DAN HALAK

p-19

by @rabiattu0444

***

XPthThNQx

💋ƊAN HALAK💋

MALLAKAR

UMMU MAHER(MISS GREEN)🍃

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION📖*

AREWABOOK

https://arewabooks.com/book?id=663

1fffa0eeb3b80f1ef8159

WATTPAD

***

_content=story_info

Ina masu son shiga adashe Amma kuna fargaba🤔yar uwa ki tsarkake zuciyan ki kizo kiyi adashe cikin aminci da kwanciyan hankali insha Allah Babu rigima ko tashin hankali kwanciyan hankali zaki Yi adashen ki Kuma mu gama lfyh da yardan Allah..🥰🤝

30k weekly parking 300k

1)Haj Maryam✅

2)Ada umar/hafsat yahya✅

3)Usman

4) barrister hauwa'u

5)shafa bello/baby daura

6)

7)

8)

9)

10)

Akama slotd

***

sRmuDuL

19

________Hankalinmu ya yi ƙololuwar tashi, tun ma ba kamar ni ba domin kuwa kowa yasan yadda nake son Anisa tamkar ƴar dana haifa a cikina. Umma sai kuka take tana kiran sunan Anisa amma tamkar dai an shuka dusa saboda ko motsi ba ta yi, cike da tashin hankali muka yi waje neman ɗan sahu muka yi sa'a wani ya kawo wasu maƙotanmu, da gudu muka sanyata a ciki Umma ma ta shigo muka wuce asibiti, sosai muke kuka Umma ce ma me ƙarfin halin tofa mata addu'ah tana shafa kanta tana ɗan siririn hawaye mai tafe da abubuwa da yawa.

Ƙaddara da tsautsayi tamkar abu ɗaya ne a fassare sai dai a baki harufan suna da banbanci, domin ita dai ta tabbatar ƙaddara ce ta sanyata afkawa kogin maganaɗisun auren mahaifin yaranta, domin ko kusa ba ta ma sanya shi a sahun manemanta ba, saboda ba shi take so ba amma da ƙaddara ta zaɓa mata shi tasan tabbas da babu yadda za a yi ta zaɓe shi a matsayin mijinta, domin ko a lokacin da ta aure shi kowa tofa albarkacin bakin shi ya dinga yi, musamman ma masu cewa wai ita matar manya ce duk da ba shi da mugun hali kamar yanzu, tunda ada can baya in har ta ce yana mata wani abu tabbas ta yi mishi ƙarya, zuwan Baba Kande ne ya canja komi rayuwar su ta zamo tamkar rayuwar ƴan bariki, sannan baya shakkar dukanta a gaban yaransa duk domin matar shi.

WACECE BABA KANDE?

Baba kande dai ƴar asalin garin Jos ce, sannan babu wanda bai san mecece sana'ar ta ba ƴar bariki ce me siyar da taba da wiwi, aƙalla aurenta ya kai shida tun ana ƙirga mata aka daina saboda aurenta na biyu ne ma ta kai shekara ɗaya amma duka aurenta ba ta kai ko cikakkun wata biyu take tafiya, kuma duka babu wanda ta taɓa haihuwa dashi domin a cewarta ba ta zo duniya domin haihuwa ba ta zo ne domin hutawa. Saboda haka Allah ya ɗora mata son mahaifinsu Humairah tun wani zuwa da ya yi Jos, ta liƙe mishi tun yana guje mata har Allah yasa ya faɗa komanta, tunda ta asirce shi baki ɗaya ya zama bawanta babu abin da yake haɗa shi da yaran shi sai zagi da hantara. Bayan ya aure ta shi kenan bata ƙara fitowa ba da zummar bazawara, har yau da take da kusan shekara 5 a gidan shi.

Mu koma labarinmu.

Sosai take shan jiki, domin ko kafin mu zo asibitin ba ta numfashi ko kaɗan hankalinmu ya ƙara tashi sosai, da ƙyar likitoci suka amsheta domin sun ce tana cikin koma sosai, wato tana cikin matsanancin hali muna ji muna gani aka shigar da ita emergency(ɗakin gaggawa).

Muka tsaya a reception muna kuka har Umma ta gaji da kukan mu ta ce" wai shin bawa yana iya canja ƙaddarar shi ne? Shin idan Allah ya so ɗaukar rayuwar ta za ku hana ne? Bakwa mata addu'ah sai kuka? Haba ku dinga yawan kiran 'LA ILAHA ILLA ANTA SUBHANAKA INNI KUNTU MINAZZALIMIN, yawan kiran wannan addu'ar yana cire dukkanin bawa musulmi acikin wani hali, saboda haka kuyi ta kiran wannan addu'ar komi tsanani akwai sauƙi da yardar Allah".

Tuni bakunanmu suka fara wannan addu'ar, muna cikin wannan halin ne wani dr ya fito kai tsaye ya yo inda muke, jikinmu duk a sanyaye sai da ya fara kallonmu a nutse sannan ya ce" ku ne ƴan uwan yarinyar nan ko? Da sauri muka amsa, ya cigaba da magana "muna so ku sanya hannu da gaggawa za a mata tiyata ne domin fitar da gubar da ta sha a cikinta, sannan za ku biya kuɗin tiyatar naira dubu ɗari".

Salati muka sanya mu dukanmu, tashin hankalinmu a fili muka fara kuka a wannan lokacin har da Umma a masu kukan, likitan ya ce" ba kuka za ku yi ba ku nutsu kuyi abin da na ce idan ba haka ba zaku iya rasa ta baki ɗaya".

Ni ce na fara magana ina kuka" likita ayi mata aikin duk inda kuɗi yake zamu nemo shi don Allah ayi mata". Na saki kuka mai ƙarfi, gami da haɗe hannayena waje guda alamar ya taimaka su yi mata.

Ganin hakan ya ce" A a, bama aiki sai an fara biya kuyi haƙuri dai ku bubbuga ku kawo mu samu mu ceto rayuwarta". Da sauri Ameerah ta ce" likita wallahi ko kaɗan bamu da wannan kuɗaɗen ko kusa, ko dubu biyar bamu da ita balle dubu ɗari ni na tabbatar akan kuɗin nan sai dai yarinyar nan ta mutu".

A kiɗime ya kalle ta sannan ya ce" shin ba ku da mahaifi ne? A iya sanina mahaifi shi ne jagaba akan dukkanin lalurorin iyalin shi, saboda haka ku kira shi ku faɗa mishi".

Babu musu na danna lambar wayarshi a wayar Umma, wacce Anty Salamatu ta bata domin ta dinga jinta tunda ita ta koma gidanta yanzu.

Bugu ɗaya ya ɗaga, da sauri na gaishe shi. Na faɗa mishi duk halin da muke ciki.

Saurin kashe wayar na yi, domin kuwa iya tashin hankali ina cikin shi domin maganar da ya faɗa min ba wacce ya kamata kowa ya jita bane domin girmanta ya girmama har ya gagari dutsen dala, ɗaukar maganar sai an naɗa gammo ɗari ba tare da an iya ɗauka ba.

HAIDAR

Kallon Mimi ya yi yana ce wa" ki fita a idona fa? Ni ba sa an wasan ki bane akan mi za ki dinga ce min ango?".

Mimi ta ƙunshe dariyarta tana ce wa"Sorry ya Haidar". Bai ƙara tanka mata ba ya zauna jiran Ammi da Alhaji.

A hankali suka fara saukowa a tare, Haidar yaji wani irin abu me masifar zafi ya sauko mishi a cikin zuciyar shi, tunda ya taso Allah bai taɓa ɗora mishi son wannan bawan Allahn ba, domin kuwa shi kaɗai ya barwa kanshi sanin abin da yasa ya tsane shi har haka, sam bai iya tsana ba idan ya so abu a farko abu mai wahala ne ya ƙi shi, idan kuma ya ƙi abu a farko to a ƙarshe ma yana matuƙar wahala ya so shi, ya kasa gane wacce kalar tsana ma yake yi wa wannan bawan Allahn, shi dai yasan tabbas tsana ce wacce har ka mutu kana yiwa mai shi.

Alhaji da fara'ar shi ya ce" A a Haidar ango, sannunka da zuwa".

Ya faɗi hakan da maɗaukakiyar fara'a. Haidar ya ɗan kawar da kai tamkar dai ba zai mishi magana ba, sai kuma ya tuna da alƙawarin da ya yiwa Ammi na gaida mijinta a duk lokacin da suka haɗu.

A ɗan basarwa ya ce"sannu da fitowa". Ammi ta yi saurin kallon shi alamar wannan gaisuwar da ya yi ba ta yi mata ba, yasan sarai dama ba za ta so gaisuwar ba amma saboda son tabbatar mata har yanzu fa wannan tsanar tana nan a cikin ran shi.

Alhaji ya amsa yana fara'a ya ce" Haidar ɗazu mun yi magana da Amminka akan gidan da za ka zauna, to ga mukullin sabon gidana mr part huɗu wanda na kammalashi kwanan nan, kuma ya kasance mallakin ka har abada domin da sunan ka aka gina shi".

Haidar haushi ya kama shi, tamkar dai zai saki kuka saki kuka domin shi dai ko kaɗan ya tsani shisshigin da wannan bawan Allahn yake mishi, ce mishi ya yi bai da kuɗin da zai sai gida ko mi? A iya sanin shi ya mallaki gidajen da ƙirga su ma tamkar ɓata baki ne saboda zunzurutun yawansu, cikinsu kuwa har da waɗanda shi da kanshi alhajin bai isa ya gina su ba.

bai gama tunanin ba yaji Alhaji yana ce wa" sannan na ware maka kuɗi kimanin naira biliyon biyar, domin ka yi hidimar biki sannan na ɗauki nauyin yi maka laife yanzu haka ma na bawa ƙanwata tana can dubai".

Cike da matsanancin haushin abin da ya yi mishi ya ce" na gode".

Daga haka bai ƙara magana ba, ya tashi gami da sanya hannuwan shi duka guda biyu a cikin aljihun shi sannan ya miƙe tsaye ya yi musu sallama. Ammi ta kira sunan shi da sauri, ya juyo yana mata kallon kar ki yi min haka. Cike da isa irin ta ɗa da mahaifi ta ce" amma Haidar kana da hankali kuwa? Kai bakasan ayi maka abin alheri ka yi godiya mai yawa ba? Shi ne ka yi mishi wannan banzar godiyar ka tafi? Allah wadai da lamarinka wallahi".

Da sauri Mashal ya dakatar da ita wajen ce wa" ahir ɗin ki Habibty, kada ki ƙara faɗawa ɗanki mummunar magana sabili da wani abu ya haɗa ku, kuma ma me ya yi ne? Godiya fa ya yi min so kike sai ya dafa ƙafafuna sannan za ki tabbatar da cewar ya yi mini godiya? Kada ki sake Allah wadai da shi kin ji?.

Cike da matsanan cin haushin ɗan nata ta amsa mishi da to, Shi kuwa Haidar rintse idon shi ya yi sannan ya fice baki ɗaya daga gidan, yau bai taho da direban shi ba dama kuma bai fiya fitowa da bodyguard ba idan zai je gidan Ammin shi ba, Yadda ya tsani mutuwar shi haka ya tsani mijin mahaifiyar shi har baya son tunawa da mugun ƙullin da ya haddasa mishi a arayuwa wanda har yanzu bai fita daga cikin shi ba.

Kiran Khausar ya dinga shigowa akai-akai, sosai yaji tamkar zai fasa wayar saboda haushi domin kuwa a rayuwar shi baya son ko tunawa da ita, musamman da ta zama ƴar aminin Mashal abokin cin mushin sa.

LULU

"Hajiya don Allah ki taimakeni ki shige min gaba wajen son na auri yaya Haidar, wallahi ina tsananin son shi da ƙaunar shi wallahi idan har ban aure shi ba bansan inda zan sanya kaina b"...

Wani irin mugun mari Hajiya babba ta gaura mata, sannan ta fara magana tana huci ta ce" Allah ina roƙonka ka sa mafarki nake, yaron da ba ɗan halak ba shi kike so"?.

$HUMAIRA

$AMEERA

$ANISA

$UMMA

$HAIDAR

$MASHAL

$AMMI

$MIMI

$LULU

$HAJIYA BABBA

SHARE

COMMENTS

CHART NO WHATSAPP📲

MRS GREEN CE