ZUCIYAR MUTUM

Chapter 48

by @khairatup01

Zuciyar Mutum.
khairat.
wattpad:Khairi_Muhd.
Arewabooks:Khairatup01.
48

*

Kun san dai mutumin naku Haidar dai Haidar ne. 

Da gudu ya bi bayanta har sai da ya kamo ta. Ɗaukarta yayi a hannuns a tana buge-bugen ƙafa amma bai sauke ta ba sai a ɗaki.

Ajiye ta yayi a kan gado ya ga iya gudun ruwanta. Ganin babu sarki sai Allah dole ta koma ta zauna ɗin don ita zata galaɓaita a banza da wofi. 

"Kin gama?" Ya tambaye ta hannu a saman ƙirjinsa.

"Tambayar ki nake yi kin gama yi min rashin kunyar ko akwai saura? In akwai saura ki ƙarasa yanzu kawai a wuce wurin don ni nan da kika gan ni ba zan ma ɗauki wani dogon fushi ba ana ci-cin magani ba ba zai yuwu ba. In ma duka za ki min zan ɗauko miki madoki ki daken son ranki amma babu maganar kina buƙatar space." 

"Saboda kai ne the grate Haidar? "

Kafaɗarsa ya ɗaga yace "Haka ne mana ai kin sani. Ni Haidar ai ba zan yarda da wannan shirmen ba. Haƙuri fa na baki ke an gaya miki akwai wanda na taɓa ba wa haƙuri a rayuwata bayan Mami da Baffan? Gaskiya so bai duba min ba."

"Ni ma ai bai duba min ba son tunda ya saka na ke son naka. Ni Wallahi Ya ROOH bai taɓa ɓata min rai ba , bai taɓa saka ni kuka ba , bai taɓa share ni ba. Ba ya iya zuwa wuri kwana babu ni an gaya maka ba don mutuwa da tayi gaggawa ba zan aure ka ne?" Ta faɗa ba tare da ta san tasirin zancen nata gare shi ba.

In ya ce bai ji kishi ba yayi ƙarya. Kuma hakan ya nuna a kan fuskar sa. Amma da ya tuna ai ba ƙarya tayi ba. Ba ma ita kaɗai ba Habib baya faɗa da kowa sai dai shi a cuce shi. Habib ne fa ake magana akan sa ai babu batun kishi. Ajiyar zuciya ya saki ya tsugunna a gabanta ya kamo hannunta ta wafce hannun tana "Ni ka ƙyale ni." 

"In kyale ki in yi rayuwa da wa? Ai shi ma Habib ɗin ya san ni ne kaɗai zan iya da ke shi yasa ya bani wasiyar na aure ki gashi ma an samo Habib in sha Allah!"

A cikin ranta kuwa tunani take yi wai shi wane irin mutum ne da baya fushi? Duk wani abu tayi don ta musguna mai amma ta kasa samun galaba.

Kin ga yunwa nake ji. Zan fara yin wanka don Allah ki sama min wani abu na ci. Daga tafiya nake maimakon a lallaba ni a yi lele na sai ake bina da tuhuma da sharri. Kai Ummu kin sauya hali ki gyara gaskiya bana son haka.

Hamma....

Bai bata damar yin magana ba ya shige banɗakin.

Murmushi ne ya kufce mata ta fita don dafa masa abu marar nauyi.


Sanda ya fito bayan ya gama shiryawa ya fito ta gama girkin talliya ce ta yi masa ita soyayiya t dafa masa shayi don ta san yana so. Ya zauna ta jera masa ta ajiye mai a gabansa.Juyawa tayi zata tafi ya kamo hannunta yace "Dawo ki zauna mu ci tare , an jima ba mu ci abinci tare ba ni da ke."

Sai da ta fara gala masa harara kafin tace "Bana ci na ƙoshi da ai ba da ni ka ke ci ba."

"Eh ai da ba kya nan yau kuma kina nan."

"Na ƙoshi ni dai."

"Sit". ya faɗa yana zaunar da ni ta ƙarfi.

Tare muka ci abincin ni da shi. Yana ta so muyi hira ni kuma na ƙi na ba shi fuskar hakan. Haka ya gaji ya kyale ni can kuma kamar an tsikare shi ya ci gaba.

"Kin ga fa duk wannan ci-cin maganin da kike yi Wallah a banza ne da wofi wannan ba zai hana ni na raɓi jikin ki ba Wallahi."

Haidar ya daina mamaki.   Na lura ma in zan biye ma Haidar ni ce zan mutu da baƙinciki don shi bai san wani abu rarrashi ko fushi ba. Gwara na saka wa kaina salama.

Da ya gama ma bai bari na fita ba. Sai da ya samu biyan buƙatarsa yadda yake ya ji ya gamsu kuma sai da ya fanshe kwanakin da bai yi ba. Don na jigata sosai kasa tashi nayi ma sai shi ne ya sa min ruwa masu zafi ya kai ni banɗakin na yi wankan a waje ya jira ni na fito ya zaunar da ni a kan gado shi ya ɗauko min ƙaramar riga na saka ya kwantar dani ya mamatsa min jikina.

"Sannu kin ji?"

"Uhm." Kawai na ce masa dama na tara bashin bacci ga gajiya kuma na ji daɗin yadda yake ta yi min tuni bacci mai daɗi ya ɗauke ni.