ZUCIYAR MUTUM

chapter 36

by @khairatup01

Zuciyar Mutum.
khairat.
Wattpad:Khairi_muhd.
36.


Ai Nata'ala na ganin ƴan'sandan gaske ne ,kuma shi ake nema sai ya yi baya zai bi katanga. Dan sanda ya yi masa jan kunne. 

"Idan ka ƙara taku biyu sai na harbe maka ƙafa." Ya faɗa yana gyara zaman bindiga a hannun sa.

Nata'ala bai ji ba ya kuma sa hannu zai dafe katanga. Dan sanda ya sakar masa kunamar a ƙafa. Ji kake tau. 

Tuni ya faɗo ƙasa tim yana ihu da raki "Wayyo Allah ! Na shiga uku Inna sun harbe ni ,sun harbe ni a lahira nake ko a duniya? Wayyo! Wayyo!."

Inna tayi kan ɗan ta tana salallami da sababi tana zagin dan sandan nan tana kwashe masa albarka. 

"Allah Ya tsine maka albarka kai mai baƙar zuciya kamar tufafin jikinsa.Azzalumi mai ɗana yayi maka ka harbe shi?"

Inna ku bamu haɗin kai mu tafi da shi, yana da sa hannu   kisan kai an kama sauran shi yayi saura. Idan kuna son sanin cikakken bayani ku biyo mu Kano."

"Kano?" Mari ta furta da ƙarfi. Dama tuni yaran Nata'ala suna ta koke-koke. Sauran matan gidan kuma suna ƙus-ƙus. 

   Furera tace "Ai dama da walakin rana tsaka ka fita ka dawo ka ce ka samu aikin yi kana ta wadaka da kuɗi kuna ɗaga mana hanci kai da matar ka ,ashe ma jinin wani bawan Allahn ne." 

Inna ta ɗauki buta kuwa ta jefa mata aiko ya same ta a kan hanci tuni jini ya soma zuba. 

"Saboda na faɗi gaskiya? Za ki min lahani n  faɗa makashi ne ɗan ki."

"Alƙur'anin Allah Yau sau Idi ya sake ki kin bar mana gidanmu shegiya me baƙin jini. Tunda aka kawo ki banda ci da kashi me kike yi mana? Nace me kike yi mana to yau ƙarshen ki ya zo."

Furera ta yi guɗa tace "Ayiririri! Alhamdullilahi yo da haihuwar irinsu Nata'ala ai gwara na zauna ban haihun ba. Meye a gidan gandun ne in banda tsiya? Ya sake ni sai me?"

Nan fa aka kama Nata'ala aka fita da shi. Yayyunsa maza suka bi bayan dan sandan dan ya musu bayanin caji ofis ɗin a Kano. Kaitsaye ya ce musu bompai.

Inna ta zauna a tsakar gida tana kuka aka tafi aka bar ta daga ita sai Mari. Sai zazzare idanuwa take yi kar sunan ta ya fito a ciki ,bata san Alhaji Habib za a kashe ba da bata ce ya je ba ,Alhaji Habib ya yi mata abubuwan alkairai da dama. Ta gama yanke cewa guduwa zata yi garinsu zata koma da kuɗin nan da ya ajiye zata gudu ta kama sana'a yaran ma uwarsa zata bar wa ta raina ba zata iya jigilarsu ba.

*
Manchester.

Tunda ya ji muryar Uwani kuwa bai ƙara samun kwanciyar hankali ba bacci sai dai ɓarawo amma ba dai don kan sa ba.

Ya kira wayar Mami yafi kuɗin a ƙirga amma bata ɗaga kiransa ba. Ya kira Habib wayarsa bata shiga kwata-kwata gabaɗaya hankalinsa a tashe yake don Habib baya kashe wayarsa.

Hakan nan ya daure ya yanke shawarar kiran Baffansa ya ji yaya ake ciki a can nigeria.

Lambar Baffa ya saka ya kira. Baffa na ɗaki yana kallon labarai a lokacin da Haidar ya kira shi. 

Ganin lambar waje ya saka Baffa ɗaga kiran da sauri baya son ma wayar ta katse.

   "Haidara jan zaki kai ne da gaske?"

"Baffana ni ne."

"Alhamdullilahi! Haidar kana ina? Me aka yi maka? Me ya faru ka tafi ka bar mu?"

"Baffa ka yi mini afuwa don Allah! Baffa Mami fushi take da ni ta ƙi ɗaga wayata, ta ƙi bani haɗin kai ka sa baki ta yafe min ina nan dawowa."

"Haidar baka kyauta ba, baka kyauta ba. Muna murna ka nutsu ka saisaita ashe da sauran rina a kaba? Ka girma amma har yau baka yi hankali ba? Bamu ji daɗin hukuncin da ka yanke ba. Haidar haƙuri ake da rayuwa ba komai ne kake so kake samu ba a rayuwa ba wani abin ba rabon ka ba ne , ita rayuwar duniyar nan nawa take ne Haidar yanzu-yanzu ne sai ka ji ana innallillilahi wa inna illair raj'un wanne kwana ya ƙare wata rana ma fa kai ma zaka inda wanen ya je. Kai ne kaɗai ɗana namiji , kai ya kamata ka tallafa min waye zai min in ba kai ba girma ya zo min, waɗanda suke kan kasuwancin nan asara suke min ina gani, ina ji amma haka na daure saboda jini na baya da intrest akan harkoki...."

"Aa Baffa ka yi haƙuri kar ka ce haka Baffa Wallahi na yi nadama na san na yi kuskure babba amma zan gyara Baffa. Ka yi haƙuri Baffana."

"Allah Ya yafe mana gabaɗaya."

"Baffa bana samun Habib."

"Allah sarki! Ka ga irin ta nan ai. Habib ya rasu. Yau wata ɗaya kenan Mamin ka ma bata dawo daga Kano ba tana can wurin Ummu bata da lafiya....."

"Baffa wanne Habib ɗin ne ya rasu?  Kar ka ce min Habib ɗina Habib ɗan'uwana?"

"Shi nake nufi Habib ɗan uwan ka."

"Innallillahi wa inna illahir rajun! Muryarsa na rawa yake ambatar kalmar innallillahi. Baffa Habib ya rasu? Anya kuwa."

"Mutuwa ɗaya ce Haidar mai rai a mamaci ne."

"Rashin lafiya?"

"Ko ɗaya tsohuwar matarsa Aisha ce ta haɗa kai da yan daba suka kashe shi har gida. Yanzu haka ma ana ƙoƙarin shigar da ƙara ne ko nace an shigar ma."

"Kashe shi"

Maganganun da tsayi kayi ƙoƙarin tahowa gida ayi komai kana nan kai ne namiji babba kuma ana buƙatar sa idon ka a cikin lamarin saboda samar da adalci.

Baffa zan kira ka.


Yana kashe wayar zaunawa yayi a ƙasa yayi shiru kawai yana kallon wayar hannunsa.

Habib ya rasu ya tafi ya bar duniyar gabaɗaya. Me yasa ya taho? Me ya sa bai yi tawakalli ba? Me yasa ka bai yi jarumta ba? Bai gana da ɗan uwansa ba. Sai a lokacin ya tuna da yaga saƙon Habin a mail amma bai duba da. Tashi yayi da azama ya nufi teburin da kwamfutar ta shi take a ajiye. Zaunawa yayi ya buɗe kwamfutar ya kunna ta sai da ta kawo ya soma neman mail ɗin da Habib ya tura masa.

Hannunsa har kakarwa yake yi wajen danna shiga wurin sunan Habib ɗin.

Ɗan’uwana na jini,

Idan kana karanta wannan wasiƙar, to hakan yana nufin lokaci ya yi , lokaci ya yi da na san zai zo, wanda zuciyata ta karɓa cikin shiru. Na jima da sanin cewa ni ba zan daɗe ba.Ina fama da cutar kansar kwakwalwa, amma na zaɓi in boye hakan. Ban faɗa wa kowa ba, ba ma kai ba, ba don bana ƙaunarka ba, amma don bana so in ga damuwa a idanunka.

Na rubuto maka wannan wasikar ne ba da hawaye ba, sai dai da ƙauna mai zurfi da yarda da kai.

Don Allah, kula da iyalina. Ka kasance ginshiƙi a gidana. Ka zama haske a cikin duhun da zai biyo bayana. Ka zama madogara ga ƴa’ƴana, kamar yadda ka kasance madogara a rayuwata. Na san ba sai na roƙeka ba, domin kai mutum ne mai nagarta da tausayi.

Amma akwai abin da ya fi muhimmanci da nake roƙonka a yau.

Matata… wadda na ke ƙauna da zuciyata gaba ɗaya. Ban taɓa ƙaunar wani kamar yadda na ƙaunace ta ba. Amma zan tafi, kuma bana so ta zauna cikin ƙunci da kaɗaici. Bana so ta zama gangar jiki mara rai. Saboda haka, da zuciya ɗaya da cikakkiyar amana, ina roƙonka ka aure ta.

Ka ba ta kulawa, ka ba ta kariya. Ka ba ta farin ciki, ka dawo mata da dariya. Ka zauna da ita ba don na roƙeka ba, sai don na san kai ne kaɗai mutumin da zai iya ba ta soyayya da kulawar da zata rayar da ita. Ka sani, ba cin amana ba ne wannan ƙauna ce mai tsarki. Na bar maka amana mafi daraja a gare ni.

Kada ka faɗa wa kowa game da cutar da nake fama da ita. Bana so a tuna da ni da rauni ko tausayi. Ina so a tuna da ni da murmushi, da ƙauna. Kada ka bari baƙinciki ya hana ku rayuwa. Ku ci gaba da rayuwa a madadina, ku gina farinciki daga cikin ɓarin da na bari.

Kai ne ɗan'uwana, jinin jikina, abokina na farko. Kuma kai ne wanda nake barin duniyata a hannunsa. Ina ƙaunarka fiye da yadda zan iya faɗa.

HabibHaidar.

"Ciwo ne... ciwon kwakwalwa... ban faɗa wa kowa ba…"

Wani irin sanyi ne ya ratsa jikinsa. Idanunsa suka ƙura wa sikirin ɗin kwamfutar ido kamar yana fatan kalmomin su canza. Amma sun tsaya a wurin gaskiya ce, mai zafi, mai raɗaɗi, maras dawowa. Ya zube a ƙasa da gwiwoyinsa, yana riƙe tuna kalmomin da wasiƙar a ƙirjinsa, tamkar maimaita kalomin, zai dawo da shi.

Ruwan hawaye ya fara gangarowa ba irin wanda ke da sauti ba, sai dai irin wanda ke fitowa daga zurfin zuciya, mai nauyi, marar iyaka.

"Me ya sa baka faɗa min ba?" ya furta cikin muryar da ba ta da ƙarfi, yana kallo sararin daki.
"Me ya sa ka ɗauki wannan nauyi kai kaɗai?" Tambayar da ya yi wa kan sa tamkamar Habib na wurin
Ya yi kuka ba don mutuwar ba kawai  amma don shiru. Don lokacin da suka rasa, don maganganun da bai furta ba, don rungumar da bai ba shi ba. Baƙin ciki ya mamaye shi kamar iskar sanyi, zuciyarsa na ciwo  ciwon da yake zuwa ne idan ƙauna ta zo... da makara.

A cikin wannan shirun, yana riƙe da kalmomin Habib  a ƙirjinsa, ya fahimci abubuwa biyu:

Ɗan’uwansa ya tafi…
Kuma ya bar masa ƙaunar da ta fi kowanne bankwana nauyi.

Ashe ma ba ciwon ne zai yi ajalin ka ba, ashe azzalumai ne zasu kashe ka. "Ba zan yarda ba.Ba kuma zan yafe jinin ka ba Habib sai inda ƙarfi na ya ƙare." Tashi ya yi ya ɗauko wayarsa ya shiga ta online neman tikitin jirgi bai samu na kusa ba sai nan da kwana biyu. Hakan bai masa daɗi ba amma ya na fatan ranar ta riske shi da rai da lafiya. 

Hawayen sa basu daina zubowa ba saboda taƙaicin karanta wasiƙar Habib a ƙuraren lokaci. Da ya sani ya duba a ranar da ya sani bai taho ba. Abubuwa da dama yake ta saƙawa da ƙullawa. 

Ummu ce ta faɗo mai ko a wanne hali take ciki?  Ko tana cin abinci? Tambayoyi dai birjik amma babu mai ba shi amsar su.

*

HOMICIDE SECTION
(Sashen bincike na kisan kai).

ASP Anwar shi ne me kula da case ɗin Habib

Duk wasu bayanai na shedu ya tattara, wayar Habib ,wayar Aisha da ta yaranta duk ya tattarasu ya yi binciken da ya dace ya yi a kai.

Aisha tayi laushi sosai kuma ta yanke faɗar gaskiya.

   Asp. Anwar ya kunna rikoda ya ajieye. Ya bi su da kallo ɗayan bayan ɗaya, kafin ya soma aika musu da tambayoyi.

"Shin kin yarda ke kika kashe shi?"

"Ni ce amma ba da gangan ba ne. Baraza ne ce nayi niyar yi masa kawai. Zuciya ce ta ɗebe ni na aikata hakan."

"Ƙarya kike yi. Daman kin yi niyar kashe shi. Da ba kashe shi kika yi niyar yi ba da ba za ki je da bindiga ba, ba za ki yi wa ma'aikatan sa lahani ba. Hotuna ta ɗauko ya watsa mata a gaban ta.  Nan hoton kan Habib ne kun maka masa abu kun fasa mai kai. Haka ne?"

"Haka ne."

Waɗan kuma a ina kika san su?

Ƙawata ce ta bani lambar su Inga yan daba ne manyan kudaɗe na basu don su min aikin.


Jakar kuɗin Asp ya ɗauko yace "Wannan ce jakar?"

"Eh!"

Shi wancan na Minnar fa?

Tsohon mijin Ummu ne matar Habib na kira shi ne don in saka ya keta mata haddi a gaban mijin nata. 

"Duk me yasa kika yi hakan?"

"Saboda ramuwa ,saboda kishi."

"Ribar me kika samu da yin hakan?"

Shiru tayi ta rasa me zata ce sai kuka kawai.

Kin raba shi da numfashinsa saboda kishi kawai. Kin raba iyayensa da shi,ga matarsa da yan uwansa da yaransa kuma ƙarshe an kama ki kema kashe kin za ayi.

Ku kuma son abin duniya ya saka ku aikata babban laifi. Sai ku jira hukuncin alƙali.