Raina!

Chapter 5

by @ayshashafiee01

Raina!

Aysha Shafiee

05

~ * * ~

Idan tace sakanni biyu sunyi yawa kafin ta tsinci kanta a wajen ofishin tare da  kafafunta dake rawa bata yi karya ba, don sakannin ma kawai zasu taru ne a wajen kokarin bude kofar da ta tsaya yi, ba don hakan ba tabbas idan wani yace mata ma bacewa tayi ta fito zata iya duba maganar don abinda ya faru a cikin kanta da zuciyarta wani abu ne da bata taba jin makamancinsa ba a tsawon rayuwar ta.

Don bayan ta fito din sai da ta dafe ƙirjinta don ji tayi kamar nauyin zuciyarta zai rinjayeta tayi ƙasa gabadaya tunda ƙafafunta ma rawa suke gabadaya.

Babu ko waiwaye tayi kwana ta mike hanyar da ta taho tare da zuciyarta dake girgizawa a ƙirjinta. Kuma bata ma san ya akayi hankalinta ya iya maida ita office din Matron Nafisan ba, kawai ganinta tayi ta koma ciki, don haka ta daure zuciyarta ta mika mata kayan tare da fadin babu gyara komai ya yi.

Sai bata karɓa ba tace ta hada da sauran gabadaya ta kwashe, sannan tace mata ta aika a kira mata Nabila, wata Nurse din da zasu yi aiki tare karkashin SRRI program, don haka ta jira ta karaso don zata yi mata ƙarin bayani game da wasu abubuwan.

Don haka sai ta koma ta zauna a wasu kujeru dake can kusa da kofa yayin da Matron Nafisan ta cigaba da magana tare da wata Nurse akan tsare-tsaren duty rosters ɗinsu.

Kuma a lokacin da ta zauna ɗin ne taji wani abu kamar kwalla na neman fito mata a idanu. Ta san tana da ƙwarin gwiwarta da kuma ƙarfin hali daidai gwargwado don ko sanda ta zabi karantar wannan aikin ma sai da Gwaggo tace.

"Bayan kokarin da kike dashi Safinatu ai kina da ƙarfin halin da zaki iya ma.."

Kuma ko lokacin da ta fara aiki ma ita bata ga wani abu da ya zame mata ƙalubale ba, rana daya ne ma da aka kawo emergency na wani mutumi da yayi hatsari da tazo saka masa IV line taga yadda jini ke ɓulɓula daga kafar ana dannewa da bandeji taji hannayenta suna rawa.

Amma wannan aikin bata san me yasa ba tun daga lokacin da hannunta ya zaro takardar nan a cikin motar Kawun Abuja, zuciyarta bata ƙara bata daidai ba. Yau kuwa tunda Baba Alhaji ya sauke ta a gaban ginin wajen wannan abin da ya ƙulle a mararta kamar fitsari har yanzu bai saki ba, idan ma ba'a lissafa da tarin taraddadin da ya baje kolinsa a kirjinta tunda da ta shigo har zuwa yanzu ba, to ta yaya kuma zata iya karbar abinda idanunta ya gano mata yanzu.

Ta runtse idanunta tana sake gano hoton, yadda jikinsa ke jike da ruwa kamar daga wanka ne ma ya fito... Inalillahi wainna ilaihir rajiun! Ta yaya mutum ke shiga wanka ya bar kuma kofar office dinsa a bude? Tsaya?! A ina ma wanka ne a asibiti?

**

Sakan daya, biyu bayan yarinyar ta fita Aliyu yana kallon wajen da ta ɓacewa ganinsa, don tamkar ɓacewar haka yaga tayi a gaban idanunsa, sai kawai ya karaso bakin kofar ya sake murda key din dake jiki ya kulle kofar.

Kai tsaye kwakwalwarsa ta badhi cewar tabbas mantawa ya yi bai kulle ba kafin ya shiga toilet din shi yasa har ta sami shigowa, kuma baiyi mamakin hakan ba tunda ba wannan ne abu na farko da ya yi ba daidai ba tun bayan wayewar garin yau.

Jiya da daddare sunyi magana da  Muhammad yace masa wani aiki ya shigo dashi Kadunan don haka ya jira shi zai sauka a gidansa wajen karfe bakwai, ya san yana da surgery din da zai kai shi karfe tara kafin ya shiga don haka jiran Muhammad din ba matsala bane tunda tsakanin gidan da yake rayuwa da asibitin tafiyar minti biyar ce, ko a ƙafa idan mutum zai zagaya, mintuna goma baza su cika ba zaka isa, amma haka kurun yaji ya kasa jiransa, tunda kwana ya yi yana juyi akan gadonsa yana neman baccin da ya san ba zai zo ba, kuma haka ya dinga kallo magungunan baccinsa dake ajiye akan dressing mirror din dákin nasa da ya zama ma'ajiyar magani kawai.

Bai sha ba kuma bai ma yi tunanin sha din ba, don ya riga ya sani cewa jikinsa ya dade da daina karbarsu, duk wasu kwayoyin jikinsa sun gama sabawa dasu don haka basa iya cinsu da yaki, abinda suke bukata shine abu na gaba wato wadanda suka fi wadannan din karfi, kuma hakan shine inda baya son matsawa, don ko a magagin bacci ya san illolin da shan su zai haifar masa idan har ya zama addicted dasu kamar yadda ya zama da wadannan.

Don haka sai wajen karfe uku ne sannan ya tashi ya shiga jero sallolinsa tare da addu'o'i, hakan yasa yaji kirjinsa ya washe abinda yake ji ya masa sauki, har ya samu ma ya je kitchen ya soya kwai sannan ya sake gasa biredin da ya kwana uku a fridge yana sanyi. Kuma yana gama cin abincin da ya yi wanka ya shirya kawai sai yaji ba zai iya zaman jiran Muhammad din ba tunda ya san bakwan da ya fada kawai a baki take, kafin ya karaso gidan nan takwas zata yi ko ta kamo hanya don haka ya gama shiryawa cikin wasu kaya kalar dark blue sosai, laushinnyadin da kyan dinkin ya kwanta a jikinsa sosai yana nuna ƙwarewar da aka nuna wajen dinka su.

Hular da yasa ma dark blue ce mai ratsin fari kadan, bai ko kalli mudubi ba ya debi wayarsa tare da robar ruwan da baya rabo dashi  a koina kuma a kodayaushe ya fito ya dauki motarsa, a ƙasan tukunyar wata jar fulawa a harabar gidan ya barwa Muhammad mukullin gidan sannan ya ja motarsa ya fita.

Kuma yana isowa cikin asibitin ne lokacin da ya gama tsaida motar a harabar Parking space din wajen, wayarsa ta shiga ƙara da kiran Muhammad, ya dauka ya shiga sauraren korafin da yake yi na ya karaso bai same shi a gidan ba, kusan watanni biyu rabon da su hadu amma ya kasa jiransa, yana jinsa yana masa lissafin yadda mahaifiyarsa ke ta dokin dawowarsa wai tun jiya ta tuƙa tuwon da zata yi masa ɗumame da safiyar nan saboda ta san akwai shi da son tuwo musamman ɗumame amma yace duk ba zai fara zuwa can ba sai yazo ya ganshi tukunna.

Bai san lokacin da yayi murmushi ba yana shafo bayan kansa da tafin hannunsa jin yadda ya dage yana ta bayanin yadda aka yi tuwon nan.

A lokacin ne kuma idonsa ya gano masa lokacin da wata matashiya ta fito daga cikin wata mota ƙirar odessy a ɗan gabansa kadan, kalar kayanta mai haske sosai da ya haska a cikin hasken safiyar shine abinda ya dauki hankalinsa a lokaci guda idonsa ya kalle ta, kuma duk da baya ganin fuskarta amma haka kurum idonsa ya tsaya akanta yayin da yake wa Muhammad din bayani cewa ya kwantar da a hankalin sa ya shiga gidan kawai ya huta, yana gama surgery din da yake dashi zai fito.

Da motar tazo zata fita sai yarinyar ta dan matsa kadan ta bata hanya, ya yi kamar zai ga fuskarta amma bai gani ba har sanda ta gyara zaman jakar hannunta sannan ta yi gaba, a lokacin ya gama wayar, sai kawai ya maida hankalinsa wajen shiga email ɗinsa don ya tabbatar date din SRRI program din nan ba yau bane don baya son duk abinda zai sa shi dadewa ya bar Muhammad ɗin yana sake jira.

Sai gashi ya shafe kusan da awa biyu a cikin surgery din nan bai gama ba, shi da yawanci cases irin na tiyatar da yayi ta simple Inguinal Hernia (Ƙumburin mara)

Baya taba wuce awa guda ko ma ƙasa da haka bai gama ba.

Ya tuna lokacin da ya shiga dakin tiyatar bayan an kammala komai an lula patient din duniyar allurar anasiziya kamar kodayaushe, don baya taba kafarsa cikin dakin tiyatar sai an tabbatar masa da cewar an kammala komai yadda yana shiga aikinsa kawai zai fara, kuma kamar yadda patient din nasa basa taba ganin fuskarsa haka shima baya damuwa ya kalli fuskokinsu, idonsa na kan wajen da yake budewa ne kawai har ya kammala ya rufe.

Amma haka kurum yau sai ya juya ya kalli mutumin dake kwance akan gadon, hasken fitilar tiyatar ya haske fuskarsa sosai da kuma farin sajensa, babba ne sosai dattijo, kuma haka kurum sai kwakwalwarsa ta hasko masa cewar watakila a shekaru zai iya kaiwa sa'an mutumin da yake kwana yana tashi manne da fuskarsa a idanunsa, mahaifinsa! Duk da ba a haka ya sanshi ba lokaci na karshe da duniyarsu ta rabe amma wucewar shekarun da bai san nawa bane a yanzu zasu iya sa wa ya kai hakan.

Kuma yana tiyatar idonsa na hango masa samarin da ya gani suna zarya a kofar wajen kafin shigowarsa wanda babu makawa yayan mutumin ne, idanuwansu dauke da rashin nutsuwa da kuma hankoro, jira suke kawai ace ayi wani abu dukkansu su yunƙuro, sai zuciyarsa ta sake matsewa da tarin wasu tunanikan yana ayyanawa a ransa cewa tabbas idan za'a jera su tare ace su fadi ma'anar kalmar uba, abinda zasu fada ya sha banban da nasa.

Watakila su sunyi sa'ar samun wannan kalmar a mutumin da ya kyautata rayuwarsu, ya ƙaunace su da irin kaunar dake tsakanin ɗa da mahaifi, ya riƙe hannunsu ya ja su zuwa ingantacciyar rayuwa, ya nuna musu daidai da akasin sa ta hanyar da zasu fahimta, ya fahimci cewa ra'ayinsu ba laifi bane, ya yarda da su kafin ma duniya ta yarda da su.

Yana tuna yadda ya sunkuyar da kansa yayin da hannunsa ke tsaye cikin tiyatar, zuciyarsa na cigaba da fente masa tasa kalmar Uban da tarin ma'anonin da ya sani tun yana ƙarami...

Tsoro.

Tsana.

Fadan da babu dalili.

Wanin da ba zai saurare ka ba.

Wanin da zai matsa maka lamba akan kuskure da ba kai ka aikata shi ba.

Wanin da ba zai taɓa ce maka 'kayi kokari' ko 'ina yi alfahari da kai' ba.

Ya lumshe idanuwansa yayin da wutar tiyatar ke cigaba da haska hannayensa da suka tsaya cak.

Idan har za a jera shi tare da wadancan samarin, to watakila zasu kira kalmar uba da  'Home' gida inda zuciya take. Shi kuma zai ce 'Rauni' wanda baya barin ɗan adam ya iya tabuka komai a rayuwa.

Tarin tunaninkan da suka dauke shi daɗewa a tiyatar kenan har sai da Matron Nafisa tayi karfin halin kiran sunansa ta dawo dashi duniyar zahiri tukunna ya samu ya karasa komai da nauyin zuciyar da bai bari ya yi sauri ba ko kadan.

Don haka bayan komai ya kammala an fita da mutumin, yana samun hanya kai tsaye ya taho ofishinsa inda yake babu nisa da dakin tiyatar kansa cunkus da tunani kuma watakila abinda yasa ya manta kenan bai kulle kofar ba har wannan yarinyar ta shigo bayan ya shiga wankan da yake ƙaidarsa a duk lokacin da ya gama tiyata.

Kuma idan bai manta ba itace yarinyar da ya gani dazu da safe, duk da bai ga fuskarta ba amma kayan jikinta sune wadanda ya gani, ya tsaya da goge jikinsa da karamin tawul ɗin dake hannunsa sannan ya kalli jikin nasa, sai kuma ya juya ya sake kallon kofar da ya tabbatar ya rufe yanzu, lokacin da ya fito ya ganta shi kansa sai da yaji wani abu ya motsa a ƙirjinsa, don bai taba tunanin zai fito yaga kowa ba musanman kuma mace, sannan baya tunanin ma a duniya bayan Ahmad da kuma mahaifiyar sa wani ya taba ganinsa a haka.

Ya sake kallon jikin nasa a karo na biyu yana wani tunani sai kuma kansa ya bashi ba lallai ne ma ya kara ganin yarinyar ba don haka kawai ya ajiye tawul din sannan ya matsa inda ya kayansa suke don ya mayar dasu.

A lokacin ne kuma kiran Muhammad ya sake shigowa wayarsa, yana sa rigar yana kallon yadda vibration din kiran ke sa wayar motsawa akan table dinsa.

Allah ya sani bai san har yau bai taba ganin mutumin da baya gajiya da godiya ta duk wata hanya da zai iya ba kamar Muhammad. Idonsa ya hango masa lokacin da ya fara saninsa.

A lokacin yana matakin farko na yin housemanship dinsa bayan ya kammala karatu.

Akan hanyarsa ta komawa daga asibitin zuwa student lodge din da yake kwana ne anan ya hadu da Muhammad, yana siyar da biredin da yake tsayawa ya siya a wajensa kullum har sabo ya shiga tsakaninsu, wani abu da shi kansa ya bashi mamaki a lokacin yana kan ganiyarsa ta ƙin mu'amala da mutane da kuma yin nesa da duk wanda zai nemi matsowa jikinsa.

A sabon da suka yi ne ya san labarinsa na shekaru shidan da ya shafe yana neman admission a makarantar koyar da horon aikin ɗan sanda (POLAC) tsananin son zama ɗan sandan ya hana shi neman admission a koina ya gwammace duk shekara ya yi ta gwadawa, kuma duk da ba wai faduwa yake ba amma yanayin ƙasar da yadda komai ya komai sai mai hanya yasa baya samu a kowacce shekara.

Don haka yake sana'ar sayar da biredin da daddare da rana kuma ya buga iskar tayar mota don rufawa kansa da gidansu asiri, tunda shine namiji babba kuma yana da ƙanne uku mata mahaifinsu ya rasu.

Kwatsam a wannan lokacin sai aka kawo Commandat (shugaban) makarantar POLAC din ta wani reshe AIG Ibrahim .I. Sada asibitinsu da zummar za'ayi masa tiyatar zuciya, Aliyu bai gama fita daga matakin ɗalibi ba a lokacin, amma dashi akayi wannan tiyatar kuma ya taimaka kwarai komai ya tafi daidai, bayan nan ma kusan shi likitocin suka dora alhakin kula da mutumin hakan yasa a tsayin sati uku da ya yi a asibitin ya saba sosai da shi har ma da ƴaƴansa, sabon da Aliyu ya tursasa kansa wajen yi dole da mutanen ba don komai ba sai don Muhammad.

Sai don alfarmar da yake son ya samowa Muhammad tare dashi, alfarmar da ya zauna a gaban AIG ya roke shi da duk irin kalaman rokon da ya san zai iya tattarowa a bakinsa, kuma sai Allah ya karbi addu'arsa, a ranar AIG yace yaje yazo da abokinsa da kuma takardunsa.

Ya tafi ya taho da Muhammad, AIG ya karbi takardunsa da hannunsa sannan yayi masa albishir din samun admission a wannan shekarar. Kuma shekarar bata rufa ba Muhammad ya buga ƙofar ba mkk da sanyin safiya idanunsa ɗauke da hawayen dake shaida masa cewar mafarkinsa ya tabbata.

A haka rayuwa ta gangaro dasu yau... Muhammad ya gama Polac har anyi posting dinsa aiki a can garin Kebbiinda yake dawowa gida Kadunan a duk lokacin da ya sami hutu, kuma har yau baya taɓa barin wata damar da zata sa ya dainyia tuna masa cewar 'Ya gode.'

***

Aysha Shafiee.

©Raina.