ZUCIYAR MUTUM

Chapter 30

by @khairatup01

Zuciyar Mutum
khairatup.
K.W.A.
Wattpadkhairi_muhd.
Pg30.

________________

Hannu ya saka ya dafe goshinsa don jinin ya ɗan tsagaita masa ga jiri na ɗibarsa. Banɗakin dake ƙasa ya shiga ya sakar wa kansa ruwa ya wanke jinin. Drower da ke jikin bango ya buɗe ya ɗauko akwatin agaji na gaggawa ya gyara ciwon. 

Wanka yayi ya sauya kaya saboda kar Uwani ta ga halin da yake cike ta shiga cikin tashin hankali. 

Sai dai yana nufar hanyar ɗakin ya ji kamar ihun Uwani a ciki. Da sauri ya isa bakin ƙofar amma a ruge gam. Ko ba  faɗa masa ba Aisha ce. Buga ƙofar ya fara yi yana umartar ta da ta buɗe ƙofar amma taƙi buɗe ƙofar.

"Aisha Wallahi in baki buɗe ƙofar nan ba sai kin yi mamakin abinda zan yi miki. Aisha wai me yasa baki da hankali ne nine na aurota ni za ki yiwa ba ita ba. Aisha in baki buɗe ba zan kira hukuma su sai su saka ki buɗe."

"Ai ko sojoji zaka ɗebo basu sun saka na bar yarinyar nan ba don sai na yi maganinta dama na gaya maka ni ce ajalinta ka zata wasa nake yi ? "

"Innallillahi wa inna illahir raj'un. Aisha wai yaushe kika koma haka? Ki buɗe ƙofar nan na gaya miki."

"Habib ba zan buɗe ba." 

Habib ya rasa yadda zai yi ga kukan Uwani yana ji har ma ya daina jin kukan nata sai bimbinin bala'in Aisha. Aljihunsa ya taɓa  bai ji komai ba sai ya tuna ashe ya sauya riga da gudu ya koma ɗakin ya lalubo makullin ya koma ya buɗe ƙofar sakin hannun ƙofar yayi ya shiga da gudu ya hakaɗe Aisha daga saman Uwani da bata san waye a kan ta ba, ta suma ga jini a gefen bakinta a hannun ma akwai rauni kamar yanka sai da ya kalli hannun Aisha da kyau ya ga wuƙa ce a hannun nata.

"Aisha! Da gaske mahaukaciya ce ke? Ashe za ki iya yin kisan kai?"

"Da na ce maka zan iya kisan kai a kan ka me ka ɗauka? Zaton ka ƙarya nake yi ko kuma faɗa kawai nake yi?.."

Bai bari ta ƙarasa ba ya sa hannu ya sauke mata mari a ɓarin hagu daga nan ya kuma sauke mata a ɓarin dama.

Ni ka mara Habib?

An mareki ɗin Aisha ko nima kashenin za ki yi? Nace ko nima kashenin za ki yi?  Shashasha mara imani muguwa azzalumma ke dai ba ki ji daɗin halinki ba.

Hannu ta saka ya cakumo masa wuyar riga tace "Na rantse da Allah sai ka yi da na sanin mari na Habib..."

"Da na sanin me? Ke ce dai za ki yi da na sani ba ni ba."

Fillo ta ɗauka ta juya tana son danaawa Uwani a fuska numfashinta ya ɗauke ta mutu. 

Habib ya daka mata tsawa  yace "Wallahi in kika kuskura ki ka ƙara taɓa ta sai na sake ki."

"A kan wannan zaka sake ni? Duk shekarun da muka ɗauka a banza kenan?"

"Ki gwada Aisha ki gani."

"Wallahi ƙarya kake yi ba za ka iya saki na ba."

"Ga fili ga mai doki."

Bata daddara ba kuwa ta sunkuya zata kuma danna mata fillon yayi ta maza ya finciko hannunta da ƙarfi tayo baya ya gwara mata kai da garu yace "Kije ni Habib na sake ki saki ɗaya."

Sai kuma tayi ɗif kamar anyi ruwa an ɗauke ta dawo cikin hayyacinta. Fillon ta saki ƙasa ta kalle shi tace "Ka sake ni  Habib?"

Bai bi ta kanta ba ya koma gun Uwani ya ɗauke ta ya fita da ita.

Ta kasa yarda yanzun nan Habib sakinta yayi saboda Uwani.Da gaske zai iya sakinta. Aiko bata ga abinda zai hana bata ɗauki mataki akan Habib ba wannan hukuncin sakin nata da yayi tayi alƙawarin shi ne kuskure na ƙarshe da zai aikata don sai ta tarwatsa masa rayuwarsa.

*

Longsight.

Firgit yayi ya tashi daga baccin da yake yi.Ƙishi ya ji ya kama shi haka ya saka ya jawo ruwan gefensa ya soma sha, bai sauke kai ba har sai da ya shanye tas. Marki yayi da Uwani kamar tana cikin damuwa baccin da bai koma ba kenan, ya shiga banɗaki ya yi alwala ya tada sallah. Ba zai iya kiran gida yanzu ba bare ya ji ko Ummu na lafiya.

"Allah Ya sa kina lafiya Ummusalma." 

*

Sai sintiri yake yi a bakin ƙofar da ake duba Uwani. Ta raunata don da ƙyar ma likitan ya amshi case ɗin don cewa yayi sai ya kawo ƴan sanda tukunna. Da ƙyar ya yarda.

Bayan ya duba ta ya ce masa da sauki ta tsorata ne amma ta bugu a hannu sai dai Allah Ya so babu karaya ko gocewar ƙashi sai wurin yankan da ya wanke ya gyara mata aka rufe gun ciwon. Ya gaya masa zasu iya tafiya ma da ta farka anjima.Habib yayi ta godiya. Be kira kowa ba sabod baya son su sani.

Bayan isha Uwani magani ya sake ta ta tashi. Jikinta duk ya yi tsami babu daɗi.

Tana cije baki ta muskuta.

Da sauri Habib ya matsa kusa da ita yace "Sannu Salma. Yaya jikin naki?"

Da sauki.

Me yake yi miki zafi.

Jikina.

Sannu.kiyi haƙuri ban san zata iya yin haka ba da ba zan bari ba. Amma hakan ba zata sake faruwa ba na yi maganin abun. Na ɗauki mataki kiyi haƙuri don Allah!. 

Hamma me ya samu kan ka?

Aisha ce ta jefe ni na je gyarwa shi ashe ta shiga ɗakin ganin bana ciki. Hakkina ne na kare lafiyar ki amma na gaza ki yafe min.

Hamma ba laifin ka ba ne. Kai ma bak san zata yi ba. Nima ganinta nayi kawai amma na yafe mata. Ba sai an gayawa Hajiya ba ma.

Na gode. Amma ni ke tabatar miki da ba zata kuma ma ganin ki ba bare tayi miki wata illar ba.

Ba komai ,ni na yafe mata ban riƙe ta a raina ba.

Za ki iya tashi mu tafi gida?  likita yace zamu iya tafiya.

Zan iya.

*

"Ɗan yi sake ni saboda ya auro wadda kike so yake so. Amma Wallahi Tallahi nayi rantsuwa ba zan taɓa bari ku manta ni a cikin rayuwarku ba ni nan sai na bar muku tabo mai wuyar gogewa, sai na yi muku illar da ko mai irin suna na kuka je sai kun firgita ,ruhinku ya girgiza." 

"Ya salam! Haba Aisha ,kar ki manta matsayina  a wurin mijinki mana. Ki nutsu ki sanar da ni abinda yake faruwa ban san komai ba."

"Hhh. Munafukar tsohuwa kin san komai kamar yadda kika saka aka yi mini kishiya kuma ta rabani da gidana. Nima sai na rabata da Habib ku ma sai kun yi nisa da shi nisan da sai kun ji dama baku ci amanata ba."

"Innallillahi wa inna illahir raj'un. Aisha ki nutsu kiyi shiru kina ina?"

"Babu ruwanki da inda nake. Saƙo ne nake son ki gayawa ɗanki, yau ranar sa ce gobe ranata ce ni kuma.Dole ne sai ya girbe abinda ya shuka. Sai na saka shi hawayen jini."

Hajiya zata yi magana, Aisha ta katse wayar kit. Hajiya ta bi waya da kallo. Kalaman Aisha yau sun saka mata faɗuwar gaba. Hakan nan ikirarin Aisha bai yi mata ba. Da sauri ta soma neman lambar wayar Habib.

Habib na tuƙi kiran Hajiya ya shigo sai bai iya ɗaga wayar ba kawai ya bar ta ya bari akan in ya je gida zai kirata. Hajiya kuwa ta ƙara shiga wani yanayi ta kuma kiransa amma bai ɗaga ba. Maganganun Aisha na mata yawo a kwanyarta. Tashi tayi ta zari hijabi ta saka.

Tana sauka ta soma kiran sunan Hassan da ƙarfi.

"Hassan ! Hassan! Wai ina Hassan ne?"

Abi da ke study room y  fito jin kiran banbarakwai. 

"Lafiya Dakta?"

"Ba lafiya ba Abi. Ban san me yake faruwa a gidan Baba ba. Matarsa ta kirani kuma naji tana ta manyan ikirari a game da Baba da rayuwarsa tsoro nake ji ban taɓa jin tana haka ba zuciyata bata taɓa raunana kamar yau ba hakan nan naji tsoron kalamanta kuma sun shige ni ku zo ku kai ni na ga Baba da matarsa don ina ta kiransa bai ɗaga wayata ba."

"Ya isa Dakta, ki nutsu Baba yana cikin ƙoshin lafiya in sha Allah! Bata isa tayi abinda Allah be kaddara zai samu Baba ba. Zamu je amma sai da safe ki duba agogo mana? Wata ƙila yayi bacci shi yasa bai ɗaga kiran naki ba."

"Da safe kuma Abi? Maganar Baba fa nake yi."

"In na isa da ke nace ki koma ki zauna da safe zamu je. In ya tashi ma zai kira ki in dai Baba ne."

Abi ya riga ya ɗaure mata ƙafafuwa ta hanyar bata umarni. Zaunawa tayi jigum idanuwanta a wuri guda abin duniya ya ishe ta. In fa da gaske Aisha ta cutar mata da ɗa? Kasa jurewa tayi haka ta kuma neman layin Habib, cikin sa'a kuwa ya ɗaga kiran wannan karan.

"Hajiya".

"Kana lafiya Habib?"

"Ina lafiya Hajiya. Sai yanzu na ga kiran ki lokacin da kika kira ni in  tuƙi."

Ajiyar zuciya ta sauke kafin tace "Alhamdulillahi. Na tsorata Baba. Aisha ta kira ni tana yi min wasu maganganu wasu kuɗi wasu bashi na kasa gane abinda ya faru."

"Hajiya ki kwantar da hankalin ki,kije ki huta da safe zan zo."

"Ka tabbata Baba babu wata damuwa?" 

"In sha Allahu babu Hajiya ta."

"Shi kenan. Allah Ya yi maka albarka."

"Amin Hajiya."

Washegari.

Bayan ya gama taimakawa Ummu shirywa ya bata abin kari sannan ya yi mata sallama zai je ya dawo gidan Hajiya zai je.

Yana fita ta saka sakata a ƙofarta don bata yarda Aisha ta bar gidan ba.

A can gidan Hajiya kuwa komai ya labarta musu. Abi mamaki bai bar fuskarsa ba ashe dai Aisha bata hankali . Amma wane mataki ka ɗauka?

Abi na sake ta.

Aa zaka je ka kai  abin gun hukuma don ba zan yarda ba ,wadda zata iya yin haka to in ta samu dama zata iya kisan kai.

Abi ba zata dawo ba.Ni na riga na rabu da ita gaskiya.

Hajiya tace "Aa gaskiya sai an kai ƙara. Baka da hankali ne? Kirana fa tayi a waya kuma ta gaya min irin abubuwan da zata iya yi. Hankalina ba zai kwanta ba sai na ga an dau mataki tukkuna."

'Hajiya kiran ki tayi wai?"

"Ta kira ni jiya da daddare. Kuma ni wayata tana recording ina da shi a waya. Zai amfane mu a can."

"Hajiya barazana ce kawai amma zan je . Ku kwantar da hankalinku khairan In sha Allah."

"Habib kana da taurin kai."In ji Hassana.

"Adda ba taurin kai bane. Ta ci darajar zaman da aka yi da na su Hussain."

"Yaran da bata damu da su ba?  Dubi goshin ka ita kan ta na san Ummun tana kwance da ba isa ba fa kashe ta zata yi a banza , iri su Aisha ba a ɗaukar maganarsu a matsayin barazana. Ita kanta don ta samu biyan buƙata kashe kanta ta so yi, tayi maka, tayi wa Ummu gobe kuma kisan zata yi." 

"In sha Allah ba zata yi ba Adda."

Shi kenan ku kyale shi tunda ya dage. Allah Ya shiga cikin lamarin.

"Amin" kowa ya amsa.

Hajiya tace "Amma dai da sauki jikin Ummu ko?"

"Da sauƙi Hajiya."

"To Allah Ya kiyaye na gaba.Adda ki sa ayi mata girki ya tafi da shi su ci anjima."

"Tam."