CHAPTER 05
by @nanameera08
HASKEN CIKIN DUHU 💋
Chapter 05: The Visit That Cut Deep
Nanameera, YOTA/023.
Malam Yusuf ya kira sunanta, Salma data daskare a wajen tana kallonsa ta ce“Malam!” murmushi ya yi yana gyara tsaiwarsa ya ce“Na'am Ummusalma kin ganni a gidanku ko?” Salma da har sannan mamaki ya isheta ta gyaɗa masa kai. Numfasawa ya yi sannan ya ce“Daman naga kwana biyu baki zo makaranta bane, dana tambayi ƙawayenki sai suka ce Abbanki ne ya ƙarye shine nace bari nazo na duba shi” ɓoyyayiyar ajiyar zuciya Salma ta sauke, ta ƙirƙiri murmushi ta ce“Allah sarki, aikuwa yana ciki bari naje na masa magana” gyaɗa mata kai ya yi sannan ta juya ta shige gidan nasu. Tunda ta shigo Umma ke kallonta har ta ƙaraso gabansu, tsugunawa ta yi tana kallon Abbanta ta ce“Abba daman malaminmu ne na islamiyya yaga kwana biyu bana zuwa shine aka faɗa masa bakada lafiya yazo ya duba ka” jinjina kai Malam Habu ya yi ya ce“Allah sarki, to ce masa ya shigo” to ta ce sannan ta tashi ta fita. Umma ta taɓe baki ta tashi ta koma wajen wuta inda take ta kokawar gama abincin dare. Tsaye Salma ta sameshi cikin bango, muryarta a sanyaye ta ce“Malam ya ce ka shigo” murmushi ya yi ya ce“To masha Allah, muje” daga haka ta koma ciki ya bi bayanta. Sosai Malam Habu ya yi farin ciki da zuwansa har wajen ƙarfe tara yana gidan suna hira, shirin inda ranka na freedom Radio da aka fara ya sanya Malam Yusuf miƙewa yana murmushi ya ce“Allah ya ƙara sauƙi ya kiyaye gaba” jinjina kai Abba ya yi ya ce“Ameen Malam Nagode sosai, Allah ya bada lada” Ameen Malam Yusuf ya ce sannan ya juya ya fice daga gidan ba tare da ya sake ganin Salma ba, wadda tun bayar shigowarsa ta shige ɗakinta ta cigaba da karatun da take. Washegari daya kasance Lahadi da wuri Umma tagama dafa zoɓonta, dan ranar an fi ciniki dayawa, around 10am Salma ta fito daga ɗakinta tana sanye cikin wata doguwar riga ta atampa mai kyau kuma a goge, ɗinkin riga da skirt, ta sanya hijabi sister colour wanda ya tsaya iya gwuiwarta babu komai a fuskarta sai kwalli wanda ta sanya a idanunta amma tayi kyau tamkar tayi kwalliya farar fatarta sai sheƙi take. Kallonta Umma tayi sai kuma ta ce“Ke ko ɗan jambakin da ake sakawa ba zaki dinga sakawa ba? Kika sani ko Allah yasa acan ki dace da wanda zai aureki?” tura baki Salma tayi tana wasada fingers ɗinta bata ce komai ba, taɓe baki Umma ta yi tana cewa“Au mahaukaciya ma kika mayar dani, ina magana kin yimin banza” a sanyaye Salma ta ce“Umma nifa banaso”
“Ai daman ke duk wani abu da zai kawo mana cigaba bakya fatansa ya za'a yi ki so?. Ni zo ki shige karki ɓata mana lokaci” ƙarasowa Salma tayi ta buɗe ƙatuwar cooler da lemo da ruwan yake ciki.
“Sauran ki ce zaki dawo baki siyar ba, yau ba fita zan yi ba zan zauna da uban naki. Kayan dubu biyar da ɗari uku ne, sauran ki dawo ki cemin baki gane ba” Salma ta ce“To Umma ban ci abinci bafa” wangale baki Umma Rahmatu ta yi tana cewa“Wato duk wanda ya ji ya ce na hanaki abinci saboda ban haifeki ba. Ni na hanaki cin abinci? Ga ragowar shinkafar da aka dafa jiya nan, mu ma ita muka ci da awara, kuma ga naki can ki ɗauka” Salma bata ce komai ba ta juya ta koma inda Ummar ta nuna mata. Murfin da aka rufe farantin ta buɗe, shinkafa da wake ce sai awara guda uku akai. Ta zauna kan kujerar dake wajen tayi bismillah tafara cin abincin. Tana cikin ci yaron dake ɗaukar mata coolern yazo Umma ta juyo tana kallon inda take ta ce“Salama abincin ne ya gagara ki cinye? To maza tashi ku tafi kar masu siya su ragu” ajiye farantin tayi ta tashi ta ƙarasa inda randar ruwa take ta buɗe ta wanke hannunta. Sannan ta wanke bakinta ta dawo inda Umman da yaron suke, ɗaukar coolern ya yi suka fita tana cewa“Sai mun dawo”
“Allah ya tsare ya bada kasuwa”.
Abacha road, Mararaba.
Girgiza kai Al-ameen ya yi yana kallonta ya ce“A'a Mami, u need to rest fa, fitar da kike shine ya haifar da wannan ciwon, ya kamata ace kin zauna kin huta koda na kwana uku ne” Mami wadda take sanye da wata Egyptian Abaya Black colour tayi rolling mayafin abayar akanta tana murmushi ta ce“Al-ameen dole na tafi wlh, bazan iya zama ba ka sani ban saba ba. Tunda dai Allah yasa nasamu sauƙi to kawai gara na tafi na samu ƙarfi” fitowa tayi hannunta riƙe da handbag ƴar ƙarama tana kallonta ta ce“Mami muje kar nayi missing lecture” harararta Al-ameen ya yi ya ce“To babu inda zata je, shige ki kama gabanki” turo baki tayi tana kallonsa ta ce“Yaya da Mami fa nake, to idan ban tafi da ita ba da wa zan tafi?”
“Yaya Ahmad ya tafi dake”
“Tun ɗazu fa ya tafi, yanzu ai ya kai Abuja ma” murmushi Mami tayi ta riƙe hannunsa ta ce“Sorry son, bazan daɗe ba”
“Mami promise?”
Jinjina kai tayi ta ce“Yeh”
“Alright, Allah ya kiyaye”
“Ameen” tafaɗa sannan tayi waje Fatiha tabi bayanta.
Sun yi nisa Fatiha ta kalleta ta ce“Mami ɗazu naji Yaya yana cewa wai su Nayla zasu zo?” murmushi Mami ta yi ta ce“Eh haka Khadijah tace min a WhatsApp, but ban sani ba ko za su zo ɗin” Fatiha ta sake cewa “To Mami u have to call them, inason na tabbatar” Mami da idanunta ke kan titi ta ce“As if wajenki zasu zo ko?” dariya Fatiha tayi tana cewa“Wlh Mami Inason ganin Sis ne, i missed her alot, rabon da na ganta fa tun a Makka kwata-kwata basa zuwa” girgiza kai Mami ta yi ta ce“Ba laifin Khadijah bane kinsan General ba ko'ina yake barinsu suje ba, so shine inda ake samun matsalar, Nima kuma ayyuka sun yimin yawa bana samun damar shiga Abujan” Jinjina kai Fatiha tayi daidai sanda aka zo inda zata sauka ta ce“Tab, aikuwa idan tazo zamu yi yawo” Mami ta ce“Tunda ke kece ƙafar yawo ba” murmushi Fatiha tayi ta ɗauki handbag ɗinta ta buɗe motar ta fita tana ɗaga mata hannu.
Maitama, Abuja.
Around 8am ya tura ƙofar ɗakin, kwance ya sameta cikin duvet bata da alamar tashi daga bacci.
“Nimrah! Nimrah”
A hankali ta shiga buɗe idanunta ta janye duvet ɗin jikinta tana kallonsa, gyara zamanta tayi ta jingina da fuskar gadon fuskarta babu walwala ta ce“Amma akan me zaka tasheni daga bacci?” tayi maganar kamar zatayi kuka, Farooq dake tsaye gefenta ya ce“Gani nayi har time ɗin tafiyarki school zai shige but banga kin tashi ba, sannan gashi nima da wuri zan fita but banga breakfast ɗina ba”
“Yanzu saboda breakfast ɗinka ka tasheni a bacci? Akan me? Shikenan banida yancin da zan kwanta na huta a cikin gidana? Duk maids ɗin gidan nan ka rasa wadda zata dafa maka abinci sai dole ni?” Farooq kallonta kawai yake dan yanzu lamarin nata ya daina bashi mamaki. Kamar ba zai magana ba sai kuma ya ce
“Kenan ina matsayin mijinki banida right ɗin da zan saka ki kimin breakfast ko?”
“As far as akwai masu aiki da zasu iya yi maka to wlh bakada shi. Ni nagaji da wannan rayuwar wlh, nagaji da takurarka, akan me zaka kawoni gidanka ka dinga azabtar dani? Wlh bazan iya ba!” ta ƙarashe maganar tana fashewa da kuka. Tsananin mamaki ya sanya Farooq sakin baki, shi da ta yiwa laifi bai yi kuka ba sai ita ce mai bakin kuka? Girgiza kansa ya yi kawai ya juya ya fice daga ɗakin gudun kada zuciya ta ɗebeshi ya illata yar mutane. Da harara ta bishi sai kuma ta koma ta cigaba da kwanciyarta hankali kwance.
****Babbar mace ce zaune kan royal sofa dake zagaye da parlon, tana sanye da wata embroidery atampa ruwan zuma ɗinkin riga da zani, baƙa ce saidai kana ganin fatarta kasan hutu ya zauna. Girgiza kanta tayi tana kallonsa bayan ya gama maganar da yake ta ce“Yanzu ni da kake faɗamin me zan yi akai? Sanda nake faɗa maka ka saurareni? Akan me yanzu zaka dinga kawomin complains? Ƴar ƙanwarta nace ka aura amma ka watsamin ƙasa a ido kace kai ba zaka aureta ba wayayyiya kakeso. Da me kayi tunani da wayayyiyar mace? Zata dinga maka biyayya, ai sai dai kai ka bita wlh, sai ka bari idan mahaifinka ya dawo wanda ya yi ruwa da tsaki saboda tasa buƙatar shima yasa ka auri yarsu ka faɗa masa. Amma ni ka cireni daga sabgar gidanka Farooq”
Farooq wanda ke zaune kujerar dake facing tata ya kalleta sai kuma ya girgiza kai a hankali ya ce“Amma Mama...” dakatar dashi tayi ta hanyar ɗaga masa hannu ta ce“Farooq babu abin da zaka faɗamin na yarda, ka aureta saboda haka dole ka zauna da ita a duk yanda take, ka koyi juriya da haƙuri”
“Mama i know I made a mistake but dan girman Allah karki hukuntani da haka, wlh nagaji da halayen Nimrah, nagaji Mama, bazan iya cigaba da jure irin abubuwan da take yimin ba, dan Allah Mama” murmushi Mama ta yi ta ce“To yanzu Farooq me kake so nayi?” numfasawa ya yi yana gyara zamansa ya ce“Dan Allah Mama ki kirawota nan gidan kiyi mata magana ko zata rage wasu abubuwan, Mama tunda muka yi aure da Nimrah ban jin ta dafamin abincin ya yi sau uku, bata da lokacina, sannan batasan maganar da zata faɗamin ba a matsayina na mijin da take aure, kwata-kwata batada tarbiyya”
“Thank god daga fuskanci haka da kanka Farooq, babu yanda ban yi ba akan kabar maganar aurenta amma ka ƙi, bayan kasan tun asali yarinyar nan ba sonka take ba, Babanta ya mata dole ta aureka. Ni nasan babu wani farin ciki da zaka samu daga gareta, saboda haka ni yanzu shawara ɗaya zan baka, idan kaga zaka ɗauka to ka taimaki kanka, idan kuma yanzun ma zaka sake watsi da maganata sai kayi”. Farooq ya ce“Bazan sake wannan wawtar ba Mama just tell me”
“Ka ƙara aure!”.
****Mommah ce tsaye ƙofar ɗakin Nayla tana kallon yanda take rolling mayafi kamar batada laka, tsaki tayi ta ƙaraso ɗakin ta kama fuskarta ta yi mata rolling ɗin tana cewa“Kinsan dai halin Yayanki kinaso ya yi miki faɗa ne yasa ki ke abu kamar bakida laka ko?” murmushi Nayla tayi tana kallon madubi ta ce“Wow Mommah nayi kyau?” harararta Mommah ta yi ta ce“Zaki tsaya tambayar kin yi kyau ko kuma shigewa zaki yi ki tafi” langwaɓar da kai tayi ta ɗauki handbag ɗinta ta yi hanyar waje tana cewa“Bari naje gurin Yaya nasan shi zai ce nayi kyau”. A corridor suka ci karo dashi, sanye yake da wata dakkakiyar shadda Madam gezner ash colour, ɗinkin ya yi matuƙar yi masa kyau, ya ɗora hular zanna mai aikin ash itama, sai tashin ƙamshin turaren Clive Christian No.1 yake, murmushi Nayla ta saki tana cewa“Wow, My handsome brother” taɓe baki ya yi ya ce“Kyaji dashi” haɗe rai tayi ta kalli Mommah wadda fitowarta kenan ta ce“Mommah kina gani nace yayi kyau shine ya gwaleni ko?” murmushi Mommah ta yi ta ce“Ni ina ruwana da sabgarku kuma?” shiru Nayla tayi bata sake cewa komai ba tayi hanyar downstairs. Ƙaraso gabansa Momma tayi tana kallonsa ta ce“Dan Allah Zayyad karka je kayi abinda bai kamata ba, kasan dai halin Adda” murmushi ya yi ya ce“Shiyasa zan tafi da headphone saboda nasan irin faɗan Mami” murmushin itama Momma tayi ta ce“Allah ya baka sa'a, ka gaishesu” jinjina mata kai ya yi sannan ya yi hanyar downstairs shima. A compound ya samu Nayla idanunta zube kan flowers ɗin dake wajen sai tashin ƙamshi suke. Matarsa ya ɗauko yazo inda take daga cikin motar ya ce“Sai nace miki ki zo mu tafi?” murmushi tayi ta buɗe front seat ta shiga. Basu fi 10mins da fara tafiya ba ta kalleshi ta ce“Yaya bamu zo ba?” Banza Zayyad ya yi mata ya cigaba da tuƙin da yake, kwaɓe fuska tayi ta ce“Yaya I'm asking you fa” tsaki yayi idanunsa bisa titi ya ce“Kina iya sauka ai” bata sake cewa komai ba ta juya tana kallon hanya, rabonta da Nassarawa har ta manta. Tunda suka shigo Mararaba-Nyanya Expressway Zayyad yake tsaki the traffic is to much, yana ɗaya daga abinda ya sanya baya son zuwa Nassarawa saboda wannan cunkuson. A ƙalla sun kai kusan 20mins kafin su samu su shige, kai tsaye kuma Abacha road ya nufa. Around 1:05pm Ya yi horn a bakin gate ɗin gidan, mai gadin dake zaune kan benci ya taso ya buɗe masa. Yana gama parking Nayla ta fito ta rungume Fatiha wadda ta tawo da gudu sanda taji horn ɗin mota, kallonsu kawai Zayyad ya yi sai kuma ya yi hanyar entrance ɗin gidan. Da sallama ya shiga parlon, Zaune ya hangeta kan kujera 2 seater idanunta zube kan wayarta tana dannawa. Tana ganinsa ta ajiye wayar tana murmushi, zama ya yi kan sofa muryarsa a sanyaye ya ce“Ina yini Mami” wani banzan kallo ta watsa masa, daidai lokacin da Ahmad ya fito daga kitchen hannunsa riƙe da mug na tea. Murmushi ya yi yana kallonsa ya ce“Nayi tunanin ai fasa zuwa kayi” girgiza kai Zayyad ya yi har lokacin idanunsa na kan Mami wadda ta haɗe rai, kallonta Ahmad ya yi sai kuma ya yi murmushi dan daman yasa za'a rina. Nayla ce suka shigo parlon da Fatiha sai dariya suke, zama tayi kan kujerar da Zayyad ke kai ta ce“Mami ina yini” taɓe baki Mami tayi tana kallonta ta ce“Lafiya, kema sai yau kika ga damar zuwa ko?” sunkuyar da kai Nayla tayi dan tasan halin faɗan Mami. Shiru parlon ya ɗauka na wasu mintuna kafin Ahmad ya yi breaking silence ɗin ta hanyar faɗin
“Mami dan Allah ki yi haƙuri, yanzu ba gashi sun zo ba”
Harararsa Mami ta yi tana cewa“Da yake kai ne wanda ka yi laifin dole ka bada haƙuri” ɗan murmushi Zayyad ya yi yana kallonta ya ce“Dan Allah Mami kiyi haƙuri, Allah ya baki haƙuri”.
“Haƙuri ka ke bani Zayyad? Okay saboda ka raina min hankali ya sanya ka ke bani haƙuri kenan? Yanzu ni banida ƙima ko daraja a gurinka da zaka zo inda nake ko? Ban isa ba. Kenan da ace Yaya tana da rai haka zaka dinga wulaƙantamu kana nuna bamu da wani matsayi a gurinka, to bari kaji ko kana so ko baka so dole a faɗa a ce mu ƙannen mahaifiyarka ne uwa ɗaya uba ɗaya. Kuma bakada waɗanda suka fi mu duk duniya wlh. Amma mune yan iska ko nace ni ce yar iska ban isa kazo inda nake ba da sunan ka zo gaida ƙanwar mahaifiyarka banida wannan matsayin, amma da ace a dangin su Hajara abu ya faru da tuni kaje saboda ita kana ganinta da gashi, bakomai rayuwa ce” Mami ta ƙarashe maganar tana haki. Ahmad ne ya kalleta ya ce“Calm down Mami kar wani abun ya sake samunki dan Allah” tasowa Zayyad ya yi ya dawo kujerar da take zaune, hannunta ya riƙe a sanyaye ya ce“Dan Allah Mami ki yi haƙuri, nayi laifi but ba zan sake ba in sha Allah. Ki yi haƙuri saboda girman Allah kinji” fashewa tayi da kuka tana cewa“Zayyad ba wai dan wani abu nake maka faɗa ba, sai dan hakan ya zame mana dolene, Yaya ta riƙemu yanda ya kamata, a lokacin da muka rasa iyayenmu, duk wani abu da uwa ke yiwa ɗa ita tayi mana, ta aurar damu, yanzu Zayyad idan muka bar rayuwarka ta cigaba da tafiya a haka kana ganin zata yafe mata? Mun kyauta mata kenan? Mun bar abin da ta haifa yana cikin rayuwar da bata dace ba. Kasani kai maraya ne wanda ya rasa iyayensa a lokacin da aka haifeshi, rayuwarka abun tausayi ce, madadin kayi abinda ya kamata sai ƙanin mahaifinka ya gurɓata tarbiyyarka da sunan soyyaya. Kowa ya sani Idris yana sonka yana tausayinka amma ba hakan ke nufi ba zai dinga maka faɗa ko kuma ya gyara maka abu ba, ya kamata ka yiwa kan ka faɗa kasani girma kake yanzu ba baya kake komawa ba”
Shiru Zayyad ya yi haka kawai yaji hawaye na zubo masa akan fuskarsa, da gaske Bashida Iyaye, shi marayane irin marayan da kowa ke tausayinsa. Goge masa hawayen Mami ta yi tace“You don't need to cry Zayyad, abin da kake buƙata shine ka sauya rayuwarka, ka samarwa da kan ka haske wanda zai fitar da kai daga cikin wannan duhun mu kuma zamu tayaka da addu'a” murmushi ya yi a sanyaye ya ce“Nagode sosai Mami, kuma in sha Allah zan yi duk abin da ki ke ce, kiyi haƙuri” murmushin itama tayi ta ce“Bakomai Allah ya yi maka albarka” Daga haka ta kalli Fatiha da Nayla wanda suke zaune ta ce“Ku tashi muje kitchen a ƙarasa abincin” tashi Nayla tayi da sauri tana faɗin “Mami kiyi zamanki nida Fatiha sai muyi na iya girki ai” murmushi Mami ta yi ta ce“Yaushe Auta ta iya girma bansani ba? Mu je dai na tayaku” daga haka ta tashi tayi hanyar kitchen ɗin suka bi bayanta. Ahmad da tun ɗazu ke tsaye ya zagayo ya zauna kusada Zayyad yana kallonsa ya ce“Tashi muje sama” taɓe baki Zayyad ya yi ya ce“To wajenka nazo da zaka ce wani muje sama” tuntsirewa da dariya Ahmad ya yi yana cewa“Kai daɗina dakai ba'a maka gwaninta, to sai kayi ta zama ai” tashi Zayyad ya yi ya nufa saman yana cewa“Sai mutum ya bari idan nace ya yi min abu ya yi” daga haka ya haye saman abinsa, da idanu Ahmad ya bishi sai kuma ya yi murmushi ya cigaba da shan tea ɗinsa.
Around 4:50pm suna zaune cikin ɗakin Fatiha Mami ta shigo, kallonsu ta yi ta ce“Har yanzu hirar bata isheku ba?” murmushi Nayla tayi ta ce“Mami inason naje Orange market kafin mu tafi, ki ce Yaya Zayyad ya kaimu” Murmushi Mami ta yi ta ce“Shikenan ku shirya bari nayi musu magana, daga nan sai ku yo mana cefane” ihu Nayla ta saki ta kanƙame Fatiha tana cewa“Wayyo Allah na zan ga gari” dariya Fatiha tayi ta ce“To ki zauna ihu yamma ya sake yi a tashi daga kasuwar” da gudu Nayla ta shige toilet tana cewa“Da nayi asara kuwa”.
Zaune Mami ta samesu Ahmad sai hira yake masa, ta kalleshi ta ce“Son ko zaku je Orange market dasu Fatiha sai su yo min cefane” Toh Ahmad ya ce sannan ta juya ta fita.
Ƙarfe 5:15pm suka fito compound ɗin, Zayyad ya kalli Nayla wadda ke faman murmushi ya ce“Ke koma ciki” turo baki tayi ta ce“Ai fa Mami ce tace ku raka mu” taɓe baki Zayyad ya yi ya buɗe motar ya shige gefen mai zaman banza. Murmushi Ahmad ya yi ya shiga driver seat yana cewa“Kayi wani saurin zama anan”
“Eh cause ni ba drivenku bane ai” dariya Ahmad ya yi ya ce“Allah ya yaye maka” Zayyad bai ce masa komai ba ya yi commenting karatun Alkur'ani a motar, wanda hakan ya sanya su Nayla suka yi shiru dan dole. Ahmad ya yiwa motar key suka nufi hanyar orange market.