Raina!

Chapter 6

by @ayshashafiee01

06

~ * * ~

And suddenly, you know… it’s time to start something new and trust the magic of beginnings.-Aliyu.

***

"Ya Farida tace wai tana ta kiranki baki dauka ba."

Ukthi ta fada idonta akan Tv tana kai lomar abinci bakinta.

Ƙarfe uku ne na rana a lokacin, Ukthin bata dade da dawowa daga makaranta ba, iya ma kuma bata dade da dawowa daga asibitin nan ba, kuma tun da ta ajiye kayan da ta shigo dasu akan kujera, kawai ta yi daki ta cire kayan jikinta ta shiga wanka.

Bayan ta fito kuma da ta buda wardrobe dinta ta shiga kallon kayan dake ciki sai taji duk abinda tasa kawai karawa zaiyi akan nauyi da take ji a ƙirjinta don haka a can kasa ta lalubo wata kamison kawai ta saka sannan ta saka wata farar hular ukthi mai raga-raga sabida gashinta da ta jika ya bushe kafin ta zura hijabi tayi sallah.

Tana fitowa kuwa Gwaggo ta fara fadan taje ta canja wannan rigar don ta zauna a jikinta sosai tana fadin bata san waye zai shigo ba, amma da ta fara bata labarin asibitin da tadda yake da ma yadda aka karbi takardar aka dauke ta sai hankalinta ya dauke ta shiga mata tambayoyi da kuma jin dadin cewa komai ya tafi daidai.

A haka Ukthi ta dawo ta same su kuma bayan itama ta tambayi yadda akayi, ko uniform bata cire ba ta zubo abinci daga flask din da Iya Nana ta shigo dashi sannan ta kunna Tv ta fara kallon wani korean drama da ta saka a flash a jikin tvn, irin fina-finan da bata gajiya da kallonsu.

Kuma tana kallon ne take fada mata sakon Faridar (ƴar gidan Kawu Babba) don a makarantarsu take service dinta don haka suna haduwa kullum.

"Wallahi na gani, duk sanda take kira wayar tana cikin jaka, sai nake cewa idan na dawo gida kawai zan kira ta."

"Ki kira ta kuwa, naga alama jikinta na rawa wani abu take son ta gaya miki."

Ukthin ta fada tana murmushi, Safina ta kalle ta sai kawai ta girgiza kanta tace.

"Allah ya shirye ki."

Gwaggo ta kalle ta tace.

"Ke ba za ki ci abincin ba? Ko kin manta da sassafen ma ba abinda kika sa a cikin ki ne?"

Ta girgiza kanta.

"Gwaggo na ci wasu snacks acan, idan anyi la'asar sai naci abincin."

Ta fada tana hango tarin kayan ciye-ciyen da Nabila ta dinga zarowa daga jakarta a gabanta tare da yi mata magiyar cewa kar ta ji kunyarta taci duk abinda taje so.

Nabila. Nurse din da Matron Nafisa ta hada ta da ita, matashiya ce kamar ita don a yau kadai da suka hadu har shekarun haihuwar ta ta gaya mata sai da taga cewar shekara daya ma aka haife su tare.

Mace ce mai tsananin surutu, surutu irin wanda zata ce bata taba haduwa da mai irinsa ba ma, surutun da zai sa dole ne ma a minti goman farko da ka hadu da ita kaji cewar kun saba, balle ita da suka fi kusan awa guda tare a yau kadai ji take kamar ta dade da saninta ne, don duk labarikan da ta bawa Gwaggo ma bayan dawowarta rabi a bakin Nabilan taji, idan ta fadi abu har Gwaggon sai ta tambaye ta, wai duk ita Nabilan ce ta gaya miki?

To iya abinda ta fadawa Gwaggo kenan ma kawai, amma tarin bayanan da Nabilan ta gaya mata kusan game da kowa da kuma komai na asibitin ita kanta ta san in zata shekara a wajen nan ita kadai ba lallai ta sansu ba, duk wani bayani game da program din da zasu yi kuwa harma da yanayin aikin nata da ta dinga jaddada mata cewar ta godewa Allah ba karamar sa'a tayi ba na samun aikin, musamman ma da zata yi aiki da Dr. Aliyu, don wai mutane da yawa na son zuwa kusa dashi.

Saboda tun zuwansa asibitin ba wanda ya san komai game dashi, baya zuwa meeting, baya mu'amala da kowa, baya ganin patients, Surgery kadai yake yi a asibitin nan kuma shi ma sai an kammala komai yadda yana zuwa kawai zaiyi aikin ne ya fita, amma duk da haka shine babban likitan tiyata a asibitin, kuma lokacin da ake ganinsa kawai shine idan yazo da safe zai shiga office dinsa ko kuma idan zai tafi tiyata ko idan zai fita.

Mutanen da zasu ce wata mu'amala ta hada su dashi a asibitin nan nasu da yawa, don ance ko masallacin cikin asibitin yaje yana idar da sallah zai fita ne, amma suna mutukar shiri da Proffessor mai asibitin kuma ko bayan da ya zama dilar kara kafuwar asibitin ma a bangaren tiyata kowa ya san yana ji dashi sosai... Don duk dokar da za'a sa a asibitin nan to banda Dr. Aliyu, kowa ya sani... Saboda shi baya ma sanin an faɗe ta balle har ya yi kokarin bi.

Shi yasa ko da aka kawo program din nan kowa ya yi mamaki da yaga sunansa a matsayin lead consultant din... Abinda ya dada sa sunan program din ma ya shahara a asibitin kenan ana so a ga yadda mutmin da baya ko normal consultation zai yi mu'amala da patients na tsawon watanni. Nurses da yawa suka dinga cizon yatsar dana sanin da basu yi applying ba, don lokacin da aka kawo abin kowa kin yi ya yi da cewar aiki ya masa yawa.

Amma tun daga lokacin da su Nabilan da aka dauka aka turo musu appointment letter din tare da lissafin maƙudan kudaden da za'a dinga biyansu duk wata,  Nabilar bata san adadin mutanen da suka dinga cizon yatsa har ma da masu nuna hassada kiri-kiri... Sai kuma aka zo aka ga kuma wai Dr.Aliyu ne zai jagoranci abin. Nabila tace mata akwai wata Nurse da har kudi tace zata kara mata akan albashin da za'a dinga akan ta bar mata aikin saboda Dr. Aliyun kawai.

Tace mata wai da shi da wani Dr. Khamis suna burge kusan duka matan asibitin, kawai banbancin shi Dr. Khamis yana da faran-faran da kula mutane akan Dr. Aliyun.

"Bari in gaya miki ba wai ma'aikata Nurse da lokitoci ba ba har patient, patient in dai sun saba zuwa asibitin nan to wucewa kadai idan yazo zaiyi haka zaki ga idanun mataaa na binsa da kallo kowacce da tunaninta."

Abinda ya bata dariya lokacin da tana faɗa shine yadda taja kalmar mataaan nan tana jaddadawa don ta fahimci abinda take nufi, wanda ita duk a bayanin nata abu daya kawai ta hango shine idan har baya son mutane har haka to kenan aiki dashi ba karamin sauki zai mata ba, don ba zai takura mata ba da komai iya abinda zata yi kawai shi zai zama a tsakaninsu komai yazo mata da sauki.

Kuma bata yi mamakin komai ba don a a iya kiran wayar nan kaɗai da akayi masa itama ta fahimci ɗabiunsa sunyi daban da irin na mutanen da zaka sani yau da gobe.

Don haka shiru kawai tayi tana ta sauraren ta, tana yi tana fito da kayan cima kala-kala daga jakarta tana mata magiyar itama ta ci... Haka dole ba yadda zata yi ta dauki wasu abubuwan ta ci, dafa nan ta tafi bata labarin cewa ai ciki ne da ita, shi ya sa take cin abinci akai-akai.

Tana tuna yadda ta dan zare ido da mamaki don ko kadan bata yi mata kama da matar aure, sai ta kara mata bayanin cewar watanni uku kenan da bikin nata, ta dauko wayarta kuma ma ta shiga nuna mata hotunan bikin da bayanin dukkan abinda ya faru a lokacin bikin, har aka gangara ma kan haduwarta da mijin nata Mukhtar.

Don haka a lokacin da ta dawo gida ba taraddadin asibitin nan ne a ranta ba... Labaran Nabila da muryarta ne kawai ke yawo a cikin kanta suna juyawa shi yasa da ta tashi wankan ma ta zuba ruwa har kanta ko zata ji jikinta ya dawo mata daidai yadda ta san shi.

Sallamar Aunty Hajiyayye ta katse tunaninta, ta juyo ta kalli sanda take shigowa da kuma muryar Gwaggo na fadin.

"Ƙadiran liman yasha''u, yanzu Hajiyayye yaushe kika bar gidan nan da har kika sake dawowa..."

Fuskar Aunty Hajiyayyen kadai ta sa ta yin murmushin da bata shirya masa ba, don koyaushe cikin yinta suke da Gwaggon, ita bata son zaman gidanta in dai mijin ta yana can garin da yake aiki, ita kuma Gwaggo obtace bata son zaryar da take yi ta zauna a gidan mijinta shi yafi komai alheri su ma duk haka suka yi.

Ga gidan nata nisa me dashi sosai don kamar sun kusa barin gari ma, to idan ana hutu ne ma Ukthi take zuwa ta taya ta kwana ko kuma ita idan ta dan sami off-din wajen aiki sai taje ta kwanan mata tunda dukkaninsu baza su iya fitowa daga nan su je wajen aiki ko makaranta ba.

Kwanaki ma har labarin wata mata da aka kashe ita kadai a gidanta a kusa da unguwar tasu tazo tayi ta jaddawa Gwaggo duk don ta sami lasisin tahowa gidan duk sanda taga dama, kowa sai da ya haddace labarin nan kuwa a gidan nan.

Don haka daga muryar Gwaggon da kuma fuskar Aunty Hajiyayyen da ta gani kadai ta san abinda za'a yini ana yi a gidan, ai kuwa hakan ce ta faru don Aunty Hajiyayyen tazo da labarin cewa sun gama shawara da mijin nata za'a samo mata wani gida a kusa da unguwar tasu kawai Gwaggobkuma tace sam bata yarda ba, tana nesa ma ya aka kare balle ta dawo kusa ai kullum tana hanya kenan, tace in banda shahanci ma ta yaya zata bar gidan mijinta ta taho ya kama mata haya? Ukhthi tasa baki da cewar.

"Wallahi kuwa Aunty, sai kinje kawai ya karo aure ya saka matar a ciki ke kina nan baki sani ba..."

Haka suka sa ta a gaba wannan ya fada wannan ya karbe, duk suka rikita ta, ita babban abinda ya bata dariya ma shi ne yadda Aunty Hajiyayyen ta zauna tana sauraronsu har da Ukthin da in za'a matse ta ba wani abu ta sani ba banda surutun dake sa wa bakinta baya shiru.

Da wannan ta samu ta manta da komai, ta manta da duk hargitsin da ta sha da safe, taji ta koma yadda take, wannan Safinan da ba inda tafi wayo a duniya da ya wuce dakin Gwaggo.

Kuma sai da daddare ne lokacin da tazo kwanciya sannan komai ya sake dawo mata sani cewar dare ne kawai ya raba ta daga sake shirin fuskantar sabuwar rayuwar da ta fara, komai ɗin da ya hada har da abinda ko da wasa bakinta bai yi gigin fadawa kowa ba, shigar ta office din nan da kuma abinda ta gani.

Ta runtse idonta tana kara jawo bargon da suka lulluba ita da Ukthi da tuni tayi baccinta... A cikin duhun fatar idanun nata hoton da tayi tunanin ta goge ya haska tar tana ganinsa... Sanda ya fito yana kallonta da kuma ita dake kallon jikinsa da babu riga babu makamancinta.

Ya Allah! Kar kasa in kara haduwa dashi ma.

Bakinta ya furta a hankali, sai dai ba kowacce addu'a ce take kaiwa gejin da zata karbu ba.

***

"Kin gama komai?"

Nabila ta tambaya tana kallon Safinan dake tsaye a gabanta tana karasa rubutu a jikin jotter dake hannunta.

A yau da safe bayan ta iso asibitin, ta kuma hadu da Nabilan da ta wanke mata duk wasu ƴan sake-sake da t kwana dasu da surutanta, sai suka nufi office din Matron Nafisa inda suka tadda sauran Nurses din nun su uku maza, Matron Nafisan ta yi musu wani wani ɗan karamin meeting da ta kara yi musu dukkan wasu bayanan da zasu nema ne, sai kowa ya gabatar da kansa da kuma sunansa sannan da aikin da zaiyi.

Wannan ya taimaka sosai don kusan dukkan aikinsu yana da alaka ne da juna, musamman Safina bayan aikin da zata yi da wannan Dr. Aliyun dole zata bukaci samun wasu bayanai daga wajensu.

Daga nan sai suka tafi zuwa ɓangaren da aikin zai gudana, anan Safina taga ashe kusan bangare guda ne ma aka ware saboda wannan program din, akwai offices da wards kusan guda biyar da za'a dinga ajiye patients, amma guda biyu ne kawai da mutane daya mata guda uku, daya kuma maza guda biyar.

Ita kanta wai office guda aka bata, amma dai ba komai a ciki ance za'a kawo kayan daga baya, Nurse station din ne kawai da komai da komai na bukata a ciki kuma har guda biyu ne shi ma don haka sai du mata ita da Nabila da kuma sauran matan  da suke cleaners da su tuni sun fara aiki a wajen (Tunda patients din da aka ajiye suna bukatar masu kula dasu) zasu yi amfani da daya, mazan Nurses ɗin ma tare da sauran mazan ma'aikatan sai suka dauki ɗaya.

Offices din likitocin shi an sa musu dukkan wani abun amfani, da na Matron Nafisan ma duk da Safina ta kula ba lallai ne ma ta dinga zama ba. Sai dai duk abinda ya faru kawai a dinga mata reporting.

Duk wannan abin anyi shi ne a cikin ɗan ƙanƙanin lokaci don bayan da aka gama komai suka koma ita da Nabila wards ɗin ta dauki report din mara sa lafiyan kamar yadda ta gani a aikinta cewar zata dinga kaiwa Dr. Aliyun da yake shugaba a wajen bayanin progress ko matsalar kowanne mara lafiya a kowacce safiya sannan ta raka shi round su duba kowa ya kuma ba da umarnin da zata rubuta ta kaiwa Nabila da sauran Nurses din maza su yi.

Idan yafi karfinsu kuma sai ta dangana da likitocin nan biyu da ta fahimci kamar zasu zama plan B ne ga mara sa lafiyar a lokutan da Dr. Aliyun baya nan, don a duk abinda ta karanta kusan shi ne komai, shi yake da say akan komai na wajen hatta Matron Nafisa itama umarninsa zata dinga bi.

Yanzu kafin tafiyar matron Nafisa ta tabbatar mata da cewar zuwa karfe tara ya iso don haka da taimakon Nabila tayi saurin hada reports na kowanne patient da iya abinda suka ga yayi daidai akalla a fara dashindaga farko.

Kuma da taimakon Nabilan ta samu ta rubuta abinda ƙwaƙwalwarta ke ganin ya yi daidai suka kammala.

"Me kika ce ma a Bed 3 kafin sign of depression?" Ta tambaya ba tare da ta dago daga rubutun da take ba.

Nabila ta gutsiri waffer da take ci a hannunta sannan tace.

"Post-amputation recovery..."

"Post-amputation recovery..."

Ta maimaita tana rubutawa sannan ta dago, har a lokacin dai idanunta na kan takardar.

"Ina ga na gama komai, so far dai iya abinda za'a samu daga patients din nan kenan."

Nabila ta ƙara gyara zamanta akan table din da take zaune tace.

"Kin kammala komai, sai reporting kawai, fatan Allah ya baki sa'a, ni dai na gaya kiyi abinda ya kai ki kawai ki taho, don ba wai na san shi bane amma wannan Dr Aliyun na san ba zai so wasa ba duk da dai kema na ga alama zaki yi aikin ki."

Sai ta juyo ta kalle ta tayi murmushi tace.

"insha'Allah, wanne ne ma akace office dinsa?"

"Shine na farko daga dama zaki ganshi babu suna, haka wancan office din nasa ma yake, ance wai baya son sunansa ne a rubuce kwata-kwata. Ko duk ƙin mutanen nasa ne yasa baya son ana wucewa ana karanta sunansa oho."

Fahimtar da Safina ta yiwa maganarta a lokacin daban da wadda zata zo tayi mata a gaba, ta tattara papers din da tayi rubutu a cikinsu da wata jotter kuma tare da wayarta da ID card dinta da bata rataya ba da kuma bironta sannan ta yi mata sallamar zata je ta dawo.

Tana zuwa kuwa ta kalli kofar ofishin sannan ta sake rike kayan hannunta ta matsa ta kwankwasa sau daya, biyu...

A lokaci guda kafin ta kai hannunta da niyyar yin na uku kawai taji ƙarar takun mutane daga bayanta suna tahowa sannan muryar Matron Nafisa na faɗin.

"Yawwa gata nan ma ta iso, dama I was about to call her yanzu."

Don haka kai tsaye kawai ta juya abinta, sai dai me? Bayan fuskar Matron Nafisan da kuma wani namji dake sanye da kayan cleaners, abinda ta gani ya girgiza duniyar tunaninta gabadaya kaf! Ya watso da komai kasa, taji ƙarar tarwatsewarsu a kunnenta kamar faduwar farantan silba akan tiles...

Wannan mutumin ne na jiya...

Wanda ta kwana tana fatan kar Allah ya sake hada ta dashi a wajen nan...

Tsaya!? Shine Dr. Aliyun?! Inalillahi wainna ilaihir rajiun!

Hannayenta suka shiga rawa a lokaci guda, zuciyarta ta shiga bugawar da ta saba, taji zata iya bada ko ma mene idan wani zai iya ɓatar da ita daga wannan wajen a lokacin... Fata kawai take yi wani abu ya faru, wani abu ko ma menene da zai sa baza su ƙaraso su same ta ba, amma fatanta bai karɓu don bata ma san me take yi ba har suka ƙaraso din,  Matron Nafisa ta kalle ta ta shiga gabatar mata dashi a matsayin Dr. Aliyun da hankalinta ya riga ta wajen sauke mata albishir ɗin.

Sai kawai ta damƙe takardun hannunta tana sauraren ta, ta kasa dago kanta ma balle ta kallu daya daga cikinsu, gyada kanta kawai take alamun ta fahimta, yayin da wannan cleaner din ke bude kofar ofishin da mukulli a hannunsa.

A ƙasan idanun nata taga giftawar mutum biyu alamun duk sun shiga ciki kafin ta hadiye wani abu a makogwaron ta motsa kafafunta itama ta bi bayansu.

A cikin office ɗin komai kanshin sabunta yake, sannan koina ɗas! An goge an share, sai da taji ƙarar wani abu sannan ta dago idonta, taga wannan cleaner din ne yake dage blinds din daje jikin windo haske yana shigowa, daga gefe inda wasu cushion chairs suke kuma Matron Nafisan ce tare dashi tana masa bayanin wani abu da saurarenta kawai yake yi yana gyada kai alamun fahimta. Fuskarsa a tsaye kyam! Kai baka isa ka tsinto wani yanayi guda daya a ciki ba.

Wani abu ya sake wcewa ta makogwaronta ya tsaya ƙyam! A kirjinta har lokacin da cleaner ya gama aikinsa ya fita sannan Matron Nafisan ta taso itama tace mata idan ta koma ta gayawa Nabila tana nemanta sannan ta fita.

"Safina..."

Tamkar saukar irin ruwan saman nan dake tahowa a lokaci guda haka taji muryarsa ta cika office din, abinda bata yi zato ba, bata yi tsammani ba.

Wani abu ya yi rawa a ƙirjinta kafin tayi ƙarfin halin dago da idonta ta kalle shi. Sai taga kamar ya kara kwarjini da yake zaune shi kadai babu Matron Nafisan a kusa dashi, kuma da yake yanzu ita yake kallo ma, idanunsa a tsaye suke a kanta hannunsa na dama rike da robar ruwan da ta tabbata taji ƙara lokacin da ya ɓalle murfinta bayan fitar Matron Nafisan, yayin da na hagun kuma yana daga bayan kansa kamar ya tallafo wuyansa don har kan nasa ya karkata kadan.

Idanunsa tar akanta, muryarsa tar a cikin iskar office din tana fitowa da wani accent da yasa taji kafafuwanta sunyi lugub kamar dafaffiyar taliyar hausa, yace

"Are you ready?" (Kin shirya?)

**

Assalamu alaikum jama'a, are you ready too? Kun shirya?

Kun shirya jin labarin Aliyu da Safina?

Kun shirya bani damar da zan sanyaya tunaninku da wata soyayya mai sanyi da dadin da zata ɗan kakkabe zuciyoyinku?

Dan Allah kuce kun shirya, ku bani ragamar da zan ɗan dauke ku daga wannan duniyar tamu mu dan manta da matsalolin dake gabanmu...

I promise you a love story so unique, it’ll leave you smiling, humming, and completely captivated insha'Allah.

Raina 1000  Naira ne a telegram!

Idan kuma kun fi son ku karanta a Arewabooks then zaku biya kudin kowacce chapter idan anyi update.

A yanzu haka mun zo karshen free pages... Kuma labarin zai cigaba ranar talata insha'Allahu.

Update zai dinga zuwa duk bayan kwana daya insha'Allah in dai ba da wani kwakwaran uzuri ba.

Zaku iya fara biya ta wannan asusun

8067794315

Opay

Aisha Mahmoud Shafii.

Sai ku kara 0 a number opay din ku turo da shaidar biyanku.

Nagode da lokacin ku.

Nagode da fahimtarku

Nagode da kaunar da kuke wa rubutuna

Na kuma gode da tarin addu'oin da kuka yiwa mijina. Allah ya amsa mana baki daya. Allah ya kyautata namu zuwa Ameen!

Aysha shafiee.

©Raina.