Chapter 28
by @khairatup01
ZUCIYAR MUTUM.
NA
UMMULKHAIR S PANISAU
Wattpad:Khairi_muhd.
Karamci Writers Association.
28
"Na ji kamar Hamma Haidar ba shi da lafiya,muryarsa fa rawa take yi kamar yana kuka."
"Wai Haidar? No ban yarda ba.Kin san ko jarumtar Haidar? Ba mamaki daga bacci ya tashi."
Ɗan jim ta yi kaɗan sai dai bata yarda cewa Haidar daga bacci ya tashi ba.
Yaga tana tunani na daban. Hakan ya saka ya zaro wayarsa daga aljihunsa yace "Matso ki ga hotan Twins."
Tuni fara'a ta sauka a saman fuskarta. Haka ya dinga nuna mata hotunansu tun kafin su fara rarrafe da wanda suke rarrafe komai dai sai da ya nuna mata sai dariya take yi.
"Hamma basu san ni ba ko?"
"Sun san ki mana."
"Tayaya?"
Ina basu labarinki. Nace musu Auntynsu ta ɓata amma ana nemanta za a gan ki daga baya.
Murmushi tayi.
Kallonta ya yi yace "Wallahi ina son ki Salma. Tun kafin ma ki haifa min yara ina son ki na girgiza a lokacin da kika tafi ba tare da kin sanar min ba. Ina cikin duhu sai dai ina mai alfahari da cewa za ki zame min haske abin haska rayuwa ta.
Hamma Meena fa? Na ji ana maganar zaka aureta.
Ba son ta nake ba. Baffa na bawa zaɓi saboda ina buƙatar mace a tare dani. Aisha ba zata sauya ba. Amma yadda na tsara gidanki daban ba zamu tare yanzu ba sai na gama shirya abubuwa. Zan tafi Cairo wani satin dama zan yi shekara guda a can sannan in dawo. Na so in tafi dake amma ba zai yuwu ba makarantar ki kina gab da gamawa. Abu na biyu dole in na je dake in je da Aisha kuma ba yarda zata yi ba. Ban gayawa kowa ba amma ke shaƙiƙiyata ce shi yasa na gaya miki don mu yi shawara a tsakaninmu kafin na sanar musu. Goyon bayanki nake buƙata kawai.
Hmm! Hamma abinda kake so shi nake so. Na gamsu da hakan ba zan so ka zamo mara adalci ba. Hakan da ka yi shi ne daidai shi ya kamata kowanne namiji ya dinga yi. Allah Ya baka ikon sauke nauyin da Allah Ya ɗora maka.
Amin Salmatu na.
Ta cuno mai baki ya kirata da Salamatu.
*
Washegari bayan ɗaurin auren Abubakar aka yi na Habib. Haidar bai zo ba yana can yana haɗa yadda zai yi ya bar ƙasar.
Ko su Mami ba zai gaya musu ba sai ya isa can zai kirasu ya musu bayani don in ya gaya musu bazasu bar shi ba.
.
KANO.
Shatu na hango cikin shiga ta alfarma. Yaran dama suna can gidan Hajiya.
Shadda ce ta saka kalar jinin kare. An mat ɗinkin doguwar riga bou-bou ta kafa ɗaurin nan na ture ka ga tsiya. Kwalliya tayi sosai har kwalliyar ma ta burgeta ta zauna tayi hotuna a wayarta.
Ta kunn data ne ta sak status. Tana gamawa ta koma kallon status ɗin mutane. Can ta hango status ɗin Sufyan Habib da haka tayi sebin lambar Sufyan.
Da farko an rubuta "Alhamdullilahi! Abokina ya yi aure yau."
Ta kuma danna na biyun nan ta ci karo da hoton da ya sa ta saki wayar ƙasa harda furta "A'uzubillahi! Me zan gani?" Da sauri ta ɗauko wayar ta kuma komawa don ganin kwaf.
A na uku kuwa kasa jurewa tayi zooming ɗin hoton tayi sosai ta ga hoton Habib da Uwani cikin fararen kaya ya rungumeta aa gefe an rubuta "My Queen" .
Daɓas ta koma da baya ta zauna ta zame ɗankwalinta. A fili tace "Kai ƙarya ne wannan kai ƙarya ne. Habib ne zai yi aure ban sani ba? aa wasa ne wannan. Ai bikin Abubakar yaje me zai wani kai shi aure ai da na sani. Da sauri ta kuma ɗaukar wayar ta koma neman lambar Adda Hussaina ko Rukkaya ko Sa'adatu nan ma da hotunan biki ta ci karo. Cak ta tsaya bayan ta gani a kan status ɗin mai gayya mai aiki Habib.
Kan bala'i bura'uba da wasali kai ni za ayi wa cin amana yaushe ? Na shiga uku Habib ya yi aure ya auri wata na bani ina zan saka kai na ni.
Gigicewa tayi tuni ta ɗauko wayar ta soma neman layin Habib.
Tana ta ringing ba a ɗaga ba. Haka ta kuma nemo layin Sufyan.
Tana ko shiga ya ɗauki wayar ya kara a kunnensa.
"Uwargida ran gida! Yau kuma an tuna da mu?"
"Aa dakata! Dakata min Sufyan me nake gani da gaske Habib aure ya yi ko kuwa wani shirin fim ake haskawa?"
Ƙaramar dariya yayi yace "Haba ke kuwa Shatu daman Habib yana fim ne? Zahiri kika gani aure muka ɗauro yau ya zama mijin mace biyu."
"Kutumar ubanka Sufyan ,Allah Ya isana na san kai ne ka haɗa masa wannan shirmen. To kuyi gaggawar warware ƙullin da ku ka ƙulla don ba zan yarda ba ƙarya ne Wallahi. "
"Abin bai kai da haka ba Uwargida. Kiyi haƙuri da ciwo na sani amma ya za ayi haka Allah Ya tsara kuma za ki yi mamaki ma in kika ji wacce ya aura."
"Ki koma ki duba da kyau ba mamaki kishi ne ya rufe miki ido." Ya kashe wayar ba tare da ya bata damar ƙara cewa uffan ba.
Cikin watsaap ɗin ta kuma shiga ta dubo hotuan. Hannunta har rawa yake yi, hawayen ma sun kasa samuwa bare su zubo ashe kuka ma rahama ne. Sosai ta duba hoton ya kai sau ba adadi tana zooming kafin ta gane wacce a hoton tashi tayi tsaye a firgice tace "Uwani" da ƙarfi.....
*
GOMBE.
Gombe Lawanti international Airport .
Haidar cikin suit baƙaƙe kamfanin armani ya sanya. Ya saka glass baƙi ya ɓoye rinannun idanuwansa da suka sauya kala daga farare zuwa ja. Airport ɗin gombe ya isa ya hau zuwa Abuja daga can zai wuce manchester ta qatar airways (via Doha).
Kallon ƙarshe ya yi ma ƙasar sa Nigeria ya zare glass ɗin kan fuskarsa ya kalli ko ina kafin ya juya ya shiga cikin jirgin ya maida glass ɗin nasa. A hankali ya sauke ajiyar zuciya bayan ya zauna ya saka belt. "Ba mamaki na bar ƙasar nan har abada kenan. Ba zan dawo cikinta ba."
Wayarsa ya kashe ta daman. Don tun safe ya ga kiran Mami da Baffa sau ba adadi amma ya kasa ɗauka baya son zuciyarsa tayi rauni. Bai fi son Ummu da su ba amma ba zai iya rayuwa babu Ummun ba. Ba zai juri kallon Ummu da waninsa ba wanin nasa ma ɗan'uwansa Habib ya sani wata ran zai iya yin ɓattaciya in zuciya ta ciyo shi gwara yayi nesa da su suyi rayuwarsu yayi tasa.
*
Rungumeta yayi a jikinsa kai kace kwace masa ita za ayi a cikin kunne ya raɗa mata "Matar Habib. Kin yi kyau tsarki ya tabbata ga Allah! An ko taɓa gaya miki ke mai kyau ce? In ba a gaya miki ba ni yau na fara gaya miki Ummusalma kina da kyau. Kyawun fuska,jiki uwa uba kyakyawar zuciya. Lallai Habib ya taki sa'a."
Kanta ta sunne a kan ƙirjinsa tana dariya. Ta rasa me zata ce masa.
Hannu ya saka ya tallabo haɓar ta ya sa na sa idanun a cikin nata.
"Kar muyu ƴar kunya da ke masoyiyata bana son ta bana son kunyar. Ni yazu halak ɗin ki ne kalle ni da kyau. Allah ne Ya kashe ya baki fine boy mai son ki."
"Hamma Habib wai dama haka kake?"
Lebbanta na ƙasa ya ciza da ƙarfi.
Ouch Hamaa....
Zan ƙara in kika kuma kira na da Hamma baki san na samu canjin matsayi ba yanzu? Gaskiya ki sauya min suna yanzu faka-faka.
Me kake so na ke kiran ka?
Aa ke za ki zaɓa min ai.
"Ya sukooni" (My peace).
Hannu ya saka ya dafe ƙirjinsa yace "Hey! Na karɓa kuma na riƙe duk ran da aka sauyan sunan nan zan yi hukunci ne.
Hukuncin meye?
Hukuncin hana zuciyata sakat.
Rungume shi tayi ita ma tana dariya.
Kwankwasa ƙofar ɗakin aka soma.
Ya ɗan ɓata rai kamar yana son yayi kuka. Murya a shaƙe yace waye?
"Kai rasa ido.Dallah rabu da yarinya ta fito ana nemata ko na tona maka asiri."
"In ba Sufyan maƙiyi na ne kai.Ya ina ganawa da my choice zaka zo ka katse min jidaɗi."
"Au haba! Shi kenan.Mami kuyo ta nan ga ango da amaryar nan a ɗaki....."
Tuni Habib ya fito daga ɗakin yana zazare idanu.
Sufyan ya fashe da dariya har da tsugunnawa a ƙasa.
Habib ko ya daddage ya maƙe mai ƙeya.
"Amarya kina ganin mijin ki ko? Gaskiya zan rama."
Dariya tayi kawai ta shige.
Saurin riƙo hannunta yayi. Juyawa tayi tana kallonsa.
Da ido yayi mata kallon ina za ki?
Ta maida masa martani ta hanyar nuna masa ƙofa.
"Kai gaskiya soyayya shegiya ce wai Habib daɗa dawowa ruwa kayi ko me ɗan iskan banza sake ta dalla ina sauke maka bomb ɗin da ya sa ni nemanka. Amarya je ki abin ki bafulatana dake zai koya miki rashin kunya."Sufyan ya faɗa. Dole ba yadda ya iya haka ya saki hannun nata yayi mata flying kiss hannu ta saka ta tare ta sa a saitin ƙirjinta.
"I love you."
"Love you to."
"Shatu ta kirani."
Hankalinsa ya maida masa kan sa.
"Shatu ta kira ka ɗazu?"
"Ƙila kai ma ta kira ka."
Duba wayarsa ya soma yi. Nan ya ga tarin missed calls ɗin Shatu. Tuni ya ji duk wata walwala ta kau masa.
Bara na kira ta.
Aa kar ka kirata ƙarfin da zafi yanzu ka bari ya sanyayya tukunna. Kawai dai ka sani akwai ƙalubalen da yake jiranka a gaba. Don nima nan da ƙyar na sha."
Hum Wallahi mutumina gaba na faɗuwa yake yi fiye da yadda kake tsammani.
Haba faɗuwar gaba asarar namiji. Komai khairan kawai dai ka kasance cikin shiri.
Toh na gode abokina. Bara na shiga nayi wanka.
Da haka suka rabu.
*
Wayar da Habib ya sai mata ta ɗauka ta nemi layin Hamma HAIDAR amma sai ta ji bayanin matar nan ta kamfanin MTN tana sanar da ita its switched off. Ajiye wayar tayi. Tana kallon ƙofa hakan nan take jin gabanta na faɗuwa, ta kasa daina tunanin Hamma ko yana lafiya?
Nan su Meenal suka shigo suna tsokanarta Amarya ba kya laifi.....
*
_Baffana da Mamina , ina son na sanar muku cewa ina son ku kuma na damu da ku. Na san kun sha ɗawainiya dani kuma na sani na kasance ɗa mai baku wahala tun ina ƙarami har kawo yanzu baku huta ba. Kafin nace komai ina son ku yafe mini matakin da na ɗauka ba tare da na sanar muku ba na yi hakan ne saboda na sani in kuka sani ba zaku bani izini ba. Yanzu ne ya kamata na tallafa maka Baffa amma ka sani zuciyata ba zata bari na aikata komai ba a ƙasar nan saboda na riga na karaya kuma bana son a gane naƙasun nawa. A halin yanzu da nake wannan rubutun hawaye basu bar zuba a cikin idanuwana ba.... Mami kiyafe min ban son tsahon wane lokaci zan ɗauka ban dawo ba amma zan dawo sai dai yaushe shi ne ban sani ba. Zuciyata ta karye na san kun lura kuma kun so ku bani abinda nake so sai dai kash ƙaddara ta riga fata. Ba zan iya ganin ɗan'uwana da Ummu a tare ba. Ina son Ummu so na hakika so na gaskiya bana son zumuncin mu ya lalalce saboda ni ko hallayata ƙila akwai abinda na aikata wanda yake bibiyata har ya saka na kasa samun abinda nake so. Zan kira ku da zarar na samu daidaito a nan. Zan gaya muku inda nake bayan na gina mafarkina. Baffa ka riƙe min Mami da amana ka kula min da ita ka yi adalci a tsakaninsu da matar ka. Mami ki ci gaba da sa min albarka kamar koyaushe. Ina son ku. Ban tafi don na fi son Ummu da ku ba na tafi ne don na warke raɗaɗin da yake cikin raina. Ƙila zamana a nigeria babu alkairi a ciki."
Mami na san a lokacin da kike karanta wasiƙar nan kuka kike yi, don Allah kar kiyi kuka saboda ni kiyi min alƙawarin ba za ki yi kuka ba. Ina son ku ababen alfaharina."
Wallahi ina son Ummu.
zamana a Nigeria ba zai bani damar barinta ta zauna da wani na ba kun fi kowa sanin halina fitinarta zan yi. Bana son na shiga hurumin ubangiji.
Aliyu Haidar.
"Da ma na sani Haidar Ummu yake so. Na gane take-takensa. Na ɗauka in aka gama bikin Abubakar zan masa magana na ji ta bakinsa in yana so ayi auren. Ashe ma ba haka Allah Ya so ba. Alhaji na yafewa Aliyu. Ni na yarda da shi in ya zauna a nan fitina zai haifar musu bashi da ɗauke kai a kan abinda yake so. Allah Ya sa haka shi yafi alkairi,Ya bashi ikon cinye jarrabawarsa. Fatana kar ya koma shaye-shaye.... ta ƙarasa faɗa tana kuka.
Dafa kafaɗarta yayi ta gefe yana lallabata."Aliyu ya yi min alƙawari ba zai sha komai ba sai taba. Kuma na yarda da shi in ya faɗa zai yi in ya ƙi kuma ba zai yi ba. Na yafe masa. Nima na jima da gane son yarinyar yake yi kuma na so ya aureta amma yaya zamu yi? Matar mutum kabarinsa. Muyi ta addu'a Allah Ya bashi wadda ta fita Ya shirya mana shi."
"Ameen."
#ZuciyarMutum.
#HabibUwani.
#Haidaruwani.