ZUCIYAR MUTUM

chapter 34

by @khairatup01

Zuciyar Mutum.
Khairat
Wattpad:khairi_muhd
pg33.

Wani irin ƙarfi ne ya zo wa Habib ya miƙe tsaye da ƙyar ,Allah Ya yi nasarar bashi dama da ikon hanƙaɗa wani daga cikin yaran Aisha.

Gaban Uwani ya tsaya ta ko rungume shi gam-gam ta saki kuka shi ma rungume ta ya yi yana fitas da hawaye.

"Ya isa Ummusalma babu komai in dai ina numfashi babu wanda ya isa ya taɓa martabar ki ko da kuwa zan rasa raina ne a cikin su babu ɗa."

Dariya Aisha ta saka tana tafa hannayeta biyu cike da izgili tace "Habib baka da bakin magana , in ma mafarki kake ka farka babu wani da zai cece ka kai da matar ta ka don na riga na yanke hukuncin kashe ku duk ku biyun."

"Baki isa ki kashe ko ki raya ba ,in kika ga na mutu ko Uwani ta mutu lokacinmu ne yayi dama. Babu makawa zamu koma ga mahallincinmu wannan gaskiya ce me ɗaci da kowannen mu yake gudunta amma fa dole zata zo kafin mu wasu sun tafi ke wanda Allah Ya yi duniyar ma gabaɗaya ba shi to mu su waye?" Jinin da ya taho mai ya tofar ya kuma kallon ta cikin ido.

"Kiyi gaggawar tuba ga Allah ba gadin duniya za a bar ki kiyi ba, mu da zamu tafi yau ke ma gobe za ki tafi."

Juyawa yayi da baya ya kuma rungume Uwani sosai ya soma yi mata raɗa a kunne "Zan yi ƙoƙarin ɗauke musu hankali ki samu ki haura sama ɗakin da yake daga hannun hagu password ɗinsa UWANI da manyan baƙi , akwai waya a ciki ki kira su Hajiya su aiko mana taimakon gaggawa ki kuma kira ƴan sanda ba zata buɗu ba sai da wannan mabuɗin sirrin Aisha ma bata san mabuɗin ba. Ina son ki Ummusalma ina son ki kar ki manta da ni. Na so nayi dogon zama da ke sai dai Allah be yi ina da tsahon kwana ba...." 

Fizgo shi aka yi da ƙarfi ,cilli aka yi da shi gefe guda har kan sa yana garuwa da garu ji kake "Timm" salati ya saki yana kakarin aman jini.

Haka ya ɗaure ya tashi yayi kamar zai yi hanyar ƙofa aiko suka rufar mai duka su huɗun da yaran Aisha da ita Aishar.

Uwani na ganin haka ta yi saurin miƙewa tsaye ta tafi da gudu tayi hanyar bene tana kuka a daidai step ɗin ƙarshe ƙafarta ta zame ta faɗi kan cikinta wani irin zafi taji da azaba a cikin nata wanda ya saka ta kasa daurewa sai da saki ƙara wanda ya ja hankalinsu Aisha kan ta.

Ɗaya daga cikinsu yace "Hajiya ta gudu,ta gudu fa." Da ƙarfi ya faɗa wanda Uwani ta ji muryar har tsakar kanta tuni ta gane muryar duk da tana cikin azaba da wahalar ciwo. 

Ita ma a hankali tace "Nata'ala har da kai?" Ta na nuna shi.

Bakinsa ya kame d sauri . Aisha tace "Wawan banza da wofi wa ya saka kayi magana?"

"Salma ki gudu nace duk wuya kar su yi nasara a kan ki. Ki tuna ni Habib me ƙaunar ki ne ina son ki kuma ban bar son ki ba har ƙarshen numfashi na ba, ki gaywa Hajiya da Abi da ƴan'uwna ina son su. Ki cewa iyayena su yafe min in na taɓa ɓata musu ki gayawa ƴan'uwana su kula min da ƴa'ƴana da ke kan ki na bar musu amanar ku. Ina son...." Bai ƙarasa ba Aisha ta kuma maka mai bakin bindiga a daidai inda aka ƙwaɗe shi ɗazu.

Uwani na gani ta yi baya da ƙyar saboda jini da ke bin ƙafarta jiri take gani ma biyu-biyu take gani har ta buɗe ɗakin tana shiga Nata'ala ya iso yana son shiga tayi ta maza ta gartsa mai cizo ta kulle ƙofar ta kuma saka mabuɗin sirrin ta kwanta a ƙasa tana numfarfashi.

Buga ƙofar suke yi amma sun kasa buɗewa, har Aisha sai da ta hawo amma bata san mabuɗan ba. Tsaki tayi tace "Ku zo mu sauka kawai zai gaya mana password ɗin ko baya so don sai na kashe ta."

Uwani na jin haka ta tashi tana haɗa hanya ta soma neman waya kamar yadda ya gaya mata kusan duk kayan sai da ta zubda su kafin ta ga wayar ƙaramar nokia da lamabar wayar kowa a ciki. Sufyan ta soma kira sau biyu bai ɗauka ba ta saki kuka na tsoro da tashin hankali. 

Hajiya ta kira ita ma bata ɗauka ba.

Daga ƙarshe ta kira layin Abi cike da sarewa har zata tsinke taji an ɗaga harda sallamar Abi.

"Abi.......ku zo ku taimake mu zasu kashe Baba...."

"Hello...Hello...wace ce?"

"Abi ni ce Ummu matar Hamma Habib Aunty Aisha ce da tsohon mijina Nata'ala da wasu zasu kashe mu wayyo...."

Ƙarar bindiga kawai ta ji ta saki wayar a ƙasa baki a wangale idanuwa sun firfito waje..

Abi lafiya kuwa? Ya na gan ka haka? 

Tashi Dr akwai matsla a a gidan Baba matarsa ce ta kira ni tana kuka cewa take za a kashe su kuma naji sauti a cikin wayar amma na rasa na meye.

Inallillahi wa inna illahr raju'un Abi Baba fa ɗazun nan ya zo mana fa, ɗazun nan wanne irin za a kashe shi su waye?

Kar ki ƙara min damuwa Dr. Muje. Nan ya zari mukulli ya fita tana biye da shi jikinsa ma rawa yake yi ya kasa ma riƙe mukullin motar ma da kyau.

Aa Abi ba zaka iya tuƙi ba bara na taso Hassan da Hussain muje can.

Be iya yin magana ba ma yayi jigum Allah ne ƙadai ya san irin halin da yake ciki a wannan lokaci na tashin hankali.

Tare su Hajiya suka fito su kan su ƴan biyun ba sa cikin nutsuwarsu. A hanya Abi ya kira layin Sufyan ya umarce shi da ya ɗauko ƴan sanda yazo gidan Habib akwai matsala.

Allah ne kaɗai Ya kai su lafiya. Daidai da lokacin da Sufyan ya iso da ƴan sanda.

Tun daga bakin ƙofa suka ga motar Habib ga gate a buɗe aka koma kallon-kallon.

Ƴan sandan ne suka yi gaba hannayensu riƙe da bindiga. Ga maigadi a kwance baya cikin hayyacinsa ,gefe kuma mai gyaran fulawa da me wanki su ma a kwance.

Ainihin ƙofar shiga cikin falon ma a buɗe take. Tuni zuciyar Hajiya ta tsinke musamman da ta hango jini malale a bakin ƙofa ga wani santal kwance cikin jini. Da baya ta koma kamar zata faɗi Hassan ya taro ta shi ma jiki na rawa.

Sufyan ne yayi ƙarfin halin isa inda mutumin yake a kwance ya tsuguna hannunsa sai rawa yake yi. 

A hankali ya sa hannu ya juyo da shi da baya ya koma ya faɗi ƙasa idanuwa a rufe yana salati.

Hajiya kuwa hankaɗe Hassan tayi da gudu ta tsugunna a ƙasa ta tallafi kan ɗanta da ke fitar da jini ta saki wani irin kuka.

"Habib ne Abi mun makara sun kashe min ɗa innalllillahi wa inna illahir rajun shi kenan Baba....Ba...baba...tashiBaba gani nan na zo ni ce Hajiyar ka na zo tashi ka ji ɗana ta shi ka daina min irin wannan wasan ka ji ka tashi ka yi min magana...kai Sufyan gayawa abokin ka ya tashi ya yi min magana hannu ta saka tana marin fuskar sa a hankali daga ƙarshe ma da ƙarfi ta soma marinsa tashi umarni nake baka da ka tashi Habib ni ce Hajiyar ka fa Baba tashi....." 

Tuni sauran ma kukan suke yi kamar ƙananun yara yanayin kisan da aka yi wa Habib dole ka tausaya masa jini kawai ke fita daga jikinsa ta ciki ta kai har da ƙafa ma.

"Abi ka gayawa Baba ya tashi haka ni bana son wannan baccin ya tashi haka."

Abi zaunawa yayi a ƙasa yace "Hajiya kiyi haƙuri Baba ya riga mu gidan gaskiya...."

"Aa ƙarya ne ɗazu fa ya zo muka ci abinci tare taya ? Tayaya ma hakan... Ina UWANI?"

Sufyan na sharɓe kamar ba namiji ba ya tashi da ƙyar ya soma duduba falon shi da su Hassan har cikin ɗakunan ƙasa amma bai gan ta ba. 

Sama suka hau nan ma jinin suka gani inda jinin ke tafiya suka dinga bi har ɗakin da ta ɓuya nan jinin ya tsaya.

"Ƙila tana nan ɗakin."

Babu wanda yake da bakin magana ba za su iya magana ba saboda alhini da tashin hankali.

Buga ƙofar suka soma ganin an ƙi buɗewa ya saka suka soma kiran sunanta suna gaya mata ta buɗe su ne.

Ta riga ta shiga cikin tashin hankali jin muryar su Hassan ya saka ta ja jiki ta isa bakin ƙofar ta soma saka mabuɗin ta buɗe ƙofar.

"Sun kashe shi ko? Sun kashe min mijina ko?"

"Ƙasa suka yi da kai me zasu ce mata?"

A hankali ta dinga sauka bata damu da na ta jinin da ke bin ta ba gabaɗaya kayan jikint sun ɓaci da jini a hankali ta zauna a gaban gawar Habib cikin jini tace "Ba fa mutuwa yayi ba,bacci yake yi kawai zai ta shi yace ba zai bari su min komai ba. Hajiya yace fa yana son ku ke da Abi yace ku yafe mai..... ai nasan ma bai muku komai ba kun yafe masa amma dai ku ce ya tashi bana son wannan acting ɗin. "

Tausayi, tashin hankali da fargaba suna nan a bayyane kan fuskokin kowa na cikin falon.

Ɗan sandan ne yace "Babu kowa a gidan ina ganin sun gudu. Yaya za ayi da rubuta rifot? Naga bata cikin hayyacinta?"

"Kai ka daina ihu fa Hamma na bacci yake yi, ku fita don Allah ku bari yayi bacci mai daɗi mana baya son ana damunsa in yana bacci." Ta faɗa tana shafa fuskar sa tana murmushi.

Sai Hajiya ta koma ƴar kallo don kamar Uwani bata cikin hayyacinta. Daurewa ta yi tana ƙoƙarin janyo Uwani jikinta Uwani na fusgewa tana kallon Habib kamar zai yi mata magana.

"Hajiya wai kuka kike? Hamma fa baya son yaga kina kuka goge...goge...goge hawayen ki Hajiya baya son kukan ki Wallahi baya so.."

A tsawace Hajiya tace "Salma Baba ya rasu , ya tafi inda ba a dawowa."

Ƙafaɗa ta make kamar wata yarinyar goye tace "Aa bacci yake yi...bacci kawai yake yi fa zai tashi in ya huta.." ta faɗa tana murmushi.

Hajiya ta miƙe tsaye ta miƙar da ita tsaye ita ma ta rungumeta "Uwani ya isa muje gida muje.."

"Bazan rabu da Hamma ba."

"Eh zai tahoda Abi ne da Hassan ki bi ni muje ni"

Cikin maye tace "Haji...ya.....bacc..i yake...ba zai ....bar ni...ba alƙawari ya yi min.." nan ta sume a jikin Hajiya.