ZUCIYAR MUTUM

chapter 35

by @khairatup01

Zuciyar Mutum.
Khairat
wattpad:khairi_muhd
35.

Da wannan Uwani ta ji sanyi a ranta in sha Allahu sai Aisha da abokanan ɓarnar ta sun je inda mijinta ya je. Sun rabata da mijinta ,sun raba ƴa'ƴa da mahaifinsu,sun raba iyaye da ɗansu sun kuma rana ɗan uwa da ƴan uwansa. Ba zasu taɓa yafewa ba.

*

Tuni aka shigar da ƙarar Aisha kuma da gayya aka hoton Aisha a kafofin sada zumunta don a samu wani bayani daga waɗanda suka santa. Ɓaro-Ɓaro aka bada sanarwar ana nemanta sunan ta Aisha Hadi kuma mazauniya garin Abuja ana zarginta da hayar area boys don kashe tsohon mijinta har gida da raunata ma'aikatan gidan da matarsa duk wanda ya ganta ya kira lamabar wayar da aka bada akwai kuma kyauta ga wanda ya yi hakan.

Wannan sanarwa ba ƙaramin tada hankalin Aisha da yaran ta ya yi ba. Don kuwa ta gani a wani group ba tare da ɓata lokaci ba kuwa ta firfita daga groups na watsaap ta ma goge duk wani account ɗin ta. 

   Tana ɗaki tana tunanin mafita babu makawa babu wanda zai bata tikiti bare ta bar ƙasar to da wane kuɗi ma zata bar ƙasar ta kashe su wa yaran da suka mata aiki a haka ma suna bin ta bashi kuma sun dame ta musanmman ma babban yaron na ta Goje da yake ta yi mata barazanar tona mata asiri. Bata da nutsuwa hankalinta a tashe yake sosai. 

 Ji tayi an doko ƙofar ɗakinta an shigo. Da gudu ta afka banɗaki don tsoro ƴan sanda ta gani da bindigu a hannayensu.

"Wayyo Allah! Ku yi haƙuri , ba da gangan na kashe shi ba barazana fa naje yi masa tsautsyai ne. Kar ku kama ni kar ku tafi dani.."

"Innallillahi wa inna illahir raj'un mun shiga uku Hadi da gaske abinda ake faɗa ta aikata kisa fa tayi yaya zamu yi ta ɓata mana suna a idon duniya." Mahaifiyar Aisha ke magana tana kuka.

Alhaji Hadi kuwa baƙinciki ya ƙi sakin shi da mamakin Aishan.

"Ki buɗe ki fito Aisha mu ne ba ƴan sanda ba ne. Fito ni ne Uban ki Abdulhadi nake son ki min bayanin abinda kika je kika yi a Kano."

"Zan fito Alhaji ,zan fito amma don Allah ku saka ƴan sandan nan su koma na tuba na bi Allah na bi ku."

"Babu wasu ƴan sanda a nan. Kawai kin tsorata ne shi ya sa kike ganinsu. Ai dama duk wanda yace ba ya ji ba zai ƙi gani ba kuwa. Aisha kisa rai fa kika kashe mutum ma kamar Habib me bawan Allahn nan ya yi miki? Wallahi fuskar bawan Allahn nan kaɗai ta isa ta hana ki kwanciyar hankali."

"Alhaji ba da gangan...."

Tsawa ya daka mata wadda sai da ta tsorata fiye da baya ta buɗe jiki na rawa tana raɓe-raɓe ta fito.

Mari kuwa mai kyau shi Alhajin ya zabga mata ya kuma ƙara mata.

"Allah Ya isa tsakanina da ke Aisha yau kin bani kunya kin saka ina kunyar kaina da kaina. Da wanne ido kike son na kalli mahaifan yaran nan? Ba laifin ki ba ne wannan matar da na bari ta ɗora ku kan munanan ɗabi'u ita ce da kwamashon duk wani iskanci na ku. Sai kin bar min gidana Aisha ba za ki zama silar da ƴan sanda za su shigo min gida ba."


Tsugunnawa ta yi ƙasa ta kama  ƙafar sa ta ci gaba da cewa "Alhaji ka yi min rai..."

"Ni waye da zan miki rai? Ke ma fa wani kika kashe akan bai miki komai ba."

"Alhaji sharrin shaiɗan ne."

"Ke ce shaiɗan ɗin Aisha  ,ke ce babbar shaiɗaniyar."

"Mummy ki saka baki..."

"Ban san me zan ce ba Aisha kin gama kulle min baki ,kin kwance mini duk wasu notika masu amfani Aisha, kin bani mamaki ƙwarai duk mugun halina ba zan iya kisa ba. Ba ƙarya ba ne ban baku tarbiya ba laifina ne duk laifina ne. Na ɗauka kin haƙura da Habib ashe ke baƙar zuciyar ki ba ta bar ki ba... innallillahi wa inna illahir rajun bana tare da ke a wannan Aisha bana tare da ke."

Wayyo Allah kaico na! Na shiga uku!.

Ba ki shiga uku ba Aisha sai nan gaba.

"Officer ku shigo."

Daga Hajiyar har Aishan ƙofar suka koma kalla.Hajiya bata zata zai iya kiran ƴan sanda ba, bata zata zai miƙa Aisha ga hukuma ba.

Alhaji yaya zaka yi haka?

Saboda hakan shi ne daidai.

Haba Alhaji ƴar mu ce fa ƴar cikinmu ce fa.

Shi ya sa nake son a yanke mata hukunci daidai da abinda ta aikata. Ita ma ɗan wasu ta kashe , hakan shi ne daidai.

Ƴar sandan nan kuwa ta saka mata ankwa a hannu. Suka tusa ƙeyar Aisha gaba.

Alhaji baka kyauta mini ba kai fa me rufawa Aisha asiri ne...

Aa tsaya babu wata magana da za ki yi min. Duk abinda yaran nan suke yi rainon ki ne kece kika saka su ke kike ɗaure musu ƙugu a komai, ko an gaya miki ban san duk wasu abubuwa da kike ƙullawa ba? kina ganin kin kai suna na gun malami an rufe min baki sai yadda kika yi dani kin ɗauka Allah baya kallon kowa da komai? Kije na yafe miki amma ba zan iya ci gaba da zama da ke ba ko ba wannan daman zan sauwake miki saboda ina son amaryata ta tare jibi."


Alhaji! Aure ka yi?aure ka yi ka ce? Na shiga uku da wanne zan ji da ɗauren ƴar da aka yi ko wannan munmunar labarin da ka kwaza min. 

Na gaya miki ki tafi can tsohon gidana na Kaduna na bar miki saboda darajar ƴa'ƴanki.

Aa Alhaji! Kar muyi haka da kai.

Fita ya yi ya bar ta a wurin.

*

Manchester.

Da kewar gida ya tashi saboda haka ya saka lambar Mami ya danna sau biyu tayi ringing sai ya kasa ci gaba da kira ya katse kiran ya ajiye wayar gefe ya kwanta kan kujera yana kallon sama.

Jawo wayar yayi lambar Habib ya nema. Sai dai bata shiga ya kuma kira amma bata shiga tambayar kan sa ya yi "Wayar Habib bata shiga ko me yasa?"

Zuciyarsa tana gaya masa abubuwa da dama game da gida da fargaba ya wuni , ranar ko aikin kirki be yi a gida ba. Har dare yana neman lambar Habib amma taƙi shiga sai ya kasa nutsuwa dole ya kuma kiran layin Mami.

      Mami na ɗakin Uwani ta saka ta a gaba so take yi ta ci abinci saboda bata cin abinci kwata-kwata duk ta rame. Tayi duhu.

   "Haba Uwanin Mami in baki ci abinci ba yaya za ayi? Ni yaya kuke son nayi kenan? Ba kya son na samu nutsuwa wancan ban san a duniyar yake ba ,Habib y rasu shi nake gani a madadin Haidar nake jin sanyi a raina ke ma so kike wata larurar ta kama ki?  ba kya tunanin yaran ki?"

Hawaye ta share tace "Kiyi haƙuri Mami don Allah! Zan ci kar kiyi fushi dani don Allah!."

In ba kya son na yi fushi dake ki ci abincin nan.

Zan ci Mami, zan ci.

Tana cin abincin ne wayar ta kuma shigowa. Duba lambar tayi tace "kin ga tun ɗazu ake kirana da wannan layin na kasa ma gane kalar lambar."

"To ki ɗaga mana Mami."

Ɗaga wayar Mami, kika sani ko me muhimmanci ne kiran.

To bara na ɗaga kiran.

"Salamu alaikum." 

"Mami na!"Ya faɗa cikin sanyi.

Shiru Mami tayi kawai.

"Mamina kiyi haƙuri don Allah! Ki amsa min." 

"Me zan ce maka Haidar? Ba ka yi mana yaji ba? Yanzu kuma da me ka zo?"

"Am sorry Mami. Ki yafe min don Allah. Zan gaya miki dalili na san na ɓata muku a lokacin da kuke da buƙata ta a kusa daku..."

"Hmm! HAIDAR ina yin aiki ne."

"Mami Haidar Hamma ne?"

Ya ji muryar Ummu , zai sake magana ya ji Mami ta katse kiran.

Aka bar shi da waya a hannu baki a buɗe Mami tayi fushi kuma Habib ne kaɗai zai shigar masa faɗan nan.

Haka ya saka ya kuma kiran wayar Habib amma still not reachable. Tsaki yayi ya yi jifa da wayar gefe.

*

"Mami me yasa kika kashe? Ba Hamma ba ne?"

"Shi ne."

"Da baki kashe ba Mami."

"Na kashe ɗin shi ba tafiya ya yi ya bar ni ba?  ba tafiya ya yi ba tare da sani na ba? Ya bar mahaifinsa saboda wani dalili ƙarami? Sai ni ce aimaka sarkin son ƴa'ƴa kawai sai na ba shi fuska. Kina ganin ni ya yi mini adalci ?"

"Be kyauta ba Mami kiyi haƙuri , ki ɗan sassauta masa kin ji kin san dai halinsa zai iya kuma kashe wayar azo ayi ta nemansa kin ga bai san ma Hamma Habib ya rasu ba muna da buƙatarsa a nan."

Mami ta yi shiru bata kuma cewa komai ba game da Haidar ba. Ki cinye abincin nan tas. Ina ga ma tare zamu tafi dake can Gombe.Ita kan ta Dakta tana buƙatar kulawa ba zata iya saka miki ido yadda nake so ba."

Don ta kwantar mata da hankali tace "To Mami.Don Allah kar kiyi fushi da Hamma ,fushin ki musiba ne a gare shi." 

"Na ji uwar kinibibi."

Murmushi Uwani tayi ta ce "Haba Mami ni ɗin?"

"Ke ɗin." 

Fita tayi bayan ta tattare sauran shirgi waje.

CHIRORO.

Jiniyar ƴan sanda ce ta dinga karaɗe kunnuwan jama'ar ƙauyen Chiroro. Yara kuwa bin motar suke yi da gudu suna tsalle suna taɓa motar suna ihun "Ga ƴan sanda ,ga ƴan sanda." 

Suna ƙara shiga jiniyar na ƙara kusantar kunnuwan gidan gandu. 

Tuni Inna ta soma mita da gunguni "Yau kuma wacce bura'ubar ake yi a garin nan ? Yau ma yan balaja'un sun shigo ne ko yaya ne?" 

Kabiru inga ne ya shigo  da gudu yana haki yace "Iya ina Nata'ala yake?"

"Wanne shegen ne yake neman Nata'ala?" Inji Mari data fito da ɗaurin ƙirji ta ɗaga labulen ɗakin.

"Ƴan sanda ne suke nemansa gasu nan ma a  ƙofar gidan nan." 


Nata'ala ya fito da sauri yana saka singileti yana tambayar Kabiru suka ce  "Kai waye ka ce yana nema na?"

"Ƴan sanda."

Iya tace "Kai wacce masifar ka jajiɓo mana?"

"Iya babu abinda na yi sharri ake yi min."


"Wanne sharri za a maka na fa san halin ka shege ne kai."

Kai Iya yawa ne wannan.

Sai ga ƴan sanda sun shigo suna tambayar "Waye Nata'ala a nan?"

Kowa ya koma kallan su.