ZUCIYAR MUTUM

chapter 24

by @khairatup01

ZUCIYAR MUTUM...

NA

KHAIRATUP

Karamci Writer Association.

Vote@wattpad khairi_muhd.

Maryam isma'il,cyamatu,Mamah 2007,nafshe,Wannan shafin naku ne kyauta.Na gode muku da soyayya.

                      24.

Mennal zata shiga ciki ta ce "Hamma mun tafi".

Bai samu zarafin amsa mata ba tunaninsa na ga rashin kula shin da Ummu tayi duk sai ya ji kamar ba shi ba.

Mami ta kalle shi tace "Ana magana fa."

"Na'am Mami."

Mami ta harare shi ta shige ciki abin ta.

Joɓe ya kunna mota yana reverse ,kawai ganin mutum yayi a gabansa. Tsayawa yayi yace "Haidar lafiya?" 

"Lafiya lau buɗe min gidan gaba tare zamu tafi." Ya tsinci kansa da faɗar haka bai san ma ya faɗa ba. 

Joɓe bai musa ba ya buɗe masa ya shiga. Gogan kuwa sai kallonta yake ta mudubi amma ko da wasa bai ga idonta ba bare ya ji muryarta.

Kirjinsa har wani dukan uku-uku yake yi "innallilahi na shiga uku ni Aliyu wai soyayya na fara da girma na har ta sa na fara rasa kaina." ya tambayi kansa da kansa yana jin wani irin tashin hankalin rashin kula shin da Ummu tayi gabaɗaya a takure yake ya daina gane komai.Joɓe na yi masa magana amma baya gane me ya ke faɗa tunanisa da ruhinsa yana ga Uwani.

Uwani kuwa tsabar miskialanci bata jin yin magana ma. Wayarta take dannawa game take yi kuma da gayya ta ƙi ɗaga kanta ta kalle shi haushinsa take ji tun shekaran jiya da ya hanata zance.

Haka suka je Billiri motar dai gata nan gata nan babu daɗi.

  Tun da suka shiga garin take kallon ko ina garin ya burgeta wani abu na daban take ji a kan garin wanda bata san dalili ba.

Ga gonaki ,ga masana'atu nan ana yi kala-kala, kiwo,ƙira,noma abubuwa dai gasu nan.

A ƙofar gidansu Meenal suka faka motarsu. A hankali suka fito daga ciki.

Tuni Yafendo ta fito daga gida bayan taji tsyauwar mota tana musu maraba da sauka sai a lokacin Uwani tayi dariya ta tsuguna ta gaida Yafendo. 

Yafendo ta haɗa su ta rungume tana murnar ganinsu.

Haidar kuwa wata ajiyar zuciya ya sauke da ya ji muryar Ummu ya lumshe idanuwansa.

Ciki suka shiga tare. Ta shimfiɗa musu tabarba ta ɗauko mafitai ta basu. Bata zauna ba ta ɗauko kwanon sha mai kyau ta soma dama musu fura ɗayan kuma ruwan randa ne ta zuba musu a ciki.

"Barkanku da isowa ya gajiyar hanya Haidar?"

"Alhamdulillahi." 

"Lallai na ji daɗin zuwan nan na ka Haidar. Na ɗauka sai ran ɗaurin aure zaka zo ashe kana nan tafe."

"Eh na gaji da zaman gidan nace bara na biyo su amma ai yanzun nan zamu koma ni da joɓe."

Joɓe ya kalle shi yace "A tunanin ka wai yau zan koma?  Lallai zaka koma  a motar haya kuwa don mu nan mun zo sai an ɗaura aure zamu koma."

Kamar ya maka mai mari haka ya ji. "Amma shi ne baka gaya min ba ka bari na biyo ku?"

Dariya sa mai. "YO ni ya za ayi na sani? Ganin ka fa kawai muka yi na san shirin ka?" 

Haushi ya tiƙe shi. Mukulin zaka bani na koma da shi ba zan hau ta haya ba.

Aa ai akwai zirga-zirgar da zamu yi shi ya sa ma Baffa yace a taho da motar in na baka ni kuma nayi amfani da me? 

Bai iya ƙara cewa komai ba. Shiru kawai ya zaɓi da yayi. 

Uwani da ta gama shan fura ta shige ɗakin Yafendo ta cire kayan jikinta ta ɗaura zani wanka zata yi zafi take ji. Hijab ta ɗauka ta saka ta fito tana kallon Meenal.

"Sahiba wanka."

"To ƙwaɗuwa sarkin son ruwa ,ai kya bari ki huta tukuna abinda kika ci ya ɗan tsarga miki."

"Uhm'uhm zafi nake ji kin san ni bann jurar sa."

"To bara na ɗauko miki ruwan." Meenal ta tashi. Joɓe ma ya tashi ya saka takalminsa yace "Ina zuwa bara na gyara parking." 

Tsakar gidan daga Haidar sai Uwani.

"Ummu!" Ya kira sunan ta a hankali kamar mai yin raɗa ko yana jin tsoron a ji shi.

Uwani kuwa sai da ta fara zumɓur baki tukunna tace "Na'am Hamma."

"Faɗa muke yi?"

"Me ka gani?"

"Yaushe rabon da ki min magana? Saboda na kori saurayin ki kike fushi da ni. Za ku yi tafiya amma ki kasa gaya mini."

"Ni ba fushi nake da kai ba. Kai ne kake fushi dani."

"Ni bana fushi da ke kawai na ji haushi ne da na gan ki da shi maimakon ki zo ki bani haƙuri sai kika basar dani kamar wani maraya."

Ɗaga kai tayi tana kallonsa , da mamakin kalmarsa ta ƙarshe wai maraya....

"Kasa jurar ganin kin ƙi mini magana nayi fa shi ya sa na biyo ki. Kuma na ga dai da gaske ba kya son kula nin shi yasa na miki magana. Don Allah ki daina fushin nan kina kula ni na rasa me yasa na kasa sukuni da rashin kulanin da kike yi." 

Nan da nan jikinta ya soma ɓari "me yake damun Hamma Haidar ne wai?" Ta tambayi kanta.

A hankali tace "Hamma ni fa ba na fushi da kai."

"To me ya sa kika ƙi gaya mini za ku taho Billiri?"

"Saboda ban gan ka ba na ɗauka ka yi tafiya ne."

"Kai Ummu ƙarya haramun. Ai kin san ba zan yi tafiya ban gaya miki ba."

Ƙasa ta ƙalla tana wasa da zoben azyurfarta.

Hannusa ya harɗe ya gyara tsayuwarsa yace "Kwana nawa zaku yi?"

"Sati biyu zamu yi."

"Iyi sati biyu kuma, in ji wa kenan?"

"Mami".

"Aa gaskiya ana gama biki za ki taho ban yarda kiyi sati biyu ba in kika yi sati biyu ai sai na....." Yayi saurin haɗiyi ragowar kalamasa. Ji yake yi kamar ya make kansa wai dama ita haka soyayyar take ta dinga saka ka faɗar maganganu marasa ma'ana kana baranbarama? Gaskiya so bai masa adalci ba.

Daidai lokacin da Meenal ta fito da ruwa ta kai mata banɗakin. 

"Zo ki shiga."

"Na gode Sahiba".

Haka ta wuce shi ta shige banɗakin. 

Shi kuma ya sauke ajiyar zuciya ya fita daga gidan gabaɗaya in ba haka ba zai aikata abin kunya.

*

Haidar be sake ganin Uwani ba sai yamma da zai tafi ya saka aka kira masa ita waje. Lokacin ta sauya kaya zani ta ɗaura. 

"Hamma ashe tafiya zaka yi?" 

"Eh zan tafi. Sai mun dawo ɗaurin aure. Amma ki kula da kan ki ban da rawar kai Ummu, bana son kule-kule aure kika zo kawai kuyi biki ki koma gida bana ganin ki amma Allah Yana ganin ki. Don Allah ki rufa min asiri kar ki bawa wani fuskar da zai kula ki." 

"To Hamma in sha Allahu zan kula."

"Kula ba ma ɗaya ba Salma kin fahimta ai?"

"Eh." 

Haka suka rabu Joɓe ya tafi kai shi tasha ya samu na shiga cikin gari.

*

Washegari Meenal da Ummu bayan sun karya suka shirya tafiya gidansu Nana. 

Hijabi ta saka dogo har ƙasa. Suna tafe suna hira har suka zagaya baya suka isa gidansu Nana. 

Tunda suka shiga gidan Ummu ta ji gabanta ya faɗi sosai. Ta sa hannu ta dafe ƙirjinta tace "Innallilahi!"

Meenal tace "Mene ne?"

"Babu komai." 

Suna shiga suka tarar da Baffajo da Dada suna zaune kan tabarma suna cin ɗumamen tuwon dawa miyar kuka. 

Tunda Dada ta ji salamar Ummu sai da taji wani irin abu ya tsarga mata da sauri ta ɗaga kanta ta kalle su miƙewa tsaye tayi da sauri tana kallon Ummu.

Ummun ma ita take kalla   bata san dalili ba amma ta ga kamar ta san matar amma bata san a ina ta santa ba.

Meenal tace "Dada duk murnar gani na ce ta sa kika kasa zama?" 

Dada ta soma ina-ina tace "Lale maraba ku shigo bismilla".

Haka suka shiga suka zauna. 

Shi kan shi Baffan sai da ya ji faɗuwar gaba. 

Dada ta shiga ciki tana cewa "Ina zuwa ku zauna Baffa zo muyi magana."

Tashi yayi ya shiga cikin ɗakin.

Dada ta kasa zama sai juyi take ;

"Ko gooto woni no ndiyam." (Shin akwai wani abu da yake faruwa yanzu?)

"Debbo A'a gooto walaa,amma nyaama,en waawi haala." (Aa babu komai ,amma zo mu yi magana.)

"Gorko mi yi'i mo fuu Heemu.(Na ga tana kama da Heemu.)

Gorko yace "Ko rewɓe makko tan? (Ko dai ƴar shi ce?)

"Hay!" (Haba).

Nana ta shigo tace "Salamu alaikum, Dada Baffa Me ke faruwa?."

"Babu komai muje".

Tare suka fito suna kallon Uwani.

Dada dai ta kasa yin shiru ,bayan ta zauna ta kalli Uwani tace "Yarinya yaya sunan ki? Daga ina kike?" 

"Ummusalma! Daga garin Kano nake."

"Zan iya ganin mahaifiyar ki?"

Shiru Uwani tayi jiki a sanyaye lokaci guda ta ji idanuwanta sun ciko da hawaye.

Da sauri Dada tace "Kiyi haƙuri don Allah,ban tambaye ki don na ɓata miki rai ba ban san me yasa ba kin yi min kama da wani ne."

Da sauri Uwani ta ɗago kai tana magana bakinta na rawa tace "Waye nake miki kama da shi? Ba a taɓa cewa ina kama da wani ba sai yau.Don Allah in da gaske kike ki nuna min shi na gani.Ban san ƴan'uwana ba iyayena sun rasu duk su biyun na taso cikin maraici da tsangwamar asali don Allah da wa na yi miki kama?" 

Dada ta kuma gyara zamanta tace "Ki kwantar da hankalinki yarinya. Mu bi abin nan a sannu. "

Uwani kuwa ta ce ina sai an gaya mata da wa take kama. Ita daman ta ji a jikinta akwai wani abu a tare da ita bayan shigowata gidan nan.

Dada jikinta ya soma rawa ita ma sai ta saka kuka. Baffa yayi ƙoƙarin saka su suyi shiru  amma abin ya ci tura.

Meenal ta tafi gidansu da gudu ta kira Yafendo haka suka taho gidan Dada.

Zaunawa tayi tace "Haba Dada, haba , ya haka kuma? Ba haka muka yi da ke ba. Ba haka muka yi ba kin ce za ki bi komai daki-daki na gaya miki ne don mu samu ƙwararan hujojji tukunna amma shi ne za ki ƙaraya tunda wuri?" 

"Na kasa haƙura ne babu ƙarya a cikin abinda kika gaya mini, babu tantama  ba sai na jira wani lokaci ba tsahon shekaru biyu ina dannewa sai yau Allah Ya amsa mini kuma naga zahiri tayaya kike ganin zan iya daurewa? Ba zan iya ba dole ne a fallasa abinda yake cikin duhu." Dada ta faɗa.

"Na ji amma ba yau ba ki bari a kira min Fatima uwar riƙon ta tukuna."

Dada tana jijiga kai tace "Ban miki alƙawari ba bazan iya ba.."

"Saboda ni." 

Dada ta kalle ta, yafedo ma ta kalle ta ,ta jijiga mata kai alamar ƙarfafa mata guiwa. 

"Me yake faruwa ne ku gaya mini don Allah kun saka ni a duhu,kai na juyawa yake yi, wacece ni?"