SO DAN RAYUWA!

7

by @nkds


❉্᭄͜͡𝘚O 𝘿𝔸𝑵☆  R̲A̳Yᑌᗯᗩ ♥️
         ☆♥︎L⋆o⋆v⋆e⋆ ᖴOᖇ 𐐛օv𝖊♥︎☆

𝗕Ⲩ 𝔸mmⅈ𝖊ყ ℓαуℓєян & ɴᴀɪɴᴀʀ kd♡

***

༆Ⴆҽʂƚ σɳ ƈɾҽαƚιʋҽ ʂƚσɾყ!!!༻

♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡

Page 7

"Bestie miey tarh?" Ta sake ambatar sunan a karo na biyu cike da Mamaki  sosái ɗin dai. Ɗan murmushi me faɗi Eaman Sufyan Turaki tayi tana ƙara sa shigowa cikin office ɗin  tare da furta. "Yeah ni ce dai ɗin ba wata ba Bestie Mee tarh!" Ɗan gumtse bakinta Esherh'n tayi tare da furta."kuma shi ne ko ki faɗin min zaki zo, hala ma saukar yaushe? Yau she kuma a gari?" Zama tayi kan rug tana me furta. "Da farko dai bara na fara wa kaina mazauni tunda yau Bestie bata ba bestien bestie'nta wurin zama ba.!" Tayi maganar tana zare eye glasses ɗin dake manne a idonta.
    Hararan ta tayi bayan ta janyeta a jikinta tana me furta, "Ai fushi nayi sauƙa babu notice haka but kawai sedai na ganki kwatsammm......
   Komawa zaune tayi kan sofar office ɗin bayan ta direwa bestin nata juice da madara me masu sanyi. Shigowan ƙira wayanta ya sanya ta miƙewa tana nufar window'n office nata  woyar manne da kunnenta da duk kan alamu wayar me muhimmanci ce. System ɗin dake gaban table na Esherh'n ta janwo zuwa gabanta tana cire password ɗin kai, wani kalan zaro ido Eaman Sufyan tayi ganin abinda ta fara cin karo dashi, dan haka ta juyar da kallonta zuwa kan Esherh dake wayar ta hankali kwance. "Bestieee kin...san..kuwa girman kasadar..da kike tare da shi? Da har kike ajje pisc nashi a woyanki? Kin san kuwa girman  hatsabibanci irin na _SAMEER OTHMAN KAMPALAH's kuwa? Bestieee........
     Chakkk Maah dake ma Esherh magana ta dakata sakamakon sunan da taji ya wani irin dakar tsaƙiyar ƙirjinta yana gilmata kana ya wuce. Tana miƙewa daga zaunen da take duk da cewan bata da tabbacin ko me sunan ne. Ita kanta Esherh'n data zubawa Eaman Sufyan Ido itama kusan daskarewar tayi tana kafe Eaman ɗin da ido, jin ko sunan waye ta ambata mata acan cikin zuciyarta take ayyana cewan dama batayi Removed email náshi da komai ba har fadeelan ta sama damar kalla. "Are You Okay kuwa Sweetie? And kina jina ma kuwa?"  Maganar da Mammah ta mata ya sanyata   dawowa daga duniyar tunanin data lula tana ƙara sa dawowa  daidai ɗin ta  har tana saƙin ijiyar zuciya.
   "don't worry my best wishes Mammah, Lubna Sufyan kemin magana ne" wani gauran numfashi ta sauƙe tana komawa zaune bawai dan abinda ya gitta zuciyar nata ya lafa bane tare da mata sallama tana cewa idan ta dawo gida sa ƙara sa maganan da suke kan maganar ganin babban likitan da aka bata tabbacin tabbas yana a cikin garin Abuja'n be kai ga barin ƙasar ba....

A natse ta koma tana zama kan kujerar data tashi tana sarƙe hannayen ta biyu tana kallon cikin tsaƙiyar idanun Lubna Sufyan ɗin.......
   "Oya tell me bestie Ina ki ka san wannan Mr arrogant ɗin?" Kai tsaye ta jefa mata Wannan tambayar tana juyar mata da system zuwa gabanta. Juice energy ɗin dake hannunta ta ɗan yi sipping tare da sanya left hand nata tana ɗan sha Re zuba duk kuwa kasancewar akwai ac a office ɗin.
  Gyara zamanta tayi tana jan wani mayen numfashi zuwa cikin cikinta tare da soma faɗin.

"Ko da yake ba abin mamaki ba ne idan kin ce baki san ko waye SAMEER OTHMAN KAMPALA's ba ko a pisc, so amma nayi Mamakin da ko sunan shi daya gama kareɗe duniyar a ce baki sani ba. The great Billionaire kenan kana MONSTER a duk abinda yasa gaba. Kwarai mutum ne hatsabibi bana wasa ba a fannin kasuwancinsa. Se dai bawai hatsabibanci irin wanda kowa ke zata ba. Wasu mutane ne daban suka bashi wannan   sunan bawai dan hakan yake ba!, Hasali ma shi mutum ne me wani irin tausayin talakawa domin kuwa ALLAH ya bashi wata irin zuciya ta rashin son ganin wani na rayuwa irin ta ƙasƙanci. Yakan sadaukar da farin cikin sa domin al'umma se dai bai bari suna ko pisc nashi su bayyana kan wannan abinda yay ɗin. Kuma kome ya ayyaka baya son a San shi ne yayi na Alkhairi. Ba kamar wasu daga cikin ɗayɗaykun mutanen mu da  idan sun yi wani abu na kirki suke post da kansu cewan sun yi abu kaza sun yi abu kaza ba.  Domin shi ya sha ayyaka abin Alkhairin mutane su juyar dashi zuwa akasin hakan sedai samm hakan baya taɓa damunsa sabo da shi da kansa da aka taɓa fira dashi sau ɗaya takkk a wata mujallar gani da ido ya ce Sa'a tana tafiya ne da tarin ƙalubale na Rayuwa bisa bigire na ƙaddara dan haka a kowanne hali muka tsinci kan mu to mu yi godiya ga Allah da Kyakkyawan  yaƙini akan hakan ma wata dama ce   ta same mu na samun ɗaukaka da kuma nasararmu..
  Kana yace.  Sunna ce ta rayuwa ga duk wanda yake son cimma nasara to kuwa  dole ne ya saba da haƙuri da kuma juriya, domin nasara ba a samunta cikin sauƙi, dan duk wata  hanyar cim mata a cike take da tarin ƙalubale na rayuwa, to mu ɗauka cewar waɗannan matsalolin dake riskarmu su ne matakan isa ga babbar nasararmu  matuƙar mutum bai  sare ba......
   Kana da aka tambaye shi kan cewar me yasa wasu daga cikin mutanen da yake temaka basu godiya ga bisa abinda yake musu?,  Kin san kuwa me ya ce musu?"........
   Lubnan tayi maganar   tare da ɗagowa tana kallon Esherh ɗin.

"_Cewa yay kada  kayi nadamar kasantuwarka mutumin kirki ga mutanen da basa godiya bisa hakan. Ayyukan kirki yakan bayyana kansa ta hanyar halayya, sannan halayyar mutum yakan bayyana asalin surarsa sa ne..... Kana yace kada ka damu idan ka yi alheri ga mutane kuma basu nuna godiya ba. Abubuwan kirkin da kake yi sune da kansu za su bayyana kansu ta hanyar halayen ka, kuma halayenka za su nuna ainihin asalin ka!!!. Ka na ya sake cewa. Halin mutanen kirki baya ɓuya, kamar yadda halin mutane marasa kirki baya ɓuya. Kai dai kawai ka  za ma mai ƙarfafa zuciyarka da juriya wajen ci gaba da aikata abin Alkhairin koda kuwa mutane basu nuna godiyarsu gare ka, kuma Ni duk abinda nayi ina yin sane ba dan a gode min ba, na yi ne sabo da ALLAH bawai don wasu cannn ɗeɗekun mutane su gode min ba ko dan gobe....._ Kin ga kenan mutumin kwarai mutumin kirki kamar Dr Sameer  othman kamfala's be chanchanta ire iren waɗan nan kalamai daga cikin al'umma ba, nima nasan hakan ne ata dalilin yaya Adeel ne domin babban na hannun damar sane sosái...."

Uban tagumin da Esherh tayi ta janye tana sauƙe wata zazzafar ajiyar zuciya me ɗan sauti saboda wasu kalaman da taji sun shige har cikin kwanyar kanta.

   ★

Can kuwa ɓangaren Maah  bayan ta katse wayar ta ƙura ma  wayar ido cike da jin wani abu me kama da zafi zafi da taji yana nemar ta so mata iyaka tunaninsa kawai taya faɗo mata domin kuwa iyaka ambatar sunan shi kan sanja duniyar tane gaba ɗaya. Duk wannan uban SOYAYYA'R da take ma Esherh jin ta take bama takai kwatankwacin wanda take masa ba. Dan haka ta  cillar da phone in  kan gadonta  tana cije leɓe wasu ruwan hawaye Masu tsananin zafin gaske na kwaranyo mata.   Kuka sosai tayi a wannan lokacin domin duk sanda ta tuna hakan tana rasa hankalinta ne gaba ɗaya shi yasa take taka tsantsan akan ɗin wani abu da ze ko jin gina da sunan shi ne. Kanta ta riƙe da hannuwa bibbiyu tana me furta....
" MARAFA  wyh, you betrayed me bayan kasan da cewan  I love you with all my heart!, why MARAFA   I soooo much hate you now, I hate you I hate you,  his love has just been part of me a kan ka  na san menene  soyayya and his my first  love kai ne kaɗai mutumin da bana haɗa son ka da  kowanne irin namiji ne, who da na chanchanta haka daga gare ka? I love U and I hate you ~ MUHAMMED MARAFA KAMPALA's nayi ladamar auren ka nayi  nadama is too let to correct her mistakes, duk da haka ba zan gaji da roƙon ALLAH ba akan yasa kayi ladama! Kayi ladama!! Kai ta yin ladamar abinda ka aikata a gareniba I hate all off you wllh..............

   ★
   SAMEER

Kamar ko yaushe haka ɗaya bayan ɗaya manyan  motocin nasu gaba  ɗaya suke kutsawa kan titin da zai sa dasu da katafaren  Suite Lodge ɗin da suka sauƙa , a yanda car's ɗin suke tafiya  sunyi   convoy kawai abin su birge mutum ne.

  Tun da suka fice a cikin company'n lafiyayyun manyan motocinsa ke zabga guda tamkar tashin duniya, shi kuwa yana lafe cikin lallausar kujerar daya lafe sosái cikinta. Girma da tsaurin ido haɗi da maganganun data yaɓa masa na ƙoƙarin birkita brain nashi. Dan haka yake a lafen shi kaɗai ɗin sa yake tsara yanda zai lalata komai ɗin da take gadara dashi idan yace komi ya a nufin komai ɗin kuwa ciki kuwa tunda yace komai ɗin kenan yana nufin harta kan Rayuwarta ze iya bi ta kai ya danne.....

Dan haka yana a cikin duniyar wannan tunanin yasa baima san sun ƙara so best Hotel ɗin da ya sauƙa ba🤗.

Wayarsa ce  tayi vibration dake cikin aljihun wandon sa dan haka ya cirota tare da  duba kan screen dan ganin me ƙiran. MY BESTEST  shi ne rubuce ɗoɗar a saman screen ɗin. Dan haka babu jin kirin komai ya katse ƙiran nata yana saka sabon call na No ɗin.
     "Hello My best Son!" 
      From d other hand yace.
"Yaeh Oum my the best ɗin bestes"  
  Yay maganan yana wani langwaɓe kansa gefe tare da shafar sukar kansa
"How are I doing there? " Ta tambaye shi cike da kewansa da tayi, Wani kwaɓe face nashi yayi tare da cewa  "Alhamdulillah Oum IN SHA ALLAH cikin week ɗin nan  i will b home,am eager to b home wlh I miss u Oum"    "Miss u too my friend sosái Masoyiya tayi kewanka.... Daga haka suka shiga wani zancen daban har zuwa inda  inda Parking car's na cikin suite ɗin suke. Zuwa lokacin kuma sun kammala woyan da Oum nashi kamar kullum wannan fararen zaratan santala santalan ƙafafuwan ne suka fara fitowa kafin me gaba ɗayan ya bayyana wato ganganr jikinsa.
      A nutse yake taka fararen zaratan sawayen sa  idanunsa na sauya launi,wani abu da yafi kama da bacin rai na ƙoƙarin sake  motsa zuciyarsa,yana jin in har be yi ragaraga da rayuwar yarin yar nan ba to kuwa Tabbas shi be cika jinin  SAMEER OTHMAN KAMPALA's ba.

"Welcome sir" 

Kattin samudawan  dake aikin bada tsaron lafiya wa mutanen da ke wajen suka faɗa suna rusunawa da kuma girmamawa, domin kuwa kowa ka kalla a wurin wani ne wanda ƙasa ke ji dashi masu gidan rana. baiko amsa su ba  hannu kawai ya cira  musu ɗaya kawai  alamun ya sallamesu.

     Da left hand nashi yay amfani wajen  buɗe ƙofar bayan ya ratsa wani hadadden balcony da aka ƙawatashi matuƙa fiye da tunani,kyakkyawan falo ne na alfarma wanda ya kerewa duka sauran  parlour da ma jerin suite Lodge  din baki ɗaya,komai da komai na cikin falon so neat komai na nan  fes ƙal kamar rai bata rayuwa a ciki, ga wasu shegun glasses out ɗin  da ya ma parlour'n ƙawan ya duk inda ka gilma  sai kaga fuskarka dama jikinka baki ɗaya. Ba abinda parlour'n yake bayarwa sai wani irin ni'imtaccen ƙamshin sa daya gama kama parlour'n haɗi da kamshin air conditioner ɗin  da dama ba'a raba parlour'n dasu.... Tsaf Mahaukacin parlour'n da yafi kama da wani shahararren ɗakin taron ya laƙume saitin kujeru biyu na alfarma, banda sofa's ɗin dake cilli² tsakan kanin kuberun. Wanda iyaka  wanzuwarka cikin falon ya isa ya baka wata irin nutsuwa da kwanciyar hankali na musamman. Lallai do le ne masu kuɗi suyi girman kai domin dai kowa yaga wannan guri yasan cewar ya kere tsara ne kawai....
Wata jimirar Glass door ya nufa yana me sake amfani da hannunsa ya  tura ƙofar dake a wajen, Wani lafiyayyeyan babban bedroom ne ya bayyana  shima da komai na cikinsa creamy white ne, kai tsaye katafaren tsararrren gadon bedroom ɗin ya nufa me ƙirar Italian da yasha wani shegen lallausan beddings fari ƙall wanda har wani sky blue ² yake nunawa tsabar farin daya masa yawa sosái..... Kwance yakai daga gefen bed ɗin komai nasa na kallon sama ƙafafuwan sa kuma na a ƙasa  yana zubawa  Pop tarts lafiyayyun fararen   Idanuwansa.... A haka wani ɗan bacci yazo yay gana dashi, ba shi ne ya farka ba se wajajen sha biyu da wani abu. Dan haka a gurguje ya faɗa bathroom Yana sakar ma kan sa shower, wata fara ƙal ɗin bathrobe ya sanyo yana fitowa faka² slippers ya ziro masu taushi yana shigewa cikin clothes nashi. Sallah ya fita zuwa cikin masjed ɗin dake cikin jerin hotel's ɗin. Bayan sun idar kai tsaye Directly Neil yasa ƙira yana cewa ya same shi a living room meeting ɗin daya ware wanda ke jere da bedroom ɗin da yake ciki....
  Cikin abinda bai wuce second goma ba sega Neil ɗin ya shigowa Room ɗin yana sanye da kaya na shan iska tamkar dai me gidan nasa da yake cikin wasu outpit na Calvin Klein. Zama yay Kan kujerar dake facing data Boss ɗin nashi. Wasu yan latse latse yay tare da tura may Ipad ɗin gabansa yana me sake cewa...................
"Lallai duka bayanan yarinyar nake da ɓukata tun daga Ranar haihuwarta har zuwa matakin da take a yanzun"   ɗan zaro ido neil yayi tare da furta. "BOSS itama wannan girl ɗin Family nata nada wani irin power sosai a cikin garin nan.  Duk inda kayi kowa zancen irin ƙarfin Ikon JEDDY's FAMILY kawai ake zance... Dan Family ɗin kansa cike yake taff da  zunzurutun matasa masu kuɗi sosái daga manyan soldier' se air Force se manyan ƴan kasuwanni wanda su kansu matan cikin Family'n ba a zaune suke ba. So kaga taɓa ɗaya daga cikin su na haɗari ne Boss, bare kuma ita kanta ESHERH KALTHOOM JEDDY's ɗin, Kana a ɗan bincikar da nayi kowa na gwada cewar ita ɗin yarinyace mara hayaniya daɗi da ƙari ma samm bata da wani cikakken lafiya na ku zo a ga.....

Wani shegen  lalataccen murmushi mara ɗan sautu Sameer ɗin yayi kafin ya dafe hannuwan sa duka biyun kan dining ɗin da Neil yake Idanuwan sa har na fidda wani kalan bala'i balain jin mugun zafin maganar da Neil ɗin ya faɗi wanda yaji kamar ma harda yabon yarinyar yayi. Ɗan kawar da kanshi yayi yana kuma janyewa daga duƙen da ya kai tare da zube hannuwansa cikin aljihun long sleeve ɗin dake jikinsa yana soma zagaye room ɗin. Wani munafikin numfashi a wahale ya fesar  tare da furta...
    "Kowa yay faɗa da damisa ya duba jikinsa. Kuma ko an kashe biri, biri yay ɓarna gaba zaki baya damisa, kowa ya yunƙuro kubarshi ya doso In kaji ana hadari malafar duniya to ni ne! Kuma nasa gabana inda nake so babu me iya tare ni bare kuma tunkarana,duk kuma wanda yay yunƙurin hakan guguwar dake naɗe ƙunshe  ta naɗe mutum idan bayyi Sa'a ba ma ta baje dashi inda ko makamancin labarinsa babu mai iya ji balle gani, dan haka ka ringa gyara wasu kalaman naka Neil right and understanding?" Daga haka ya fice a ɗakin yana sake jaddada masa cewan lallai a goben yake da buƙatar sabbin bayanai dan ga ne da Esherh'n.....

Around 9:20am.
Tun da ta dawo gidan ta shige ɗakinta babu wanda ya ganta ciki kuwa harda Maah, dake can ita ma ta a jinyar kanta. Daga gaisuwa babu abinda ya sake haɗata data mutanen parlour'n dan haka abincin kawai taci ta miƙe tana barin musu wurin. Duk kuwa da cewar yadda lateeb yaso ko magana ɗaya ce suyi. Shi kuma Fawaz wani aikin ujila ne ya taso musu a headquarters nasu dake Lagos dan haka tun sassafiyar ranar yabi jirgi zuwa Lagos ɗin. Omer kuma yau basu fito ba wanda da dukkan alamu Umar iyan sa ce ta hana hakan dan yana son matarsa babu ƙarya sedai son da yake jin ya na Esherh'n ya zarce nata sau cikin masaki... Daɗi ma taji sema hamdala haɗi da godewa ALLAH da tayi, yau kawai ta tsinta kanta da son zuwa wurin mohjaddan'ta. Inda take sanye cikin wasu half ready made play gown fuscia pink colour. Me tsayi sosai da faɗi wanda ya ɗan buɗe daga saman daya bama ƙugunta damar bajewa ta ciki. Amma fa kai tsaye baka isa gane ainihin hakan ba se har in ka ƙure tane da ido......
  Babu zata babu tsammata taji an wani fisgi  hannunta ɗaya dai dai lokacin da take dap da shiga parlour'n mohjaddan'ta.........

     BY NAINERH KD and AMMEY LAYLERH ✍️☑️