HASKEN CIKIN DUHU

CHAPTER 02

by @nanameera08

HASKEN CIKIN DUHU💋

Page 002

Nanameera, YOTA/23.

Even when darkness takes over your life, there’s always a light, you just have to find it.

Mommah ta bi shi da kallo sai dai bata ce komai ba, badan bata da abun faɗa ba, sai dan tasan faɗar bashi da wani amfani. Tsaki Dad ya yi ya juya ya fice daga parlon gabaɗaya, Mommy dake zaune ta taso tazo gabanta, dafata tayi tana ɗan murmushi ta ce“Khadijah, ki daina ɗaukan abu da zafi irin haka, idan bai so Zayyad ba wa zai so?, duk abubuwan da yake masa akan gaskiyarsa yake, ki daina nuna kamar bakya jin dadin hakan” ɗan murmushin takaici Momma tayi kafin ta ce “Nifa Mommy ban ce kada ya nuna yana son ɗansa ba, daman ai kowane uba dole ne yaso ɗansa, amma wlh abin da yake yiwa Zayyad it's too much, yaushe zai yi hankali?, yaushe zai zaunar dashi ya dinga masa faɗa?, sai dai ni kullum nayi?, kuma idan ma nayi faɗan a gabansa zai nuna ni ce ban yi daidai ba, zai goyi da bayan ɗansa. Haka yake son ya cigaba da rayuwa?, kuma sannan ki ce na daina damuwa, amanar Allah ce fa” shiru Mommy ta yi can kuma ta ce“shikenan, Anjima idan Zayyad ya dawo zamu zaunar dashi mu yi masa faɗa ba sai Yallaɓai ya ji ba okay?” jinjina kai Mommah ta yi ta ce “tom Allah ya kaimu”.





Maitama, Abuja

1:55pm

Zaune yake kan sofa yana danna wayarsa, time to time yana ɗan murmushi. Fitowa tayi tana sanye da wata riga ta atampa hannunta riƙe da ice-cream, ta zauna tafara shan ice-cream ɗinta ba tare data kalli inda yake ba

“Nimra”

Ɗagowa tayi ta ɗan kalleshi kafin ta ce“yes” yanda tayi maganar irin in i don't care manner ya ƙara ƙona masa rai, ya ajiye wayar hannunsa still looking at her eyes ya ce“hala baki san ina zaune a parlon nan waiting for u ba ko?” ɗan ɗaga kafaɗa tayi bayan ta lashe cokalin hannunta ta ce“nasani mana, ba kaga nazo na zauna ba, hira zan taya ka ai, but I think u're doing something” cikeda rainin hankali ta yi maganar still kuma bata kalleshi ba. Miƙewa ya yi a fusace yana kallonta ya ce“ke wace irin mata ce wai?, kinsan kuwa abin da ki ke yi?, kinsan darajar auren dake kan ki kuwa?, kin je islamiyya ma kuwa?” a fusacen itama ta miƙe tsaye tana masa wani shegen kallo cikin ɗaga murya ta ce

“stop raising ur voice at me, ka daina min shouting aka, ni ba yar ka bace, kuma ni ba ƙanwarka bace, ni ba irin wadda zan tsaya kana gaya min maganar da kaga dama bace, I'm ur wife. Aure nake ba wai wahala ba, saboda haka kada ka sake cewa zaka yimin faɗa idan kuma ba haka ba...”

“Idan kuma ba haka ba me?”

“Then definitely I'll show you the other side of me”

Ta ratsa ta gefensa ta bar parlon tana tafiya kamar zata tashi sama, da idanu kawai Farooq ya bita sai kuma ya girgiza kansa. Kamar ya bita sai kuma ya fasa, wayarsa ya ɗauka ya yi waje.

Nimra na shiga ɗaki tafaɗa kan luxury bed ɗinta ta fashe da kuka, wace irin ƙaddara ce wannan? har zuwa yaushe zata cigaba da zama da wanda bata so? meyasa za'a mata haka? meyasa Daddy zai barta cikin duhu wanda zai iya kai wa da yin ajalinta?. Sake fashewa da wani sabon kukan tayi dan shine kawai abin da zata yi taji sanyi a ranta. Tana nan kwance har after one hour sannan ta tashi ta shiga toilet, wanka ta sake yi ta shirya cikin wata Abaya Black colour wadda ta haska farar fatarta sosai, ta fito bayan ta ɗauka car key ɗinta. Kai tsaye makeken compound ɗin gidan tayi, ta buɗe wata Accord maroon colour ta shiga, tayi horn mai gadi ya buɗe mata gate tayi waje a guje. Tana tafiya a hanya taga kiransa sai ta share, sau uku Farooq na kiranta daga ƙarshe ta saka wayar a dnd ta cigaba da tuƙinta hankali kwance.


Mararaba, Nassarawa state

Orange Market, 2:05pm.

Hadari ya mamaye sama, gajimare ya rufe rana tamkar dare ne ke kokarin sauka kafin lokaci. Iska tana kadawa da ƙarfi, tana daga tarkace, leda da ƙura cikin iska.

Orange Market ya cika kamar kullum, masu sayar da kayan lambu, 'yan kasuwa, da masu hayar kaya sun baza komai a kasuwa, amma idan ka kalli fuskokinsu zaka fahimci hadarin ya fara tayar da hankali. Thunder yana tsawa daga can nesa, lightning na haska saman ginin katako da zinc, fitattun shagunan roba da kayan miya suna rawa a ƙarƙashin iska.

A cikin wannan hayaniya, take tafiya,  yarinyar da ba zata shige shekaru sha bakwai, sanye da uniform wanda suka ɗan gaji, riga da siket mai ɗan duhu, ta fito daga layin gefen kasuwa.
Hannunta riƙe da tsohuwar jaka mai ɗinki iri-iri, books ɗinta na tsalle-tsalle a ciki saboda hanyar ba daidai ba. Iska tana kadawa tana haɗa gashinta a fuska, sai ta share da yatsunta cike da ƙura. She's walking fast, ta ratsa cikin kasuwar, tana matsawa tsakanin masu siye da masu sayarwa, tana ƙoƙarin kai gida kafin ruwan sama ya biyo.

Tsohuwar tabarma da aka shimfiɗa a gefen hanya ta keta, yara suna tsalle cikin laka suna dariya, amma ita bata tsaya ba, zuciyarta na cike da damuwa.

Thunder ya sake tsawa, hadari na kara kumbura, amma ta ci gaba da tafiya cikin kasuwa, kafarta na nutsewa cikin laka, idanunta a lumshe da fatan zata isa gida lafiya kafin sama ta ɓalle da ruwan sama.

Cikin wannan tunanin ta ƙarasa unguwar Kabayi inda nan ne gidansu yake, wani gida wanda ya kasance uncompleted, tun daga nesa ake hango tsurar bulon dake gidan, domin babu ko siminti a gidan, ta ƙarasa tana tafiya da sauri, tura ƙofar gidan tayi wadda ta kasance tsohuwa sosai, dan da ace za'a yi batu na kiwon lafiya to babu abin da zai sanya abar wannan ƙofar a gidan. Bakinta ɗauke da sallama ta shiga, tsakar gida ne mai faɗin gaske, sai dai babu interloke ko tiles, sai malalen siminti wanda duk ya farfashe. A hankali ta ƙarasa inda ɗakuna uku suke, zaune ta samesu suna dan taɓa hira, cike da ladabi ta sunkuya ta gaishesu cikin murya mai haushi. Ɗaya daga cikin matan wadda take sanye da mayafi ta kalleta fuskarta ɗauke da fara'a ta ce“Har kin dawo?” gyaɗa mata kai tayi daga durƙushen da take, ɗaya matar wadda ta wani haɗe rai ta ce“gidan ubanki ki ka tsaya sai yanzu za ki dawo daga makarantar?, kina tsayawa a ina ne?” cikin ɗaga murya tayi maganar, yarinyar ta shiga girgiza kanta muryarta na rawa ta ce“Ban tsaya a ko'ina ba Umma, teachern mu ne bai tashemu da wuri ba yau”

“Sai da an yi magana kina da abun kare kanki, wannan makarantar sai kin daina zuwanta nan kusa wlh, tashi ki bani waje, kuma yanzu ki fito ki yi wanke wanke, kafin anjima nayi magana ki ce makaranta za ki tafi, ina ga makaranta, Al huda huda” ta ƙarashe maganar tana zabga mata wata uwar harara. Tashi tayi jiki a sanyaye ta shige ɗakin wanda ya kasance nata, wani empty ɗaki ne, babu komai a cikinsa sai wata tsohuwar tabarma da bargo wanda ya gaji da tsufa akai, daga can ɗaya side ɗin kuma wani Ghana must go ne, black colour da alama a nan ne take ajiyar kayanta. Ƙarasawa ciki tayi ta zare hijabin jikinta, nan take tarin gashin dake kanta ya baje, ɗan tsaki tayi sannan ta sake ɗaureshi da wani yanki. Tana gamawa ta miƙe tsaye, hijabin ta linke sannan ta fito daga ɗakin ta nufi inda kayan wanke wanken suke, duk da basu da wani yawa. Sai da ta ɗebi ruwa a wata baƙar roba ta zauna sannan tafara dube-dube, sai dai duk iya dubanta bata ga abin da take neman ba, hakan yasa ta tashi ta ƙaraso inda mahaifiyartata ke zaune ta ce a hankali

“Umma babu Omo”

“Kin ga irinta ko?, to komai sai dai ni nayi, ubanta bashi da hali sai Zuciya da kakkafi, kina gani dai yanzu Omon da za'a yi wanke wanken ma babu cikin gidan, shi ya saka ƙafa ya fita, ita kuma ba zata yi neman kuɗi a rufawa kai asiri ba, sai dai taje makaranta, idan an yi magana ubanta ya ce zai yiwa mutum wa'azi.” ta ƙare maganar tana kallon Hajiya Jinjin dake gefenta. Ɗan murmushi matar ta yi ta buɗe jakarta ta zaro ɗari biyar, ta miƙa mata ta ce

“Tashi ke ji ki siyo Omon kin ji”

Karɓar kuɗin ta yi sannan ta tashi ta shige ɗaki, wani hijab na tayabo ta zuro maroon colour daga gani kasan ya daɗe amma kuma tass dashi a goge, ta zura slippers ɗinta tayi waje tana tafiya cike da nutsuwa. Sai da ta fita sannan Hajiya Jinjin ta ce“Wannan faɗan da ki ke ai bashi da amfani Rahmatu” tsaki tayi ta ce“ba zaki gane halin da nake ciki a gidan nan ba, nagaji, ni ban fita nayi sana'a ba, ita ma yar ya hanata sana'a, bashi da hali sai kifaɗi, yarinyar kamar wannan ya ce wai sai taje makaranta, yaƙi ya aurar da ita ballantana na saka rai da samun wani abu daga wajen mijinta. Je bi yarinyar nan, ji sura, ji kyau amma duk a banza, kullum sai gantalin bokon da ba zai amfaneta ba, yanda ki ka san ubanta ƙaruna ne haka take ji da zuwa makaranta” girgiza kai Hajiya Jinjin tayi ta ce“To wai har yanzu shi Malam Habu ɗin bai barta ta yi ko talla ba?, yara kamarta zaki dinga gani suna talla gwanin sha'awa suna rufawa kansu asiri, idan aurenta ya tashi da me za'a yi?”

Caraf ta amshe ta ce“Kin gane inda matsalar take ashe, ba zai bari ba, taurin kai ya yi masa yawa, ko zan mutu akan faɗa masa ba zai yarda ba, gani yake ma kamar tsanar yarinyar nan nayi” taɓe baki ta yi ta ce“Ai ko wannan ba rayuwa ba ce, a cikin wannan halin kanada yarinyar ai ka nuna mata hanyar samun taro da sisi, Yarinya da girmanta amma tana zaune sai dai komai a yi mata”

“Idan muna da abin yi mata ɗin kenan, sai dai komai dai ta rasa, kullum haka yake zaunar da ita a wajen nan yana mata nasiha mara amfani, ita kuma tana faman gyaɗa kai kamar ƙadangaruwa” Dafata ta yi ta ce“Calm down, haƙuri za ki yi, cikin kissa zaki yi masa magana, kefa mace ce, kisan yanda zaki jawo hankalinsa ya gane abin da ki ke nufi, amma tashin hankali ba zai miki magani ba, tun da kin san halinsa” jinjina kai Rahmatu ta yi ta ce“Tom, zan gwada sa'a ta, amma halin Malam...” murmushi ta yi ta zaro wata sabuwar dubu ta miƙa mata ta ce“Ki riƙe wannan a hannunki, Allah ya rufa asiri, nima jiya saurayin Maryam ya zo ya bata kuɗi him shine na karɓe” washe baki Rahmatu ta yi tana dariya ta ce“Kinga harkar arziki, kai Allah ya ƙara arziki, Nagode, Nagode Hajiya, yanzu da a ce nima yar nan tana da mashinshinin ai da ba haka ba, to ita wai Allazi boko” Murmushi kawai Hajiya Jinjin tayi, daidai nan tayi sallama ta dawo gidan, har sannan kuma garin a haɗe yake da hadari, ƙarasawa wajensu ta yi ta tsuguna cike da ladabi da miƙa mata canjin, girgiza kai Hajiya ta yi ta ce“Riƙe a hannunki, kema kya kashe” shiru ta yi sai kuma ta girgiza kanta ta ce “A'a nagode”


“Munafuncin banza, za ki tashi anan wajen ko sai na kwaɗeki, baƙin hali irin na ubanki” tashi tayi ta koma inda ta haɗa kayan wanke wanken jiki a sanyaye, murmushi Hajiya ta yi ta ce“Ai daidai kenan, hakan ma wata tarbiyyar ce”

“Yo tarbiyya ko munafurci?”

Ita dai tana jin su bata sake cewa komai ba ta cigaba da wanke wankenta,a zuciyarta tana karatun haddarta dan anjima zata bayar.

****Around 5:45pm take tafe a hankali, sanye take da wani hijabi Ash colour wanda ya rufeta ruf, ko ƙafafunta baka gani, tafiya take tana sake ɓoye littafan hannunta gudun kada yayyafin da ake ya jiƙa mata su.  Namiji ne tsaye jikin wani bango jikinsa sanye da wasu kaya wanda suka matseshi sosai, kansa ya yi wani irin aski wanda kana gani zaka iya faɗar kowane shi, fuskarsa duk tabbai na yanka da ɗinki, hannunsa riƙe da ledar gyaɗa yana cillawa a baki yana taunawa. Tun da ta hangoshi gabanta ya yanke ya faɗi amma ta dake, da sauri tafara tafiya tana shirin shige shi ya juyo yana kallonta ya ce


“Kut, duk jiran naki da nagama shine za ki zo ki shigeni? Haba my love” cak ta tsaya amma bata juyo ba, ya tako har inda take, ban da warin wiwi babu abin da yake, ga tsami na rashin gyara, tayi saurin ɗauke numfashinta tana runtse ido.

“Ummusalma!”

Aka kira sunanta a tsawace. Juyowa ta yi ta kalli mai kiran nata sai kuma ta sunkuyar da kanta, wani babban mutum ne mai kamala zai iya kai wa 55yrs ɗin nan, yana sanye cikin wani yadi mai sauƙin kuɗi, kansa ɗauke da hula. Fari ne tas kuma kyakkyawan bafulatani, sai dai rashi ya ɓoye asalin kyawun nasa. Ƙarasowa gabanta ya yi, ya kalleta, sai kuma ya juya ya kalli Bashir dake tsaye, ɗan sunkuyar da kansa ya yi yana shafa ƙeya ya ce“Barka da Yamma Dad” bai amsa maganarsa ba, sai cigaba da kallonsa da ya yi kamar mai son gano wani abu. Juyawa Bashir ya yi ya bar wajen, girgiza kai Malam Habu ya yi sannan ya juyo yana kallonta. Sunkuyar da kanta tayi yayyafin na dukanta, bai ce mata komai ba ya kama hanyar gida, ganin haka ya sanya Ummusalma min bayansa tana tafiya da sauri.



A tsakar gidan ta sameshi ya naɗe hannayensa yana kai da komo, tana shigowa ya juya yana kallonta cikin faɗa da kuma hargagi ya ce“Wanene wannan? Menene haɗinki dashi? Me ki ke tsaye kina yi dashi Ummusalma?” girgiza kanta ta shiga yi bakinta na rawa ta ce“wlh Abba ban kula shi ba, kawai kullum sai ya dinga yimin magana, bana kula shi, shine Umma ta ce idan na sake shigewa yana yimin magana sai ta zaneni”

“Kaji annamimiyar yarinya, ni nasan inda ma ki ke zuwa ballantana nasan da waɗanda ki ke gamuwa? Ni za ki yiwa sharri? Ke ki ji tsoron Allah”

Rahmatu ta yi maganar hannunta riƙe da buta da alama daga banɗaki ta fito. Kallonta Malam Habu ya yi sai kuma ya kalli Salma ya ce“Babu ruwana da abin da aka ce miki, amma ki sani duk ranar dana sake ganinki da wani sai kin gwammace kiɗa da karatu, banason shashancin banza. Ilimi na aika ki ki yi ba wannan rashin albarkar ba, kar na sake gani...”  Daga haka ya juya ya bar wajen, sai a sannan Salma ta ɗago Idanunta tana kallon inda ya bari, Rahmatu ta zabga mata uwar harara sannan ta dire butar a gabanta ta bar wajen. Da gudu Salma ta ƙarasa ɗakinta tana zuwa ta faɗa kan tabarma ta fashe da kuka, to ita mene laifinta? Akan me za'a dinga yi mata faɗa irin haka?...



Asokoro, Abuja,
6:22pm.

Horn ɗin mota ya ɗan yi ƙara a bakin gate, nan da nan maigadi ya buɗe kofa da girmamawa. Black tinted Benz ɗin ta shigo cikin harabar gidan kai tsaye kuma ƙofar entrance na gidan tayi parking.Tana zaune a baya, ta sauke wayarta daga kunne, idonta na kallon window, kamar bata jin daɗin dawowa gida amma ba ta da choice. Gashinta a gyare, simple packing amma classy, fuskarta babu kwalliya mai yawa, natural beauty ɗinta ya sake bayyana.Sanye take da wani fitted trouser mai launin navy blue da white top mai sauƙi amma expensive, sai wata gold chain mai sauƙi a wuyanta, da wristwatch ɗin designer. Ta ɗora wata kimono black colour akai, idanunta sanye cikin shades glasses. Fitowa tayi daga motar ta ɗan ƙarema katafaren mansion ɗin kallo sai kuma ta nufi hanyar da zai sadata da cikin gidan, tana tafiya cike da izza da kuma tarin nutsuwa. Babu kowa a main parlon na gidan kasancewar yammaci ya yi kowa yana apartment ɗinsa, kai tsaye stairs ɗin benan ta nufa, tana gama hawa ta yi hanyar nata apartment ɗin, sai dai kafin ta ƙarasa ta tsaya, shiru tayi sai kuma ta juya ta nufi hanyar ɗakin Mommy. Tura ƙofar ta yi ta shiga ba tare da sallama ba, zaune ta hangesu kan kujera da alama labari take bawa Mommy, ƙarasawa ta yi ta zauna kan ɗaya daga luxury sofas ɗin dake zagaye da ɗakin

“Oh my god!”

She said. Murmushi Mommy ta yi ta ce“An ɗebo wahala ko?, da tashi ki ka yi ko wanka ki yi kya samu sauƙi” bata ɗago ba, sai ma sake kwanciya da tayi akan kujerar tana lumshe idanunta. Taɓe baki Nimra ta yi ta ce“lazy girl” sai a sannan ta buɗe idanunta ta zuba mata, kamar zata yi kuka ta ce“saukar yaushe?” tayi maganar tana tashi tsaye. Ɗan murmushi Nimra ta yi ta ce“ban jima ba, kuma tafiya zan yi” jinjina kai Mufeeda ta yi, ta ɗauki handbag ɗinta tana cewa “Ina mijinki?”

“Yana gida” ta ce a taƙaice, ɗan cute smile Mufeeda ta yi ta ce“My regards to him please, na ɗan jima ban ganshi ba” Toh kawai Nimra ta ce sannan ta cigaba da danna wayarta, Mufeeda ta kalli Mommy ta ce“lemme take shower Mom” gyaɗa mata kai ta yi ta ce“Idan kin gama make sure kin ci abinci, nasan halinki” langwaɓar da kai ta yi ta ce“Sure Mom” daga haka ta fice daga ɗakin, sai a sannan Mommy ta juyo tana kallon Nimra ta ce“Kin dai ji nafaɗa miki” kamar zata yi kuka ta ce“Naji fa Mommy”...

****Mufeeda na fita suka kusa cin karo da Khalil wanda shigowarsa kenan, murmushi ya sakar mata ya ce“Shagwaɓa princess, school ɗin ne?” gyaɗa masa kai ta yi, ya ce“ohya je ki huta, zuwa anjima muje yawo”

“Really Bro?”

Gyaɗa mata kai ya yi ta ce“Awwwn, bari naje na shirya” daga haka tayi hanyar apartment nata da ɗan sauri.

No.34 Wuse 2, Abuja.

Zaune yake cikin katafaren office, hannunsa riƙe da wayarsa yana dannawa, buɗe ƙofar office ɗin aka yi ya shigo bakinsa ɗauke da sallama. Zama ya yi kan kujera har lokacin Zayyad bai ɗago ba, ɗan tsaki ya yi ya ce“Ni zaka wulaƙanta? Wai kai menene matsalarka ne?”

“You”

Zayyad ya faɗa still looking at his phone. Ƴar dariya Ahmad ya yi kafin ya ce“Then karka sake kirana a waya, kuma nima ba zan kira ka ba, kowa ya yi rayuwarsa” kashe wayar hannunsa ya yi ya ɗago yana kallonsa, sanye yake da wata suit black colour wanda suka yi masa kyau, fuskarsa da kamala kamar ba wancan Zayyad ɗin ba. Furzar da iska ya yi daga bakinsa sai kuma ta miƙe tsaye ya ɗauki car key ɗinsa ya yi hanyar waje yana faɗin

“Sai ka kwana anan”

Girgiza kai Ahmad ya yi sai kuma ya tashi ya biyo bayansa, a parking lot ɗin babban asibitin ya sameshi yana ƙoƙarin shiga motarsa. Dafashi Ahmad ya yi, Zayyad ya juyo ya zuba masa idanu yana kallonsa.

“Yanzu ina zaka je?”

“Club” ya ce ba tare da ya kalleshi ba, shiru Ahmad ya yi sai kuma ya ce“kenan kullum sai kaje club? Sai yaushe ka shirya daina wannan rayuwar ne friend?” ɗan murmushi Zayyad ya yi ya dafa kafaɗarsa ya ce“You can't understand”

“Ai daman ba zan taɓa ganewa ba, har abada kuwa, amma kasani wannan ba rayuwa ba ce, watarana zaka yi danasani” harɗe hannayensa ya yi a ƙirji ya zuba masa idanu yana ji yana masa masifa, sai da ya gama tas sannan Zayyad ya juya ya shige mota ya figeta da gudu ba tare da ya bawa Ahmad amsa. Girgiza kai kawai Ahmad ya yi sannan ya ƙarasa gaban tasa motar ya shige ya bar asibitin.



Around 9pm ya yi shiga gidan, zaune ya yadda Nayla tana danna wayarta tana ganinsa ta taso ta rungumeshi tana dariya, janyeta ya yi a jikinsa fuskarsa a haɗe ya ce“Kin raina ni ko? Ina Mommah” dariya ta sakar masa ta ce“A'a fa big bro, dan nayi maka welcome back?. Mommah nasama, kuma tana jiranka nasani”

“Yen yen”

Ya faɗa yana taɓe baki, tuntsirewa ta yi da dariya tabi bayansa ganin ya yi hanyar sama. Kai tsaye apartment ɗin Mommah ya nufa, ya tura ƙofar bakinsa ɗauke da sallama, zaune ya hangeta kan sofa tana danna system ɗin gabanta, ƙarasawa ya yi ya zauna kusa da ita. Kallo ɗaya tayi masa ta ɗauke kai ta cigaba da abin da take, Nayla dake tsaye ta kalleta ta ce“Mommah ga Yaya fa” kallonta ta yi ta ce“Me zan yi masa to?” yanda tayi maganar ya sanya Nayla yin shiru ta juya ta fice daga ɗakin. Sai da taga ta fita sannan ta rufe system ɗin dake gabanta ta ɗago ta kalleshi, gani tayi yana kallonta. Bata ce masa komai ba ta tashi ta shige kitchen nata, not too long ta fito hannunta riƙe da tray, a gabansa ta ajiye masa sannan ta shige bedroom ɗinta. Kamar jira yake ya gyara zamansa ya shiga buɗe warmers ɗin, lafiyyayiyar White rice ce, wadda taci kayan haɗi sai ɗaukar ido take, ya sake buɗe ɗaya warmer ɗin mai ɗauke da miya wadda taji nama sai ƙamshi take. Plate ya ɗauka ya yi serving kansa sannan ya yi bismillah ya fara cin abincin dan daman yunwa yake ji.

Tsaye take cikin toilet ɗin hannunta riƙe da wayarta lokaci zuwa lokaci tana kallon screen ɗin wayar, kiran data gani ya sanya tayi saurin ɗagawa murya can ƙasa ta ce“Eh ya ci, nasan ya ci” daga ɗaya ɓangaren aka ce“Ki tabbata dai ya ci, idan ba haka ba aikin zai tashi a banza”...

# HCD
# Light within the darkness
# Nanameera
***