JIRWAYE

CHAPTER 5

by @deejasmah

JIRWAYE

Khadeejah Bint Ismail

Young talented writers association (YOTAWA)

CHAPTER 5

Daren ranar dai ba ta wani yi bacci mai daɗi ba, ranta da rayuwar ta a hautsine suke ga na ɓacin rai don duk wani abu da TeeTeen take mata bai ƙona mata rai kamar yanda na ranar yayi mata, tambayar kanta take yi tana ƙarawa me tayi mata da zafi har haka ne amma ta rasa amsar hakan. Hakan ya sa ta ɗauki system ɗin ta ta fara aiki don dama tana da pending ayyukan da bata yi ba musamman wanda aka bata akan binciken wanda yayi encoding saƙon da ta warware, binciken ta fara sai dai ta rasa gano bakin zaren don komai na shi a dabaibaye yake da tayi nisa kuma a binciken ne sai yayi diverting ɗin ta tayi hitting bug. Tsaki tayi tana jin frustration ɗin ta na ƙaruwa da yake itama akwai defence mai tsauri a system ɗin sai bai taɓa system ɗin ta ba ta cigaba da binciken yanzu kam ta samu kusan location fin goma na shi Windheok, Washington, Atlanta, New York New Zealand da ma wasu locations ɗin duk dai a yankin America. In ta fahimta dai-dai kamar mutane da yawa suka haɗu suka yi aikin in that case za ayi saurin kama su don ba lallai dukan su suna da tsaro mai ƙarfi ba, da mai raunin kuma za'a yi amfani wajen tarwatsa taron na su. And in that case dole su nemi taimakon CBI don su ke da alhakin kula da yankin na America ba su ba tattare duk abinda ta samu tayi ta turawa DIA ɗin sai lokacin ta iya yin bacci feeling a bit satisfied ta kuma nemi damuwar TeeTee ta ajiye gefe.

The following day ba ta tashi da wuri ba don bata da class Friday, Mufee ce ta tafi ita ko sai after 11 shi ma ɗan anacen nata ne ya kira ta yana shaida mata zai zo dole ta tashi ta tarar Mufee ta musu ɗanwake brush ta yi ta ɗaura ruwan wanka kana ta zauna yin breakfast tana yi tana kallon time. Wanka ta samu ta yi da yake ba mai ƙyale-ƙyalen shiri ba ne sai ga shi cikin ƙanƙanin lokaci ta shirya cikin wani dull green gown irin mai dus ɗin nan, gashinta ta sanyawa hula baƙa ta ɗauki jersey veil grey ta yane kan ta and as usual crocs ɗin ta ta sanya sanda ya kira ya shaida mata yana ƙofar hostel ɗin su.

Tsayawa tayi a windown ɗakin su ta hango motar shi parke, ajiyar zuciya ta sauke tana sauka ƙasa. Kamar kullum yau ma ƙureta yayi da idanu har ta ƙaraso, fuskar nan tata kamar kullum ba ko murmushi shi ko kamar gonar auduga.

Kallo ta masa tsaf yana sanye da kaftan milk colorn da yayi contrasting skin colorn shi da ke nan chocolate, baƙaƙen takalma ya sanya da wristwatch na fata ƙirar kamfanin Graff bai sa hula ba sai gashin shi da ke ƙyallin man da aka gyara shi da shi. Sallama ta masa daga ƙarasowa ya amsa kamar zai lashe ta yana cewa '' kyakkyawata''.

Idanu ta yi rolling tana cewa '' Doctor'' murmushin shi ya faɗaɗa don yana jin daɗin in ta kira shi da hakan cos it means ƴan soyayyan suna kusa.

''My Lady ''.

''Ya aiki? Ya kake?".

''Ina lafiya and aiki is always the same nothing new I'm just missing you ''.

''And here you are ka zo gani na ''.

''Yeah I'll be more fine Mine, ya hutu ya kyau oops I know that kin yi aiki right?" Ya tambaya da kulawa don ta faɗa masa zata yi aiki jiya da dare. Da kai ta amsa masa tana cewa '' ku ne ai masu kyau''.

''Da gaske na yi kyau Baby?" Ya tambaya a zaƙe kamar zai shiɗe saboda murna, yanda yayin sai ya sakata yin murmushi kawai ba tare da ta ce masa komai ba. Shi ma murmushin ya saki yana cewa '' ba ki amsa ba fa na kuma ce ya kike?".

''Toh I'm good and yes you look good happy?".

Kafin ya kai ga bada amsa kiran Amah ya shigo wayarta ɗagawa tayi tana excusing kanta matsawa tayi gefe tana cewa '' ina kwana Amahna''.

''Lafiya lau baby, kina lafiya? Yau ba ki kira ba''.

''Ina lafiya Amah, I'm sorry ban tashi da wuri ba ne that's why yanzu nake maganar kiranki''.

''Ayyah my baby, I thought something happened ne''.

''Ba abinda ya faru, ya gida and Affah?".

''Yana lafiya ya tafi Zaria for a wedding, you can call him later I'm sure yanzu ya na hanya ma''.

''Alright I'll in shaa Allah''.

''Ba ri in bar ki baby will call you later okay? And don't forget to call your sister I love you ''.

''I love you more Amah ''.

Ta amsa tana mai lumshe idanu, tana kashewa dawowa tayi gaban shi tana cewa '' sorry''.

''It's okay, was it Mommy?".

''Yea it was her''.

''Tana lafiya ko? Even though kin ki kai ni in gaisheta''.

''I'd in shaa Allah but it'll have to be after my exams''.

''Ohh yeah Allah ya kai mu, when is the exams?".

''In the next 2 weeks ''.

''Alright Allah ya bada sa'a, now where do we go?".

''Ba ko'ina, I'm just out because of you''.

''Well, let's go somewhere ban yi breakfast ba''.

Kallon shi ta tsaya tana yi wai bai yi breakfast ba, toh ita ina ruwan ta da ƙin yin breakfast ɗin shi. Kawar da fuska tayi gefe alamun she's not going shi ma ya san halin kayan shi, sai kuma yaji tace '' let's go to ploutous''.

''Alright then''.

Ya ƙarashe yana buɗe mata ƙofar motar shiga tayi ya ja suka bar wajen, kamar yanda tayi suggesting can suka tafi menun ya duba yana tambayarta abinda take so cewa tayi she's okay sai da yayi insisting kafin tace a bata coffee kawai don da gaske take she's full ta ci abinci ta ma rage ragowa a ɗaki, sawa yayi su kawo mata har da meat pie sanda aka kawo kuwa sai da ya tuna mata da TeeTee don ita ce ke masifar ƙaunar pie amma ba ta ko kira ta ba don abinda ta aikata mata sosai ya zafe ta. Ko da ya gama ɗaukan ta yayi suka koma school bai kuma jima ba ya tafi saboda masallaci amma ya shaida mata kar ta tafi Almara hub inda za'a yi founders Friday ɗin ta bari zai zo ya kaita don yau off yake, ce masa tayi ya bar shi kawai in ya so sai ya dawo da ita.

Around 3:30 ta wuce don 4 ne panel session ɗin na su ba ta ko canja kaya ba don ita a ganinta tayi ba sai ta canjan ba, har kuma lokacin Mufee ba ta dawo ba sun dai yi magana akan sai ta dawo za su tafi dinnern.

Magrib ta dawo hostel ba ma shi ya dawo da ita ba saboda yana masallaci time ɗin, ta samu har Mufee ta shirya makeup take yi. Gaisawa kawai suka yi ta wuce toilet wanka ta yi ta fito a gaggauce ta shafa cream, buɗe akwatin ta tayi tana neman kayan sakawa. Mufee da ke bayan ta tace '' ki saka wancan pls'' ta furta tana nuna mata wata rigar lace mara nauyi da akawa ɗinkin A line, a kaf laces ɗin ta ita ɗaya ce ba Boubou ba duk da dai colorn sai a hankali don Maroon ne da yarfin ash da pink a ciki amma bai da hayaniyar zane don ita ba ta son ƙyale-ƙyale.

Tura baki tayi don ita ba ta son sakawa tace '' wai da fa atampa zan saka''.

''Abeg don't, ki saka wannan Please''.

Ba don ta so ba haka nan ta zaro shi da gyalen da take haɗawa da shi silver color, jakarta ta jiya ta ɗauka tana saka kayanta ciki. Shiryawa tayi duk ko da rashin kyau da haɗuwar colorn amma ya mata kyau sosai, ya fito da skin colorn ta hakaza ɗinƙin da aka masa ya ɗan fito da jikinta. Cukurkuɗa ɗankwalin kayan tayi iya yanda zata iya duk ko yanda Mufee ta so gyara mata cewa tayi ta bar shi ita dai ɗaurinta yayi kyau, toh ba ma ce bai yi ba don irin dai ɗaurin ƴan gayun nan ne amma bai yi kalar zuwa wajen biki kamar dinner ba.

Ta dai samu ta saka flat shoe instead of Crocs ɗin da tayi niyya, tana gamawa suka fita don already yana waje yana jiransu. Yau ma jarumar ta shi ta masa kyau ainun, bai kuma ɓoye ba sai da ya gaya mata ita dai ɗan murmushi tayi tana kawar da kanta ga wayarta inda take replying wani message na client ɗin da zatawa web design.

A dome suites ake yin dinnern sanda suka iso ko har wuri ya cika da mutane, Mufee ne ta fita ta nemi Aunty Mamin ta amso musu pass ɗin su har da na Rhidwan don yace ba zai tafi ya barta da kurayen Kaduna a wurin ba esp yanda tayi kyan nan. Rolling idanunta tayi kawai Mufeen ta ƙara fita tana dariya don tana son rigimar ta shi ainun, don da ba don shi ɗin rigimammen gaske ba ne da sun daɗe da rabuwa da Adeeyah nacin shi ne ya sama masa matsayi mai yawa a wurin ta.

Zuwa can sai ga ta ta dawo da pass ɗin na shi ba shi tayi yace '' ko ku fa? Haka kawai in tafi in bar matata a nan wurin?".

''Ai ka san matar taka ba kula su zata yi ba, ba sa gabanta'' Mufee ta furta tana mai ƙoƙarin danne dariyarta don ta san Deeyahn ta shaƙa sosai, murmushi yayi yana cewa '' na yarda da ita kam, amma ban yarda da mazan wurin nan da sunga mace mai kyau sai sun bi ''.

''Tunda ba wanda suke jira sai ni ko?" Ta tambaya tana harararsu su biyu, cewa yayi '' isn't it obvious? Ni dai ƙafata ƙafar iyalina gwara duk duniya su san she's mine, yes you're mine''.

''Awnnnn I love this, god when'' faɗin Mufee cikeda nishaɗi don har ga Allah tana son kalar son da yake wa Pookien nata fiye da tunani ko ba don komai ba sai don yanda take ɗin ko ba ta faɗi ba ta san she's going through a lot akwai banbanci mai yawa tsakanin ta da ƴar uwar haihuwarta, duk da ta san har da yanda abun duniya bai dame ta ba amma abun yayi yawa. Ƙaramin misali shi ne ita Teeyah tana da mota Porsche mai mugun kyau baƙa ita kuma ko da Honda ba ta taɓa ganin ta ba, ta gefen waya ma iPhone 14 ce a hannunta ita kuma Samsung ce amma A series ce flip ta wannan gefen kam an ɗan yi adalci don wayar almost 800k take bayan nan kam a sutura ma akwai banbanci though ba fashion sense ɗin su ɗaya ba ko school ma haka tun daga secondary suke makarantu daban har zuwa yanzu da suke jami'a komai na TeeTee yana saman na DeeDee. ( Iya wanda kika sani ma kenan).

Sai kusan 8 aka fara shiga hall ɗin suma bin ayari suka yi suka shiga, a front table na tsakiya suka zauna. Duk abinda ake yi suna gani babu distraction tun daga kan shigowar amarya har da friends ɗin ta, inda kamar jiyan yau ma dai Hajiya TeeTee tana cikin tawagar ƙawaye. Mufee da ke gefen ta ne tace '' ga fa Teeyah Manya''.

Murmushi ta ɗan yi ba tare da tace komai ba don ko jiya ba ta gaya mata me ya faru ba, Rhid ne ya kalleta ya na cewa '' twin sistern ki ko?".

Kai ta gyaɗa tana cewa '' yeah ka ganeta ashe?".

''Ya ba zan ganeta ba? You look more alike though you are not identical''.

''Wa su fa suna cewa ba da bambance mu''.

''Something is quite wrong with their eyes, kuma kama ko makaho ya san haka but not that alike to the extent that ba za'a gane ku ba''.

''Uhmm'' ta furta tana kawar da kanta.

Teeyah da ta ganta ta zaci zata zo inda take sai dai har aka ci aka ƙare ba ta ko zo inda take ba, infact ko gefen ta ba ta kalla ba tun bayan maganar su da Rhid wanda ya zaci zata je wurin sistern nata but da bata je ba ko kusa bai yi judging ɗin ta ba though abun ya ba shi mamaki ainun amma a ran shi yana mamakin rashin shaƙuwarsu bai dai zurfafa ba.

Ko ita ko sai da tayi mamakin rashin ganin tan sai ta bar shi a ƙila sai an tashi zata zo amma ga mamakinta har aka ci aka cinye DeeDeen ba ta ko nuna ta santa ba, hakan ko ya matuƙar taɓa ta a ƙasan rai take ta kumfan bala'i faɗi take tana kumawa cewa wulaƙanci ne take shirin mata ba komai ba ta nunawa duniya ba ta da daraja ko mutunci a wajen ta. Sai dai ba zata bar hakan ya yi nisa ba sanda aka fito waje sai ga ta ta biyota tana kiranta da sunan da ita ɗaya ce take da damar kiranta dashi wato '' DeeDee''.

Juyowa tayi ganinta sai ta faɗaɗa murmushin ta tana '' Tee''.

Ɗan murmushi ita ma tayi tana rungume ta tace '' my baby, ya kike ya school? ''.

Fine tace daga haka ba ta kuma cewa komai ba don ba su saba hira mai tsayi ba dama Deen ce gwanar jan hira yau kuma ba tayi niyya ba, ganin haka sai ta ɗan diririce ranta na kuma ɓaci ta saketa tana cewa Mufee '' hi''. Abinda ta faɗin ta maimaita tana ɗan murmushi juyawa kan Rhid tayi shi ma ta ɗan gaishe shi da fara'a shi ko ya amsa yana cewa '' ai da har zan yi fushi in ce ko dan twinnien mu ta gan ni ne ta ƙi zuwa wurin half ɗin ta'' duban Dee tayi tana cewa '' ko kusa na bari ne dama sai in tashi ban ma yi tunanin kai zaka kaisu ba da ni zan yi dropping ɗin su''.

Cewa yayi '' ai ko na hutasshe ki,ina zan iya barin matata a daren nan ta bi hanya ai ko ke ma in da ya yanda zan yi ba zan bar ki ki yi driving ba''.

''Ai ni ban jin dare, I'd drive by myself lemme just go bye'' ta ƙarashe tana juyawa, bin ta Dee tayi har zuwa wurin motar ta ba su wani yi hira ba sai cewa da tayi sai sun haɗu gobe a gida.

Daga haka ta dawo wurin Rhid ya ja suka wuce su ma..

Da alamu dai Deeyah an fara dawowa daga rakiyan Teeyah.

Is this a bad sign?.

Deejasmah 🎭