kuma ina da.."

Caumarta yayi ya haɗa da bango ya shaƙe mata wuya ta soma kakari da ƙoƙarin kwatar kanta idanuwa a waje.

Saffiya Da Sa'adatu suka sa ihu suna son kama hannun Haidar suna tsoro kawai sai suka sa kuka suna neman taimako.

Mami da Hajiya da Yafendo kusan tare suka shiga falon da gudu don ganin abinda ke faruwa.

"La'ilaha ilallahu muhammadar rasulillahi sallalahu alaihu wa salam! Me zan gani haka ni Salame?" Yafendo ta faɗa tana dafe ƙirji.

Mami tace "Haidar meye haka ? sake ta baka da hankali? So kake ka kashe ta innalillahi wa inna illahir raji'un Haidar..."

Hajiya ta karasa ta sa iya ƙarfinta ta janye shi daga jikin Afeeya ta sauke mai mari "Haidar ka ci ubanka shegen yaro me baƙar zuciya." 

Yana huci ido jajir jikinsa sai rawa yake yi yace "Saboda me? Saboda me kuke nuna son kai saboda ita bata da gata? Saboda ita talaka ce sai ace za a zalunce ta in kyale? Wallahi sai na sa an ɗaure ki Afeeya."

"Idan kai baka sa an ɗaure Afeeya ba ni zan saka a ɗaure ka Haidar. Ni da kai shege ka fasa a gidan nan." Umma ta faɗa daga bakin ƙofa. 

Falo ya rikice haya-haya kawai kake ji an rasa me tsaida wani. An manta da Uwani baiwar Allah wadda ta fita daga cikin hayyacinta ma.

"Meya faru Haidar wacece bata da gata?"  

"Yafendo kalli abin da wanan yarinyar tayi wa Uwani. Ƙila ma ta kashe ta."

Kowa juyawa yayi inda yake nunawa.

Mami ta saki salati tayi saurin kwance ɗankwalin kanta ta rufewa Uwani jiki da sauri.

"Waye yayi mata wanan abin?"

"AFEEYA!"

"Afeeya ke? Uban me tayi miki? Ashe da ma baki da imani? ashe baki da hankali."

Hajiya ranta ya gama ɓaci tace " Haidar ku kai ta asibiti."

Haidar ya juya yana kallon Saffiya yace "Ke kuma ki jira haɗuwata da ke .Ba aure ba ko me za ayi miki sai na ci ubanki. Kamar ba mace ba kina kallo ana yi wa ƴar'uwar ki mace irin wanan cin mutuncin kike bada goyon baya saboda baki da halin ƙwarai? Tir da wanan ɗabi'a taku ta mata. Kin bani kunya Saffiya yau dai kin sa naji da ma ba ƙanwata bace ke."

Saffiya tayi tsuru-tsuru tana kuka bata san abin zai kai haka ba bata ma san Hamma ya ji furucinta ba ta shiga uku ita kam.

Haidar ya kalli Meenal yace ki samo mata riga ki sa mata da hijab ba zai yuwu muje asibiti a haka ba.

Ya juya ga ƙawar Safiya Mommy ya ƙarbe wayarta.

"Wayata ce fa?"

"Na sani maras mutunci mara tarbiya. Baki yi ƙoƙrin hana faɗan ba amma kin iya yin bidiyo dan ki yaɗa a duniya. Allah wadai da wanan tunanin naki. " 

Tayi ƙasa da kai bata san ya ga tana bidiyon ba kunya ta rufe ta.

"Kalar ka kalar abokan ka. Yau  na gani kuma na yarda Saffiya."

"Don Allah Hamma ka yi haƙuri ka bani wayata.Zan goge." Inji Mommy.

Hadar ya ɓalla mata harara. "kin isa ma ki kiƙi gogewa da ma? Baki isa ba. Shaida recoding ɗin zai zame min a wurin hukuma."

Afeeya cike da bushewar zuciya tace "Ko me zaka yi sai dai kayi amma ina raye ba zan bari wata ta shige ni ba a zuciyar mijina ba. Gwara ma ka sani gida ɗaya,mata ɗaya! Kuma ba za ta samu wannan ba ko da ƙafarta ta hagu."

"Mijinki a ina? Ko kin manta na sake ki saki ɗaya?"

"Ban saku ba Haidar nace ban saku ba. Ai ko ka saken sai na koma ban gama idda ba. Laifi ne don nayi kishin ka."

"Afeeyaaa kishin banza haka ake kishin? Na ga ba sona kike ba ko na gaya miki son ta nake?"

"Ai ba a raba so da kishi,kamar yadda ba a rana ruwa da ƙankara. Kowa ya zo ya ce zai ƙwacen miji ,to ya shirya tafiya da rauni.

"Haidar ka tafi da yarinyar nan asibiti kar ƙaramar magana ta zama babba."

"Yagedo da gaske hukuma ce zata rabani da wannan yarinyar."

"Wallahi nan gani nan bari ehe." Afeeya ta faɗa tana huci babu alamar da na sani a tare da ita.

Gida kowa yayi shiru kamar ana zaman makoki.

Umma ta kalli Mami tace "Yo ni wannan tsatewalar da ake ta wannan tashin hankalin akan ta wacece ne? Ko wanne tarkace aka kwaso sai a kawo gidan nan haba fisabilillahi ."

"Umma budurwarsa ce fa saboda ita ya sake ni."

"Yi min shiru shgeiya marar zuciya mara aji. Ni ?  Ni Zaliha ashe zan iya haifar ƴa a cikina mara lissafi shashasha? Kin bani kunya Wallahi."

"Umma kunya saboda miji...."

"Wacece Afeeya a nan?" Daga waje suka jiyo muryar wata mata kakaura da izza a ciki. Duk juyawa suka yi suna kallonta.

Ta ƙara maimaita tambayar tace "Wacece Afeeya a nan?"

Afeeya ta matso gaba tace "Ni ce Afeeya."

"Mun zo tafiya da ke."

"Tafiya da ita ina?" Inji Umma.

"Caji ofis an kawo mana ƙararta ana zarginta da ƙoƙarin kisa."

"Inji wane shegen?" Inji Umma.

"Hajiya ki gyara kalamanki. Ya kamata ki sani da hukuma kike magana ba sauran mutane ba."

"Waye ya kai ƙarar caji ofis?"

"In mun je kya ji. Amma ki sani in kika ƙara yin wata magana ana zai zama hujja a gareki.Muje Hajiya."

Aka tusa ƙeyar Afeeya aka yi waje da ita daga gidan. Tuni ta raina kanta. Ko da Haidar ke maganar kai ƙararta bata ɗauka da gasken zai yi ba duk da ta san zai aikata ɗin. Amma ita? 

Umma kuka ta saka ta zaro wayarta daga cikin jaka ta kira layin Baffa.

Baffa na ɗagawa yace "Wai me yake faruwa a cikin gidan nan ne?  An kirani wai jami'an tsaro a gidana."

"Alhaji waye zai aiko jami'ai in ba wannan ɗan iskan ɗan naka ba Haidar. Alhaji in baka ɗauki mataki ba na tabbata sai ya ja maka abin kunya fiye da baya. Ni yaran nan zai tozarta a idon duniya?"

"Hajiya Zaliha kalamanki sun yi min tsauri a kunnuwa na. Ai ko ba komai kya yi mini kara....."

"Ni waye yayi mini karar? Ƴa ta fa ya saka aka kama saboda an raina ni sai an nuna mini iykata. Uwarsa na ƙulla mai makirci da kutunguila to ba zan yarda ba."

"Afeeya Haidar ya saka a ka kama? Me yaron nan yake son zama ne? Me tayi mai?"

"Me zata yi mai. Iskanci ne kawai."

"Haba dai Haidar ba haka yake ba dole akwai abinda tayi masa gani nan zuwa gidan dai."

Goyuwa da bayansa zaka yi saboda shi jininka ne ita kuwa agola ce?

Gani nan zuwa gidan. Ya kashe waya.

Umma ta juya ga Mami "Kin haifo mana baƙar ƙaddara. Kin haifo mahaukaci ai dama ina ɗan sholi ina nutsuwa ban yarda ma cewa ya daina shan ƙwaya ba Wallahi ki janzarta ja ma sa kunne ya saka a sakar mini ƴa."

"Amma baki da hankali Haj. Zaliha. Baki da tausayi ai da ma ban yi mamakin hallayar Afeeya ba sun yi daidai da naki. Ya za ayi tayi irin wannan kuma ki goyi da bayanta. Da ta mutu fa? Baki ga wannan ta'asar da tayi ba? Sai son kai kika iya da son zuciya. Komai kika kwaso kice Mamin yara komai ita kiyi ta jifan ɗan ta da suanaye barkatai. Haidar yayi shaye-shaye da na sani duniya ta sani amma kin manta cewa mun san kece kika koya ma sa tun bai saba ba har ya saba yayi degree da masters?  Amma dake Allah Ya fi ki ai sai ya shirye shi ke kuma hakan ne ba kya so saboda kina baƙin cikin shi ne kaɗai namiji?...."

"Dacta kiyi haƙuri don Allah ki kyale maganar nan muje muga halin da yarinyar take ciki."

"Aa Mami taga ana mata shiru ne ko ince taga kina mata shiru ne shi yasa ta rainaki amma ban ga laifinta ba ita kaɗai har da laifin ki da na Baffan."

"Ke munafuka ba da ke nake ba ai da ma na sani ita kike so ni ba..."

"Ya isa haka! Ba kwa jin kunya kuna faɗa da cece-kuce a gaban ƴa'ƴanku."

Falon yayi tsit.

Baffa yace "Ina Haidar ɗin? Kai wai ni meya faru ne a gidan nawa? Kamar ni ne kaɗai mutum a unguwar nan da mutuncina da girmana a unguwa amma kun maida ni abin kwatance kullum ni kullum ni."

"Ai Alhaji baka so a zauna lafiya ba?  Tun daga ranar da ka auro wannan matar komai ya rikice maka. Ka auro masifa..."

"Zaliha!" 

Abba ya faɗa a tsawace irin tsawar da bai taɓa yi mata ba a rayuwarsa. Nan da nan ta shiga taitayinta baki a buɗe tana kallon Baffa da mamaki bata taɓa tsanmmata ba,bata taɓa gani ko ji ba da gaske dai aikin ya karye dole ta kama kanta kafin ta sake sabon ƙulli.