ZUCIYAR MUTUM

chapter 31

by @khairatup01

Zuciyar Mutum.
Khairat
wattpad:khairi_muhd
pg 31.

*

    Ko da ya dawo ya same ta tana ɗaki tana kallo a waya. Yana shigowa ta ajiye wayar tace "Sannu da zuwa Ya rooh."

"Yauwa baby na. Na gode ya zaman gida?"

"Babu daɗi baka nan ,amma yanzu na ga gidan yayi haske da dawowar ka."

Murmushi yayi ya tsugua daidai saitin kanta ya sumbaci goshin ta yace "Ina son ki. ki fito mu ci abinci, Hajiya tayi mana girki."

"Allah sarki Hajiyarmu mun gode." 

Falon suka fita tare suka zauna a ƙasa. Tashi tayi ta ɗauko musu plate da spoon ta ajiye ta zuba musu. 

Tare suka ci suna zolayar juna. Abin gwanin ban sha'awa. Can Ummu tace "Ya rooh an samu Hamma Haidar kuwa?"

"Aa fa lambar shi bata zuwa. Na fi tunanin ma ya ajiye layin. Kin san ɗan iska ne in aka ɓata masa rai sai yayi balaguro kawai ya yi ƙaura da mutane."

"Ai Hamma Haidar kam akwai faɗa. Amma dai ba shi da matsala sai an taɓa shi ma fa yake yin faɗan."

Haka ne.

Ya Rooh ba zaka dawo da Aunty ba?

Haba Ummu ,in dawo da ita ina? Haba ke har kina da bakin bada wannan shawarar? Aa taje Aisha bata da hankali zata iya kisa Wallahi. Ni kuma in ada buri da mafarkin samun ƴa'ƴa daga jikin ki, ki basu kula ki kuma tarbiayantar dasu tafarkin addini. Ki daina min maganar Aisha in muna tare.

Amma baka ganin za ace daga zuwa na na kori matar ka?

Su yi ta faɗa ban damu ba. Zancen mutane baya da mu na.

Nan dai suka ci gaba da yin hira a tsakaninsu.

  *

Watan Haidar biyu kenan  a garin Manchester ya ma soma sabawa da mutane a can daga aiki sai gida sai ko in za shi sallah. Har zuwa lokacin bai samu ya kira gida ba kuma yana kewarsu. Baya son ya kira a tambaye shi dalilin tafiyar musanman ma Mami ba zai iya yi mata ƙarya ba gaya mata gaskiya zai yi dailin Ummu ne ya tafi.

Wayarsa ya ɗauko ya kunna hasken ta nan hoton fuskar Ummu ya bayyana tana dariya bata san yayi mata hoton ba amma hoton yayi kyau sosai. Shi ma murmushin yayi yana shafa kan screen ɗin wayar. 

Ya san ba daidai bane amma ba zai iya manta Ummu a rayuwarsa ba. Ajiyar zuciya ya sauke ya kwanta kan kujera yana kallon sama. Kullum sai yayi tunanin Ummu kuma kullum sai yayi hasashen ko akwai wani abu da yake faruwa a nigeria tunda sarai ya san halin Aisha da faɗa da wulakanci amma Ummu ba zata iya maida martani ba saboda ba mace bace mai faɗa ba.

"Ba zan manta ki ba Ummusalma ina sonki."

*

"Hajiya ni fa ba ɗan daba ba ne kuma ba fashi da makami nake yi ba. Gaskiya ba zan iya yin abinda kike so ba. Wai tsaya ma a ina kika samu lambar wayata?" 

"Zaka iya kuma za ka yi. Manyan kuɗaɗe ne zan baka amma ina son a kashe min su."

"Na lura ba kya nema na sai bala'i ya tasar miki ni in kwana a ciki ke ki kina can a gida a kwance babu wanda zai kama ki ni kuma ƴa'ƴana fa? Matata fa? Mahaifiya ta fa? Ki nemi wani."

"Bijirewa umarnina tamkar janyo wa kan ka wani sabon tashin hankali ne. Akwai sirrikan ka a wurina wanda zasu iya jawowa a ɗaure ka. Kaga kuwa dole ka bi ni. Ko ka yi na baka kuɗi ko na ba wa wasu su yi kuma na yi maka shunen ƴan sanda har inda kake  a kama ka.

Hajiya zan yi shawara da  matata.

Ina jiran kiran naka.

*

"Wallahi Adda Hussaina bani da komai kawai ƙiba fa na ƙara amma ni lafiyata kalau kuma a tambayi Ya ROOH."

Addar tayi dariya tace "Gasiya baki da lafiya Ummu. Allah kina nan kina ganin kamar lafiyar ki ƙalau kuje asibiti likita ya duba ki. "

Ummu ta zumɓuri baki sama ta juya ta kalli Adda Hassana tace "Adda don Allah ki rabani da Adda Husai ni lafiya ta ƙalau. "

Dariya suka saka mata gabaɗayansu. Rukkaya ce tace "Rabu dasu matar Hamma maman twins wasa suke yi miki so suke kiyi kukan da kika saba."

Ai na daina tuntuni fa. 

Eh na ga alama kam.

Nan mai aikin Hajiya ta shigo falon dake ranar hutu ce duk suna zuwa ran lahadi. 

"Yauwa Iya Tala an gama mini mandakon?"

"An gama gashi nan."

"Yauwa na gode."

"Ah'a wai ko dai da gaske baki da lafiyar?" In ji Rukkaya.

    Adda.....

Yi haƙuri ai ko baki da lafiyar abin ayi miki barka ne, da alamu wannan akwaɗai ne.

Taya ni gani Rukky. Tana zuwa fa ta tada wannan aikin. 

Hajiya ce ta taka musu birki. "Ku kyale min yarinya gaskiya babu ruwan ku da ita. Ke Hussainar nan kin fiya neman magana fa. Kin baro gidanki za ki damar mi ƴa."

"Ayi haƙuri masu ƴa kar a ɗaga mini nono."

Yafi miki dai.

Nan Habib ya dawo ya same su suna ta raha ya zauna shi ma aka ci gaba da shi.

Su hussain ma suna falon.

Suna gidan yan biyu suka dawo daga islamiya aiko suka ɗane kan mahaifinsu suna ihun murnar ganinsa.

"Inye yan biyuna me Hajiya ke baku ne ku ka zama chubby haka?"

"Biskit,sweet,cingum,chocolates lemo..."

"Woh ho ho dole kuyi ƙiba amma ba kwa san min? Kun gan ni duk na bushe ko Mummyn ku ma ta zama Chubby kun min wayo."

Suka sa dariya suka sauka suna tsale ance sun yi ƙiba.

Hjjiya tace "Bari kul maza ku shiga ku yi wanka ku sake kaya ku zo ku ci abinci ba ku ma yi homework ba fa".

"To Sweetheart."

Suka shige ɗakinsu.

"Hajiya matar nan ta koyi cin yaji da yawa kalli fa irin yajin da ke gabanta."

"ka kyale ta zata daina lafiya ce fa."

"Cin yajin?"

"Eh mana lafiya ce akwai dalili shi yasa nace taje asibiti take min shakara Hajiya na biye mata."

"Aiko dai zamu je asibitin kam."

"Ni fa am ok YaROOH."

"Aa Salma ba ki da lafiya."

Ta yi shiru kawai ta zumburi baki. 

Nan yake gayawa Hajiya ya kira Aisha tazo ta kwashe kayanta na gidan tunda ta fita daga idda. Tace zata zo in ta dawo daga Abuja taje gidan Yayanta.

To madallah. Sai ta zo.

*

          Zaune suke a falo yana yi mata yankan farce. Farcen ƙafarta ya fito sosai ya yayi tsayi. 

Ƙasa-ƙasa suke hira a tsakaninsu irin dai ta mata da miji. Nan take gaya masa tana son zuwa Billiri bikin Meenal da Nana da za ayi. Wani satin. 

Kwana nawa za ki yi gaya min da kan ki in ga kalar naki adalcin.

Wayo Ya Rooh!

Aa ba wani wayo ki gaya min.

Sati ɗaya.

Hararata yayi ya murɗe mata yatsa.

Wayyo Allah! Da zafi fa Hammana.

Ai so nake kiji zafin nima haka na ji da kika kira satin nan muguwa kawai. 

Dariya ta saka mai tace "Ni ce muguwa yau Hammana?"

"Ƙwarai ma kuwa ke muguwa ce. Taya za ki ce sati za ki tafi kiyi a Billiri ni kuma fa?"

"Amma dai Hamma tunda aka yi bikinmu fa ban je ba."

"Akwai dokar da ta ce dole sai anje in anyi aure?"

"Allah Ya baka haƙuri ,niyata ma fa na yi kwana biyu  a Gombe wurin Mamin Haidar na ma gaya mata tare zamu wuce can da ita."

Allahu Akbar me karatu na gaba.

Ya Roohhhhhh ta ja sunan a shagwaɓe.

Aa fa ba ki isa ba kwana huɗu kacal in kin yarda in baki yarda ba fakat ki sha zaman ki kawai a gida.

Aa Wallahi zan je na gane ma wayon so kake nace na fasa zuwa to Allah kuwan sai na je.

Eh na ji.

Hamma ka bar ni ....

Wayarsa ce ta soma ƙara ya duba ya ga lambar Aisha ce. 

"Aisha ce".

"Ka ɗauka mana."

"Salamu alaikum Aisha."

Daga ɗaya bangaren ta amsa mai "Wa'alaikum salam Habibullahi mijin Ummusalma."

"Kin faɗa daidai. Yaya gida?"

"Komai lafiya lau na kira ne in sanar maka da jibi zan shigo Kano zan zo a kwashe kayana kamar yadda ka buƙata. Zan taho maka da tsaraba ina fatan zan same ka a gidan in na zo?"

"In sha Allahu za ki same ni mana. Ai dole a gabana za ayi tunda ni ne namiji. "

"Hakan yayi daidai Allah Ya kaimu ka gaishe da Madam."

"Zata ji."

Suka ajiye waya. 

Jibi zasu zo kwashe kaya.

Allah Ya nuna mana da alkairi.

Amin.

*

Nawa tace zata biya ka?

milliyon biyar.

Zare idanuwa tayi haɗe da saurin sa hannu ta toshe masa baki tana zazare ido tace "La'ilaha illallahu amma waɗanan manyan kuɗaɗen ne kake son zubar dasu?  Zaka yi aikin nan ai ba kama ka za ayi ba ka kirata kace ka yarda maza-maza kirata. Ai wannan ba ƙaramin dama muka samu ba ni da kai da gobenmu."

"Ke wai mayyar kuɗi ce kina son kuɗi. Me yasa ba kya hango mana gaba?"

"Ina ganewa mana ai ta mu nake shi yasa na ce ka yarda."

Shi kenan amma ki sani ina tsoron kar ta kwana.

Kar ka damu ina nan ina yi maka addu'ar nasara. Da haka zaka goge.

A take ya kira Hajiyar ya sanar mata da ya yarda zai yi aikin da take so. 

Yana ajiye waya ta aika masa da million biyu ragowar sai an gama aiki.

Ai ranar daga mijin har matar babu wanda yayi bacci saboda zumuɗi da farincikin samun waɗanan maƙudan kuɗaɗɗen.

*

    A gaban kwamfutarsa yake a zaune yana duba ma'adanar saƙonninsa. A nan ya ci karo da saƙon Habib be yi mamakin yadda aka yi ya samu wannan adireshin ba saboda ya san akwai amana tskaninsa da Habib shi ya saka ma ya haƙura ya bar masa Uwaninsa.

Bai kai ga buɗe saƙon ba  kira ya shigo masa waya yana ganin lambar ya tashi haɗe da kulle kwamfutar. 

A nutse yake amsa kiran da alamu kiran na gaggawa ne kuma ya shafi aikinsu haka ya saka ya ɗauki mukullin gidan ya kashe fitulu ya fita daga gidan.Taxi ya tara ya shiga still yana amsa wayar har ya isa inda zai je.

A wurin amsar baƙi ya sa hannu aka nuna masa inda zai shiga kasancewar meeting zasu yi da wata mata wadda suke son yin aiki da ita.

  Ƙamshin turarenta da na turaren ƙamshi ya gauraye ofishin wanda yana buɗe ƙofar ya daki hancinsa.

Knocking ya yi sau biyu kafin aka bashi umarnin shiga. Kamar yana tsoron ƙofar haka ya sake ta a hankali ya shiga.

Kujerar na kallon bayansa hakan ya saka ya samu gu ya zauna kawai ba tare da an mai izini ba kun san dai halin mutumin naku.

"Har yanzu baka sauya halayen ka ba ALIYU."

"Na'am wace ce ke?"

"Baka ɗau muryata ba kenan? Gaskiya baka da kirki."

"Afuwa ban gane ki ba sai dai na ga kamar ke kin san ni."

"kai ma ka san ni. So nak ka canka da kan ka kafin na nuna maka wacece ni."

"In ko kin san ni to kin san ni ba a irin wannan game ɗin dani. Ruwanki ne ki bayyana kan ki ruwanki ne ki ɓoye kan ki ba damuwata bace. Sannan aiki ne ya kawo ni zan fi son ki maida hankali wurin yin abinda ya kawo mu akan sanin ko ke wace ce."

"Hhh! Tabbas mai hali baya fasa halinsa. Ba zaka taɓa sauyawa ba."

Bai bata amsa ba shiru yayi kawai ya riga da ya gama tsara mintinan da zai yi ya tafi ko da kuwa basu yi meeting ɗin ba. Agogonsa yake kalla yana kuma kallon ƙofar fita.

     A hankali ta soma juya kujerar kafin ta juyo gabaɗaya ta cire tabarau ɗin kan fuskarta tana dariya haƙorin makkanta ya ƙara ƙawata farar fatar ta.

"Maryam Sanda kece?"

Kafaɗa ta ɗaga tana murmushi tace "Ni ce."

"Ya Allah! Wai kina nan ƙasar dama? Kece mai ƙamfanin nan?"

"Aa Daddy dai. Kawai ina riƙon kwarya ne.Ai tuni ina da labarin kana Manchester kuma kana aiki da ƙamfanin da suke son yi mana aiki. Da ganin sunanka kawai na san kai ne shi yasa na buƙaci haɗuwata da kai."

"Lallai kin kyauta an jima gaskiya ko waya bare message."

"Botsararren mutum da kai waye zai neme ka? Ƙarshe ma ka ce baka gane mu ba. Aa ai Aliyu ba a iya maka."

Murmushi yayi ya lashi leɓɓansa yace "Bana son sharri. Ni ba haka nake ba amma duk kun bi kun ɗora min wasu hallaye."

Yatsunta ta haɗe ta kuma gyara zamanta tace "To ya rayuwa? Na miƙo maka mutuniyar ne?"

"Baki manta ba?"

"Babu abinda ya shafe ka da na manta ALIYU."

"Na gode,amma na daina shan komai."

"Miracle.Aliyu da ajiye kayan maye anya kuwa?"

"Kin san bana magana biyu. Na daina na shiryu."

"Gaskiya na ji daɗin hakan."

"Zan so mu fara abinda ya kawo mu in yaso wata rana ma tuna baya."

"Oh! Haka ne Mr.Ƙa'idatullah."