ZUCIYAR MUTUM

chapter 39

by @khairatup01

Zuciyar Mutum.
Khairat
wattpad:Khairi_muhd.
38.

Tunani kawai yake yi barkatai game da yuwuwar tarrayarsa da Ummu a gaba ,yadda ya lura tana son Habib sosai kuna cire son Habib zai yi matuƙar wahala daga gareta amma ba zai sare ba zai gwada sa'arsa shi ma zai wuce wurin yadda Habib ya kafa gwamnatinsa shi ma da yardar Allah zai kafa ta sa har ma ta fi ta sa.

Bai yi aune ba kawai ya ji kamar hannun mutum a saman fuskar sa yana yawo. Da sauri ya buɗe idanuwansa don ganin wane ɗan rainin wayon ne.

Afeeya? 

Hamma.

Afeeya sau nawa zan gaya miki ki daina shigo mini ɗaki ? 

Babu adadi amma ka san in har kana nan dole zan zo. Magana ce nake so mu yi da kai.

Afeeya kamar yadda a baya na gaya miki ba ni da wata magana da ke yau ma zan ƙara maimaita miki ba zan yi magana da ke ba. Ki tashi salin alin tun kafin na ɓalla miki waɗanan ƙafafuwan masu kama da na sillen kara kiyi waje.

Ƙafafuwan nawa ne na silen kara? Saboda me ka tsane ni haka ne wai? Me na yi maka?

Ke wai a marasa hankali da tunani ma lamba ta nawa zan baki ne? Na rantse da Allah in ba ki tashi kin fita ba sai na miki lahanin da ba ki zata ba.

Tashi tayi tana kallonsa cike da taƙaici da ɓacin rai. "Yau zan tafi amma ka sani zan dawo da shiri na".

"Mtsw" Ya yi mata tsaki kawai ya juya mata baya.

Ƙwafa tayi ta juya ta fita.

Ƙofar ya bi da kallo yana jin dama ya mareta ya ɗan bar mata shati a fuska.

*

Rayuwa bata zuwa da sauki kuma bata kasancewa ɗari bisa ɗari sai dai kawai mu godewa Allah da kuma roƙon ikon cinye duk wata jarrabawa da yake jarabtar mu da ita a kowanne mataki na rayuwa don gwada imaminmu. 

Ummusalma ta fita daga takaba. Duk da haka mutuwar mijinta sabuwa take koma mata a kodayaushe.

Bata ma fara zuwa ko ina ba sai da ta ƙara wata biyu a gida bayan waɗancan wattanin a gida cike da kulawar Mami da Baffa.

Haidar ya kan je Manchester yayi sattituka ya dawo wata doguwar magana ma ba haɗasu tayi ba har lokacin. Zai tambayeta yaya take kullum zata ba shi amsa ya fice.

Yau ma ta gama shirya kayanta kala goma zata can Billiri wurinsu Dada ta kwana biyu don gidan ya ata shiru sosai babu kowa sai Mami da Baffa. 

Ta fito da kayan falo ta ajiye ta koma ciki don ɗauko mayafinta da wayarta.

Mami ta samu a falo ita ma cikin shiri tare zasu tafi don duba ma Baffa Isa da jiki yaƙi daɗi ya samu shayewar ɓarin jiki.

Mayafin ta yafa tace "Mami muje?"

"Eh! Mu je ina son na dawo ma da wuri saboda Haidar na masa girki."

"Yana nan dama?"

"Jiya ya dawo da daddare na san yana can yana baccin gajiya."

"To."

Bakin motar suka tsaya Joɓe ya saka kayan Ummu a booth ya rufe. Zasu shiga daga ɗan nesa kaɗan ta hango Haidar yana kallonsu. Jallabiya ce a jikinsa fara. 

A hankali ta ga ya taho inda suke. Mami tace "Ya kika tsaya kuma shigo muje."

"Mammi Hamma ne ya taho."

To.

Bai ƙarasa inda suke ba, da hannu kawai ya yafito ta da ta je.

A hankali ta ke takawa har ta isa inda yake.

"Barka da rana Hamma."

"Ba zan amsa ba. Sai da kika gan ni a nan za ki min wata barka? Ba wannan ba in za ki je?"

"Billiri."

"Me ake yi a can?"

"Babu komai ,zan je na kwana biyu ne a can wurinsu Dada na kuma dua jikin Baffa Isa."

"Ke jindaɗi ya miki yawa na san wannan aikin Mami ne ma ta kitsa miki. Don za ki Billiri ni ba zaki gaya min na baki izini ba?"

"Hamma ai na gayawa Baffa kuma yace na je."

Ƙwafa ya yi ya buɗe baki yace "Ummu kin gama raina ni naga alama. Wato ba za ki tambayen ni ba? To Baffan da ya ce ki je mene ne ai a ƙarƙashin ikona kike saboda ni Habib ya ba wa amanar ki. Shi ma Baffan yana sani ya shiga maganar nan. Daga yau in za ki yi abu ni za ki gayawa na gaya miki."

Mamaki bai bar Ummu ba yadda yake yi mata kamar wani mijinta ko saurayinta amma da ke ta san hali sai ta amsa masa da to "Kayi haƙuri. Yanzu in tafi?" 

"Eh je ki." 

Tare suka jera har bakin motar ya gaida Mami ya kuma aika ƙorafinsa na ƙin sanar masa da ta yi ta lallaba shi ta ba shi haƙuri ya tambaye wa zai ba shi abinci  Mami tace ya duba dinning anjima da wuri zata dawo tayi masa na dare. 

*

Tashi suka yi babu Mari babu kayanta sai yaran da ta bari suna ta zabga ihun kuka a gida.

Iya da ta gaji da koken yaran ta daka musu tsawa suka ko kame bakinsu. 

Yau na ji jaraba uwar ku ta gudu ta bar ku ,uban ku yana can  a kulle sai baba ta gani, ku nan kun haɗa baki zaku kashe ni da kuka ku bar ni na ji da ɗaya mana?

Tsit suka yi yaran suka koma zazzare idanuwa suna ajiyar zuciya yunwa suke ji.

Iya ta saki tsaki ta juya ta kalli Hajara tace "Ki zubo musu abinci  mana su ci da gani yunwa ce ke cin uwrasu da ubansu. Kai ni kam na ga rayuwa ƴa'ƴa kamar ƴan Allah bani duk babu masu mutunci su yi ta ɗauko mini magana a gari abin nan ya ishe ni Wallahi.

Hajara ta ɗan kanfato abinci ta zuba musu a kwano guda su uku wanda mutum ɗaya ma abincin yayi masa kaɗan.

Iya ta kalli kwanon abincin ta karkace baki tace "Yau na ga sabon masifa. Ke Hajara ki fita daga idona in rufe."

Hajara ta turo ɗan kwali gaban goshi tace "Iyakar ta kenan Iya su ci su sha ruwa. Ai ana ma musu ƙoƙari wurin ciyarwa"

Ai na ga cefanen wan ubansu ne yake yi ko?

Haba Iya a zuba miki a zubawa mijinki sanan a zubawa kattin samarinki yan zaman kashe wando yanzu kuma ga waɗanan ni mijina in ji ne ko meye?

Eh ƙwarai. Zai zo ya gaya mini ko shi ne ya gaya miki ya gaji da ciyar da mu shegiya ƴar dangin matsiyata mayya.

Hajara ta saki ihu ta dire a ƙasa kamar ƴar bori ta saki kuka an zage ta da iyayenta.

Iya kuwa ta ɓantari goro ta gyara zamanta tace "Yau za ki ga iko na uwa don uban ki. Sai kin kwana a gidanku yau."

Hajara ta sani sarai Idan Iya ta ce mijinta ya aikata gida aikata zai. Don suna jin maganar uwarsu sosai fiye da kowa a cikin gidan.

Rarrafawa tayi ta kamo ƙafar Iya tana magaiyar tayi haƙuri ba zata kuma ba akasi aka samu tuntuɓen harshe ne.

Iya kuwa ta murza kambun nata. Ta juya mata ƙeya ai yau sai kin kwana a gidan uba.

*

Baffa isa babu bakin magana sai hawaye kawai da ido ɗaya.Musanmman da Ummu taje duba shi sai ya ji kunya. Ya yarda duk abinda ba naka bane sai Allah Ya raba ka da shi. Iya mugunta ya yi wa ɗanuwansa da ƴar sa ga shi yau babu komai a cikin dukiyar komai ya ƙone wasu kuma sun nutse. Ga shi a kwance babu ƙafafu babu hannaye bakin ma babu damar magana. Duk waɗan da yake tsammanin zasu taimake shi basu ma zo ba musanmman Umma da yake yi mata aiki. Amma Mami ma ta zo ace yadda yake da Umma bata zo ba.

*

"Ai Isa ya ga isharar Allah."

"Gaskiya ne ka ji tsoron hakkin wani. Allah baya yafewa sai dai wanda ka yiwa ya yafe maka. Ina zai ga Hemmu da Hindu ai babu."

"Wallahi Mami ba zan yafewa Isa ba . Yaje can ya ƙarata."


"Salamu alaikum!"

"Wa'alaikumsalam"

Mami ta juya da mamaki bayan amsa sallamar tace "Haidar?"

"Mami.Ba zan iya zama ba."

Kallo kawai ta bi shi da shi. Ta juya suka ci gaba da hirarsu da Dada.

Da ya gaji ya tashi ya shiga ciki sai dai bai ga Ummu ba nan da nan ƙirjinsa ya harba ya fito ba tare da ya kula su Mami ba ya fita.

Mami ta kalli Dada tace "Dada wannan yaron fa Ummu ya biyo. Dama na san zai biyo mu amma ban ɗauka da wuri haka ba."

"Ai na lura da haka.Ba ki ga ya duba bai gan ta ba ya fita neman ta."

"Zan taka masa birki bana son kayan shirme."

"Babu ruwanki. Ki ƙyale shi kika sani ko ayi ƴar gida?"

"Ai yanzu ya yi wuri Dada. Kar a ga rashin hankalinmu."

"Aa wannan kuma iko ne a mai duka. Mu sa ido kawai.Ni ina son na ga hankalin Ummu ya kwanta. Ai ko ba daɗe ko ba jima dole zata yi aure nawa take dukan ta ita Ummun? Ai dole sai ta yi auren kinga da na waje gara na cikin gida."

"Allah Ya yi mana zaɓin da ya fi alkairi."

"Amin."

*

Gidan Yafendo ma bata nan. Kuma ba zai iya ce musu ina Ummu ba kar a ɓaro jirginsa hakan ya saka ya koma gidan Dada sai dai a tsakar gida ya zauna suna hira yana kallon ƙofa wani bin kuma ya duba agogonsa. Tsaki kuwa ya yi shi ba adadi.

Sai daf da magariba ta dawo sallamarta ya jiyo Mami da Dada suka amsa sai ya kulle idanuwansa.

Wata sallamar ya kuma ji ta namiji tuni ya buɗe idanuwansa ya ga waye.


Mami ce ta amsa tana murmushi tace "Tare kuke Kamalu?"

"Eh Mami. Ashe kin zo kema? Ya hanya?"

"Alhamdullilahi! Ina ka samo ta?"

"A bayan layi ina tahowa na gant sai muka ƙaraso."

"Ka kyauta. Dama ina shirin kiranta naga mariba ta yi ashe ma kuna tafe."

"Eh Mami."

Mami na gaji.

Ai dole.

Kamal ya miƙe yace "Ummu zo mana."

"To Hamma." 

Tashi tayi ta bi bayansa. 

Haidar tuni ya shiga cikin tashin hankali. Zuciyarsa na ta masa zafi. Bai motsa ba kusan sakan biyu daga bisani ya zari buta ya shiga ya kama ruwa ya zo ya yi alwala ya fita ba tare da ya kula kowa ba.

Dada na dariya tace "Kishin ƴan maza ya tashi."

Mamin ma dariya tayi tace "Ai na lura tuntuni."

Ko kallon inda suke bai yi ba ya fice zuciyarsa na tafarfasa.


"Hamma Kamal ka yi haƙuri don Allah! Ina buƙatar lokaci kafin na ƙara samun nutsuwa sai mu duba lamarin mu gani."

"Haka ne. Allah Ya shige mana gaba. Ya yi mana zaɓin da ya fi alkairi amin."

"Ita ma Amin ɗin ta amsa."

Ya yi mata sallama zai tafi massallaci.

Juyawa tayi zata shiga ciki ta ji kawai an riƙo hannuta da ƙarfi. Tsabar zafin riƙon da ta ji sai da tayi ƙara kaɗan "Argh!"

Juyawa tayi da sauri ba sai ta tambaya ba ta san waye saboda tuni ta ji ƙamashin turarensa na armani. Amma bata san ya zo garin ba don ko da ta shiga bata lura da shi ba.


"Abinda ya sa kika zo garin kenan?"

A hankali tace da shi "Hamma akwai zafi ka cika min hannu."

"Come on, ki ba ni amsar tambayata. "

"Aa." Ta faɗa bakinta na rawa.

"Waye wancan ɗin?"

"Hamma Kamal ne fa."

"Ummu na lura so kike ki kashe ni kafin ki huta."

"Innallillahi wa inna illahir rajun aa Hamma me na yi maka?"

"Kin sani sarai. Kin sani bana son na gan ki da kowa. Kina sane amma sai kin yi abinda bana so ranki yake miki daɗi. Wallahi ki shiga hankalinki baki ji yadda ƙirjina yake sama da ƙasa ba. Ki saka hannun ki a kan ƙirjina ki ji.""

Duk ta tsorata.Jikinta sai rawa yake yi. Ƙoƙarin kwatar hannunta take yi amma ta kasa ya riƙe gam.

"Bana so Ummu, bana so kada ki ƙara kula kowa na gaya miki. Kamar na sani zuciyata tace in zo in gani kuma na gani."

"Ka yi haƙuri to na daina." Ta tsinci kan ta da faɗar haka.

A hankali ya saki hannun na ta ya shige ya bar ta a wurin.

Bayansa ta bi da kallo tana mamakin abinda ya yi mata yanzu. Tunani ta faɗa kan ko dai ..... tunanin hakan ma kaɗai ya ɗaga mata hankali.

Sum-Sum ta shige ciki kaitsaye ɗaki ta shige. 
Shi kuma bai ƙara bi ta kanta ba yana zaune yana jijjiga ƙafafuwansa.

Mami dai bata kula su ba. Dada ta zuba masa tuwon dawa miyar kuka ta sha man shanu ga nama a ciki da yajin daddawa. 

Yunwar yake ji haka ya saka ya sa hannu bayan ya wanke ya soma cin tuwon kuma ya mai daɗi sosai tuwon. Ya kai lomar ƙarshe aka yo sallama.

Wani yaro ne hannunsa da wata leda ƙatuwa.

Dada tace "Iro daga ina?"

"Dada Hamma Kamal ne yace a kawowa Adda."

Ba Haidar kaɗai ba ita kan ta Ummu dake ɗaki sai da taji faɗuwar gaba. Ta dafe ƙirjinta haɗe da sakin ajiyar zuciya.

Hamma kuwa ajiye lomar ya yi ya tashi ya wanke hannunsa. Ya fice daga gidan.

Dada ta amsa leda tace "Kace masa an gode."

Ya fita.

"Ke Ummu fito ki amsa saƙon naki."

"To Dada."