Chapter 23
by @khairatup01
ZUCIYAR MUTUM...
NA
KHAIRATUP
Karamci Writers Association.
Vote @ wattpad khairi_muhd.
23.
Afeeya tana son zuwa Abuja wurin ƙawarta Ifeoma amma Umma ta hanata zuwa. Gabaɗaya ta kasa yarda har yau Haidar ya kasa maidata ɗakinta. Gashi bata kwantar da hankalinta ba bare ta samu wani ta aura. Kusancin Haidar da Uwani ya fara bata tsoro tana lura mafi yawan lokuta Haidar a ɓarin Mami yake wuni musamman lokutan da Uwani take gida hakan ba ƙaramin baƙanta mata rai yake yi ba. Sun yi waya da ƙawarta Ifeoma kuma ta bata tabbacin tana da malami mai zafi wanda aikinta zai ci yadda ya kamata. Sha yanzu magani yanzu.
Kullum ƙwaƙwalwarta a tunanin yadda zata fita take.
*
Kano.
Kin san ba zaki iya kula da yaran nan ba kika rabasu da uwarsu? kullum babu abinda kika iya sai yawo da gantali? babu abinda kika sani sai kan ki baki san farincikin kowa ba sai na ki ke kaɗai? Aisha me yasa kika sauya ne? Shekaru nawa muna roƙon Allah Ya bamu haihuwar kuma Ya bamu maimakon ki gode ki riƙe su da amana da kula da soyayya irin ta uwa amma kin gaza? To saurareni kiji zan kwashe su na maida su wurin Hajiya ita zata iya kula da su.
Haba Habib na gaji! Na gaji fa. Kullum magana ɗaya. Twins yanzu yara ne? Nono suke sha ko me? ga nanny na ajiye musu da aikin zan ji ko rainon su? Ka kai su gun Hajiya suyi me? Naga ita ma ba zaman take ba mace ce mai neman na kanta ku ma da haka kuka girma baku mutu ba suma ba zasu mutu ba.
Ƙarya kike yi ki haɗa kan ki da Hajiya. Hajiya ba irin ki bace. Tana da lokacinmu ko a yanzu ma tana da lokacinmu.
Baki ta buɗe tana kallonsa da mamaki. To wai me yake so tayi masa ne?
Kaga Habib ka daina kwane-kwane na gane me kake nufi na fahimci inda ka dosa. Aure kake so kayi shi ne ka biyo ta nan, to saurare ni da kyau, ni nan da ka gan ni nice daga ni ba ƙari daga ranar da ka yi kuskuren kawo wata cikin gidan nan sai na kashe ka na kashe ta in yaso nima a kashe ni ko nayi gidan yari kaga ba wan ba ƙanain. Ka san halina ka san wacece ni tsab zan aikata hakan da na faɗa. Saboda haka kayi nazari da kyau ka nutsu.
Na gane kin gama raina ni. Kuma gani kike yi wai ke ɗin tsoronki nake ji ko shakkar ki nake yi. Ba haka bane idanuwana sun buɗe yanzu, da ne suka rufe in ma magani kika yi mini Shatu maganin ya karye ya lallace. Na dawo hayyacina zanyi aure kuma za ki zauna da ita ko ki fita ki bar mata gidan ai igiyar a hannuna take ruwana in riƙeta ruwana in datse ta kuma babu wanda ya isa ya hana ni yanke hukuncin da nayi niyya.
Babbar bara.... "Kai Habibu " ta faɗa tana cakumar rigarsa da kyau tana kallon sa ido cikin ido ta ci gaba "Wallahi! Wallahi! Allah ɗaya kenan ƙarya kake yi , na ce ƙarya kake yi. Na fi ƙarfin ka kuma dole ne ɗankwali ya ja hula bana boka bana malam amma na yarda da kaina da makamaina."
Fincikar rigarsa ya yi ya sa hannu ya ɗauke mata fuska da mari. Bai bari ta farfaɗo ba ya kuma sauke mata wani marin ya nuna ta da yatsan sa "Hauka kike taƙama da shi da rashin sanin ciwon kai da tarbiya ya kamata ki koma islamiya ki sake zaman aji. In taƙamar ki masifa ni nan na fi ki , kyale ki nake yi amma naga abin naki ƙara gaba yake yi. To saurare ni da kyau ni Habib zan yi aure kuma zan tare da ita kuma zan zamu zauna lafiya kina ji , kina kuma gani baki isa ki yi komai a kai ba."
"Ƙarya ne! Baka isa ba."
Fita yayi ya barta a wurin.
Tsugunnawa tayi a ƙasa ta zunduma wani uban ihu kamar wata zararriya ko dangin fafaroma.
*
Tun da ya karyo kwana ya hangi wani a ƙofar gidan a gefe kuma Uwani ce da hijabi a jikinta. Wani irin ɓacin rai ya ji ya ziyarce shi.
Da ƙyar ya ƙarasa. Megadi ya buɗe mai ya shiga ciki. A farfajiyar gidan ya faka bai ma gyara faking ɗin yadda ya kamata ba ya fito.
"Ummu." Ya faɗa da ƙarfi .
Tuni jikinta ya soma rawa ta kalli saurayin tace 'Don Allah ka tafi Hamma na ya dawo. "
"Ai na fi son ma da ya dawo ɗin kin ga sai na gabatar masa da kaina." Ya faɗa yana murmushi.
Uwani da ta tsorata ta haɗe hannayenta biyu tace "Don Allah ka tafi. Kaga na gaya maka baya son mu dinga zance sai mun gama makaranta ban so ya dawo ya gan ni ba."
Ganin ta rikice ya sa yace "Shi kenan sai anjima, amma ki nutsu don Allah na ga duk kin ruɗe babu abinda zai yi miki. Sai gobe."
Bata ma tsaya ta ƙarasa sararonsa ba ta shige ciki jiki na rawa.
"Waye wancan?" Ya tambayeta kaitsaye.
"Wani ne."
"Sarai kin gane tambayata. Sau nawa na gaya miki bana so naga kina zance? karatu za ki yi ko soyayyar banza?"
"Aa kayi haƙuri Hamma ba soyayya muke yi ba kawai.."
Tsawa ya daka mata haɗe da nuna mata hanyar shiga ciki. Da gudu kuwa ta shige ciki.
Mami da Baffa na hirarsu kawai suka ganta a guje.
Mami tace "Lafiya Ummu ke da waye?"
Kusa da ƙafar Mami ta ƙarasa ta tsugunna. Tana haki.
Sai ga Haidar ya shigo kana ganinshi ka san yana cikin ɓacin rai.
"Au ca za ki yi Haidar ne ya biyo ki. Ni dai zan ga ranar da Haidar zai girma."
Baffa yace "Haidar yaushe zaka yi hankali?"
Kallon Baffa yayi yace "Haba Baffa a gaban Ummu zaka gaya min haka salon ta ƙara raina ni ? Dama ta raina ni." Ya faɗa da zallar bacin rai kwance a muryarsa.
Mami tace "To ƙarya aka yi maka? Kayi hankalin ne? Girma kake amma kana ƙara cin ƙasa. Ba zaka dinga takurawa yarana ba ka hana yara sakat. Ka ji da baƙin halinka kai ɗaya mana. Ni Wallahi Baffa gwara ka yi masa aure ya ƙarata can ni na gaji da halinsa."
Baffa ya yi dariya yace "Ku na son ku dinga taro faɗan da ba ku da ƴan wasa. Zo nan Aliyu na, gaya min waya ɓata maka rai na san dai daga wurin aiki kake ko a can aka ɓata maka rai?"
"A'a Baffa. Ummusalma ce."
"To ka ce yau abin naku ne. Me ya faru?"
"Baffa bata ji. Bata jin magana."
"Me tayi maka?"Baffa ya tambaya yana murmushi.
"Baffa na hana su kula kowa basa ji na fi son ta samu ta kammala karatu tukunna amma bata ji ta raina ni."
Baffa yace "Bata kyauta ba,amma ai ka san dole ta dinga kula samari ko? Wata ran ai aurar da ita za ka yi."
Kallon Baffa ya yi kamar zai yi kuka. Amma ya cije bakinsa ya haɗe rai sai kawai ya tashi ya bar falon fuuu kamar iska.
Baffa ya yi murmushi ya kalli Mami ya kuma kallon Ummu.
"Ummun Haidar ki kiyaye ɓata ran Hamma ɗin ki. Ya fi so ki yi karatu ko don goben ki saboda haka ki maida hankali."
Uwani tace "In sha Allahu Baffa."
"Tashi ki shiga ciki."
Bayan ta shiga ciki ya kalli Mami yace "Yaron nan na lura kamar yana son yarinyar nan ne."
Mami tace "Haba dai wane so kuma ana zaune ƙalau? Kawai dai takura ce irin ta Haidar."
"Hmm! Ashe ma baki san ɗan naki ba. To za ki ce na gaya miki nan gaba."
"Ikon Allah. Ai ni nafi son ya yi auren sama da shekara amma yaki aure tunda ya rabu da Afeeya."
"Ai shi aure lokaci ne Mamin yara. "
Allah Ya kai mu da rai da lafiya.
Baffa ya amsa da amin.
ƁILLIRI.
Dada ce zaune kan tabarma, albasa take yankawa zasu yi dambu. Amma hankalinta ba ya nan kafin tayi aune ta yanke hannu da wuƙa da sauri ta saki wuƙar tana salati tana yarfe hannu yadda jini ya soma zuba. Tashi tayi da ƙyar ta isa gaban buta ta ɗauko ta jijiga taji babu ruwa a ciki dole sai ta jawo a rijiya. Gashi gidan babu kowa.
Ta ɗauko guga kenan sai ga Nana ta shigo da sallama halin da ta ga Dadar ta a ciki ya firgita ta da sauri ta amshi gugar ta soma jan ruwan ta zuba a wurin ciwon ta wanke mata, madafi ta shiga ta ɗauko gishiri ta barbaɗa mata a wurin.
"Dada garin yaya?"
"Nana tsautsayi ne kawai. Ina yanka albasa ne na yanke hannu ba wani ma zurfi ne da ciwon ba."
"Wanne ba zurfi daman haka za ki ce ,na san kina can kina tunanin abinda ya shuɗe ya kamata ki sauƙaƙawa kan ki haka , kika sani ma ko sun rasu shekaru goma sha bakwai fa kenan Dada. Da suna nan ai da sun zo."
"Nana bana san haka gaskiya ki tashi ki bani wuri."
Shiru Nana tayi tana kallon mahaifiyarta , tausayi take bata amma basu da mafita anyi neman duniya ba a samu Gwagwonta ba bare Baffajo amma Dada ta kasa fawalawa Allah ta kasa yarda da cewa sun rasu don irin wannan shirun in yayi yawa ba na lafiya bane.
"Shi kenan Dada Allah Ya baki haƙuri ya huci zuciyrki, Allah Ya bayyana miki su."
"Ameen."
Nana ce ta tashi ta ƙarasa girkin ta share gidan tas ta wanke bayi. Komawa tayi ta zauna suna hira da Dadar take gaya mata ai Meenali tace zata zo cikin wannan satin."
"Ya kamata ki shirya mata kam."
*
MINNA.
(CHIRORO.)
"Kai malam tashi zaka yi ka nema mana abinda zamu ci , tayaya ina nan ina fama da ciki ga wannan shi ma ka sani ba haƙuri yake da shi akan ciki ba amma ka wani zo ka naɗe hannu a ƙirji kana bacci. Wallahi sai ka fita ka nemo ehe."
Tsaki ya buga ya tashi a fusace ya kalle ta "Jaraba kawai na auro mai baƙar ƙashi. Kin wawashe min dukanin wani abu da na samo ai ni kam na yi da na sanin aurar ki yasin."
"Ahaye! Yay! Sannu butulu sannu tantiri yo ai daman in baka yi haka ba baka cika namiji ba da sai an sauya maka suna daga namiji ka koma Hajara. Kai ba ai kai ɗan kunama ne. Ni nan ni nake da na sanin auran ka. "
"Ke..." ya soma ƙoƙarin yin faɗa da ita yana kama mata wuyar riga ita ma tana son cakumo masa kwalar riga kowakwa ya ƙaure a ɗakin bai yi la'akari da cikin jikinta ba bai duba ita mace ba ce ba da alamu ma dai sun saba damben.
Ɗaga labulen ɗakin aka yi hasken rana ya shiga cikin ɗakin aka soma magana faɗa-faɗa.
"Yau na ga abinda ya ishe ni gatalallu shegu ,baku da aiki kullum sai gwada kwanji ku ƴan iska. Ku na gaji da halinku kullum faɗa kamar zakaru ko kuku kaɗai ne a cikin gidan nan."
Nata'ala ya juya ya kalli Inno ya saki wuyan Mari yana tsaki.
Mari kuwa ta juya ta kalli Inno ta fara aika mata da saƙon harara kafin tace "Ga nan babban gatalalle ,wahalalle ,ɗan iska,matsiyaci, me ake da auren irin wannan mutumin na auro wa kaina bala'i da masifa."
Inno ta kama haɓa tace "Ah wannan baki da kunya ba a gasa miki bakin ki ba kin ko karanci biyayya wa miji ko a haka aka haife ki aka yasar a titi?"
Gashi nan wannan shi aka haifa a gantale. Be iya juya taro ya bashi sisi ba kullum yana ɗaka kin kashe mai zuciya kina kawo mai abinci ba zai fita ya nemo ba. To tunda haka ne a bani abinci ko na kai ƙara Wallahi.
Inno ta gaji da halayen Mari a lokuta da dama tana cewa da ma Uwani na nan. Saboda haƙurinta da ɗauke kan ta duk yadda suke taka ta bata cewa uffan bare ta kalle cikin idanuwansu. Amma wannan matar da ya auro ga ta nan ta adabi kowa a cikin gidan.
"Ga shi nan ai Nata'ala ka auro ƴar marasa kunya sai ka jura."
"Haba Inno duk ba ku ne kuka kori Uwani ba ?..."
"Dakata shege! Don uwarka sai yau ka san an kori Uwani? Nace sai yau ka san an kori Uwanin don uwarka?"
"To ba wancan ɗan hau ɗin ne ya yi ƙoƙarin keta mata haddi ba kina kallo ta gudu amma ba ki masa komai ba?"
"Ubanka zan mai? Kai zo ka bar gidan nan ma."
Yana ƙunƙuni ya sa silifas ɗinsa daga ƙasa ma ya tauye ya cinye saboda tsufa , ya kalli Mari ya nuna ta da yatsa yace "Hawainiyarki ta kiyayi ramata." Ya fice.
Ta bishi da ihu "Wooo faƙiri mai ci da arziƙin mace mun san komai, da ba a san asalin balbela ba da sai ace daga masar take."
Inno dai sa kai ta fita daga ɗakin.
Nata'ala bayan ya karɓi kuɗinsa daga wurin Hajiya Aisha.Mari ma ta karɓi na ta kuɗin suka yi sallama da Aisha suka bar gidan da sun sami gida na haya a cikin gari a Kano suka zauna da farko komai lafiya lau ne ana ta watayawa da kuɗi a ci banza ci wofi a tunaninsa kuɗin ba zai kare ba be yi tunanin ya nemi sana'a ya sa kuɗinsa yana juyawa ba ,burinsa kawai ya fantama ya wala ya wataya ace masa mai kuɗi. A haka suka shekara har Mari ta haihu ta haifi namiji bayan nan suka je Chiroro ganin gida. Kwanansu bakwai suna wasan kuɗi a gidan da garin yana fafa shi yayi kuɗi a birni suka koma Inno na ta ɗaga kai a gari ɗan ta yayi kuɗi iskanci da rashin mutuncin ta ya karu. Nata'ala baya maganar Uwani saboda ya san Uwani na birni a gidan Hajiya Aisha.
Bayan sun koma ya haɗu da wani mutum suka kulla abota da juna ya dinga yi masa famfo su saka kuɗi za a juya musu a kasuwa ya saka kuɗi da farko aka ba shi riba mai yawa ya ji daɗin kasuwancin. Ya kuma kwasar wasu ya saka sai dai tsahon watanni biyar babu labari aka zo aka ce jirgin da aka kawo kaya ya nutse ana nemansa.
Daga nan fa rayuwa ta fara juya masa baya har ta kai kuɗin hayar ya taho karewa ,gashi babu kuɗin shi ba zuwa kasuwa yake ba bai san sana'a ba bai san aikin ƙarfi ba ci da kashewa kawai ya sani ita kuma Mari ba ta kwaɓar sa sai dai ta taya shi kashewa ita matar mai kuɗi ce.
Har ta kai yanzu abinda zasu ci ma wahala yake yi masa haka ya saka ya tattara ya koma asalin garinsu Chiroro. Tun da suka koma fa bala'in yau daban na gobe daban bata ganin girmansa bata ganin mutuncinsa kullum suyi ta faɗa Innon ma ta raina ta babu wanda take ragawa a gidan sun so juya Mari yadda suke yiwa Uwani dan ta fi su tijara. Sai suka ja bakinsu suka yi shiru ko an zuba mata ko ba a zuba mata ba in aka gama girki zuwa take ta ɗauki na koma waye ta ci ita da ɗanta don bata jurar yunwa saboda cikin jikinta.
Tun jiya da ya ga Uwani da Malaminsu yake jin wani iri a ransa. Ya kasa sukuni gabaɗaya wayarsa ya kalla ya kai sau biyar amma ya kasa kiran Uwanin.
Yana nan a zaune yaji takun tafiya. Juyawa yayi ya ga Meenali ce a bayansa. Juyawa yayi ba i ce komai ba.
Meenaln na zuwa ta tsuguna ta gaishe shi.
"Barka da yamma Hamma."
"Barkanmu Meenal ya karatun?"
"Alhamdullilahi."
"Yayi."
"Hamma! Da ma tafiya zamu yi Billiri zamu wuce sai wani satin zamu dawo za ayi bikin Hamma Abubakar."
"Na sani. Amma da wa zaku tafi na ji kina jam'u"
"Ni da Ummu zamu tafi."
"Ummu dai?"
"Eh!."
"Ina Ummun take yanzu?"
Tana wurin Mami suna haɗa kayan da za a kai wa Yafendo.
Waye zau ka ku?
Hamma Joɓe ne zai kai mu.
To Allah Ya kiyaye hanya.
Amin.
"Yarinyar nan ta raina ni tayi min laifi , amma bata damu ba bata gaya min zata yi tafiya ba? lallai ta raina ni kam nima ba zan kula ta ba bazan neme ta ba tunda nima bata neme ni ba." Yayi tsaƙi ya fi a ƙirga.
Kusan mintina goma sha biyu yayi a nan a zaune daga bisani kuma ya tashi ya kasa daurewa ya kama jiki ya bi ɓaroin Mami nan ya hango su suna sallama zasu shiga mota. Kallo ya bita da shi ta masa kyau wani haske ya ga ma ta yi. Atamfa ce ya saka tayi ɗaurin nan na zara buhari gashin ta ya fito ta baya. Mayafin a ƙafaɗa ta ɗora wani irin kyau yaga tayi masa tambayar kansa ya soma me yake damunsa ne? Yana kallo tana kallonsa amma ta ƙi yi masa magana in yaga daidai ma ɗauke kai tayi. Ba dai fushi take dani ba? Ya tambayai kansa...