ZUCIYAR MUTUM

chapter 22

by @khairatup01

ZUCIYAR MUTUM...

NA

KHAIRATUP.

Karamci Writers Associations.

Vote @wattpad khairi_muhd.

*

Fitattu Huɗu... Littattafan da suka girgiza zukata!

Daga ranar 10/6/2025, zaku fara ɗanɗana kyawawan kalmomin soyayya, sirri da ƙiyayya pages na farko kyauta!

Wutar Ƙaiƙayi – daga Sanaz Deeya
Wa'adi – daga Cute Hafcie
A Cikin Ido – daga KhairatUP
Tazarar So – daga Nafsal kz

Kar ku bari a baku labari! Ku shiga duniyar da kalma ke ƙona zuciya, soyayya ke fashewa kamar wuta, kuma sirri ke lullube shafi na gaba.

Karanta kyauta, ka kamu da sha'awa, sannan ka biya domin ƙarin zafi!

               22

A daren bayan an kammala shagalin kamu. Aminu ya kai amaryar Saffiya asibiti don duba Uwani. 

Sama-sama ta dubata ba yabo na falasa. Ko cikakken minti biyar basu yi ba suka tafi.
.

Washegari kafin ɗaurin aure Haidar ya je asibiti duba Uwani. Habin ya so ya bi shi amma wani aiki ya taso dole da shi Baffa suka tafi.

Mami ta zuba abinci a fulas ta sa mai a kwando ta ce ya tafi mata da shi can.

Tun daga harabar wajen asibitin ake kallonsa, sam bai damu ba shi fa dama kalar shigarsa kenan,gashi da ma baya damuwa da zantukan mutane. 

Ɗakin da Uwani take ciki ya shiga.Da guntuwar sallama akan leɓɓansa.

Uwani a kwance take amma ba bacci take ba. Jikinta ke mata ciwo, hannun ya matsa mata sosai kun san dai karaya ? 

Amsa masa sallamar tayi a hankali tana cije baki. 

"Sannu." Ya faɗa kaitsaye a gajarce.

"Yauwa Hamma ina kwana?"

"Lafiya lau Ummu. Yaya jikin naki?Meye yake yi miki ciwo?"

"Hannun ne kawai amma na sha magani. Zai warke."

Ya ji tausayinta. Ya ja kujera ya zauna a kai. Kwandon ya ajiye a gefe yace "Kin ci abinci kenan?"

"Eh wannan nas ɗin ta bani abinci. Bata da matsala."

"Yi haƙuri na makara ban kawo miki da wuri ba. Kin san yau za ayi ɗaurin auren Saffiya ana ta hidima,jiyan ma na so zuwa amma na gaji naje wurin Kamu. Ah! Yauwa! Saffiya ta zo kuwa?"

"Eh! Ita da mijinta."

"To. Na ɗauka rainan hankali ta yi. "

"Hamma kana son saka waɗanan kayan a jikin ka. Ba taɓa ganin ka da manyan kaya ba tun wancan ranar farkon da na gan ka har ka taimake ni kuma sun fi yi maka kyau da cikar kamala."

"To ni waɗan nan nake so su na ga damar sakawa. Kun fiye sa ido Wallahi." 

Shiru ta yi kamar ba zata yi magana ba sai kuma ta ce ma sa " To ai gaskiya ce muke gaya maka. Manyan kaya sun fi maka daraja. Ka dinga sawa musanmman in zaka fito."

Kallon ta ya yi da kyau tuni ya ƙanƙance ido ya yi mici-mici dasu a tausashe cikin kalma guda yace "Bana so, Ummu Bana son sa ido."

Uwani bata ƙara cewa komai ba.

Haka ya gama zamansa ya tashi ya saka hular nan facingcap.

"Na tafi sai dare zan dawo kuma. Zanje na shirya lokacin ɗaurin auren ya gabato. Allah ƙara sauƙi."

"Amin. Na gode, gaishe da Mami."

"Zata ji."

Bayansa ta bi da kallo. Sai ƙofa da ke ta motsi ta yi gaba ta yi baya har ta daina ta tsaya cak. 

Idanuwanta suka cika da ƙwalla. Duk fa rashin gata ne ya jawo mata da ace yau iyayenta na da rai da yau ba za a rasa wani a gefenta ba . Ta  jima tana jinjina zafi da raɗaɗin ciwon rashin mahaifanta biyu a rayuwarta sai dai yau jin kewarsu take yi sosai.

Fuskar yaranta taga ya gilma mata ko a wanne hali suke ciki yanzu,ko sun manta da ita? Dariya ma maganar ta bata ya ba za su manta da ita ba? Hawayen fuskarta ta share. Ta koma ta kwanta da baya zuciya na yi mata ciwo.

*

"Wai ina ka tafi ne?"

Ba tare da ya kalle shi ba yace "Wurin Ummu naje. Na je na ga yanayin jikinta ne." Ya faɗa yana ɗaura agogonsa.

Habib yace "Wacce haka ne ?  Tunda na zo kake zancen yarinyar a ina take?"

"Amanata ce!"

"Amanar ka kuma?"

"Habib ko za ka bari mu dawo daga ɗaurin auren nan ne ko kuma na zauna mu ci gaba da hira?"

"Uhm Allah Ya baka haƙuri, Muje Amma fa  kayan  nan sun maka kyau. Kai sai lokaci-lokaci ake ganin ka da manyan kaya."

Yamutsa fuska ya yi yana kallon kayan ta mudubi ,yaga sun mai kyau. Hular yake jujuyawa ya rasa ta ya zai kafata saboda gashin da ya taru a kansa yayi yawa. Aski yake son yi amma babu lokacin hakan.

"Baffa ne ya ɗinkan."

"Baffa na ji da one boy ɗin nan." Suka tafi suna dariya.

Bayan azahar aka ɗaura auren Aminu da Saffiya kan sadaki mai daraja.

Gida ya cika. Hakan ya saka Haidar da Habib da sauran abokan wasansu suka yi ƙaura daga gidan. 

Amma ko da aka yi la'asar Haidar kasa zama ya yi gabaɗaya hankalinsa na kan Uwani. Ganin hirar banza kawai suke yi ya saka ya tashi ya ce "Habib bara naje na dawo."

"Zuwa ina?"

"Asibiti zanje."

"Wurin Ummu?"

"Eh!."

"Zan bi ka."

"To tashi muje."

Haka suka tafi su biyu ,Haidar ne ya ke tuƙa motar.

*

Tunda suka shiga cikin asibitin ya ji wani yanayi ya shige shi,gaban shi ya buga da ƙarfi har sai da ya tsorata da hakan. A fili ya furta "Ya salam!." 

"Mene ne?"

"Babu komai."

"Ka tabbata?"

"Eh babu komai,muje."

Tare suka shiga ciki suna yan hirarakinsu. 

Har suka isa ɗakin.

Da sallama suka shiga. Tun da suka nufo ɗakin ya ji bugun zuciyarsa ya tsananta fiye da baya. A hankali ya taka ƙafarsa ya bi bayan Haidar ciki.

Uwani kuwa fuskarta na kallon baya ne ma'ana ta bawa ƙofar baya. 

Bayanta Habib ya bi da kallo a kowacce daƙiƙa yana jin wani irin bugun zuciya. Uwani ce ta faɗo masa  a haka kamar Uwani, amma ya sani babu abinda zai kawo Uwani Gombe, Gomben ma gidansu Haidar ajiyar  zuciya ya sauke.

Haidar ne ya juya ɓarin da take ya tsugunna ganin kamar bacci take. Nan kuwa allura aka yi mata saboda ta huta don hannun ya matsa mata sosai ta kasa bacci. 

Kallon tausayi yake yi mata. A hankali yace "Habib bacci take."

"Ayya! Allah Ya sauwaƙe ,Ya sa kaffara."

"Ameen. Amma garin yaya ta yi wannan raunin?"

"Afeeya mana."

"Afeeya kuma?"

"Eh! Afeeya." 

"Me tayi mata haka?"

"Kishin banza mana."

"Ikon Allah kishi! Amma me ya sa? Farko ma ina ka samo ta?"

"A k..." 

Uwani ta soma motsi tana son juyawa .

Da sauri Haidar ya kuma tsugunnawa yace "Sannu Ummu. Yaya jikin?"

A hankali tace  "Da sauƙi. Ka dawo?"

"Eh ! Na dawo."

"Allah...sanya...alkairi."

"Ameen. Ki kwanta ki huta , naga allurar bata sake ki ba. Bara na koma da safe zan dawo."

"To".Ta faɗa. Tana jin kamar ƙamshin turaren Hamma Habib a ɗakin sai dai ta sani babu abinda zai kawo shi garin da take. Wani sabon miƙi ne ta ji ya taso mata. A hankali ta lumshe idanuwanta ta rufe su ruf lokaci guda bacci ya kuma ɗauke ta."

Fita suka yi daga ɗakin. Habib na ƙara juyawa don kallon ɗakin da bayan Uwani da kallo irin kallon nan mai cike da tarin tambayoyi da wasi-wasi.

*

Bayan sati ɗaya aka sallamo Uwani daga asibiti. Ɗakin da yake a ƙasa Mami ta saka aka gyarawa Uwani. An sa mata gado ɗan matsakaici an shirya ɗakin dai yayi kyau sosai. 

Da akwai banɗaki a ciki. Da kayan kwalliya an zuba mata.

Wasu lokutan tana ganin Haidar wani lokacin ba ganinsa take ba ya koma bakin aiki. Allah-Allah take ta warke ta shiga makaranta kamar yadda Mami ta ce mata. 

Afeeya kuwa bata ƙara shiga harkar Uwani ba ko barin Mami bata zuwa shi kan shi Haidar ɗin bata ƙara sa shi a idanuwanta ba, so take sai ta sake shiri tukunna.   

*

Hijabin jikinta dogo ne har ƙasa ko ƙafar ta ba a gani bare takalminta sai jan ƙasa yake. Kalar hijab kalar sararin samaniya ne.Gashinta a tsefe yake hakan ya saka yayi cika a baya kamar acuci maza kamar yadda ake faɗa.

Hannunta jaka ce baƙa tana tsaye da alamu akwai wanda take jira a farfajiyar gidan. Niƙabi na hango ɗaure a saman kanta. 

Da ma can Uwani akwai kala mai kyau. Samun hutu da cima mai kyau da amfani da mayuka da sabulai masu kyau ya saka ta ƙara yin kyau fttar ta har sheƙi take yi. Kalar bakinta kuwa ja ne tamkar ta shafa jambaki ja. Asalin ƙirar Uwanin Chiroro ta fito diri ne mai  sunan diri irin dirin nan da ake kira coca-cola shape.

A cikin shekara ɗayan nan rayuwar Uwani ta sauya , nutsuwa da nagartar ta sun ƙara bayyana. Uwani sai ta zamo kamar wata zara a cikin mata da ma can ba ta da hayaniya bata kuma da son tashin hankali. Kana ganin fuskarta ka san mace ce mai sanyi. 

Daga sama Mami ta leƙo tace "Salma jiran me kike yi har yau baki tafi ba ko ba kya duba lokaci?"

"Mami Meenal nake jira fa. Daga ɗauko jakarta shiru kamar malam ya ci  shirwa."

"Kuna son yi latti ne kawai. Zan gayawa Haidar ne ,na ga kwana biyu abin naku ya fara zama wasa."

"Mami kiyi haƙuri don Allah! Hamma zane mu zai yi kin sani."

Mami zata yi magana Meenal ta fito. 

Ta kalli inda Uwani ke kalla . Mami ta hango a ta balcony tuni tayi saurin jan hannun Uwani suka yi gaba.

"Kullum sai kin sa mun makara yanzu."Uwani ta faɗa tana zumburar baki.

"Kiyi haƙuri. Jakar na nema na rasa fa."

"ke kika sani."

Haka suka tafi suna hira. 

Suna isa suka shiga ciki. Ajinsu suka shiga kaitsaye. Ba jimawa malaminsu ya shigo yi musu ƙarin alqurani.

Bayan sun gama karatu misalin ƙarfe shidda da rabi suka shigo gida. A gajiye suke baren ma Uwani da ke ciwon ciki alamu baƙonta na wata ne zai zo. Sai cije baki take yi.

"Sannu Ummu. Yanzu zamu shiga ai ki samu ki sha ruwan zafi da gishiri kaɗan za ki ji salama."

"Uhm. Wallahi ji nake kamar bayana zai ɓalle."

"To ya za ki yi ? Haka muke mu mata kullum muna fuskantar abubuwa."

Haka suka isa ciki. Tunda ta shiga ta ji ƙamhshin turaren Hamma Haidar.

Can ta hango shi a ƙasa da takardu a gabansa yana rubutu gefensa laptop ce. 

"Salamu alaiku".

"Wa'alaikum salam." Ya amsa musu ba tare da ya kalli inda suke ba.

"Hamma ina wuni."

"Lafiya lau."

Meenal dai tunda suka gaishe shi ta shige nata ɗakin.

"Yaushe ka dawo Hamma?"

"Ummuuuu..." ya faɗa da ɗan ƙarfi kaɗan.

Ta kama bakinta sai kuma ta zauna kan kujera mai zaman mutum ɗaya ta cure a guri guda ta dunƙule kamar wata mage. Tsabar azabar ciwon da cikinta yake yi mata ne. Kuka ma take son yi amma tana tsoron Hamma Haidar don baya son kuka.

Shi kuma yana lura da ita a ankare yake da motsinta. 

"Cikin ne Ummu?"

A hankali ta buɗe ido ɗaya ta kalle shi a ɗan sace , ta san zai gane dama amma bata san da wuri haka ba.

'"Akwai zafi sosai Hamma".

"Sannu. Ta shi ki je kiyi wanka da ruwan zafi kiyi pressing wurin." 

Kunya ta kamata ,ta kuma sunne kai a tsakanin ƙafafuwanta.

"Kunya da gaske?"

"Hamma!"

"ok fine." Ya faɗa ya ci gaba da aikin da yake yi. Amma yana lura da ita. 

Saɗaf-saɗaf ta tashi ta wuce ɗakinta da gudu. 

Murmushi ya bi bayanta da shi. "Silly girl".

A nan ta bar jakarta.
*

AFEEYA!