Chapter 47
by @khairatup01
Zuciyar Mutum.
khairat up.
Watppad:khairi_muhd.
Arewabooks:Khairatup01.
47.
*
Umma na zaune a falonta tana nazarin abubuwa da dama da suke yi mata yawo a kai. Wayar da aka bugo mata ita ce ta saka ta dawo cikin hayyacinta. Ɗaga kiran tayi da mamakin lambar wayar da aka kira ta da shi. Lambar babn Afeeya ne wanda ba waya suke yi ba m ta jima bata ji daga gare shi ba.
"Salamu ala...."
"Riƙe sallamar ki azzaluma. Ni za ki rufe a kan ƴata?."
"Kai Saminu ya aka yi ? Yau kuma da wacce ka zo? "
"Tambaya ta ma kike yi? Nace tambayata kike yi to ki buɗe wayar ki ,ki duba za ki ga abinda yake faruwa."
Kashe wayar yayi ba tare da yi mata wani gamsashen bayani ba. Duk ta rikici sa'i ɗaya. Me Affeya tayi har da shi ya samu labari ita bata samu labari ba? Da sauri ta kuma kiran layin Afeeya amma bata shiga kamar ma a kashe ake gaya mata. "Yau me Affey ta yi ni ƴa su?"
Tana hawa onlayin ta soma cin karo da saƙonin jaje daga wurin ƙawayen ta bata daina mamaki ba sai da ta ga wani bidiyo na yawo kamar Afeeya ta gani an saka mata ankwa ana nuna cewa ta kashe mutum. Ajiye wayar tayi tace "Ƙarya ne wannan ba Afeeya ba ce." Garin saukowa daga bene ta taɗe saboda ba ganin gabanta take yi sosai ba sai ga ta ta gangaro ƙasa tun da ga saman bene kanta ya bugu da ƙasa ya ko fashe ta suma a wurin.
Kaɗan kuka soma gani Umma.
*
Baffa na wurin aiki ya ji aikin da aka ce Afeeya ta aikata. Ya dinga nanata innallillahi a fili. Hularsa ya cire ya ajiye ya ɗauki wayarsa tana ruri ya duba ya ga daga can gida ne. Mami ce take gaya masa sun tafi asibiti Umma ta faɗo daga bene bata ma san waye a kan ta ba.
Dole babu yadda zai yi haka ya wuce asibitin da suka kwatanta masa.
Yau dai ga Umma duk izzar,duk wulaƙancin, duk iya shegen duk ikon babu halin yi ga ta nan a kwance sambal babu kyan gani ko kaɗan sai yau ya ga ma kamar an sauya masa kammaninta shi fa ya jima yana tambayar kansa yadda aka yi ya aure ta. Don sam ba tsarar sa bace sai daga baya da ya ji tana faɗin yadda aka yi Isa ya haɗa auren da irin asirce-asircen da suka dinga yi masa da matarsa da ɗansa tilo mafi soyuwa a gare shi. Yau ga ta nan ga halin da take ciki kaico ke duniya ina za ki damu? Wanda ya ɗauke ki da zafi ma ya sauke.
Mami tace "Ina ga ta ga abinda yake faruwa ne da Afeeya.Ni dai Baffansu na kasa yarda Afeeya ce ta yi kisa."
"Hmm Fatima kenan. Ki bar shaidar ɗan yau. Yarinyar nan da uwarta ba mutanen arziƙi ba ne."
"Duk da haka ka kyautata mata zato. Muje mu ji me ke faruwa a can."
"Aa uban ta ya je mata."
"Kayya Baffa ban san ka da haka ba.Ko ba komai ai kai ma uban ta ne. A gabanka fa ta girma a gidanka ta girma komai kai ne ka yi mata shi to yau kuma me yasa zaka janye."
"Don ke zan je."
"Na ji na gode muje."
*
A can reshen bincike kuwa an tarfa Afeeya sai kuka take yi tana rantsuwar bata yi komai ba. Amma ina doka da shaida take amfani ba gaskiyar ka ba.
"Yallaɓai ba ni na kashe ta ba. Ƙawata ce fa amimiyata ce. Ban ma san ta zo garin ba. "
"Me ya kai ki Otal ɗin?"
"Wurin saurayina na je. Saurayina Ashiru ne ya kira ni ya zuba mini magani a lemo na sha na fita daga hayyacina ya yi amfani da ni. Nima tashi na yi na gan ni cikin jini kuma ga Ife."
"An samu hoton yatsun ki a jikin wuƙar."
"Zan cire mata wuƙar ne sai kuka shigo."
"Babu wani mai suna Ashiru da ya zo Otal ɗin da kika sauka, da sunanki aka kama ɗakin ke ce ma kika kama ɗakin ba wani ba. Mun duba cctv camera ma duk babu kowa sai ke ƙadai. "
"Innallilahi wa inna illahir raj'un na shiga uku. Me kuke cewa Yallabai? Wallahi da Ashiru a ɗakin kuma ya yi amfani da ni a je ayi min medical check up."
"Za ayi duk za ayi. Amma ki sanar mana me yasa kika kashe ta?"
Hannu ta sa a sama ka tana kuka hadda majina ta ci gaba da koro jawabin bata san komai ba ita.
Tsawa ya daka mata haɗe da dukan kan teburin da ƙarfi sai da ta tsorata tayi baya da sauri tana kuka.
"Ki gaya mana gaskiya me yasa kika kashe ta?"
"Yallabai bakinsu ɗaya da me Otal ɗin da Ashiru bakinsu ɗaya. A duba kiran wayata za a ga kiran Ashiru da ya yi min a duba wayata ban yi waya da Ife ba a duba bani da...."
"Kar ki koya mana aikin mu. Wayar ki tana tare damu dama kuma za a duba ta tana can forensic ana duba ta."
Afeeya ta kwanta saman teburin tana jin wani irin ɗaci da tashin hankali na fizgarta. Wai yaya ake cewa ita ce tayi komai? Wai babu wani Ashiru da ya zo Otal ɗin ?
To dai mu ma muna son sanin ba'asi.
*
Duk yadda Baffa da Abban Afeeya suka so ganin ta ba a bar su ba. Ita Afeeyan ma zuwa yanzu ta daina cewa komai ta daina magana hawayen ma sun daina zuba kamar ta zare ko sun ƙare hawayen.
Ko da aka nuna mata reording da call records ɗin ta babu komai sai ta kama bakinta tayi shiru ta yarda kawai ta faɗa cikin wani irin tarko irin tarkon da babu mai wanke ta sai Allah. Bata son ganin kowa ma. Don bata san me zata ce da kowa ba? Bata da shaida r komai sai ma ita da dukanin wani shaida ya ke a kan ta.
Ko da ta ji labarin Ummanta na asibiti rai a hannun Allah kuka ta dinga yi tambayar kan ta tayi ko dai wannan ita ce ranar ƙin dillacin? Ko dai ta ce ranar da ake kira da ranar da na sani ? lallai shi bawa ba a bakin komai yake ba. Duk tsarinka da makircin ka da kitimurmurarka a rayuwa a cikin ƙiftawar ido kaɗai Allah zai nuna maka matsayin ka da ikon wanzuwar sa. Me yasa bata yi haƙuri ba? Shi ne tambayar da take yi wa kan ta gashi ita kanta bata da amasar tambayar lokaci ya ƙure mata... Wato ita zuciya babu abinda bata saƙawa bawa babu wanda ya san gaibu sai Allah kuma babu wanda ya san abinda ke cikin ran wani. Tabbas zuciyar mutum birninsa.
*
Da na ji abinda ya faru da Afeeya sai jikina ya ƙara yin sanyi da al'amarin duniya. Afeeyar da suka gama musayar yawu kwanakin baya, Afeeyar da ke son auren mijinta,Afeeyar me ji da rashin mutunci kala-kala? Lallai ka ji tsoron mutum ka ji tsoron Allah.
Duk wani ƙunci da take ji sai ta ji sa'i guda ya yaye mata ya wanke bata jin bacin rai kamar kwanakin baya. Cikinta ta shafa kawai.
Haidar da bai sanar musu da zuwansu ba kawai ta jiyo ƙamshin turaren sa a hancinta. A hankali ta ɗaga manyan idanuwanta ta sauke masa su a kan fuskar sa.
Sai taga ma ya ɗan ƙara mata kyau fatar sa sai ɗaukar mata ido take. Baƙinsa ya mata wani kalar kyau a ido. Basarwa tayi ta ɗauke masa kai.
Hannunsa daman a ƙirjinsa yana kallonta ko da kuskure bai ɗauke su daga kallonta ba. Da ya ankare da cikin jikinta baki ya buɗe ya isa kusa da ita da sauri ya sa hannu biyu ya ɗago ta sama.
Ta fizge hannun ta ya kuma riƙota ya ja ta. Tsayar da ita ya yi da kyau kafin ya tsugunna a gaban ta. Hannunsa ya saka yana shafa cikinta yana jin wani irin farinciki a ransa. Da gaske ne Ummu na ɗauke da juna biyu? Juna biyun ma nasa ne? Kiss ya kai wa cikin ya rungume ta a haka ya soma magana "Na godewa Allah! Na godewa Allah da ya azurtani da wannan ƙaruwar. Ummuna na gode miki da kika kula min da cikina ba tare da sani na ba. Duk da laifin da na yi miki ba ki ƙi jinina da ke kwance cikin ki ba. Wallahi ba zan iya baki haƙuri ba saboda ban san ma me zan ce miki don kare kaina ba. Amma ina son na miki alƙawarin ba zan sake yi miki irin haka ba. Nima ban san me yasa na yi haka ba amma ko ma meye ina mai baki haƙuri.Don Allah ki samu wani wuri a cikin zuciyar ki yafe min ki bani wani matsugunni a cikin zuciyar ki kamar da ko da ma bai kai irin na da ba."
Bana son na nuna masa na karaya amma dole sai na nuna masa cewa nima mace ce , ya kamata ya san me ake kira da hukuncin ƴa mace.
Hannu ta saka ta tunƙuɗa shi gefe.
Ta yi hanyar fita daga gidan ma.
Da sauri ya riƙo ta yace "Yau ni kika ture Ummuna?"
"Ban san me zan ce maka ba. Ban sani ba ko zan manta ba. Kai a wurinka bada haƙuri wani abu ne mai sauƙi wanda in an cuci mutum kawai a ce masa am sorry shi kenan ka daina jin raɗaɗi da zafin abinda aka yi makan aa ni ba haka nake ba ina da buƙatar lokaci na sani ma ko gaba ka yi min abinda ya fi wannan?"
"Ummu..." Ya isa Hamma
Ka san yadda na ji?
ka san yadda na ji lokacin da ka ƙaurace min haka kawai ba tare da na yi maka laifin komai ba?
Ka san yadda na ji lokacin da na san ina da ciki amma baka kusa da ni bare mu yi farincikin tare?
Ka san adadin dararen da na yi ba tare da cikakken bacci ba?
Idan zan soma lissafo maka ba, ba ,ba kai da kan ka kunyar kan ka za ka ji. So lets call it a day. Ina buƙatar lokaci nima.
Buɗe ƙofa tayi tayi ficewarta ba tare da ta kuma kallonsa ba.
Haidar bin bayan ta ya yi kawai da kallo kamar an dasa shi a tsaye. Har haka ya cusguna mata daman?