Chapter 43
by @khairatup01
Zuciyar Mutum.
khairat.
Wattpad:Khairi_Muhd.
Arewabooks ayi following ɗina masoya @Khairatup01.
43.
*
HAIDAR.
Shi kan shi ya fara jin haushin kan sa yadda yake takurawa Ummu daga jiya zuwa yau. Mamakin kansa ma yake bai san haka yake da son kasancewa da abinda yake so ba sai jiya. Haƙiƙa yana son Ummu ko nesa da shi baya son tayi Wallahi. A hankali ya jawo wayar ta shi.
Layin nata ya kuma gwada wa.
Kasancewar wayar na hannun ta wannan karon bugu ɗaya tayi ta ɗaga.
"Salamu Alaikum Hamma na ka daina fushin? Ka yi haƙuri zan dinga riƙe wayar a hannu."
Daga can ta jiyo ajiyar zuciyarsa.
A hankali yace "Am sorry!"
Sai suka yi shiru na kusan minti ɗaya kafin ya yi ta maza yace "Na san na takura miki amma ki yi haƙuri da halina a haka nake ba na son ne na yi nesa da ke. Ina son na ji ina tare da ke a rayuwata. Ina ƙara baki haƙuri a kan halina."
"Babu komai Hamma. Laifina ne ya kamata na tafi da wayar nima ka yi haƙuri."
Murmushi ya yi kafin ya gyara zaman sa yace "To yanzu dai me kike yi? Ni kin gan ni nan tunanin ki da begen ki sun hana ni sakat ko tea ban sha ba."
"Haba dai? Gaskiya ka samu ka ci wani abun bana son na gan ka da yunwa gaskiya."
"An gama Hajiyata ai dole na yi abinda kike so shi ne zaman lafiyata. Amma dai yau zamu tafi ko?"
"Anya kuwa? Ban dai sani ba."
"Wallahi ki sani kuwa don yau zamu wuce ko da su ko ba su."
Tayi masa dariya kawai.
"Ki turo mini kwalliyar ki ta watsapp na rage zafi ko amaryar Haidar?"
"Hamma..." ta faɗa da shagwaɓa a muryarta.
"Za ki ƙarasani matar nan adana mini wannan salon sai mun je gidanmu."
Ajiye wayar suka yi tare.
Wayar ta manna da ƙirjinta tana jin wani irin daɗi a cikin ran ta. Ashe bayan Habib akwai wanda zata ji ya sace mata zuciya? Tabbas al'amarin zuci yawa ne da shi kuma zuciyar nutum birninsa.
Bata tura masa hoton ba sai da ta ƙara gyara fuskarta ta ɗauki hoton harda bidiyo tayi kafin ta tura mai. Tare da kalaman soyayya masu sanyayya zuciya.
Ya ko aiko mata da emojis kala-kala. Sun jima suna lallacewa a wayar gabaɗaya sun manta ma da lokaci da komai kiran sallah ne ya ankarar da su suka yi sallama.
*
Da yamma aka ɗauko mai DJ aka raƙashe an sha rawa an yi annashuwa kowa ya ji daɗin gidan bikin an rabu ana walwala da raha.
Misalin ƙarfe tara da rabi na dare Haidar ya kasa jurar rashin ganin matarsa haka ya kama hanya ya fita a mashin ma ya je.
Tana tsaka da bacci saboda gajiya ta ji wayarta na vibrating ko bata tambaya ba ta san Haidar ne ya kira ta.
Cike da kasala da muryar mai bacci ta amsa kiran tace "Hello Hammana."
"Ina waje fito."
Tuni ta wartsake ta buɗe idanuwanta tar tana ware idanuwa.
"Ummuuuuuu" Ya ja sunan ta.
"Hammana wai da gaske kake?"
"Eh da gaske nake."
Tashi tayi ta soma neman hijabi ta saka. Kamar marar gaskiya haka ta fito wasu basu ma kwanta ba.
Yafendo tace "Ah ba kin kwanta ba? Ina za ki je yanzu?"
"Yafendo ina zuwa saƙo zan amsa a wurin Hamma."
"To."
A ƙofar gida ta gan shi zaune a kan mashin ɗin na sa ya rungume hannayensa biyu a ƙirji idanuwansa na kan ƙofa tana fitowa ya saki ajiyar zuciya ya sauko daga kan mashin ɗin ya isa kusa da ita ya rungomo ta jikinsa haɗe da yi mata sumba a goshi.
"Matata."
"Mijina."
Da gaske kin yarda ni mijinki ne?
Eh mana.
Alhamdullilahi. Yau na kasa samun zuwa sai yanzu naga zan hallaka kafin gobe dole na zaburo na taho wurin ki. Kuma yanzu na dawo daidai da na yi tozali da kyawawan idanuwan ki.
Kan mashin ɗin ne ya ɗora ta ya tsaya a tsaye kawai yana kalonta yana murmushi ƙasan ransa bai san kalar adadain son da yake yi mata ba. Wai tambayar kansa yake yi dama haka ake jin son? Kai zai iya zaucewa haka yake tunani.
Hira suka yi ta yi ba tare da tunanin komai ba, sun manta ma a ƙofar gida suke da kuma lokacin dare ne.
Basu ankare ba sai da suka ji Yafendo tace "To Romiyo juliyo ya isa haka zamu ƙulle gidanmu.
"To Yafendo ayi haƙuri. Ya faɗa yana rungume Ummu."
"Sai da safe masoyiya ki kwanta kiyi bacci ki huta abin ki da rana zamu tafi ni da ke. Ina ƙara maimaitawa da rana zamu tafi."
"To Allah Ya kai mu."
"Amin." Ya faɗa yana sumbatar lebbanta. Sai da ya ga shigar ta sannan ya burga mashin ɗinsa ya tafi.
Asuba ta gari masoya.
*
Enugu State.
Nsukka.
Afeeya da Umma da ƙawr Afeeya ifeoma ta raka su wurin wani shahararren hatsabibin boka. Iyamuri ne yana da shekaru da dama a harkar bokanci. Sunan shi Chukwudi. A wani daji yake zaune mai duhu a garin Aku,kusa da wani rafi. Wurin da ba kowa ke iya tsallakewa ba sai an ba da izini.
Bayan isar su duk a tsorace suke saboda yanayin dajin ga shi kuma dare ne daman. Chikwudi ya basu izinin wucewa.
Ko ina na dajin ya mamaye da duhu, kowanne lungu da saƙo iska na kaɗawa ,tana ɗauke da sautin murmurɗen ganye kamar ana faɗin wani tsafin.
Afeeya ta tsaya gaban wata ƙaramar ƙwarya mai ƙamshin ƙasa da jini, hannunta na rawa don fargaba.
Chikwudi kuwa tsohon boka da baya tsufa , a zaune kan tsakiyar zane mai launin ja da baƙi. Idanuwansa kuma sun haske wajen da hasken jan wuta dake fitowa daga tanderun da ke gabansa.Ya ɗaga kansa murya mai amo da sautu marar daɗi ya ce da Afeeya "Kin taho da hoton su?"
Hannu na rawa Afeeya ta zaro hoton Haidar da na Ummu daga cikin jakar ta.
Ƙarba ya yi ya kalli hoton ya bushe da dariya yace "Za ki yanka hannun ki, za ki rubuta sunan su da jininki a wannan farar takardar. Yadda ya faɗa hakan ta yi. Ya karɓa ya yamutsa da hoton da ta ba shi.
"Me kike so ayi musu?"
Afeeya baki na rawa tace "Ina son ya dawo gare ni. Ina son ya guji Ummu kamar yadda mutum ke guje wa mutuwa. Ina son ya manta da ita. Ya tsani ko numfashinta. Ya zama nawa ni kaɗai!.
Chikwudi ya yi dariya, dariya mai sanyi da sauti kamar na maciji da kwarkwata.
"Zuciyar namiji ruwa ce mai tauri,amma idan mace mai zuciya ta buɗe ,zata iya zama nasa...har abada. Amma ki sani komai yana da farashi!".
Hoton ya saka cikin tukunya. Ya zuba wani gari a ciki ,ya zuba jinin tsuntsun da ya yayyafa daga kwandonsa. Wuta ta hargitsa tukunya, tana fitar da hayaƙi da ke ɗauke da ƙamshin turaren sihiri.
Chikwudi bakinsa bai yi shiru ba yana ta ambataon sunan uwargijyar daji,da izinin garken duhu...Afeeya ta mallaki Haidar Ummu ta zama ƙaya a zuciyarsa. Ki ɓoye mata haske, ki juya zuciyarta zuwa inuwa. Tuni hoton Ummu ya ƙone a cikin tukunyar yana fitar da hayaƙi mai siffar mace da ke kururuwa da baƙin murya.
Tuni zuciyar Afeeya ta bushe ,imanin ya gudu ta saki wata iriyar dariya ta tafa hannaye "Ba za ku sake samun kwanciyar hankali ba. Yanzu ne zan soma na wa wasan."
Chikwudi ya bushe da dariya a karo na ba adadi ya kuma gimtse ya kalle ta yace "Aikin ki zai yuwu amma ki sani akwai sharuɗai guda uku da zan baki in kiyayesu shi kenan in kuma kin karya ɗaya za ki fuskanci ƙalubale.
Ko da aiki bai kama da wuri ba kar ki ce za ki matsa masa da maganganu da kan shi zai kawo kan sa.
Bayan mu da muke nan kar ki sake ki sanarwa da kowa batun wannan aikin.
Kada ki sake ku kuma kwanciya da wani namijin ko waye shi bayan Haidar.
In kin karya wannan dokokin tabbas za ki gani a ƙwaryar ki.
Afeeya tace ta aminci.
Ya bata wani kwalli yace ta shafa in ta ga Haidar zai mai da ta ɗakinsa. Kuma zai rabu da Ummu.
*
Billiri.
An gama sha'anin biki lafiya.
Amarya da Ango sun shirya zasu wuce Gombe.
Don ya tada musu bori ba zai yarda wai sai sun kai ta ba shi a ba shi matarsa a haka ba wani abu da za ayi mata ita yake so ba wani jikinta ba. Wannan maganar sai da ta ba wa kowa kunya amma mutumin naku ya fuske ya haɗe rai. Hajiya tace "kai Haidar tattara matar ka ku tafi bana son maganar banza da wofi. Marar kunya."
Kai Sweetheart! Harda kora abin? Ko dai na jira ki lullubo min amaryata ki kawo min ita da kan ki?"
"Ungo nan" ta faɗa tana masa daƙuwa.
Dariya ya saka kawai.
Ƙarfe bakwai na dare suka isa Gombe. Bai bari ta taka ƙasa ba ya wuce da ita ɓarinsa kaitsaye.
A kan gado ya ajiyeta ya yi mata rumfa yana kallonta fuskarsa ɗauke da murmushi.
"Masoyiya."
"Masoyina."
"Yau ga ki ga bawan Allah Haidar?"
"Aifa da bawan Allah!"
Suka yi dariya tare.
Bara na je na dawo. Ki yi wanka ki sauya kaya ba za a rasa kaya a ɗakin can ba.
To sai ka dawo.
Fita yayi. Ita kuma ta shige banɗaki ta yi wanka.
Kayan maƙulashe ya siyo har da kazar amarci da yogurt.
Tare suka ci suna hira yana bata labarai.
Sun jima a haka suna tuna Habib da hallayensa. Nan take gaya masa twins ɗin ma Adda ta so amsar su amma Hajiya da Abi sun hana sun ce suna ɗebe musu kewar Habib.
Ya ce ta kwantar da hankalinta nan ba da jimawa ba zai dawo da su wurinsa.
Tace "Aa ka bar su ai Hajiya ma ba zata bari ba. Zasu rage musu zafin Hamma Habib."
"Shi kenan. Allah Ya jiƙan HABIB."
"Amin."
Yanzu me yayi saura?
Bacci mana Hamma.
Bacci?
Eh.
Ke muguwar yarinya ai yau babu bacci sai neman lada.
Aa fa Hamma...
Haka za ayi ƙanwar Hamma.
Uhm'uhm....bai bari ta ƙarasa ba ya haɗe bakinsu wuri guda.
Na ja ƴan matan ƙafafuwana na yi waje.
Washegari.
A hankali ta buɗe idanuwanta da suka yi kalar ja saboda gajiya da kasala.
Ta na buɗe su tar tayi tozali da kyakyawar fuskar mijinta Haidar yana murmushi.
"Morning Sunshine."
Gefe ta yi da kai tana murmushi.
Yatsun sa ya saka ya juyo da fuskarta suka haɗa ido.
Yace "Babu kunya a tsakani na da ke."
"Hamma ina kwana?"
"Lafiya lau Alhamdullilahi. Yaya gajiyar jiya?"
Hamma da gaske ba ka jin kunyar kowa?
kunyar ki zan ji ? Me ya yi saura to da ban gani ba ko ban ji ba?
La'ilahaillallahu na banu.
Kin ga ni bana son haka. Gulma kawai. Tashi kiyi wanka na haɗa miki komai a banɗaki.
To na gode.
Ɗaga ta ya yi sama ya rakata banɗakin can ma sai da ya gama luguiguita ta sannan ya bar toilet ɗin.