ZUCIYAR MUTUM

chapter 32

by @khairatup01

Zuciyar Mutum.
Khairat.
Wattpad:Khairi_muhd
Karamci Writers Association.
32.

*

   Shi kenan mu koma kan cinikayya. Akwai wani building da muke so a gyara mana a sake masa fasali da tsari , an yaba kamfaninku sosai hakan ya ja hankalina da na Daddy muka ga dacewar mu baku aikin. So ni dai bani da damuwa na san zaka jajirce ka yi abinda ya kamata na san aikin zai yi kyau. 

In sha Allah! Mamaki ma fa nake yi wai kin zama mutum.

Hararasa tayi haɗe da miƙewa tsaye  ta miƙa masa hannu su gaisa. "Ina fatan zan ji daɗin wannan aikin da kai?" 

Miƙewa yayi shi ma ya haɗe hannunsa biyu wuri guda yace "Na gode. Kuma da yardar Allah za ki ji daɗin aiki da kamfaninmu." 

Oh! Na manta. 

Na sani.

To in ba damuwa ka bani lambar wayar ka.

Ba damuwa. Nan ya gaya mata ta saka a wayarta. Har ƙasa ta raka shi kafin suka yi sallama ita ta shiga ta ta motar shi kuma ya tari Taxi.

*

Nigeria.
Kano.

Tashar filin jirgi Aminu Kano international airport.

Abaya ce a jikinta fara da ratsin ruwan ƙasa anyi mata adon fulawa. Ta yafa mayafi ta saka tabarau da ƴar ƙaramar jaka a hannunta ruwan ƙasa. Agogon hannunta take dubawa akai-akai. A hankali ta saki siririn tsaki ta juya a hasale....

Karo ta ci da shi. Matashin saurayi dogo bashi da haske amma da ka gan shi ka ga mara ji saboda yanayin shigar sa da ma fuskar sa. 

Ka tsora ta ni fa.

Haba ke da tsoro ? Ban yarda ba.

Ba wannan ne ya kawo ni ba ina motar?

Gata can muje.

Bin sa tayi suna tafe tana ta yi masa bala'i ko da suka halba kan titi kallon ko ina take yi tana murmushi "Mutanen cikin garin Kano sun bani raunika marasa warkewa nima lokacina ya zo. Zan basu fiye da yadda suka bani." 

Ina muka nufa?

Rijiyar Zaki.

An gama.

Yaran nan duk sun hallara kuwa?

Duk sun zo mutum ɗaya ne kawai bai iso ba amma muna sa ran zuwan shi anjima.

Waye?

Wannan da kika ce zai zo.

Tsaki tayi tace "Tsiyar ɗan ƙauye kenan." 

Kun san dai bana son failure? Gobe nake son a gama komai mu fita daga garin Kano gabaɗaya daman ba a san mun shigo ba kuma ba za a san fitar mu ba.

Kar ki damu ,Komai an tsara shi yadda ya kamata babu wani disappointment da zamu baki kawai dai ainihin aikin yana hannunki in ba ki yi ba mu ma ba zamu samu shiga ba.

Baka da matsala da ni. 

*

Misalin ƙarfe bakwai na yamma ya dawo daga ofis yazo bakin gate kuma sai wata zuciyar tace "ka je ka duba Hajiya tukunna." Haka ya juya kan motar ya koma hanyar gidansu.

Yana hanya aka kira shi a waya daga jin kiɗan ya san Ummu ce da fara'a kwance kan fuskar sa ya amsa kiran ya saka a hansfree.

   "Haba guy baka ga lokaci ba?"

"Na gani masoyiya na dawo fa na juya ban ga Hajiya da Abi ba yau."

Gaskiya ne sai ka taho in a nan ina jiran ka.

Shi kenan baki gaya min wannan kalmar ba.

Aa sai ka dawo zan gaya maka.

A a ban yarda ba gaskiya ni yanzu za ki gaya min kika sani ko in ba yau ba bazaki ƙara samun damar gaya min ba?

Haba Hamma meye haka? Ni bana son haka fa.

Yi haƙuri kawai dai ya kamata mu dinga tunawa da mutuwa. 

Gaskiya na daina kula ka.

In kika daina kula ni wa zan kula?

Uhm ban sani ba nima.

Kinga zan yi parking in zan taho zan kira ki.

To a dawo lafiya drive safe.

In sha Allah!

Tana ajiye waya yace "Ummu rigimatu kenan."  

Cikin sa'a kuwa Abin ma ya dawo Hajiya ma na nan da yan biyu abincin dare ma suke ci haka ya shiga cikin kitchen ya wanko hannunsa ya zo ya zauna a ƙasan shi ma.

"Gaskiya Abi na yi kewar wannan lokacin da muke cin abinci dukaninmu."

"Ka zo zaka cika cikin ka a nan ka bar na ƴata ko?"

"Wallahi aa Abi ita ma zan ci wannan ɗin ma zan ci ba zan ƙoshi ba ko da na ƙoshi zata fahimce ni."

"Allah sarki! Ummu ta bata da matsala yarinyar. Yanzu na san ka yi aure Baba Allah dai Ya baku zaman lafiya mai ɗorewa Ya kawo zuri'a ɗayyiba."

Sunkuyi yayi da kan sa kawai ya rasa me yasa jikinsa yayi sanyi tsoro yake ji hakan nan wani irin abu yake ji a ƙirjinsa numfashinsa ma ya sauya.

Baka da lafiya ne Baba?

Aa Hajiya lafiya ta ƙalau kawai bana son rasa ku ne.

Be san ma y  faɗi hakan ba sai da ya ga kowa ya sauke hannunsa abincin ya zube tukunna.

Kuyi haƙuri don Allah Wallahi lafiyata ƙalau kawai dai yau ina jin ina son in dinga tunawa da wata rana fa zan mutu.

Hankalin Hajiya ya tashi tuni ta ji kan ta ya sara mata ɓari ɗaya.

"Bana son haka fa Habib bana so na meye haka?"

"Afuwa Hajiya. In na samu baby girl sunanki zan saka fa in kuma namiji ne sunan Abba zan saka."

"Mara kunya kawai."

Ya ɓata lokaci a nan kafin ya kama hanya ya tafi cikin ikon Allah har gidansu Adda sai da yaje babu wacca ya shiga cikin gidanta daga ƙofa suka gaisa ya tafi duk suna mamakinsa bai taɓa yi musu haka ba.

Tun a hanya yake kiran Ummu bata ɗaga kiran ba daf da wurin me tsiren nan da take so ya faka ya fita ya sai mata. 

Yana shiga motar ya kuma kiranta amma bata dauka ba karshe ma busy ya ji ana kira masa. Tsaki yayi. 

     Kiran Sufyan ne ya shigo masa ya ɗauka.

"Mutumina ya da tsohon daren nan?"

"Wallahi normal ban san dalili ba kawai ji nayi ina son kiran ka har fa na kwanta na tashi nace bara dai na kira ka sai faɗo min kake yi a rai."

"Allah sarki! Nima kana raina har zan zo sai naga dare yayi amma da safe zan biyo."

"Allah Ya kaimu."

"Amin Sufyan."

Bakin gate ɗin gidan ya tsaya yayi horn sau uku amma ba a buɗe ba. Tsaki yayi ya sauka ya taɓa ƙaramar ƙofar ya ji ta a buɗe. Shiga ya yi sosai ya leƙa ɗakin maigadi amma bai gan maigadin ba.

Yana juyowa yaji an maka masa abu a kai. Hannu biyu ya saka ya tallafi kansa yana sakin salati bai ga fuskar kowa ba saboda jini ya soma ɗaukar sa nan ya faɗi kasa sumamme.

*

Dishi-Dishi yake gani bayan ya buɗe idanuwana a hankali. Wani irin ciwo kan sa yake yi masa haka ya sa ya dafa kai ya na son tashi hannunsa na zamewa saboda tsantsin tiles da jini  a hannun sa. 

      Falon yake bi da kallo   a wahalce nan ya hango Uwani a tsugunne tana kuka ga maza guda biyu manya masu kauri  tsaye a kanta. 

Yunkurin tashi yayi amma ya kasa ya koma yaraf ya faɗi ji kake tim ya baje a ƙasa.

  "Su waye ku? Me kuke so? ku sakar min mata ta." Ya faɗa yana cije baki saboda raɗaɗin da kan sa yake yi masa.

"Hamma sannu ka zauna kawai ka daina motsi don Allah jini ne ke zuba fa a kan ka." Ta faɗa tana kuka.

"Har yanzu kana kiranta matar ka Habib?"

Muryar ya san ta ƙoƙari yake ya ga ya tuno a ina idanuwansa ya ƙarawa girma yace "Aisha wannan shirin ki ne?"

Dariya ta babbake da ita tan  tafa hannaye tana zuwa kusa da Uwani ta sa hannu ta kwaɗa mata mari aiko Uwani ta kife a ƙasa ta saki kuka.

"Kar ki ƙara taɓa ta , ni za ki yi wa ni ne nayi miki laifi."

"Ai laifin saboda ita ka yi min. Sakina fa kayi ai dama na gaya maka sai ka yi da na sanin sakina da ka yi,na gaya muku zan dawo kuma dawowata ba zata muku da kyau ba. Yau ranar ɗaukar fansa ce ,yau ranar kece raini ce ,yau ranar dillanci ce yau nake son na nuna maka kai ba kowa bane a hatsibibanci ni babar ka ce sai ka jira Wallahi."

"Aisha ban zata haka kik ba..." 

Tsawa ta daka masa haɗe da jefa masa wata sanda a kai. 

Ƙara ya saki yana kum  dafa kai yace "Hasbunallahu! Wayyo ALLAH kai na."

"Ba ka ga komai ba Habib yau ban zo dan na bar ka ba na zo ne da ƙudiri da kyakyawan niyan aika ka barzahu kai da matar taka in yaso kuyi soyayyar a can."

"Aunty Aisha kar kiyi haka. Ba daidai bane abinda kike ƙoƙarin aikatawa ba. Allah subahanahu wata'ala baya son zalinci ,ribar me za ki ci in kika kashe mu? Duka fa abin bai kai a yi haka ba Aunty Hamma zai iya maida ke ɗakin ki...."

Bata barta ta ƙarasa ba ta sakar mata naushi a baki tuni ya soma jini bata tsaya iya nan ba ta dunƙule hannu ta maka mata a ciki.

Kukan azaba Ummu ta saki. Yayin da Habib ya yi ƙoƙarin zuwa inda Uwani take, ƙafa Aisha ta sa ta take masa hannu da takalminta kwava shoe mai tudun nan.

Aisha in kuɗi kike so ki ɗauka amma kar ki kuma taɓa Ummusalma.

Dariya ta saki tace "Ai a gaban ka zan yi maganin ta don sai na saka yarana sun keta mata rigar mutunci a gaban ka. In ya so na ga ƙarshen soyayya in ka isa ka cece ta." 

Kai Nata'ala gata nan yau dai ka cika burin ka ka ɗanɗani zumar da baka lasa ba a baya. Dalilin da ya saka na ɗauko ka kenan so nake ka koya mata hankali.

Nata'ala dama kai ne? A karo na biyu zaka ƙara cin amanata? Ashe za a iya cuta ta da kai?

"kin san shi ne Ummu?"

"Shi ne tsohon mijina fa".

"Aisha matar aurena za ki sa a ketawa haddi saboda banzan dalilin ki?"

"Kai a wurinka banzan dalili ne, ni kuma a wurina dalili ne mai ƙarfi. Kai wai me kake jira ka sauke mata mayafan kan ta ka yi mata kaca-kaca a gabansa nake so ayi ta yadda ba zai taɓa mantawa ba..."

"Aa Aisha kar kiyi haka"

Uwani ta soma ja da baya tana kuka ta na roƙon kar su yi mata haka.