Raina!

Chapter 4

by @ayshashafiee01

*Raina!*

*Aysha Shafiee*

*04*

~ * * ~

_She came for work… but destiny came bare-chested.-Safina._

***

Idanun Safina a zare suke tun daga lokacin da suka tunkaro katafaren ginin da take kallo a gabanta da sunan asibiti, lokacin da Baba Alhajin ya tsaida motar a gabansa kuma sai da ta kifta idanunta ta sake bude su akan ginin.

Baba Alhaji ya kalle ta ya juya ya kalli ginin da take kallo sannan yayi dariya.

"Wai mamakin wajen kike?"

Sai ta juyo ta kalle shi.

"Baba Alhaji abinda ya fi mamaki nake yi, wallahi ban taba tunanin haka wajen nan yake ba. Yanzu duk nan asibiti ne?"

"Asibiti ne mana, wannan wajen da kike gani ya fi shekara ashirin a haka, ni nayi mamaki ma da kika ce wai baki san wajen ba, ko da yake ke ba fita kuke yi ba."

Safina bata amsa ba juyawa tayi kawai ta sake kallon ginin, yau ta tashi da wani irin nauyin jiki da ma na zuciya, tun karfe ukun dare da ta tashi bata koma ba duk abinda ta san zata yi a wannan lokacin na kafin asuba ta yi shi ta gama, don haka bayan tayi sallar wanka kawai tayi ta shirya, amma duk da haka sai da Inna tayi mata faɗan bata sauri sannan ta dage ta yaki zuciyarta ta ƙarasa shirin.

A jiya da daddare ne Gwaggon ta kira Baba Alhaji tave ta gaya masa wajen da zata je ya kaita tunda da sassafe zata fita ba lallai ta sami abin hawa da wuri ba, kuma tana fada masa sunan asibitin yace ya san shi har ya kwatantawa Gwaggo ma da cewar itama ya taba kaita gashin kafa asibitin, bayan haka kuma ya shiga mamakin yadda ta sami aiki anan tare da taya ta murna.

Ita dai tun daga nan jikinta yayi sanyi jin yadda ya dinga yabon asibitin da taya ta murna, to da ta tashi kuma da tunanin fara sabon aikin da bata san komai akansa ba sai komai ya dada ninkuwa akan yadda ta kwana tana ji, to amma duk da haka a cikin lissafinta kaf! Bata lissafa cewa wai girman wajen da zata tunkara ya kai haka ba.

Idanunta ya sake bin ginin da kallo tun daga sama har ƙasa, idan aka ce ta siffanta shi a bayani to zata ce marabarsa da ginin bankin CBN da take gani a hoto kawai girma ne, amma kawai shi aka kwaikwaya akayi abinda take gani a gabanta.

Wani irin ɗumi ya baibaiye tafin hannunta dana ƙafarta a lokaci guda, taji mararta ta ƙulle, wani sbu kamar fitsari ya 'na cika wajen ai kawai tayi karfin halin hadiye yawu a maƙogwaronta sannan ta damƙo jakarta dake ajiye a gefen kujerar.

"Nagode Baba Alhaji. Bari na sauka."

"Karfe nawa zaki gama? Ko da wani abu zai  sake kawo ni ta nan bangaren nan sai in tafi dake. "

Ta girgiza kanta.

"Ai ban san komai game da aikin ba Baba Alhaji, kawai kaje duk sanda Allah ya yi zan dawo."

Ta fadi hakan muryarta a karye don Allah ya sani a wannan lokacin ji kawai take yi kamar tana shirin tunkarar wata runduna ne guda ne da zasu ƙalubalance ta.

"To shikenan, Allah ya bada sa'a ƴanmatan Gwaggo."

Ya kira ta da sunan da yake yawan kiranta dashi, kuma duk sanda ya fada din ta kan yi murmushi tana kallonsa, amma a yanzu kunnenta ya ji me yace amma bata ko kalle shi ba har ta fita daga motar ta rufe, shi kuma ya ja ya janye ta daga gabanta yana barin hoton tarin motocin dake ajiye a harabar wajen a idanunta kai ba zaka ce safiya ce ba.

Ta dago wayarta dake hannunta ta kalli lokaci, har yanzu bakwai saura minti uku. Sai ta kashe ta, ta bude jakarta ta mayar da ita, sannan ta rataya jakar a kafadunta. Rigar jikinta doguwa ce mai tsarin budewar umbrella daga ƙasa kamar mafi yawancin kayanta, don ita ba mutum ce mai son duk wani abu da zai dami ƙafafunta ba.

Atamfar dake jikinta kalar sea green ce da kuma dark blue. Sai ta yafa mayafi kalar sea grean mai adon duwatsu da yawa a jiki. Ukthi tace tayi kyau, duk sanda tasa kayan ma haka take gaya mata, tace wai kalar tana dacewa sosai da hasken fatar ta... Kuma ko a yau ma da ta kalle ta sai da tace,

"Yadda kika yi kyan nan Yaya, ke ya kamata ace zasu ji tsoro ba ke ki dinga jin tsoro ba."

Sai ta gallara mata harara tana fadin a yaushe ta gaya mata cewar tsoro take ji kafin ta ɗauki jakarta ta fito. Don Ukthin ma ba tare suka fito ba tunda ya yi wuri ta biyo su zuwa makarantar ta.

Ta kara gyara ratayen jakar, ta saita mayafinta sannan ta shiga karanto addu'o'in da duk taji sun zo kanta a wannan lokacin kafin tayi gaba.

Kuma bayan ta bar harabar wajen bata san ina ne hanyar shiga ba sai da ta ga inda mutane ke ta bi sannan itama ta karya kwanar, anan ta hango ƙatuwar barandar dake dauke da wata faffaɗar ƙofar gilashi, ta bi bayan wasu mutane biyu suka shiga ta katuwar kofar.

Idonta ya gane mata wani dogon hall mai fadi dauke da kofofi kala-kala a kowanne ɓangare. Kowa kawai harkar gabansa yake yi daga ma'aikatan asibitin dake sanye da kayan aikinsu har sauran mutane, wasu na fitowa daga kofofin suna shiga cikin wasu, wasu kuma suna mike dogon hall din.

Sai kawai itama ta shiga mike wajen har zuwa tsakiya, anan dogon hall din ya koma waje mai fadi dauke dawadu hanyoyin da kuma kafafun bene ta kowanne bangare. Daga tsakiya kuma anyi wani abu kamar round about da aka zagaye shi da fitulu da kuma kujeru irin na zama idan mutum yana jira.

Daga ɓangaren hagu ne idonta ya gano mata zagayayyen wajen da aka kange da a matsayin wajen receiptionist. An zagaye wajen da ƴar karamar katangar da aka yanyame ta da fararen tiles.

Ga computers har guda biyu akai da  manya-manyan screen da tambarin apple ga sauran kayan printers da scanners. Don haka kanta tsaye ta nufi wajen. Idonta akan mutane biyun mace da namiji dake gaban kowanne screen din computer.

Ƙafafunta suna tsayawa a wajen namijin ya dago ya kalle ta kuma kawai sai ta ga ya yi mata murmushin, murmushin da ya yayyafa wani dan danshin kwarin gwiwa a tare da ita.

"Barka da aiki, dan Allah ina neman office din coordinator din SRRI ne."

Ga mamakinta sai taga ya gyada kansa kawai tare da fadin.

"Okay, mu ga letter of appointment ɗinki."

Ta gyada kanta da sauri sannan ta bude jakarta tana kokarin zaro takardar, kwakwalwarta na gaya mata cewar daga yanayin yadda ya amsa kuma da abinda ya tambaye ta ta san tabbas ba ita kadaice tazo da irin wannan tambayar ba.

Ta ciro form din ta miko masa ya karba sannan ya shiga danna wasu abubuwa a jikin computer yana kuma raba idanunsa tsakanin form din da fuskar computer.

Har ma ya sake kallonta yace mata 'minti daya' sai taji ta ɗan ƙara sakewa, wani abu na nauyin dake kirjinta ya kara raguwa, har ma ta fara juya idanunta tana ƙara kallon wajen.

A daidai da lokacin da wata matashiya sanye da fararen kayan aikin Nurse ta ƙaraso ta tsaya a gefenta hannayenta duka biyu rike da wasu takardun da ta dire su a saman kantar, daya macen tasa hannu ta karba ita kuma ta kalli namijin tace.

"Salim.... Ya aikin?"

Bai kalle ta ba ya girgiza kai.

"Dr. Hafsa tayi updating folder room 39?"

"Eh tayi, na tura miki da link din, kamar ta rubuta sababbin instructions ne akan fluid balance na patient din."

Ta gyada kanta tana murmushi.

"Yawwa dama so nake nayi adjusting chart dinta yanzu."

"Pharmacy ma sun ce an sami delay a antibiotics dinta sai zuwa yamma za'a samu."

"Ba komai dama sai gobe zamu fara dora ta akansu, bari naje."

Ta fada tana kokarin juyawa, sai yayi saurin tsayar da ita.

"Dan Allah in zaki wuce ga wannan, team din SRRI ce, office din CMO zaki nuna mata."

"Okay ta biyo ni." Ta fada tana kallonta.

"Ga wannan, zaki hada duka ki kai masa."

Salim ya miko mata appointment letter tare da wasu takardu da ya yi printing.;ta karba tayi masa godiya sannan ta bi bayan Nurse din.

Suka yi kwanar hagu inda dogon hall din ya cigaba da mikewa, lokacin da  suka karasonwani waje mai dauke da manyan gilasai daga can sa sanyin iskar safiyar nan ya taho ya ratsa ta sai taji kamar tana shirin kaɗe ɗan kwarin gwiwar da tayi kokarin tattarowa.

Basu yi nisa sosai ba ta tsaya a kofar wani office da aka sa Chief Medical Officer (CMO)

"Ga office din, kiyi knocking kafin ki bude."

Ta fada da murmushi, tayi mata godiya kafin ta tafi. Ta juya ta kalli ƙofar office din, ta gyara zaman jalarta a kafada sannan ta rufe idanunta ta bude tare da yin ajiyar zuciya.

"Shekarar ki nawa kina aiki?

CMO din ya tambaya yana kallonta bayan tayi masa dukkan wani bayani kuma ya karbi takardun hannunta. Wani kakkauran mutum ne fari tas, yana sanye da gilashi a fuskarsa wanda kallo daya zaka yi masa ka san ya dace da matsayinsa na likita, kuma duk tun bayan shigowarta office din har zuwa yanzu bata sake ba, amma kuma sai take jin ganin nasa bai sa taraddadin dake yawo akan kirjinta ya karu ba.

"Kusan shekara ɗaya."

Ta fada a hankali kamar raunin muryar tata zai sa ya tabbatar da cewar babu yawa.

Sai ya gyada kansa.

"So duk da dai ba wani abu ne mai wahala ba aikin naki, amma it would have been better ace kin sami training din da aka yiwa duk wanda aka dauke su a program din.

Amma tunda you are already in the field kuma ba wani abu zaki yi practicing ba ina ga ba zaki sami wata matsala sosai ba, don patient din ma basu da yawa, so far mutum shida muke dasu. Yanzu zan hada ki da wanda zasu baki duk materials din da aka gaya miki sannan kuma inaga zan sa ayi miki bayanin yadda aikin yake kafin ki hadu da Dr. Aliyun tunda you are not familiar with everything."

Duk abinda yake fada tana gyada kanta a hankali ne tana saurarensa. Sai ya dauki wayarsa dake gefe ya shiga dannawa alamun neman kira.

"Bari na kira shi naji idan zai iya ganinki yau, saboda starting date din sai gobe dana za'a fara aiki, yau scheduling ne kawai."

Magana yake amma Safina bata san me yasa ba a wannan lokacin ba saurarensa take yi sosai ba, ƙarar shigar kiran da ya saka a speaker kawai take saurare tana jin yadda kiran ke dannawa kamar da nauyi a ƙirjinta.

"Assalamu alaikum..."

Wata irin murya mai zurfi da zaƙi ta cika kunnuwanta a lokaci guda.

"Wa'alaikum salam, Aliyu ka shigo ne?"

"Eh ina office, amma ina da surgery by 8."

"Your secretary is here, zaka ganta yau?"

"Secretary? Ya tambaya a hankali.

"For what?"

Ba shiri bugun zuciyarta yayi wani dan tsalle sannan ya dawo ya dira daidai.

"For SRRI, Aliyu mun tura maka komai fa, baka duba emails dinka ne?"

Shiru sosai sannan yace.

"I've checked now, Naga Safina Sadiq Kalla?

A kunnen Safina ji tayi wannan ba sunanta bane, ba sunanta ya furta ba.

"Itace, zaka ganta yau?"

"First remind me again why do I need someone to manage what I already know how to control?" (Fara tuna min tukunna me yasa zan nemi saktariya akan aikin da na riga na san abinda zanyi?)

Shiru ya sake ratsa office din, bacin rai na nunawa akan fuskar CMO yace.

"Go and read your emails Aliyu, zata zo ta same ka early morning gobe kafin ka fara ganin patients ɗin."

Yana fadin haka ya kashe wayar kuma bai kalle ta ba kawai ya jawo wata takarda da yace zai bata ta kai inda za'a bata kayan ya shiga rubutu akai.

Sai kawai ta hadiye yawu a cikin makogwaronta tana kokarin gayawa zuciyarta ƙaryar cewa abinda taji ba komai bane.

***

"Me yasa baki zo training ba?"

Matron Nafisa kamar yadda Safina ta kalli sunanta a jikin wani ɗan allo akan teburinta ta tambaya, a lokacin ta shafe kusan awa biyu tana jiranta don bayan ta gama da CMO tun da safen wajenta ya turo ta da cewar itace zata yi mata dukkan sauran bayanai da kuma bata abubuwan da zata bukata.

Kuma a nan ne ma ta tadda mutum biyu mace da namiji wadanda suka ce su ma anyi posting dinsu ne akan program din, amma da ta dan tambaye su sai ta fahimci nasu kansnun role ne sosai kamar ma masu goge-goge ne... A bakin macen take jin cewar ai kusan duk ma'aikatan asibitin aka dauka a aikin program din, yan kadan ne kamar ita suka zo daga waje, don itama wata yaruwarta ce dake aiki a cikin asibitin ta saka ta.

Ita dai bata ce komai ba, banda saurarenta da take yi da kuma murza yatsun hannunta, anan suka zauna zaman jira Matron Nafisan har kusan awa biyu don a lokacin da ta iya gano ofishinta ance ta tafi surgery. A ran Safina ta ayyana tabbas tare da Dr. Aliyun nan da aka kira ta shiga surgery din tunda shima abinda yace zaiyi kenan.

Kuma da wannan tunanin ita bata san sau nawa ta dinga debo ruwa a wata despencer tana sha ba ba ko zata ji saukin yadda zuciyarta ke bugawa duk sanda ta tuno wannan muryar da kuma dukkanin abinda yace.

Gwaggo ma ta kira ta yafi sau a kirga tana tambayar komai ya tafi daidai ko? Yanzu me take yi? Me akace?... Har sai da ta gaji tace mata ta bari idan ta dawo gidan zata mata bayanin komai.

"Me yasa baki zo training ba Safina?"

Ta sake maimata mata tambayar da taga kamar bata ji ba.

Sai kawai ta gyara zamanta sanna ta kalle ta ta amsa.

"Ban anyi training kafin daukan aikin ba."

Ta fadi haka iya gaskiyarta don idan tace zata yi karyar ma a lokacin bata san me zata ce ba, kuma ga mamakinta sai kawai taga ta yi murmushi sannan tace.

"Ai daga ganin appointment dinki na san daga sama kika zo, zan gaya miki gaskiya sai kin dage sosai zaki yi aiki da Dr. Aliyu, don haka duk sanda kike bukatar guidance zaki iya zuwa nan insha'Allah... Sannan zan hada ki da Nabila ma, na tabbata zata baki duk taimakon da zaki bukata."

Safina ta gyaɗa kanta alamun amsawa ba tare da ta damu da maganarta ta farko ba. Don ta sani bata da dalilin damuwar, tabbas ta sama akayi appointing dinta wannan aikin ta sani, sannan Dr. Aliyun da ta kira da sai ta dage akansa, a yau kadai a cikin sakannin kiran wayar nan ita kanta ta fahimci haka ba ma sai an jaddada mata ba. Don haka abinda kawai ta yanke a ranta shine addu'a zata dauko ta dora akan komai tunda ita kadaice abinda ta san ba abinda yafi karfin ta.

Matron Nafisa ta ɗauko wani file ta buɗe shi tana fadin.

"Ku biyar akayi posting a wanda ba ma'aikatan asibitin nan ba, sauran hudun sun zo tun kafin in shiga surgery na basu kayansu, so zamu yi meeting ne gabadaya gobe da safe in briefing dinku game da aikin. Don haka yanzu kayanki kawai zan baki , sai gobe tukunna zamu yi briefing kafin a fara aiki."

Safina ta gyada kanta tare da amsawa.

Matron Nafisa ta tashi ta bude wata drawer a bayan kujearata ta shiga zaro wasu tarin kayan da Safina bata maida hankali taga komai da komai ba, taga dai manya-manyan joters kwalayen biruka da da sauran tarkace sai kwallin wata sabuwar Tablet da ya dallare mata ido.

"Ga uniform dinki, amma ki duba fittings din tun yanzu idan baiyi ba za'a gyara saboda ba ma son wani style din bayan wannan kuma kinga gobe zaki fara aiki dole sai da uniform."

"Okay Ma." Ta fada tana karbar uniform din dake cikin sabuwar ledarsu.

"Akwai changing room idan kika miƙe hall din nan kika yi hannun hagu ƙofa ta uku."

Ta sake amsawa da guntun murmushi sannan ta miƙe, bata dauki komai ba a cikin kayan da zummar zata je ta dawo, jakarta kawai ta rataya sannan ta dauki kayan ta fita, tunani da yawa na yawo a cikin zuciyarta, tunaninkan da ta kasa samun wata matsaya ko ma wani kwakkwaran abu daga cikinsu, kuma a cikin tunanin nata ne ta ɓata a kwatancen da Matron Nafisa tayi mata.

Lokacin da ta kai karshen hall ɗin, maimakon tayi ɓangaren hagu kamar yadda tace sai kawai tayi kwanar dama, ta tsaya a gaban ƙofa ta ukun ba tare da ta manta wannan ba, babu wani rubutun a jikin kofar ko samanta don haka ko kaɗan a cikin kanta bata kawo cewar ba inda bai kamata tazo ba tazo.

Ƙwanƙwasawa biyu ta bude ƙofar ta shiga tunda damava cikin kanta bata kawo cewar zata sami wani a ciki ba.

Akwai mukulli a jikin kofar daga ciki, kawai sai ta murda shi ta kulle ƙofar gabadaya yadda ko da tsautsayi ma ya kawo wani ba zai bude ta ba sai in tazo ta bude.

Sai dai tana juyowa ta tsaya turus akan ƙafafunta, don ko kadan wajen baiyi mata kama da wajen canja kaya ba, nan ai office ne, office hadadde ma mai zaman kansa wanda duk da an saki labulayen blinds din dake jikin maka-makan windunan guda biyu, kana iya ganin yadda komai ya haɗu cikin tsari da kuma tsaftar ko ma waye mamallakinsa.

Kuma sai a lokacin daddaɗan ƙamshin dake gauraye a iskar wajen ya xiyarci cikin hancinta, sassanyan ƙamshinsa yasa tsigar jikin dake hannayenta mikewa a lokaci guda.

Kuma a lokacin ne babu zato babu tsammani ƙofar ƙofar toilet din cikin office din dake fuskantar ta ta bude.

Aliyu ya fito daga shi sai dogon wandon aikin tiyatar da ya fito a jikinsa... Idonsa ya shiga cikin nata yayin da ita kuma nata ya sauka akan jikinsa da babu riga ba makamancinta...

**

Aysha Shafiee

©Raina!