ZUCIYAR MUTUM

chapter 49

by @khairatup01

Zuciyar Mutum
Khairat.
Wattpad:khairi_Muhd.
Arewabooks:Khairatup01
49

*

Haidar yana kwance a kan kujerar Mami yana jiran aikin Ummu wayarsa ta soma ƙara ko da ya duba lambar mahaifin Afeeya ya gani. Bai yi ƙasa a guiwa ba ya ɗaga kiran. Suka gaisa nan ya gaya masa saƙon Afeeya.

Kaitsaye yace "Ka yi haƙuri Abba amma ba zan iya zuwa ganin ta ba."

"Haidar na san ta aikata maka abubuwa ba daidai ba amma ka sani ba don ni ba kuma ba don ita ba sai don girma da buwaya ta Allah ka je"

Guiwarsa tayi sanyi ya amsa masa da to zan je.

Na gode.

Mami ta kalle shi tace "Yaya?"

"Abban Afeeya ne wai tana son gani na don Allah na je."

"To ka je mana meye a ciki."

"Zan je ai amma sai gobe."

"Dama ai yau ta ƙare.Allah Ya nuna mana da rai da lafiya."

"Amin."

*

Mun ci abincin safe yake gaya min za shi ya ga Afeeya a station tana son ganinsa .

Bata nuna mai komai ba kuma ba ta ji komai ba ita da kan taAfeeyar tausayi take bata. 

A halin da ya ga Afeeya sai da ya ji yau rana ɗaya ya tausaya mata. 

"Baki da lafiya ne?"

"Eh."

"Ba su kai ki asibiti ba?"

"Sun kawo likita ya duba ni."

"To yaya jikin na ki?"

Da sauƙi.

Allah Ya sa kaffara. An ce kina nemana.

Eh! Hamma kiran ka na yi na baka haƙuri daman.    


In ma kin min na yafe miki.

Hamma na yi maka abubuwa na sani. Amma ina son ka yafe min. Ni nayi maka sanadin abubuwa da dama a kwanakin nan da na nesan ta ka da matar ka. Ka ƙaurace mata ka daina kula ta........ komai ta kwashe ta gaya masa.

Ya ko yi mamaki kenan da ace asirin yayi ƙarfi sosai zai iya sakin Ummu saki uku.lallai a jinjina wa ƙaramar ƙwaƙwalwa irin ta mata da kishi yake rufe musu ido da zuciya.

Na yafe miki ita ma na ari bakinta na ci mata albasa ta yafe miki. Wannan kaɗai ma aka bar ki da shi ya ishe ki. Duk saboda ni kika sayar da imaninki ba kya duba da cewa komai sai Allah Ya yi zai same ka. Kin manta babu wanda ya isa ya yi maka sai Allah ya so kuma sai ya amince. Ni da kika yi don ni ai gani baki same ni ba kuma ba ki raba ni da Ummu ba ke kuma ga inda kika tsinci kan ki saboda bamu da hakkin ki a komai. Amma kije mun yafe miki Allah Ya yafe mana gabaɗaya.

Amin na gode. Na san na yi kusure Hamma. Kuma na tuba kullum istigifari nake yi ko zan samu sassauci a raina. 


Ya kamata kam ni zan koma Allah Ya baki lafiya ya kawo miki sauƙi.


Amin na gode.

Bayansa ta bi da kallo har ta daina ganinsa. Shi ne Haidar ɗin da mahaifiyarta ta so ta tagayara rayuwarsa ya bi duniya ya faɗa shaye-shaye da neman mata da bata samu ba duk da a da ta samu galaba daga baya Allah Ya rusa shirin Umman ta hanyar Hajiyar Kano. Ta so na aure shi kuma na aure shi don mu kashe shi mu samu dukiyarsa nan ma Allah be yi ba, ta so ta raba shi da uwarsa da mahaifinsa da matarsa ta juya shi yadda take so Allah be bata iko ba ƙarshe yau gata  cell ana tuhumarta da laifin kisan kai. Ga can kuma Umman a kwance bata san ma zata tashi ko ba zata tashi ba zuciyarta zafi take yi mata da raɗaɗi sosai.

*

Rayuwar gidan Haidar da Ummu abar koyi ce da sha'awa. Haidar mutum ne da bai iya ɓoye soyayarsa ba ko a gaban waye. Yana da rigima kuma ba za a ce babu ƙalubale ba a gidan aure ba sai dai ɗan abinda ba za a rasa ba wata rana zafi wata rana sanyi hakan sha'anin yake.  Ummu kuma ta iya tafiyar da mijinta tana bin shi yadda yake so wannan ya saka zaman na su ya yi musu daɗi da kyau. Shi Haidar bai iya fushi ko gulma ba kuma ko shi ya yi mata abu ba zai bada haƙuri ta fatar baki ba sai ya san yadda ya lallaba ta ba tare da furta kalmar haƙuri ba. Yana ganin girman ta yana kuma kula da ita da cikinsa. 

Mami kuwa ta zame mata uwa don komai ita ke yi mata yanzu ma da cikin nata ya kai wata takwas bata bari tayi girki ta so ma ta maida ita can ɓarinta Haidar ya kafa ya tsare yace babu abinda zai dinga saka ta ko ya yi mata har sai ta haihu amma baya son zacen raba su don ba zai iya bacci ba.

Ta so ma ta je kano yace sai ta haihu. Nan ta ce masa in ta haihu ta huta zata je Minna ta ga mutanen Chiroro ko ba komai sun talafe ta da iyayenta a wani mataki na rayuwa a  baya musamman ma na basu muhalli.

Da ya ƙi daga baya kuma ta lallaba shi yace zai kai ta da kan sa.

*

A safiyar yau alhamis saƙon rasuwar Afeeya ya riske su. Wattanin ta uku a gidan yari bayan an yanke mata hukuncin ɗaurin rai da rai a gidan yari.

Mutuwar Afeeya ta taɓa mutane amma ya za su yi kowa ma na haka ne. 

A gidan Baffa aka yi mata komai aka kai ta gidanta na gaskiya. Umma dama tun bayan da ta farka aka gano tana fama da ciwon taɓin hankali. 

Tana can gidan masu kula da masu irin ciwon.  Saboda haka ba a ma gaya mata ba don babu wanda take ganewa hauka take haikan tana tonawa kan ta asirin duk irin badakalar da ta shirya.

Haka fa rayuwar take. Ka shuka alkairi ka girbi alkairi. Ka shuka tsiya ka gibi tsiya. Kowa yana samun hukunci daidai da abinda ya aikata a rayuwarsa.

*

Bayan sadakar bakwai  da daddare Haidar ya gama aikawa Ummu sakoninsa a inbox ɗinta. Ciwo ya tasar mata gadan-gadan ya ga mata sai mustu-mutsu take yi tana yarfa hannaye da cije baki.

"Meye Ummu?"

"Hamma ciwo bayana, kwankwasona. Wayyo Hamma ban taɓa jin irin wannan ciwon ba ka kira mini Mami." 

Tuni ya miƙe ya saka mata riga doguwa ya ɗauke ta duk nauyin nan da yake faɗa yau bai ji ba burinsa kawai ya ga ya kai ta asibiti. Yana saka ta a mota ya koma ya ɗauko akwatin kayan haihuwar ya saka a baya shi ma. Ya tada motar ya isa ɓarin Mami don in ya ce da ƙafa  zai je ya kirata zasu ƙara ɓata lokaci. 

Yana fakawa ya shiga ciki da gudu ya soma buga ƙofar ɗakin Baffa don ya san Mami na can.

Ta fito da hijabi a jikinta. "Haidar ya ya?"

"Mami Ummu ce haihuwa ce ina ganin."

"Muje to." 

Tare suka tafi. Asibitin da suke zuwa ya kai ta ai kuwa haihuwar ce dan ko rabin awa ba ayi ba ta haihu. Ta haifi namiji. Fari tas da shi gashinsa da yawa. 

An gyara yaro tas kafin aka ba wa Mami shi.

"Tabaakallah Alhamdullilahi. Allah Ya raya mana Muhammadu Habibu."

"Amin Mamina." Ya faɗa bakinsa kamar zai yage.

Ya ba wa nas tuƙuicin wannan dadaɗan labarin da ta ba shi.

Ummun ma lafiyarta ƙalau. An mata ɗinki amma. Bayan an maida ta ɗaki suka je ganinta. 

"Sannu ƴar nan." In ji Mami.

"Mami akwai wahala Mami na gama."

Dariya Mami tayi tace "Me aka yi da maza? Ai yanzu kika fara Ummusalma."

"Wayyo Allah Mami akawai wahala. Na hango lahira." 

Suka sa mata dariya.

Haidar ya miƙa mata baby yana cewa "Ga Habibuna ya dawo. Allah Ya yi masa albarka."

Idanuwanta suka ciciko tace "Amin Hamma."

Mami tace "Haidar ai ka koma gida ka samu ka saka kayan arziƙi ko?"

Sai da Mami ta yi maganar ya kalli kan sa ya kalli Ummu suka fashe da dariya.

"Gajeran wando ne iya guiwa kawai a jikinsa sai sigileti fara mai ƙaramar hannu. Shaf ya manta da wasu saka kaya.

Amma dai Mami baki kyauta min ba a haka na dinga yawo a asibitin nan? Innalillahi.

Suka sa mai dariya.

Ya kalli Ummu yace "Kya yi dariya mana ai duk kece kika jawo."

"Aa babu ruwana gaskiya." 

"Ai haka za ki faɗa dama."

"Ka je ka dawo."

"To sai na dawo."


Sai yamma aka basu sallama dama daga asibitin kaitsaye wurin Mami suka wuce. Nan suka tarar da Dada da Yafendo sun iso daga Billiri don ganin sabon angonsu.

Kowa ya ga jariri sai yayi Ma Sha Allah! Yaron jajir da shi kamar bature. Ga gashi kamar balarabe. Yafendo ta tofe shi da aduuo'i ta miƙawa Dada ma ita ma hakan ta yi. 

Kafin dare Hajiya tayo waya ba adadi harda vedio call musamman ma da ta ji an ce sunan Habib ɗin ta aka maida.

Aka yi mata tuwon dawa miyar kuka lafiyyya da man shanu ga nama a ciki. Da kunun gyaɗa. Mami sai da ta ga ta cinye tas ta saka aka kai ruwan wanka. Yafendo ce tayi mata wanka irin na mutan da.

Dada kuma ta wanke yaro tas aka sake masa wanka.

Angon ƙarni kuwa yana dawowa ya ga wayam dole ya koma gun Mami ya ji wai a nan zata yi jegon yace "Shi kenan ai nima jegon nake nan zan dawo ba zan zauna ni kaɗai ba tsoro nake ji gidan ya yi min girma akwai duhu babu hasken gidan ki taho da hasken."

Mami tace "Ga ɗaki can ka koma babu ruwana."

Mami ba a ɗaki ɗaya zamu yi jegon ba? Kin manta haihuwa muka yi?

Wallahi Haidar ranka zai ɓaci da gaske.

Suka dinga dariya.