ZUCIYAR MUTUM

CHAPTER 44

by @khairatup01

Zuciyar Mutum.
Khairat.
Wattpad:Khairi_Muhd.
Arewabooks:Khairatup01
44

*

Yadda Haidar yake kulawa da Ummu ita kanta tana mamakin hakan. Haidar ko fita baya son yi sai dole. 

Ko da Mami da Baffa suka dawo sai da suka biko da kan su. Ya yi ta yi musu dariya kawai

Bayan sati biyu Afeeya ta diro Abuja. Ta girgiza da ganin yadda Haidar ya yi kyau ya yi shar da shi. Har wata ƙiba ya ga ya yi. Haka ta danne zuciyarta saboda ba yanzu ne ya kamata tayi faɗa ba. A hankali da siyaysa zata kama shi bata son ta yi aikin gaggawa.

"Alhaji Haidar kenan manyan ƴan ƙasa. Ka ga kuwa yadda ka koma lallai amarya na yin aikin ta yadda ya kamata."

"Ai ba sai na gaya miki yadda take bani kulawa ba. Ba fa wai irin kulawar da ki ka bani a lokacin da nake tare da ke ba.Da ke yanzu na san meye aure ai dole ne na kile." Ya faɗa yana murmusawa.

Ita ma murmushin taƙaici ta mai da masa don ta ji zafin abinda ya faɗa mata.

"Haka ne. Nima ina fatan dawowa ai na ɗora daga inda na tsaya. Ina fatan zaka buɗe mini ƙofa?"

"Ƙofar Haidar ta kulle babu waje ke ko da waje ma Ummun dai zan ƙara cusawa. Bata da buƙatar abiyar zama abiyar zaman ma irin ki." 

"Haidar kenan. A juri zuwa rafi dai wata ran tulun zai fashe."

"Wannan tulun na ƙarfe ne, Ba zai fashe ba."

"Zamu gani Haidar ni na sai na zame maka ƙarfen ƙafa sai ka gwammaci da kan ka ka maido ni cikin rayuwar ka don Wallahi izayar da zan yi maka kai kan ka sai ka ji ka tsani kan ka. Sai na hana ka sakat."

Dakatawa ya yi ya tafa hannayensa biyu yace "Good! Wannan labarin ya yi mini daɗi. Ina jiran ki Afeeya ai dama irin wannan wasan ya fi daɗin bugawa. Mu zuba ni da ke."

Baki ta cije ta yi hanyar ciki.

Shi ma tarikicen sa ya ɗauka ya nufi ɓariyinsa.

*

Tunda ta ji tsayuwar motar sa ta yi hanya waje saidai ta taga ta hango shi tsaye da tsohuwar matarsa. Kishi ne ya zo mata. Bata taɓa jin irin wannan kishin ba yau ma sai ta soma mamkin kanta. Ashe dai Haidar ya zauna daram a cikin zuciyarta ba sai yau.

Ta gama cika ta yi fam bata ma ga tahowarsa ba bare shigowarsa ba kawai ji ta yi ya rungume ta ta baya.

Bata nuna masa komai ba ita ma ta juya ta rungume shi.

"Sannu da zuwa."

"Yauwa matata. Ya zaman gida da kuma kewa na?"

"Babu ko ɗaya da ya gundure ni."

"Aww gaskiya ni ɗan gatan Ummu ne . Shi ya sa nake son ki nake mararinki. Ina can amma hankalina da tunanina yana wurin ki abar ƙaunata."

Murmushin ƙarfin hali kawai tayi masa.

Har zai shiga ɗaki sai kuma ya juyo yace "Au na manta fa kin san da wa na haɗu yanzun nan da zan shigo?"

"Aa" na faɗa ina tambayarsa kamar ban sani ba. Ban zata zai kawo maganar ba. Sai ga shi.Ruwan da ke kan dinning mai sanyi da na ɗauko masa na miƙa mai.

"Na gode fa."  Sai da ya sha ruwan tukunna  ya ci gaba.


"Afeeya mana na gani ina ga unguwa taje ko ina ma oho ban sani ba. Wai na yi kyau, tana son ta dawo, ko na dawo da ita ko ta dawo ta ƙarfin tsiya. Kin ji fa wai ni  Haidar take yi wa barazana. An gaya mata ina tsoron barazana ne?  Ni wadda ta kawo ta duniyar ma ana fi ƙarfinta bare ita. Kin san me na ce mata?"

Na girgiza masa kai da sauri.

"Na gaya mata na gama rufe ƙofa in ma zan buɗe  ƙofar ke ɗin dai zan  buɗewa ki shiga ke kaɗai ai i daga ke babu ƙari." 

Sai a sannan ma na yi murmushi. Wai kai Hammana baka iya ɓoye sirri? Kun yi abu da mata zaka zo ka tona?

Aa ai dai ni kin san bana ɓoye miki komai. Gwara na gaya miki na ga kamar kin gan mu kar ki ɗauka wai soyayya muke yi ni da ita don dai na ga sauyi ba haka aka saba taryata ba zuwa ake a rungume ni amma yau dake kishin ya zo sai kika ƙi buɗe min ƙofar ma. 

Na kama baki ina dariya nace "Kai Hamma yaya aka yi ka san na gan ku?"

"Uhm ke kika sani."

Da kunya ta bi shi ɗakin tana lallaba shi yana basarwa.

Ni bana son sabgar ɓoyo na ga kina son sauya hali ne.

Aa kayi mini afuwa ban san...

To yau na gaya muki daga ke ba ƙari.

Na yarda na amince.


Bayan ya fito ya shirya ta jera masa kayan abinci. Tare suka ci suna hira. Nan yake gaya mata za shi Dubai wani aiki da tare da Baffa ma za su je amma Baffa baya jindaɗnin jikinsa.

Kwana nawa zaka yi?

Kamar sati zan yi daga can dai zan wuce Manchester Sanda ta kira ni muna da aiki.

Wace haka?

Tsohuwar budurwa ta ce a London tare fa muka yi makaranta amma yanzu kamfanin da nake aiki da su a can muna wa kamfaninsu zanen wani gini zata yi mana approving ne tukuna.

Wai don Allah Hammana yaya kake iya gaya min wanccar budurwar ka ce ko matar ka ni gaskiya bana son haka.

Ah to da na ɓoye miki fa? Ni dai kin san bana yin haka ai.

To ka koya gaskiya.

Yau na ga rigima kike ji , amma zan yi maganin ki.

Magani na kuma ne na yi maka?

Gashi nan kin turke ni sai tambayoyi kike min.

Shiru tayi kawai ta ɗauko kankana ta sa a baki. 

Naga kamar kin ji haushi ?

Mutum kamar me Juju. Sai kuwa ta kuma haɗe rai ta ci gaba da cin fruits ɗin ta ba tare da ta kula shi ba.

Sai kuma ya rikice ya tashi daga wurin zamansa ya zauna a gefenta. Hannunsa ya saka ya juyo da fuskar ta yace "To ba zan kuma ba ki yi haƙuri kin ji?"

"Ni me na ce maka? Ai ban ji haushin ka ba."

"Aa kin ji."

"To ai na ga kamar ka fi son ƴan matan naka da ni."

"Ki kalle ni mana Ummuna, ba ki ga yadda soyayyar ki ta mayar da ni ba gabaɗaya kamar ba ni ba kin sauya ɗan Mami ya rikice a kan ki. Ni Wallahi in ma wani abin kike sha don ki gama dani ki daina a iya haka ma kin cin gari."

"Haba dai Hamma mai zan sha ni kuwa?" Ta faɗa tana dariya.

Amma da gaske kin san zamu koma can Manchester fa. Amma sai kamar ƙarshen shekara.

Gaskiya Hamma can da nisa fa.

To ya za ki yi a can sana'ar ta wa take.

To Allah Ya kai mu da rai da lafiya.


*

Afeeya kuwa ta gama shirya tuggun da zata yi wa Haidar komai ta yi shi a kan tsari lokaci kawai take jira. Sai da ta yi kwana biyu tana nazarin shige da ficen Haidar. A wurin Umma ta ji labarin za tafi Dubai. 

Da daddare ya shirya zai tafi. Bayan sallar magariba suka ya shirya ƙananan kaya ya saka sun masa kyau sosai. Ummu kuma ta saka abaya zata raka shi airport. Da Mami ma zasu je rakiyar Joɓe ne zai kai su.

Cikin doguwar rigar atampa ta fito tana taunar cingum tana karairaya. Ba ta ji kunyar komai da kowa ba ta je ta tsaya gaban Haidar da zai shiga mota.

"Haidar" ta kira shi a hankali cike da sanyi.

Juyowa ya yi idanuwansu na haɗuwa wuri guda ya ji gabansa ya faɗi. Take kuwa cikinn ransa ya yi a'uziya. 

Wani irin turare mai ƙarfi ya ji ya shaqa. 

Ummu kuwa tsintar kan ra tayi da hararar Afeeya. Ta yi tsaki ta shige cikin motar.

Jin gabansa ya tsananta bugu ya saka a cikin zuciyarsa ya dinga maimaita innallillahi wa inna illahir rajun. Lafiya ya fito amma yanzu ransa babu daɗi cikin ikon Allah kafin su isa iyafot ya ji kan sa ya ɗan sarara masa. 

Bayan sun yi sallama da kowa aka bar shi da Ummu a cikin mota. Sai da ya gama son ransa da ita tukunna ya fita ya saka baƙin gilas ɗin sa saboda ya ɓoye idanuwansa.

*

Kwanaki biyu ya yi amma ya soma kewar gida can ƙasan ransa kuwa Afeeya ce yake ta tunani ya rasa dalili har mafarki yake yi da ita. Kafin a kwana biyar ma ya gama galabaita da tunanin Afeeya wayarsa ya zaro ya nemi lambar wayarta sama ko ƙasa ya rasa. Tsaki ya yi . Lambar Sa'ada ya kira a kashe ji ya yi kamar ya yi tsuntsu ya koma Najeriya. 

Yana ganin kiran Ummu sai ya ji baya son ɗagawa duk da ƙasan ransa yana son ɗaga kiran amma zuciyrsa na hana shi. Ƙarshe ma kashe wayar ya yi gabaɗaya. 

*

Ummu.

Sau uku tana kiransa a ranaku mabambamta amma bai ɗaga ba. Gabaɗaya tunaninta yana kan ko laifi tayi masa a rashin sani?  Babu mai bata amsar nan sai Haidar kuma shi Haidar ɗin ya ƙi ɗaga kiran na ta.

Tuni idanuwanta suka cika taf da hawaye bata saba ba, ba haka yake yi mata ba. Bai taɓa ma yi mata irin haka ba duk da tana son ta yi masa uzuri ta kasa yin hakan saboda ta fi kowa sanin waye Hamma Haidar ba zai iya cikakken awa guda bai kira ta ba. Hawayen dai ta take ta ƙoƙarin riƙewa sai da ya zubo ta share ya kuma tahowa kawai sai ta saki kukan gabaɗaya ta kwanta akan kujera. 

Tana kukan bacci ya ɗauke ta daman kwana biyun nan ba wuya bacci ya ɗauke ta koma a ina take da ta kwanta sai bacci. 

*

Bokan Afeeya Chikwudi bai tsya a guiwa ba wurin hura wa Haidar son kasancewa da Afeeya ba duk da yana samun tagarɗa a aikin asirin kaman baya kai wa Haidar sai ya ga kamar an zo ƙarshen abin sai kuma abu ya koma amma dai yana jin Afeeyar a cikin ransa.

Ita kuwa Afeeya kullum idanuwanta na kan wayarta da waya ta yi ƙara zata yi maza ta ɗauko ko zata ga kiran Haidar amma ina ba shi ba ne. Haka ya saka haƙurinta ya soma gazawa ta dinga damun Boka Chikwudi shi kuma yana bata amanar ta ƙara haƙuri zata yi mamakin aikin yadda zai ci Haidar. Don ma yana da wani tsari ne .

Umma da ta gama jin abinda Boka ya faɗa ta yi dariya tace "Ai na gaya miki Afeeya asiri ya daina taɓa Haidar yadda ya ke kama shi a baya. Kina ganin a banza na dinga mulkar shi da uwarsa? Ko ɗaya nima aiki aka yi min zazzafa a kan shi da Uwarsa na tsani na buɗe ido na ga yaron nan. Na sa aka mai asirin ya bar gida, baya jin magana ,ya kangare, ya faɗa shaye-shaye amma duk waccar ƙanwar uban nasa ta Kano Hajiya Dacta ita ce silar rushewar komai , ita ce ta lalata mini kowanne shiri a kan Haidar. Asirin da ya ci shi na ƙarshe kan auren ki ne ke kuma baki san irin wahalar da na sha ba kika kaso auren da za ki bi shawrata ma da kin ƙyale shi ki ba wa Hamisu dama ya aure ki bana jin wannan sabgar akwai amfanu ciki.

Afeeya kuwa ta karkace baki tace da ita "Umma tunda kika yi asiri ya kama Baffa  ya kama matarsa ya kama Haidar da ma waɗansu da ban sani ba nima ba zan yi ƙasa a guiwa ba zan cika nawa burin nima ta hanyar asirin ke dai kawai ki zuba ido ki gani."

"Haka ne. Ai dama ita barewa ba zata yi gudu ba ɗanta ya rarrafa ba. Ni nan da kika gan ni na san abinda nayi fa ba abin alkairi ba ne a rayuwata a yanzu haka in na ce miki bana iya bacci kar ki musa muryoyi da maganganu nake ji kawai suna min yawo ta ko ina da na runtsa zan farka kaɗan daga cikin sharrin asiri kenan. Kina ganin da Isa namu yadda ya koma yanzu ko ɗaga hannu ma baya iya yi dukiyar ma babu. Kina ganin nima Mamin ta daina shayina matar da a baya in na saka kara bata isa ta sa ƙafa ta tsallake ba. Ke ko tari nayi ta san me  nake so na kwace mijin ko unguwa zata je ni nan ni nake bata izini. A lokacin da zata haifi Haidar tsayaw na yi a kan ta saboda na ga me zata haifa na kashe ke a lokacin da take naƙudar Baffan na offishinsa daga ni sai ita sai Baba Saude haka na yo fitsari na bata tana cikin wahala a matsayin rubutun sauƙin naƙuda ba ma ta sha ba na ɗura mata sai dai a take ta amayar da shi a lokacin babu abinda ban saƙa ba na in kashe ta kawai i huta. Cikin ikon Allah ta haifi Haidar zan jefar da shi ta saman bene sai ga Baffan dole na wayance. Amma yanzu Mami saboda ɗanta ya kai kuma ya cika sai ta daina tsorona....."

"Umma ni fa ba gudu ba ja da baya.Yadda kika ci naki zamanin haka zan ci nawa. Ki ɗauka alƙadarinki da tauraron ki ne suka dishi yanzu kuma lokacina ne."

Umma tace "Haka ne!."

Afeeya ta soma kiran Ifeoma ita bata gamsu da boka Chikwudi ba in da akwai wani ta kai ta wurin sa.

*

A maimakon sati ɗaya sai da ya yi sati biyu a Dubai. Daga can ma ya wuce Manchester. 

A kwanakin yadda ya tsani jin Ummu haka ya tsani ganinta a blacklist ma ya saka lambar wayarta kuma ma sai zuciyarsa ta raya masa ya yi zaman sa ba sai ya koma can Nijeriya ba. 

Ko da suka yi waya da Baffa ce masa ya yi zai dawo amma sai an kwana biyu ana buƙatarsa a nan sosai sun fara aiki ne. Baffa bai kawo komai ba ya gayawa Mami. 

Mami tayi ta faɗa tana jajanta lamarin ai ya gaya mata sai ƙarshen shekara zasu koma can taya kuma daga zuwa wani aikin sai ya koma wani wurin ya ce sai an kwana biyu ai ba haka ake ba.

Kai ai koma mene ki mai addu'a zai dawo ai. Ba ga matar tana gabanmu ba.

Ai shi kenan.

*


Idan aka ce zata iya sati bata ji Hamma ba ,zata ƙaryata hakan. Sai ga shi yau an yi wata da tafiyarsa bata ji daga gare shi ba kuma in ta shiga wurin Mami tana gaya mata sun yi waya ita ce marainiyar sa.

Cikinta ta shafa tabbas tana kewar Hamma kuma tana son ta gaya masa tana ɗauke da cikinsa abinda yake matuƙar son ya samu a rayuwarsa ɗa sai dai ya juya mata baya. Sati biyu ya ce mata amma yau an kai wata guda kullum sai ta tambayi kanta shin me tayi masa da zafi haka? Sai ta soma jin zafinsa ita ma zuciyarta ta soma tsanar tuna shi ma (Asiri ya soma yi mata tasiri.) Ji take yi ƙirjin ta na mata suya kamar ana hura wuta a ciki na tsanar Haidar wani bin ma ji take dama ta gudu ta bar gidan sai ta yunƙura kuma sai ta koma bata iya fita daga ƙofar gidan. 

Haka ya saka ta kasa jura ta kira Adda Hussaina ta gaya mata halin da take ciki. Saboda ta fi kusanci da Addar tun asali saboda kusancin ta da Hamma Habib cikin ƴan'uwansa.

Adda ta yi shiru sannan tace "Kina wasa da addu'a Ummu. Kin ɗauka  rayuwar yanzu da ta baya ɗaya ce? kin ɗauka zama ake yi a haka? Kafin ki fara ganin laifin Haidar ki tambayi kan ki ina kika kai koken ki? 

Ki koma ga Allah kawai kiyi ta addu'a Allahn dai shi ne mai maganin komai. Shi ne ya ke rayawa yake kuma kashewa yanzu ba ke kaɗai bace ya kamata ki nutsu ki kiyaye lafiyarki.  Zan turo miki wasu addu'o'i ki dinga yin su.

In sha Allahu Adda.

Sannan bana son ki gayawa kowa ko da kuwa Mami ce in sha Allahu  Haidar zai dawo ba da jimawa ba koma waye yake son shiga tsakaninku Allah shi ne maganinsa.

Amin Adda in sha Allahu zan yi duk yadda kika ce.

Yauwa.