chapter 37
by @khairatup01
Zuciyar Mutum.
Khairat.
Wattpad:Khairi_muhd.
37
Nata'ala idanuwa zuru-zuru yake kallon Asp gabaɗaya ji ya yi duniyar ta juya masa baya to wai shi wacce riba ma ya samu ne? Tambayar da ya yi wa kan sa kenan amma ba shi da amsar tambayar a karan kan sa.
Haka aka gama rubuce-rubuce aka saka hannu aka kuma tura su prison kafin a saka ranar sauraren na su.
Sai a lokacin Aisha take nadamar abinda ta aikata, da furtawa kawai take yi ashe abin bai kai zuciyarta ba, barazana ce take yi masa saboda ta san yadda Habib yake tsananin son ta. Ko idanuwa ta rufe sai ta ga Habib kwance cikin jini kallon da ya mata kaɗai yana saka ta firgita sosai. Bata iya bacci yadda ya kamata gizo Habib yake yi mata. Kashe Habib da ta yi shi ne abu mafi muni da ta taɓa aikatawa saboda Habib bawan Allah ne.
*
Safiyar garin alhamis jama'ar Billiri suka ci karo da wani iftila'i da ya faru da Alhaji Isa ɗan kasuwa da ludayinsa ke damu. Kuɗaɗen da kowa ya san da yadda ya same su har ma ana zargin shi ya yi wa ɗan uwansa kurciya ya bar gida dawowar da be yi ba kenan shi da matarsa .
Alhaji Isa tunda ya samu labari ya bazama da gudu don gani da idanuwansa wuta ta ƙona komai kurmus babu wani abin mamora zuba ruwa ake amma kamar ba ayi.
Baki hangam ya saka hannu a ka ya tsugunna ya kurma ihu a lokaci guda.
Kamar zautace yace "Komai ya ƙone shi kenan tawa ta ƙare. Komai ya ƙone , komai ya ƙone."
Alhaji! Alhaji! Kayan ka da suka taho sun nutse a ruwa.
Ai Alhaji Isa na tashi ya cakumi wuyan Yaron nasa da ƙarfi yace "Kai Tanko ƙarya ne, nace ƙarya kake yi. Wannan sa hannun maƙiya ne da ƴan hassada ina ba zan lamunta ba."
"Dama duk wanda ya ci dukiyar maraya sai ya gani. Gashi nan yau ka ga sakamakon ka da ma ai ba gumin ka ba ne kowa ya san ta yadda ka same su. Ko godewa Allah a iya dukiyar ya tsaya" Baffan ya faɗa ya yi tafiyarsa.
Alhaji Isa yanke jiki ya yi kawai ya faɗi a wurin.
*
Mami da kin bar ta a nan ɗin ma ko don yaran nan. Bana so ta koma can.
Aa ba zan bar ta ba Dakta. Ke kan ki kina da buƙatar a kula da ke don ki manta da wannan raɗaɗin duk da na san abu ne me matukar wuya. Ina son ki fahimce ni zamanta a nan ba zai bari ta manta da Habib ba. Ita kan ta ba zata saki jiki ba ,kullum tunaninsa zata dinga yi ,daga nan sai kuka sai ciwo ya kama ta. Amma a can zan maida ta makaranta ƙila shiga cikin mutane ya saka ta ɗan samu sauƙin tunani barkatai.
Ba na son tafiyar ta amma na san yadda kika faɗa ɗin haka ne. Allah Ya bamu ikon cinye jarabawarsa.
Amin Dakta.
Yaushe zaku tafi?
Tace a bari a ƙarasa ƙarar sai mu wuce don Asp yace ana buƙatar shaidar ta dole.
To Allah Ya bamu nasara.
Amin.
*
Wayarsa yake dubawa da alama lamba yake ƙoƙarin kira.
Agogon hannunsa ya duba ya saki siririn tsaki. Ƙare masa kallo na yi da kyau ganin irin shigar da ya yi ta yi matuƙar yi masa kyau ya ƙara cika. Gashin kan sa a murmurɗe baƙi siɗik sai sheƙi yake yi saboda ya sha gyara. Takalminsa ma abin kallo ne kana ganin Haidar kallo ɗaya zaka san Allah Ya yi hallita a wurinsa. Ba fari ba ne sannan ba zaka saka shi a sahun baƙaƙe ba sai dai kalar sa mai kyau ce da kuma sheƙi. Lebbensa baƙi ne.
Mota ce ta tsaya a gabansa baƙa.
Tsaki ya kuma saki haɗe da hararar motar da wanda yake cikinta.
"Afuwa namijin duniya hold up ne ya riƙe ni ka san ana gyaran tituna zagaye na yo."
Ci kan ka bai ce masa ba ya kuma sakin tsakin ya zagaya ya shige ciki.
"Kai daɗina da kai baka da uzuri ɗan iska ban maka ma gwaninta ba da na baro matata na taho tarbar ka. Babu komai akwai lokaci zan rama."
Wallahi ka fiya surutu Taheer. Ka bar ni in ji da abinda yake damuna mana? Yaya kake so na yi ne don Allah." Ya faɗa a ɗan hasale.
"Yi haƙuri. Ya ƙarin haƙuri mu?"
"Taheer na ji zafin rashin Habib sosai. Da ace na karanta wannan saƙon da ya turo min a lokacin da ya kamata da ƙila tuni na taho Nigeria da waje zan kai shi a duba shi sosai ashe ma kwanakinsa kaɗan ne a duniya."
"To ya za ayi? Ai ba a tara sani da Allah. Addu'a kawai zamu dinga yi masa mu kuma duba bayansa shi ne kaɗai gatan da zamu yi wa Habib."
"Haka ne."
"Kotun zamu ko gida?"
"Kotu."
"Me yasa?"
"Tambaya ma kake Taheer?"
"Bana son ka je ka yi wani abun da bai dace ba ne . Na san halin ka sarai za ka iya shiga hurumin hukuma."
"Ba zan yi ba."
"Zaka yi Haidar kai ne fa."
"Ba zan yi komai ba ,amma ina son ganin fuskokin makasan ɗan uwana."
Taheer bai kuma cewa komai ba.
*
Kotu.
Bayan gama zayyano laifukan da ake tuhumarsu da shi a gaban alƙali. Aka saka su a witnnes box suka tsaya. Dama basu ba wa hukuma wahala ba kaitsaye suka amsa laifukan da ake tuhumarsu da shi na kashe Habib.
Kotu ta yanke musu hukuncin zaman gidan yari na rai da rai tare da aiki mai tsanani.
Mahaifiyar Aisha da ƴan uwanta suka dinga kuka. Mummy ta rungume Aisha wadda bata cikin hayyacin ta ma ta yi tsaye kawai tana bin kowa da kallo kamar zararriya.
"Aisha ba ki kyauta mana ba. Kin ja wa kan ki baƙin tabo. Allah Ya baki ikon cinye wannan jarabawar."
"Mummy son sa ne ya min yawa wanda rabuwa da shi ya haifar min da baƙar ƙiyaya.kishin sa nake. Ashe zan iya ..."
"Ba kya son sa munafuka. Me ya miki? Me ya saka kika kashe min amini kuma ɗan uwa? Shin kin san da kin yi haƙuri ma shi lokaci yake jira? Haukan ki bai saka kin lura da ciwon da yake yi a tsaitsye a ɓoye ba amma kika hallaka shi. Tir da mata irin ki Aisha."
Hannayen ta biyu ta haɗe wuri guda ta saki kuka tace "Haidar ku yafe min."
Ji ya yi kamar ya bangajeta ta kifa ƙasa ya yi ta duka kamar Allah Ya aiko sa amma babu dama.
Be san Nata'ala ba haka ya saka ya kira sunan da ƙarfi.
"Waye Nata'ala a cikin ku?" Ya tambaya shaye da toka.
Baki na rawa yace "Ni ,ni ne Nata'ala."
Wani irin kallo ya yi masa sai da ya ji hanjin cikinsa kamar zasu faɗo. Ya haɗiyi yawu da ƙyar.
"Allah Ya so ka da rahamarsa. Da ace hannun ka sun kai jikin Ummusalma da Wallahi sai na yanke maka hannaye in ya so nima a kama ni. Ko a mafarki ka kuma ma ganin mai kama da Ummu ni nan nine zan zame maka dodo a mafarkin sai na kar ka har lahira."
"Ban san taba ma Alhaji. Wannan ma tsautsayi ne da azal suka hau kai na."
"Mtseee ƙazami kawai." Ya faɗa yana yin gaba . Mamaki ma yake yi da aka ce wai Ummu ta taɓa aurar sa.
Tunda ya hango ta ya ji gabansa ya tsananta bugawa fiye da lokutan baya. Ta rame masa a fuska ai dole ta rame mutuwar miji ai ba wasa ba musamman ma mutum irin Habib da bai ɗauki duniya da zafi ba. Daga gafenta Mami ce a tsaye dasu Abi da su Adda har ma da Hajiya. Uwanin ma shi take kallo sai ta ga ma ya sauya mata.
Yana zuwa a gaban ta ya tsaya yace "Ummusalma ya ƙarin haƙurin mu?"
Uwani sai ta tsinci kan ta da fashewa da kuka ta sa hannayen ta ta rufe fuskarta tana yi.
Hankalinsa ya tashi ya rasa yaya zai yi ya rarrashe ta in bai yi controlling ɗin kan sa ba zai iya kamo ta ya rungume wanda ya san hakan haramun ne sosai. Kamar zai yi kukan shi ma haka ya tasaya yana kallon ta jiki na rawa fuskarsa ta sauya tayi kalar tausayi.
"Mami don Allah ku sa ta tayi shiru ,kuka fa take yi."
Mami bata kula shi ba. Hajiya ce ma tayi ƙarfin halin magana.
"Kyale ta tayi kukan Haidar dole ta yi mijinta fa ta rasa.Kai kuma yaushe ka dawo?"
"Hajiya yanzun nan na sauka."
Mami ta ja hannun Uwani suka yi gaba cikin mota suka shiga. Saitin da take ya saka kan sa ta ciki ya soma yi mata magana "Kiyi haƙuri Ummuna Allah Ya fi mu son shi ,mu ma zamu je inda ya je ki daina yi masa kuka addu'a yake da buƙata kawai. Hawayen ki tayar min da hankali yake yi don Allah kiyi shiru bana so na yi abinda nima zan zo ina jin kunya.kiyi shiru kin ji?" Ya faɗa ƙasa-ƙasa cikin raɗa ko Mami da ke kusa da Uwani bata ji abinda yake faɗa ba.
"Ka bamu wuri mu wuce ko?"
Matsawa ya yi da baya duk sai da ya ga fitar motocinsu kafin Taheer ya tsaya a gabasa.Buɗewa ya yi ya shiga cikin motar suka ja.
Duk ka bi ka damu akan kukan matar mutane kai wai a cikin mutane wanne iri ne kai?
Mstw bana ina saita kai na Wallahi in dai akan Ummu ne. In dai zan ganta to sai wani mayen ƙarfe ya ja ni gurin ta ,sam-sam bana iya riƙe kai na shi ya sa ka ga na bar ƙasar kai ka sani ban iya ɗauke kai a abu ba. Tana fita daga takaba zan aure ta ba zan bari ya huce ba.
Kai Haidar me mutane zasu ce ,kamar kana jira daman?
Babu ruwana da mutane ai dama aikin mutane ne surutu.
Duk da haka ka ɗan bari a shekara.
Wallahi ba zan iya ba.
Haba mutumin shekarar fa kamar yau ne ka ga by then kai ma ka gama aikin ka da mutanen Manchester.
Taheer ba zan iya ba kar ta samu wani, ka ga ni dama ban gaya mata ina son ta ba ka san fa Zuciyar Mutum!.
Haƙuri za ka yi ta ƙara samun nutsuwa mutuwar nan har yau tana dukan ta ɗanyar mutuwa ce a gareta ba zata so ta yi aure nan kusa ba ka daure.
Ajiyar zuciya ya sauke yace "Shekara ɗaya".
"Eh abokina Shekara ɗaya."
Allah Ya nuna mana da rai da lafiya.
Abi da Baffa suka kira Aliyu ɗaki.
Babu wanda ya san me suka tattauna a tsakaninsu bayan dawowarsu daga kotu.
Ya dai fito yana zazzare idanuwa Ummu yake nema.
Falon sama ya hau bai gan ta ba haka ya saka ya sauka zai tambayi Mami inda take.
Yana shiga ɗakin Mami ya gansu har da Hajiya sun haɗa kai suna ta kuka da alamu sun san cewa Habib na fama da ciwo cikin shiru da jarumta bai iya faɗawa kowa ba saboda baya son kowa hankalinsa ya tashi.
Tsugunnawa ya yi a gabansu ya soma rarrashinsu duk su ukun yana basu baki.
"Saboda haka Habib ya ƙi gaya muku game da ciwon da ya yi fama da shi don a duniya baya son ɓacin ran kowannenku bare tashin hankulan ku. Kar ku yi masa haka ɗan uwana jarumi ne. Addu'oinku kawai yake da buƙata musanmamn ma ke Hajiya ku bar koke-koken nan haka. In sha Allah Habib ta sa ta yi kyau mu ma muna fata mu cika da kyau da imani. In kuna kukan nan gani nake kamar ni ba ku ɗauke ni Habib ba in dai kuna kallona kamar Habib ku yi shiru haka ku ma sai wani ciwon ya kama ku, kun manyanta fa ke kuma kin biye musu kin male baki kuna ta kuka come on share hawayen ki.
Hajiya ta shafa kan Haidar tace "Haidar Allah Ya yi maka albarka. Amma duk ranar da ka kuma tafiya baka gaya mana ba tabbas ranar ni kai na sai na yanke duk wata alaƙa ta da kai."
"Na bari Hajiya ba zan kuma ba Wallahi."
"Shi kenan."
Hajiya ki tayani bawa Mami haƙuri ta yafe min na sani na mata laifi na ɓata mata rai amma ba zan kuma ba ta kalle ni ta yi min faɗa ma ni zan amsa amma don Allah ta yi haƙuri ta yafe mini.
Hajiya ta kalli Mami tace "Ni da ɗana muna barar yafiya ayi haƙuri a yafe mana don Allah."
"Ya ci darajar masu daraja amma da yadda na tsara Haidar babu ni babu kai kaje can ka kare kai ka sani."
Ƙafafuwan Mami ya kama da sauri ya ɗora kan sa akan cinyarta yace "Na tuba Mami na bi Allah na bi ki. ko fita zan yi sai na sanar miki amma kar kiyi fushi da ni haka in kika bar ni kuma Mami wa zan kama? Ai rayuwata ta shiga cikin kwalekwalen wahala da tashin hankali kenan."
"Ta wuce Allah Ya yafe mana gabaɗaya."
"Amin."
"Yaushe zaka tafi Gomben?"
"Da ku zamu tafi ai."
Mami bata kuma cewa komai ba kar ya zo ya yi ɓarin baki don zai aikata babu ruwansa.
Tashi yayi yace "Wanka zan je na yi in ci abinci in huta na gaji."
"To hakan ya yi. Ka je za a aiko maka da abincin."
"Na gode Hajiyata ni kaɗai." Ya faɗa yana hararar Uwani.
*
Afeeya!
"Umma yanzu shi kenan mun haƙura kenan mun zub da makaman yaƙin mu na ganin mun ɗauki fansa a kan ƴan gidan nan?"
"Bamu haƙura ba amma dole mu tsagaita saboda rashin madogara a halin yanzu."
"Umma ina malami ne kike nema mai zafi?"
"Afeeya Malamin nake nema irin wanda aikinsa ya fi ma na yankan wuƙa. Ga iftila'in da ya faɗawa Isa an ce yana can bai ma san waye a kan sa ba dukiyar sa ta tashi a iska ta ƙare. Kuma dama shi ne kusan ƙarfina."
"Umma ai ki manta da Baffa Isa kawai ki fara tara kuɗaɗe manya don akwai wai malamai iyamuri a can da aka haɗa ni da shi ance sha yanzu magani yanzu in dai an bi dokokinsa."
"Inyamu ri kuma? Ke Afeeya shi fa iyamuri ance shan jini suke fa jinin uban ki zamu kai?"
"kai Umma wanne ubana kuma ana zaune ƙalau."
"Yo ai dole ne na tambaye ki. Ki bari Baffan ya dawo daga Kano in na samo kuɗi sai muje na ji ance Haidar ɗin ma ya zo gari."
Afeeya ta gyara zamanta tace "Umma ya dawo da gaske?"
"Ya dawo mun yi waya da Baffa shi ne ya ke gaya mini Haidar na tare dasu a Kano."
"Alhamdullilahi! Faɗuwa ta zo daidai da zama."
*
Kwana biyu suka ƙara a Kano suka taho Gombe. Ɗakin ta dai a ka gyara mata an tsab sai ƙamshi ke tashi a ɗakin.
Wanka ta fara yi kafin ta kwanta baccin ma bai gama ɗaukarta ba Iya ta kawo mata abinci wai Mami tace ta cinye shi tas.
Da to ta amsa ta shiga banɗaki ta kuskuro bakinta, abincin ta ci kaɗan ta haɗa da ruwa ta sha. Wayarta ta janyo ta shiga watsaap "Ya ROOH sunan da ta fara cin karo da shi kenan ta shafi sikirin ɗin wayar tana kallon sunan. Cikin ma'adanar saƙonsa ta shiga ta kunna voice ɗin da ya yi mata ta saurara ya fi sau shurin masaki tana maimaitawa tana hawaye. Da ta gaji da nan ta koma kan hotunansu ita da shi da na sa shi kaɗai wani vedio ɗin ta yi dariya wani kuma ta yi kuka.
"Ya Rooh ina kewar ka! Ba zan taɓa mantawa da kai ba a rayuwa ta. Allah Ya jajada rahama a gare ka."
A haka baccin ya kwashe ta waya a hannu fuska da busheshen hawaye.
Daga taga yake kallonta kuma hawayenta na taɓa shi kamar ana ɗiga masa ruwan dalma. Da ƙyar ya bar bakin tagar ya koma na sa ɓarin ya zauna kan kujera ya lumshe idanuwansa.