CHAPTER 9
by @deejasmah
JIRWAYE........
Khadeejah Bint Ismail (Deejasmah)
***
Wattpad Deejasmah15
Tiktok Deejasmah_writer
Young talented writers association (YOTA).
In dedication to women in tech 💻
CHAPTER 9
Ya ƙarashe furucin na shi yana mai kuma fashewa da dariya karon farko da wannan matsalar take ba shi nishaɗi kenan, wato mutane suna da abun dariya da zarar sun ga sun ɗan iya latsa system sai su ga ai komai sun iya ne har su ke yin shisshigi a farfajiyar da ta fi ƙarfin su. Ji dai yarinyar da ba a daɗe da ƙyanƙyashe ta a duniyar technology ba har ta san ta masa shigar sauri kuma sai tace wai ita ta tsira har da sarƙafe bayanan ta ita ga ƙwaruwa ko? A da yayi niyyar lalata komai na ta amma sai ya dakata don ba ta kai ya ɓata effort ɗin shi ba shiyasa Snake ya masa gargaɗi kan saka Empire a ciki kenan?.
Sai kuma ya girgiza kai yana cewa '' amma fa ba a raina abokin gaba komai ƙanƙantar shi''.
Ƙwarai kam musamman a wannan duniyar ta su ta dakarun ɓoye, don abu ɗaya ne suka sani ko dai ka kashe ko a kashe ka ba fa kisa irin na sara da suka ba a'a ta ƙwamushe bayanan juna. Duk wanda ya shiga gonar ka kawar da shi shine mafita don in ka ƙyale shi zai iya maka illar da kai kan ka sai ji tausayin kan ka, haka za babu bayar da dama ko na second ɗaya ba kuma a yafiya don ita ɗin rauni ce da zata iya sakawa ka yi nadama. Sai dai kamar yanda Snake yace tsuntsu mai wayo ta wuya ake kama shi, to tabbas zai bi ta a hankali ba kuma wai ba zai mata komai ba a'a zai mata talala ne ya ɗana mata tarko ba kuma zai motsa ba har sai ta faɗa a ciki.
Wasu ƴan bincike yayi sai da ya tabbatar da ya goge sahun shi kafin ya kashe systems ɗin, kun san hackers a duniya ba su da yarda ko da a kan kansu ne ma. Za su iya gaya maka komai amma ba ka isa ka taɓa musu system ba ko ya kuke da su, ba ma iya nan ba ko a system ɗin na su komai kaf-kaf suke yi gudun su bar kafar da ka iya zama musu jalli-joga shiyasa yanzu ma sai da ya yi baɗ-da-kama kafin ya iya tashi yana jin shi a bit satisfied da komai kashe systems ɗin yayi har da hasken ɗakin kafin ya fita.
Kan couch ya koma ya zauna sigarin shi ya ɗauko ya kunna ya fara ɗayan abinda ya fi ƙwarewa a kai, yana cikin shan ne ma ya kira yi Snake ɗin da ya ɗaga wayar a firgice don ya tsani kiran shi musamman idan suna tsaka da aiki irin haka ya fi gane shi ya kira shi don a kiran shi ba a cika wanyewa lafiya ba.
''Scor 2 hours ɗin fa ba su cika ba'' ya furta yana mai son mazewa don ya zaci wani abun ne, sai ya tsinkayo dariyar shi cike da mugunta yana cewa '' ho matsoaci, me kuma ya faru?".
''Kai zan tambaya ai don ban san me ya faru ba''.
''Well komai ya faru and ka kwantar da hankalin ka kar kayi rushing komai okay? Ka bi a hankali ku ajiye min duk bayanan da kuka samu a kanta ba yanzu zan fuskance ta ba''.
''Amma Scor......''
''I know your concern amma ina son ka sani ina sane ba kuma ina shirin yafe mata ba ne You know that we don't forgive kawai akwai abinda nake tunani kan ta ne and she might be of help to us we are going to use her in a way she won't expect kai dai kawai ka zuba ido za ka gani''.
Shiru yayi sai kuma ya fashe da dariya yana cewa '' shege Scor kai ma fa mugu ne, I'm sure wasu potentials ka gani a tare da ita so what's the plan''.
''Ba zaka ji ba, sai in lokacin yayi bye''.
Yana faɗin hakan ya yanke wayar guntun sigarin shi ya ma zuƙa guda yana miƙewa direct wajen gadon shi ya nufa yana faɗawa kai, cikin lokacin ƙalilan bacci ya ɗauke shi cike da farincikin da natsuwar da ya kwana biyu bai da ita tun da maganar yarinyar can ya ɓullo.
Ko me Scorpion yake shiri ne jama'a? Uhmm?
A lokacin da suke ta wannan faɗi tashin don neman Hajiya decoder ita kam ta na can hankalin ta kwance tana shirin exams don tun a week ɗin da ta dawo timetable ɗin su ya fito hakan ya sa ba ta da wani lokacin kan ta, saboda ya haɗe musu na ba su gama curriculum ɗin su ba ta tests ga kuma na tutorials da suke haɗawa wanda tana cikin organisers ɗin don taimakon juna a faɗi tare a tsira tare in don ta ita ne zata iya cewa ko yau ayi exams don a experience ɗin ta da kuma abinda ta sani da wasu kan iya cewa zuwa makaranta ma ɓata lokaci ne don ta san abubuwan da lecturers ɗin su ba su sani ba. Ba kuma komai ya ja haka ba sai yanda take da kurɗe-kurɗe wajen neman ilimi komai ƙanƙantar shi kan na'ura, ba kuma iya neman ba ne sosai take aiki da shi tun bayan kammala secondary school ɗin ta infact shi ne ma driving force ɗin ta a kan son karantar computer science. Abinda ta sani da iya inda ƙwarewar ta ta kai ko shi mahaifinta bai san da shi abinda ya sani kawai tana ɗaya daga cikin ɗaliban da ake ji da su a kaf faculty of computing, bayan nan ko sai ayyukan da take yi remotely daga gida na KAD ICT HUB da KADA HIVE ko ta aikin bayan fage da take wa DIA bai san da shi ba don daga ita sai wanda take wa aikin ne suka sani wanda a yawon hackathons ɗin ta ta haɗu da shi wanda technical officer ne babba na control room ɗin ma'aikatan. Ko Tail da Snake yayi planting a cikin Agencyn da ƙarfin ikon da suke da shi, maƙasudin sanin shi saboda yanda ya sawa jami'in ido ne sosai saboda da fari ya zaci shi yake wasu ayyukan har ya fara bin shi a son shi na initiating ɗin shi zuwa tsagin su sai ya gane ba komai yake yi ba duk da dai shi ma hatsabibi ne na gaske amma ayyukan su kan masa yawa shiyasa ya nemi Adeeyah take rage masa su.
Da ya gane hakan ne kuma ya kuma saka idanu akan sanin wacece Ita dai dai hakan ya gaza yiwuwa saboda yanda ya iya takun shi, ko shi wannan ma abinda ya sa ya san itace saboda a daren da aka yi decoding saƙon suna tare suna wani aiki ya kuma ga sanda email ɗin ya shigo masa har da wayar da suka yi yana yaba mata. Bai yi zaton aikin na su ba ne sai da Snake ya kira yana son sanin me yake faruwa ne da yayi bincike ta hanyar kwana a ma'aikatar da sunan ya na aiki sai da kowa ya tafi ne ya buɗe system ɗin wancan ya ga saƙon bai kuma kai ga sanin wacece Ita ba don email ɗin shi akwai tsaro bai kuma yi ƙoƙarin bincika ba gudun ya gani. Amma fa duk abinda ake yi da uzzurawar Snake bai san yana da alaƙa da Scorpion Stings ba ko kusa bai ma kawo ba don ya san hatsarin shi ya wuce duk inda ake tunani ga shi kuma ba ma a san a wace ƙasa yake ba balle har su haɗu da shi.
Da alamun ma you are not tailing well......
Duk kuma wani hope ɗin su Snake sun ɗan saka shi ne kan jami'in da son ya bada wata hint, Amma kuma duk sa idon shi a kwanakin bai yi waya da ita ko sau ɗaya ba tunda suka yi chat ta shaida masa tana exams ta tsayar da aiki har sai ta gama bai kuma kiran ta ba. Ko baya ga haka ma bai da aiki wa ita a ƙasa, shiyasa suka samu ɗan relief da Scor ya shaida masa ya bi komai a hankali ba sauri yake yi ba hakan ya sa suka sake yin lambo suka zura masa idanu suna masu jiran tsammani.
Sanda ta bawa Mufee labarin ai Rhid ya shiga ciki rawa ta saka musu a room dama akwai ƴar jam box ɗin ta da take da shi don Allah ya wa ƴan Royal Tropicana ƙaunar ta, ai ko ta ƙure musu volume ta dinga kalolin rawa tana yi tana faɗin '' Finally zan zama chief bridesmaid, kan bala'i akwai shagali Deeyah-Rhid's love story ke ƙasar nan sai sun san zan aurar da ƙawa'' hararar ta tayi tana cewa '' shi ne har da kira mana bala'i a nan wajen''.
''Au bala'i nace? Ke ni ban ma san na faɗi ba in ma nayi suɓutul-kalam but ehnn Arewa weddings sai sun san da mu Aradu''.
''Ni dai na gaya miki bikina babu wata bidi'ar da za'a yi walima za a yi kowa ya ci shinkafa ya tafi''.
''In kin isa in bi Momo, ai wallahi duk wani wulaƙanci da ake mana a biki sai mun rama''.
''Ji wacce ke magana sai kace ba mai tsoron mutane ba, duk wannan fa rawar kan a gaban ni da kika raina ne kina fita ko a corridorn floorn nan ba za'a ji tarin ki ba''.
''Ke kafin nan na daina jin tsoron mutane, zan canja from Socio phobic to Socio-philic you'd see''.
''Ai ko indai kin canjan babu abinda zai hana ayi duk events ɗin da kika lissafo'' ta furta tana kaiwa kwance don ta san abu ne da ba zai taɓa faruwa ba.
Zama tayi gefenta tana cewa '' A'a Pookie, Kar ma ki ce haka fa bikin kin fa nake son farawa kai ƴan RT ma sun shiga uku kullum sai na tura IVn ki kamar sau hamsin a group''.
''Dole ko su cire ki daga group ɗin su tabbas''.
''Ba inda zan je ai talaka bai tashin talaka''.
Dariya kawai ta yi don ta san indai cika baki ne ba wanda ya kai Mufee amma fa bai wani tasiri, ko yanzu ma tana faɗin ne da ta tashi ta ajiye shi wajen don Abu ne da zai yi wuya wai gurguwa da auren nesa.
Ridhwan ko iyayen shi ba su samu zuwa wajen Affah ba sakamakon tashin jikin Ummyn shi hakan ya sa duk hankalin su ba a kwance yake ba, Adeeyah ta je duba ta ita da Mufee bisa umarnin Amah su dai ba su je ba sun dai kira shi suka masa ya mai jiki. San da ta je ma babu kowa sai babbar yayar su Aunty Ade ashe wai lecturern su Mufee ce, sosai ta musu tarba mai kyau ta tana musu godiyar duniyan da suka zo ita dai burinta su tafi don ba cika gane abun surukan nan ta cika yi ba inda Allah ma ya taimake ta Ummyn na barci. Lallaɓawa dai tayi Rhidwan ya maida su hostel shi ma sai godiya yake mata don bai san zata je ba sai da suka isa ne suka kira suna tambayar shi room number kafin ya sani, ita dai bata tanka ba sai Mufee ce ta amsa masa.
Ko da ya ajiye su ma ba su zauna study materials ɗin su suka kwasa suka wuce SMS inda suka haɗu da Aisha da suke kira Aysh da Nazeefah ( Nazey) wainda friends ɗin su ne da su kan zo su yi squatting a lokacin exams, su ne kuma wanda Ateey ke jin haushi hakan don a nata hangen wai sun maida DeeDeen kamar wata mara wayo ne.
Kowa gefen ta ta kama don ba department ɗin su ɗaya ba Mufee Microbiology ta ke, Nazey Industrial chemistry ita kuma Aysh Biochemistry. Don haka kowa ta shi ta fisshe shi ake yi, Adeeyah dai ba ma karatun take yi ba don ta riga da ta yi karatu bi kawai take yi tana kallon videos a YouTube don ita karatun ta rabi a can take yi ko kusa ba ta iya garbage-in garbage-out ba. Amma saboda ta san ita ce motivation ɗin friends ɗin nata ya sa ta zauna. Sai after 2 kafin suka gamsu da karatun da suka yi, suka kwashi takardun su zuwa room ana shiga kowa ya baje kan bed.
Ko da suka yi sallahr asuba Adeeyah ce kawai ta kwanta sauran kam karatu suka cigaba da yi don suna da morning exams ita ce nata sai 2, sanda ta farka ma sun wuce ba su ma ko tashe ta ba ta waje su kayi locking ƙofar suka tafi da key. Sauka tayi daga gadon da addu'a a bakinta, kallon ɗakin ta tsaya yi ko ba a gaya mata ba ta san ba su yi breakfast ba suka fita. Kai ta girgiza tana fara tattara ɗakin sai da ta gyara shi tsaf har da mopping tana cikin yi ko aka kawo wuta hamdala tayi ga Ubangiji sai da ta ɗaura ruwan tea kafin ta shiga toilet nan kam ta samu an wanke shi tsaf brush ta yi ta fito.
Toasting bread ta yi a pan ta soya ƙwai sannan ta yi zaman karyawa sai lokacin ta samu daman kiran Amah sun daɗe suna hira kafin ta kira Affahn na su shi ma dai yanda ya saba amsawa haka ya amsa yau dai ya ƙara da tambayar jikin Ummyn Ridhwan hakan ya bata mamaki amma tuno zumuɗin shi kan maganar ya sa ta amsa da lafiya lau daga haka bai kuma tambayar wani abu ba madallah kawai yace ya yanke wayar. Kamar yanda ta saba jin ɗaci a kullum ta kira shi ya amsa mata kamar ba ƴar shi ba yau ma sai da ta ji amma ta lallashi kan ta da jaddadawar cewa daga randa tayi aure komai zai wuce. Ajiyar zuciya ta saki tana juya akalar kiran ga Ridhwan don ta tarda misscalls ɗin shi, bai ɗaga ba sai da ya katse kafin ya kirata cikin zumuɗin shi yace '' Sunshine''.
Murmushin sunan da ya kira tan ta saki tana cewa '' Doctor, Barka da safiya ''.
''Yawwa Barka Mine, kin tashi lafiya ya shirin exams?".
''Alhamdulillah, na rana ai nake da shi''.
''Toh Allah ya bada sa'a, you'd definitely rock it na sani''.
''Ka san mene''.
''Na san that mine Guru ce, a komai ma''.
''Ban da dai cika baki, ya jikin Ummyna?'' Ta tambaya cike da kara, murmushi ya saki yana cewa '' Alhamdulillah,kin san ko jiya sai da tayi faɗa akan wai ba a tada ta da kika zo ba?".
''Kai dai Doctor''.
''Wallahi har Abu sai da ta gayawa''.
''Allah sarki, ai sai kace mata ni ce ban zo a time ɗin da ya dace ba in da na san tana bacci da ba zan zo ba ''.
''Ai kin min bazata ne Love, ban yi tunanin fa zaki je ba''.
''Saboda ba Ummyna bace taka ce ko?''.
''Nope Bae ba haka ba ne''.
''Ko ma miye ai ciwo ya wuce komai, musamman condition ɗin ta that is really critical''.
''Wallahi Bae, thanks once again Aunty Ade dai tace tace wai kin yi sosai kin san ba ta san wacece ba tace ta san Mufee student ɗin ta ce shi ne tace ko ita ce nace a'a mai blue ɗin hijab na nuna mata pic ɗin ki shine ai wai ba ta san ki ba amma akwai wata mai kama da ke a IG nace twin ɗin ki ce ai''.
Murmushi ta saki tana cewa '' ai kowa ya san Teeyah''.
''Yeah, and that's what makes me love you more Love ba wanda ya san ki sai ni ɗaya and that's what makes you the precious gem that you are ''.
Maganar da ya faɗi compliment ne but sai ta ji shi kamar insult don ta san ita ma an santa sai dai ace fuskarta bai yawo a duniya, gyaran murya yayi da sauri yana cewa '' ba fa wai ina nufin ba a san ki ko kaɗan ba, nope an san sunan ki if I'd say ma fiyeda nata amma in a different way''.
''Uhmm ai na zaci ba ka son wacce aka sani a duniya ne''.
''Ni kaza? Sai kace ba abu mai kyau kike yi ba? Da fa na kalli videon panel session ɗin ku a YouTube wani mugun sense of pride ne ya shige ni ina cewa Sahib ' this is my woman''.
Dariya ta saki jin yanda yai maganar tana cewa '' wai this is your woman''.
''Yeah I have to mark my territory, kuma a nan gaba zaki gane how proud I'm to have you Girl you are a dream''.
Wani kalar alfahari ne itama ya shige ta da abinda ya faɗin, ba na komai ba face na yanda yake son duk wani abinda take yi hakan ne ke ƙara mata ganin girman shi don ko ba komai mai son abinda kake yi ai shi ne mai son ka.
Ƙiris bakin ta bai suɓuce wurin faɗin '' You are also a dream'' ba amma ta taune harshen ta da abinda ta saba na shanyewa, sai murmushi mai sauti da tayi wanda ya ke kuma kashe shi da ƙara masa son ta don har ga Allah komai nata yana so fiyeda tunanin mai tunani.............
Gaskiyan Mufee ne da tace '' God when?" Ni kam cewa na yi God abeg as this love is loving.........
Deejasmah 🦂