SO DAN RAYUWA!

6

by @nkds

❉্᭄͜͡𝘚O 𝘿𝔸𝑵☆ R̲A̳Yᑌᗯᗩ ♥️

☆♥︎L⋆o⋆v⋆e⋆ ᖴOᖇ 𐐛օv𝖊♥︎☆

𝗕Ⲩ 𝔸mmⅈ𝖊ყ ℓαуℓєян & ɴᴀɪɴᴀʀ kd♡

P6.

Wani irin tsayawa suka yi cak gaba ɗayansu kamar waɗan da aka yi ma bishara da suna ƙara taku ɗaya bomb ne zai tarwatsa su, cikin wani irin rikitaccen kallo duk suka juya suna duban Jameelah Auwal Nasib da ta yi maganar cikin tashin hankali sai dai ganin sun tsaya ne ya sa ita ma take yi musu duba irin na mamaki da kuma alamar tambaya a saman fuskarta.

“What the hell are you waiting for?! Cewa fa nayi ku dakatar da shi daga shiga wurin Madam Esherh!!”

Ta yi maganar a tsawace ita sai yanzu ma da ta sake magana taga irin matsanancin tashin hankalin dake fuskokinsu sai kuma taji jikinta ya ɗan yi sanyi dan ta fahimci dalilin tsayawar nasu tun da har ta furta masu waye shi wato SAMEER OTHMAN KAMPALAH's dole su jijjiga su kuma kasa aikata komai ko dan su tsira da ayyukan da mutuncinsu sunansa suna ne dake jijjiga hantar cikin manyan ƴan kasuwan na Duniya haka za sunansa wani irin suna ne da kowa ya san da shi masoya da maƙiyansa kuma ko da sunansa a ka furta take jikin maƙiyansa kan hau kyarma, bare kuma a furta yana wuri, sunansa ya yi wani irin shahara fiye da yadda fuskarsa ta yi domin ɗaiɗai kun mutane ne suka san cikakkiyar fuskarsa. Ɓoye fuska kuma da yake wannan kuma wani ra'ayi ne nashi na daban.

🔥💔🔥❤️

Kwance take cikin yanayi na kwanciyar hankali cikin living room ɗin idanunta a lumshe ta miƙar da santala-santalan ƙafafunta saman doguwar kujerar da take kwance ta yi hugging na matashin Kujerar irin tightly ɗin nan wani irin azababben ciwon kai take fama da shi shi ya sa ta kwanta ta ɗan samu relaxing kafin ta ci gaba da ayyukan dake jibge suna jiranta.

Lokaci guda taji doorbell tare kuma da alamar buɗe ƙofar living room ɗin da kuma jin taku a nutse ana tahowa ciki da yake bata fara baccin ba shi ya sa ta iya jin ƙarar takun mamaki ne ya ɗan kamata sai kuma taji ranta ya ɗan ɓaci saboda ta riga ta sanar ma Jameela kar kowa ya shigo muddun ba wani abu ne mai muhimmanci ba saboda hutawa zatayi kuma koda abin ne mai muhimmanci sai Jameela ta fara sanar da ita sannan amma takun da ta ji da kuma wani rikitaccen ƙamshi da ya karaɗe living room ɗin ya tabbatar ma ta da ba Jameela bace hakan ya sa ta ware fararen idanunta a hankali tare da miƙe wa tsaye daidai lokacin da shima ya bayyana.

“Oh What the Heck, Jameela mene ne ya fa....”

Sauran kalamanta suka tsaya a maƙoshinta sakamakon idanunta da suka sauka a kan sa ya yi tsaye harɗe da hannu a ƙirji yana yi ma ta wani irin duba duk da bata fahimci duban da yake mata ba sakamakon Shade ɗin dake fuskar nasa.

“Who the hell are you and who let you in?”

Ta faɗa ba tare da da ta iya control na fushin da taji yana ƙara taso ma ta ba.

Wani irin tsitt Room ɗin ya yi kafin ya wani irin nodding kansa, a kaf rayuwarsa da wannan kalmar ya taso ana yi masa wannan tambaya na waye shi sai dai baya taɓa buɗe baki ya bada amsa domin kafin ya bayar sunansa ya ziyarci kunnen mai tambayar saboda haka yanzu da ta yi masa tambayar sai yaji ta zo masa a wani kala daban kamar ba yadda ya saba ji ba, bai ce da ita komai ba cike da izza sai da ya ƙari sa saman ɗaya daga cikin expensive luxury sofa dake jere a wurin ya zauna ƙafa ɗaya kan ɗaya lokaci guda yana zare Shade ɗin da ya yi ma idanunsa shamaki da duban tsakiyar nata idanun.

“_SAMEER OTHMAN KAMPALAH's_ sai dai an fi ganewa idan na haɗa MONSTER sunan da aka laƙabamin ta ƙarfin tsiya a Duniyar kasuwanci.”

Ya wani ɗan taɓe baki irin He doesn't care ɗin nan.

“Anyway kallon da ake min ke nan kuma hakan nake...”

“Get out!”

Ta faɗa dan zuwa yanzu ya gama ganar da ita wanene shi ne ɗin tsaurin idanunsa take gani da har ya iya kawo ma Companyn ta ziyara bayan burinsa ya kwace Companyn ya siyeshi ta ƙarfin tsiya dalilinta na cewa ya fitar kuwa shi ne ranta ya gama ɓaci bata so zaman ya kai su wani mataki daban shi ya sa domin gudun kada ta faɗa masa mara daɗi salin'alin ta ce ya fita dan kuwa so yake yaga ya tada Esherh Sweety da hakan ba zai musu kyau ba gaba ɗaya wannan Esherh'n gabansa ba Sweety ba ce domin mugun Sweety ta farga tafiyar ba za yi musu da daɗi ba.

“Woww haka ake tarbar baƙi a naku Companyn da kora?!”

Ya faɗa cikin wani irin low voice yana dubanta.

“baƙin mutunci su ake ma tarba ta karamci amma baƙin da suka zo da tsiya tarbar su a ke ta yaren da za su fi ganewa.”

Ta bashi amsa kanta tsaye tana gyara tsayuwarta tare harɗe hannu dan ganin inda drama ɗin nasa zai ƙare.

“Lallai ba shakka naga alama sai dai ba wannan ya kawoni ba domin nazo ne na mallaki wannan Company ta salama da mutunta juna sai dai ganin tarbar da a ka yi min yasa na canza shawara...”

Ya yi maganar yana miƙe wa tsaye tare da ƙari sawa dab da ita har suna iya shaƙar numfashin juna.

“Ki rubuta ki a je ni SAMEER OTHMAN KAMPALAH's zan mallake wannan Companyn kota halin ƙaƙa koda kin shirya ma hakan ko baki shirya ba.”

Wani irin karkata kanta ta yi tana dubansa cike da haushi domin ya ɗan kereta tsayi.

“Da kyau Mister Playboy fatan nasara amma ka sani zakayi shirin yaƙi ne da Esherh Kalthum Jeddy's AkA Sweety saboda haka ka shirya shiri mai kyau kuwa dan ba ƙaramin yaƙi ka taro ba.”

Ta ƙare maganar tana sakin wani shu'umin murmushi dan ba zata tsaya yana gaggaya ma ta magana ba tare da ta bashi amsa daidai da abin da ya faɗa ma ta ba koma fiye domin wani mugun haushinsa takeji da ta rasa lokacin da hakan ta kasance.

“Well you're right da alama kin san abubuwa da yawa a kaina kin ga ke nan bani da buƙatar sake tunatar dake waye ni.”

“Exactly na sani wannan dake tsaye a gabana shi ne dai wannan tantirin ɗan kasuwan da baya iya samun sukuni har sai ya durƙusar da sauran ƴan kasuwa kamarsa ba iya nan ba ɓoye fuskarsa yake saboda ya san shi ɗin Mutumin banza ne da baya iya taimakawa sai dai lalatawa sai dai ka sani Bayan giwa sai barbaje kuma nan da kazo komai kwakwakon ka haka zaka haƙura ka kyale domin Esherh ta wuce tunanin duk wani tantiri.”

Tun ba yanzu ba yana son challenging irin haka shi ya sa zai biye ma ta yaga iya gudun ruwanta duk da Yarinyar ta bashi mamaki domin yanayin Innocent face nata idan ka kalla ba zaka yi tunanin zata iya faɗin waɗan da kalami ba sai dai koba komai ta burge shi dan ta nuna masa ita ma jaruma ce sai dai zai tabbatar ma ta da kalamansa ya kuma nuna ma ta da SAMEER OTHMAN KAMPALAH's take challenging.

Biye ma ta ya yi suka ci gaba da yaɓawa juna baƙaƙen magana son ran kowanensu domin Esherh ji ta yi ciwon kan nata ma ya tafi nasa wurin daban.

“Well kamar yadda na faɗa ne ki zuba idanu kisha kallo.”

Ya faɗa a ƙarshe tare da juyawa cikin takunsa na izza zai bar room ɗin.

“Ba ka ji ba!”

Ta faɗa da ɗan ƙarfi lokacin da ya kusa ƙofa, dakatawa yayi sai dai bai juyo ba.

“Hausawa suka ce; Abin wani da wuya, nemi naka. Kuma sannan Birnin kura ba a sa kare dillanci. Anan ni ce kurar ka tuna da hakan.”

Ta faɗa tana yi masa nuni da kanta.

Juyowa ya yi yana fuskantarta karo na farko da ya saki wani malalacin murmushi kafin ya furta.

“Maraya ba ya shakkar mutuwar uwar wani. Ki jira ki gani zan tabbatar miki da hakan sannan idan kece kura ki sani Zaki nake uban gayya akwai ban tsoro ki riƙe wannan, Har a naɗe ƙasa ungulu ba ta rama gayyar zabuwa.”

Yana gama faɗar hakan ba tare da ya bari ta lalubo abin faɗa ba ya yi ficewarsa daga Room ɗin.

Yayin da Esherh ta yi tsaye tana bin bayansa da wani irin mugun kallo kamar idanunta zaku zazzago sai bayan fitarsa kuma taji ciwon kan nata ya dawo komawa ta yi ta zauna tana faman sauke ajiyar zuciya kafin ta miƙe tare da ƙari sawa ta buɗe Fridge ta ɗauko bottle na rowa ta buɗe murfin ta hau sha sai da ta sama nutsuwa sannan ta koma ta zauna tana dafe kanta.

Kusan minti biyar tana a haka kafin taji an buɗe ƙofar an nufo ciki takun tafiyar ya sanar da ita ko wacece saboda haka ba tare da ta ɗago ta dubeta ba ta furta.

“Jameela Auwal Nasib bana buƙatar wani takura a halin yanzu please.”

Cikin girmama wa Jameela ta furta.

“Sorry Ma'am dama baƙuwa kikayi shi ya sa nazo na sanar dake kuma mai muhimmanci ce sosai.”

“bana cikin yanayi da zan iya ganawa da kowa ki sallame ta kawai.”

Esherh ta faɗa.

Jameela bata sake furta komai ba ta fita sai dai tana mamakin abin da ya faru lokacin da SAMEER OTHMAN KAMPALAH's ya shiga Room ɗin har fitowarsa bayan wani lokaci da kuma barin Companyn da motocinsa suka yi.

Esherh tana nan a inda take ta sake jin alamar an shigo Room ɗin ba tare kuma da sallama ba, saɓanin Jameela da ta saba muddin zata shiga da sallama sai dai bata yi tunanin ba Jameela'n bace saboda taga bata daɗe da fita ba.

“Jameelaaaa wai me na faɗa miki ne? A barni na huttt.....”

Kasa ƙari sa maganar da ta yi cike da wani irin zallar mamaki ta ware manyan idanunta tana duban wacce take tsaye gabanta tana sakar ma ta wani kyakkyawan murmushi ba shiri Esherh ta miƙe tsaye baki na rawa ta furta.

“Be..Be...Bestie!”