chapter 40
by @khairatup01
Zuciyar Mutum.
Khairat.
Wattpad:Khairi_Muhd.
40.
Gaban mudubi taje ta tsaya tana kallon fuskarta. Shafawa ta yi don ba ƙarya fa ta maru wurin zafi yake yi mata sosai. Rau-Rau ta yi da idanuwa cikin ranta kuwa tunani ta soma. In wani abu ya same shi fa? Da sauri ta je kan gado ta soma neman wayarta a ƙasan filo ta ga wayar.
Sau uku tana kiransa amma bai ɗaga ba sai ta ji hankalin ta ya tashi sosai. Ta kuma gwada kiran wannan karon katse kiran ya yi. Haka jiki a saluɓe ta ajiye wayar ta kishingiɗa ta soma tunanin yadda zata yi ta shawo kan sa ba.
Sai Kamal ya faɗo mata a rai. Shi ma kiran sa ta yi. Ko bugu biyu bata yi ba ya ɗaga kiran.
Kafin tayi magana ya yi saurin katse ta. "Na san haƙuri kike son bani amma bana buƙata na hutashe ki. Kira na ma da kika yi kaɗai ya faranta mini rai. Na gamsu, kar ki ji komai Ummu ni son ki nake da gaske kuma aure nake so mu yi ni da ke....."
Katse shi tayi tace "Hamma Kamal da farko ina son na baka haƙuri bisa abinda ya faru tsakaninka da Hamma Haidar. Na biyu kuma ina roƙon ka da Allah kada ka kuma kawo zancen aure a tsakaninmu.Wallahi bana son tashin hankali. Na san halin Hamma ba zai bar faɗan nan ba...."
"Ba na tsoron Haidar. Soayyar ki yake nema nima ita nake nema kuma ba zan janye saboda Haidar ba sai dai in ke kika ce ba kya sona. Ni ban tsoron Haidar waye shi?"
"Ba tsoro ba ne. Amma tabbas bana son ɓacin ran Hamma. Bani da tamkar shi a duniya shi ɗin wani bango ne a gare ni . Don Allah mu tsaya a iya matsayin mu."
"Son shi kike?"
Shiru tayi ta kasa ba shi amsar wannan tambayar.
"Shi kenan na fahimta. Allah Ya yi mana zaɓi ma fi alkairi. Amma kiyi tunani mutumin da ya iya marin ki a gaban duniya saboda kishi wata ran zai iya dukan ki ma." Daga haka ya kashe wayar. Ta bi wayar hannunta da kallo. Kalmar "Son shi kike" ta dinga yi mata yawo a kwanyarta , wanne irin so dama sau biyu ake soyayya? Ita fa bata tsanmmanin baya Habib zata iya son wani. Amma me ya sa ake cewa sun dace? Ake musu kallon masoya alhalin Hamma Haidar bai taɓa cewa yana son ta ba? Amma ta lura da abubuwan da yake yi sun yi kama da na mai son nata? Ajiyar zuciya ta sauke ta sauka daga kan gadon ganin ba zata samu amsoshin tambayar ta ba.
*
Shigar sa gida ke da wuya ya shiga ɓangaren Baffan ya same shi yana cin abinci. Umma ce ma a ɗakin. Tana ko ganinsa ta saki tsaki ta banka mai harara.Da ke Haidar ba a cikin nutsuwarsa yake ba bai bi ta kan ta ba yi ya yi ma kamar bai ganta a wurin ba.
"Ina jin ka Babana."
"Baffan da kai kaɗai nake son yin magana." Ya faɗa ba tare da shayi ko shakku ba,ya kalli matar Baffan na sa Umma da gefen ido.
Umma kuma ta kalli mijin na ta da mamakin jin umarnin basu wuri da ya yi.
Ita dama ba mace bace mai ɗaukar raini ko ta ɗauke kai. Bata iya ba.
"Ai kuwa babu inda za ni."
Haidar ya kalle ta ya yi ƙwafa ya gyaɗa kansa dama a cikin tsininsa yake. "Wallahi Baffa in bata fita ba nima ba zan fita ba kuma ko a tsakiyar ku ne sai na kwana don na isar da saƙona."
Baffa yace "Ba fa na son shirma wanne irin zance ne wannan abu babu daɗin ji babu tsari?"
"Ai dai na ja kunne ko? Kuma an san zan aikata. Bana son lamarin da a gaba za a ce ban faɗa ba ko Haidar baka kyauta ba."
Baffa ya rasa me zai ce da Haidar. Ya sauke ajiuar zuciya ya kalli Umma yace "Tashi ki je ki ɗan bamu wuri."
Taƙaici da baƙinciki suka saukar mata lokaci gudaa duniya bayan Fatima Haidar ne na biyu a mutanen da ta tsana Wallahi. Yau ko wuƙa aka bata aka ce an bata dama ta kashe mutum to Haidar ne na farko da zata kawar a doron ƙasa. Tsaki ta saki tace "Da ni kake zancen. Munafukar uwar ka ce ta aiko ka don ka ɓata min shiri to ƙarya kuke nace ƙarya kuke."
"Ba ki da aiki sai na biyewa Aliyu ke kam. Ki je na ce ni bana son irin wannan shirmen."
Fuuu ta wuce kamar iska ta banko ƙofar ɗakin.
Tana fita Haidar ya kwantar da kan sa a kan cinyar Baffa ya saki kukan da yake cin sa tun daga Billiri. Hankalin Baffa ya tashi ba zai iya tuna ranar ƙarshe da ya ga Haidar na irin wannan kukan ba. Duk sai ya ruɗe jiki na rawa ya soma shafa kan ɗan sa tilo yana tambayarsa ba'asi.Amma Haidar ya kasa cewa komai jikinsa rawa kawai yake yana kuka.
Baffa ya ɗau wayarsa da ke gefensa ya soma kiran layin Mami.
Mami na ɗakinta tana kallon labarai ta ga kiran Baffa ta san ba kwananta ba ne amma tunda ya kira ta akwai abinda yake so.
"Ki same ni a ɗakina yanzu." Abinda ya faɗa kawai ya kashe wayar.
Miƙewa tayi ta saka slippers ɗinta. Cikin ƙanƙanin lokaci ta isa wurin Baffan.
Tana buɗe ƙofar tayi kyakyawan tozali.Hannu ta saka ta kama haɓa tace "Ni ƴasu mai zan gani? Haidar ke kuka da gaske?"
Baffan ya yi murmushi kawai ya nuna mata wuri ta zauna.
"Lafiya Alhaji?"
"Yadda kika gan shi ,haka na gan shi ni ma shi ya sa ma na kira ki. "
"Haidara yaya aka yi? Haba namijin duniya saifullahina me ya faru?"
"Mami ,Baffa don girman Allah ku taimaka wa rayuwata ku ba ni abinda nake so. Zuciyata zafi take yi mini da raɗaɗi na kasa nutsuwa kullum ina hanya, ba zan iya ba ba zan jura ba Baffa ganinta fa na yi da wani ni kuma kun ce na jira ta samu nutsuwa wacce nutsuwa kuma? "
Sai a lokacin suka gane kan maganar.Mami tace "Turƙashi sannu sarkin kishi. Yanzu me ka aikata ma zan fara tambayar ka tukunna.Da ka gan ta da wani sai ka yi me?"
"Duka na yi masa ita ma na mareta."
"Ahaf! Ai shi kenan sai ka nemo mai auran ka. Mari fa? Yaushe zaka yi hankali Aliyu?"
"Mami bada niya ba ne idanuwana ne suka rufe."
Tashi Mami ta yi tace "Ga ka ga Baffan ai ni bacci zan bani da lokacin rigima da rashin gaskiyar Aliyu."
"Aliyu baka kyauta ba. Ai in an girma a san an girma. Ka wuce wannan matakin ni wai baka son na huta ne? Baka son a huta ko don baka haihu ba shi yasa kake gani kamar har yanzu kai yaro ne? Ko gani kake abinda kake yi daidai ne? Ba fa tsoron ka nake ji ba son ka nake yi kawai. Amma fa son ba zai hana ni na ƙirɓe ka ba kamar jajjagen kayan miya. Na gaji da abubuwan da kake aikatawa ,na gaji."
"Baffa..."
"Let me finish Aliyu. Me yasa ka mare ta? Baka san dukan mace babu kyau ba? Kana ganin bayan wannan abinda ka aikata zata ga girman ka ne? Kallon mai dukan mace zata na yi maka."
"Baffa haushi ta bani.Don me zata dinga kula wasu?"
"Ta kula ɗin. Nace ta kula."
Da sauri ya kalli Baffan yana jin wani sabon tashin hankalin.
"Kalle ni da kyau am serious. Auren ta kake yi da zata ƙi kula wasu?"
"Innallillahi wa inna illahir raji'un na shiga uku Baffa ka ɗauki wuƙa ka daɓa min kawai a ƙirjina kawai na mutu da wannan maganar da kakr faɗa na Ummu ta kula wasu bayan ni."