ZUCIYAR MUTUM

Chapter 50

by @khairatup01

Zuciyar Mutum.
khairat.
Wattpad:khairi_muhd.
Arewabooks:Khairatup01
50.

Kwanakin da Ummu ta ɗauka a gaban Mami an sha dirama da Haidar ba kaɗan ba yadda ka san shi ne mai jegon ba Ummu ba komai aka yi wa Ummu sai an mai sai yace ai shi ma jegon yake yi. 

Yaro ya ci sunan Habib suna kiransa da ainihin sunan sa. Suna aka yi na gani na faɗa don Haidar ya yi bajinta. 

Bayan sun yi arba'in tare suka dinga zaga dangi don bangajiya. Ta so zuwa Minna a wannan tsukun amma ya hana yace sai suna daf da tafiya Manchester zai kai ta yanzu ya baro ayyuka da yawa a ofishin Baffa.

Satin ta biyu a Kano gidan Hajiya tsakanin ta da Habib shan nono ne kawai don koyauhse yana hannun Hajiya tana lelensa don ita tana ganinsa kamar Habib ne ya dawo mata a matsayin jariri.

Su Adda ma suna zuwa ganin Habib. 

Bayan sun gama yawo ya ɗauko su ya tafi da su. 

Wani sabon babin shafin soyayya suka buɗe a gidansu Ummu ta ga meye asalin so da ƙauna har ma da kulawa. Idan ma ta ce wai Haidar baya son ta ƙarya ne. In tace Haidar baya ƙaunarta ba zata taɓa yarda ba. Kallon da wasu mutanen suke masa daban ita kuma kallon da take masa daban. Ana mai kallon mutum mai faɗar magana gaba-gaɗi babu taunawa sai ya fesar shi kuwa a wurinsa ba haka ba ne kawai shi mutum ne marar ɓoye abinda yake cikin ransa. Be iya gulma ba kuma ba shi da riƙo mutum ne sha yanzu magani yanzu daga nan kuma ya wuce a wurinsa sai dai kai kayi ta riƙonsa ko na yi fushi da shi a banza don sai ya san yadda yayi ya faranta mata rai sai ya yi bai yarda da ɓacin raina ba. Nima duk abinda zan faranta masa rai ina yi ina kuma kiyaye kishinsa . Duk da ko yau in budurwa ta kira shi zai  ɗaga  a gabana babu ruwansa kuma in ya gama zai ce min Sanda ce ko yace wance ce sona take ni kuma bana sonta ai kin sa kece nake so ke kaɗai kullum zancen sa kenan.

Muna ta haɗa kayan tafiya. Haka na lallaba shi zamu je Minna kawai ahalin su Nata'ala na ke tunowa. 

Ya shirya mana tafiya kwana biyu zamu yi mu a can mu dawo. 

Doguwar tafiya muka yi kafin muka je Minna state can ƙauyen chiroro. Ƙauyen na nan yadda na bar shi babu abinda ya sauya ko ya ɓace min. Da kaina na kai mu gidan gandu. 

Tsakar gidan dai na nan jiya i yau. Ana ta dirama irin dai na shekarun baya. Kowanne ɓari sai da na bi da kallo ina murmushi wani abin in na tuno sai na yi dariya wani kuma in na tuna in shiga ƙunci.

Da sallama na shiga cikin ɓarin Iya.

Furera ta amsa da fara'a "lale wa'alaikum salam."

"Furera kina nan ashe?"
Jin na kama sunata sai ta koma kallona da mamaki ita bata gane ni ba.

"Ban waye ki ba baiwar Allah daga ina a ina kika san ni?"

Murmushi nayi mata nace "Haba baki gane ni ba?  Uwani ce."

Sai kuwa ta saka hannu ta rufe baki da mamaki ta zaro idanuwanta waje. 

"Uwani da gaske ke ce?"

Iya da ke kwance ta miƙe tace "Wacce Uwani Furera ke kuwa?"

"Iya Wallahi Uwani ce Uwani dai ta mu Uwanin Nata'ala." 

Nayi dariya nace mata "la la haram wannan Uwanin Haidar ce."

"Eh kuwan haka ne." Ta soma kiran matan gidan da su Gwagwo duk da wasu sun rasu  a manyan gidan kan kace me an tattaro jama'ar gari da suka san ni ga Uwani ga Uwani ta bayan gidan ma shigowa nake yi. Cikin raina kuwa mamakin mutane nake yi wato yanzu da na zama mutum shi ne ake tururuwar zuwa gani na da ace da wata muguwar kama na dawo sai sun fi gane ni. Amma da yake Allah Ya rufa mini asiri sai ya sauya ni ya rufa mini asiri wai basu gane ni ba. Rayuwa kenan.

Kowa so yake ya gan ni na kula shi kowa Uwani kowa ni. 

Sai ga Iya ta kawo mini fura da nono har da dambu wai na ci. Na yi mamaki wai Iya ce take min haba-haba yau tab za ayi ruwa da ƙanƙara.

"Tare nake da mijina."

Amma kika yi shiru ƴar nan. Aje a shigo da shi.

Baffa yace mutane su fita sa dawo anjima don na huta.

Haidar ya shigo aka shimfiɗa mana tabamar muka zauna shi ma furar aka dama masa. 

Wasu yara ne suka shigo su huɗu kan su ɗaya maza uku mace ɗaya kuma kaminsu guda da Nata'ala.

Ba sai an gaya min ba ƴa'ƴan Nata'ala ne.

Iya tace "Kai Dikko ku zo ku gaishe da Auntyn ku." 

Suka ko tsugunna suka gaida ni na amsa ina kallonsu da yadda suke cikin raina kuwa nace "Da tuni nawa ne a haka ko?"

Iya ta soma bani labari ai bayan an kama Nata'ala uwar ta gudu da komai ta bar musu ƴa'ƴan babu wanda ya san inda taje. Gashi babu kowa ƙarfinta ya ƙare ita ma hutun take buƙata.

Na ji tausayinsu haka ma Haidar shi ya ɗauki alƙawarin kula da yaran har karatun su Iya ta dinga godiya tana kuka tana bani haƙurin abin da ta yi min. 

Nace na yafe ni ban riƙe ta ba Allah Ya yafe mana gabaɗaya.

Bamu kwana kamar yadda suka so ba. Haidar yace cikin Minna zamu koma na basu lambar wayata da kuɗaɗɗe. 

Ya karɓi lambar wayar Yaya Aminu babban wan su Nata'ala zasu dinga magana. 

Ganin da na yi wa Sageer sai na ji na yafe mai don ƙwaya ta sauya mai tunani ya haukace. 

Ƴa'ƴan da Iyan bata son laifinsu tafi so duk sun tagayare sun bar ta daga ita sai halinta duk ta yamushe ta bushe.

Haka na tafi zuciyata fes babu riƙon kowa a raina. 

Bayan mun isa Minna mun sauka a otal. Wanka muka fara yi kafin muka ci abinci. 

Nan na yi masa godiyar karamcin da ya yi wa mariƙana.

Ya harare ni kawai. Na san ya gaji ya kwanta na dinga mai tausa har bacci ya ɗauke shi. 

Ni kuma sallah na je na yi har ƙarfe biyu ina miƙa buƙatuna ga Allah. Cikin ikon Allah Habib ma bai farka ba. 

Kwana biyu muka yi muka koma Gombe. Don sati na gaba zamu tafi Manchester shekara biyu zamu yi mu dawo ya gama aiki da su kan sanan.

*

      "Kin gan ki kuwa matar nan ? Wai munis." Ya faɗa yana mini dariya ni kuma na ɗauki fillon da ke kan kujerar na maka masa a kai.

Ya ko riƙe kan yace "Bala'i ke wai cikin nan bayan munin da ya saka ki harda daba-daba ya koya miki ko me? kin raina ni bini-bini sai ki dake ni kamar wani Habib.

Ai kana sani bana son wannan tsokanar amma baka da aiki sai na tsokanata to waye ya saka ni na yi munin ba babynka ba ne? Ba ajiyar ka ba ce?

Eh kuma fa haka ne. Amma kiyi haƙuri dole ne in faɗa sai a hankali.

Ba bari zai ba haka ya sa na shiga kitchen na ɗebo madara da bomvita na haɗa na caƙuɗa ina sha.

Wallahi ki tausayawa kan ki. So kike yi sai an farka ki za ki haihu ko? Ba ki san wannan na ƙara ma mai ciki girman baby ba?

To yaya zan yi don Allah ni kam?

Jiki magayi.

Irie-iren diramar mu kenan kullum. 

Zaman lafiya muke sosai.

Da yamma muka je yawo ni da shi. Don Habib na wurin Sanda ita kuma Allah Ya ɗora mata son Habib ko son da take wa uban ne ya koma kan ɗan Allah ma sa ni.

A wani yammaci na soma naƙuda ya kai ni asibiti aiko na ga kayan zaƙi don sai da na yabawa aya zaƙinta awa ta huɗu cir ina labour har na karaya na saka rai ma CS ɗin za a min. Don shi Hammm ya ce a yi aiki ba zai iya gani na a wanna yanayin ba kamar yayi min kuka haka yake ji. 

Daga ƙarshe dai na haihu ko na ce na haifi yara biyu ƴan mata har sun fi Habib haske amma fa kamaninsu na ubansu ne.

Likitan ya kalli Hamma yace "Kai Yallaɓai kamar kai ne mai labour ɗin takalmi daban-daban fa ka saka".

Ya kalli ƙafar na kalla duk muka sa dariya. 

Yace ni dai Allah Ya sani ina shiga tashin hankali in kina naƙudar nan.

Kafin safiya an gama gyara mu tas yayi wa yara hotuna kawai sai tura wa ƴan Najeriya ya yi hotunan su ta waya. Sai ko ga kiran Mami bakinta ya kasa rufuwa don farincikin wannan kyauta da Allah Ya basu har da ƙari. Ƴan biyu fa mata. Lallai Baffa da Abi sun yi amare.

Ana gobe suna muka yi manyan baƙi daga Najeriya. Su Mami ne Yafendo, Dada ,Hajiya ,harda Minal da Sa'a Adda Hussaina ma ta biyosu na ji daɗin zuwan su sosai Allah Ya so ɗakuna huɗu ne muka bar musu sauran. 

Yara suka ci sunan Mami da Inna ta. Fatima da Hindatu. Ana ce musu Amna da Anam.

Rayuwa bata zo min da sauƙi ba amma Alhamdullilahi da lokacin jindaɗina ya zo gashi nan Allah Ya bani komai. Miji mai ƙaunata , ƴa'ƴa na uku , iyayen miji nagari ,ga ƴan uwana kowa yana sona. Ni kam me zan ce da Allah in ba Alhamdulillahi ba. Ina karatu online a nan. In ka gan ni ba zaka ce ni ce Uwanin Inna daga Chiroro ba. Hamma Haidar ya zame min garkuwa ya zame min bango majingina ya yi mini komai. 

Habib tsani ne da ya yi sandain da zan kasance da ni'imomin nan kala-kala da bai ɗauko ni daga chiroro ba da ƙila ina can ina fama da matsatin rayuwa kala-kala amma sai Allah Ya so ni ya dube ni ya ƴanta ni. Na samu ilimi na samu iyali na kafa sana'a yo ni kam ai lafiya lau ne bani da sauran buri. 

Nn samu rayuwata fiye da yadda na yi tsanmmani , ban ce ɗari bisa ɗari ba amma kaso 97% cikin ɗari ina zaune lafiya ne. 

Rungume ni ya yi ta baya  .
"Madam me ina nan me kike tunani?"

"Babu ko ɗaya Hammana rayuwar baya nake tunawa nake aunawa da ta yanzu. Zuwan ka cikin rayuwata komai ya zame mini daidai."

Juyo dani ya yi ya sumbaci goshina yace "Ina son ki Uwanin Chiroro." 

Ƙirjinsa na ɗan  daka cikin wasa. 

Ya kuma rungomo ni "Ina son ki matata ni fa ban daina addu'ar in zan mutu mu mutu tare ba don ni bana son wani ya san abinda na sani na ki?"

Na ko ƙyal-ƙyale mai da dariya nace mu bar yaran a ina?

Mu bar su a hannun Allah. Su zasu jura ni kuma ba zan jura ba.

Na ƙara rungume shi na sa dariya. Yaranmu uku suka shigo suma suka cusa kawunansu  a tsakiyar mu suna dariya.

Suka ce "Mum Dad you should hug us to."

Tsugunnawa muka yi muka yi pecking ɗinsu a kumatu. Muka rungume su happy family type.

Can na hango jama'ar Uwani da Haidar suna tafi jikunansu kuma yayi sanyi zasu yi bankwana da Uwani da Haidar ɗinta.

Ni kuma na ce bisallam. Mu haɗu a sabon littffi mai suna Wutsiyar Raƙumi zai zo nan ba da jimawa ba. Labarin Nadeeya da Nabeel.

Ƴar mutan panisau ce.✍🏻