8
by @nkds
❉্᭄͜͡𝘚O 𝘿𝔸𝑵☆ R̲A̳Yᑌᗯᗩ ♥️
☆♥︎L⋆o⋆v⋆e⋆ ᖴOᖇ 𐐛օv𝖊♥︎☆
𝗕Ⲩ 𝔸mmⅈ𝖊ყ ℓαуℓєян & ɴᴀɪɴᴀʀ kd♡
༆Ⴆҽʂƚ σɳ ƈɾҽαƚιʋҽ ʂƚσɾყ!!!༻
♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
Page 8
ꨄ
Baki ta buɗe da niyar fasa ihun ɗauki da neman temako taji an kuma rufe bakin shi ma tare da janta can ta baya wajen balcony na bayan ɓangaren. Suna zuwa tsaka nin mararrabar dake tsakanin balconyn da kuma second floor ɗin dake wurin ta tirje. Tsaida ta akan diga diganta yayi yana sauƙe wani ɓoyayyen numfashi har kuma lokacin hannunta na riƙe a nasa. Idanunta ta buɗe tarrr kuwa se gasu akan lateeb elmaska, Wani irin shegen ɓacin rai me taji ya mata dirar mikiya tana jin brain nata na neman ƙara sa juyewa tun da dama bawai tana a mood me daɗi ba ne. Dan haka ta wani irin Fisge hannunta idanunta na wani irin cikowa da ruwan hawayen takaicin abin da lateeb elmaska'n ke mata. Ja da baya da baya ta soma shi ma yana sake kusantota, "Ya teeb ka de na min kalan waɗan nan abubuwan da kake min domin neman soyayyata!, Domin a hakan da kake kallar so kaka ka gina kanka da fadar ka a wajena to ka sani ire iren hakan da kake min ba komai yake janyo maka se na ruguza fadar naka da kake yi. Muddin ka ce haka zakaci gaba da min to kuwa tabbas ZUCIYANA na dap da jin tsanarka ne Ya teeb!!!."
Ta kai ƙarshen maganar da ihu tana toshe kunnuwanta ta re da kaiwa ɗurƙushe a wajen tana fasa wani kalan kukan da ya sarƙafe mata ƙirji..... "I hate all my life! I hate all of you about it!!, Wllh na tsanake bazan taɓa son kaba Ya teeb, bana son ka, kuma har gaban abada bazan taɓa son ka baaa....... Shiru tayi da duk maganganun da take yaɓo mishi dan haka babu zata taji ya wani kalan fisgota ta faɗa saman jikinsa har tana jin yadda zuciyarsa ke bugu da hucin ɓacin ran baƙaƙen maganganun ta gare shi. Itama a kufulen ta sake kwace jikinta tana jin wata irin tsana me ƙarfin gaske na taso mata ga duk mutumin dake gangancin taɓa koda yatsar hannunta ce. Sake yowa kanta yay dan haka ta ja ƙafarta baya tana tirjeta tare da huna masa yatsarta manuniya tana furta.
"Stop, and dare don’t touch me, me ya sa ba zaka fita daga cikin rayuwata ba? Na ce ka rabu dani kafita daga rayuwa na ga ba ɗaya! let me be right there" ta faɗi tana juyawa zata bar wurin a guje sedai taku ɗaya tayi a na biyun ya kuma cimmata tare da sanyata a tsaƙiyarsa yana dafe hannuwansa duka biyun da jikinta da take tsaye. Kallonta yay da rinannun idanunsa da suka juye zuwa kalan ɓacin rai... Wani numfashi me zafi ya fesar tare da furta.
"I hate love some body ask me why???. Sometimes I just hate my life and all the decisions I made along the way, because that's why I'm in so much pain right now?....Am glad we will soon get married da kike faɗin hakan, bayan kin kusa zama mine and Ina son da ga yau ki dena duk kalolin wannan haukar right?"
Ya maganan ne kuma Yana neman matse jikinta da nashini. "I hate you Ya teeb!!!" Ta sake faɗi tana yin ƙasa da niyar son zamewa ta gudu. Hannuwanta biyun ya ɗago tare da miƙar dasu sama yana bin ta da wani shegen kallo. Kafin ahankali cikin wani murya ya ce da ta, "Uhm- uhm let me feel u" wani shegen haushi ne ta ji ya sake cikata har tana jin kaman ta ɗauka wuƙa ta lumamai.
Bata tsammata ba Se sake jin sauƙar kalamansa tayi tamkar daga sama yana me sake faɗin....
"My dream is to spend my life with you nice you can't imagine how much I love you sweetie, I always think of you I can't stay a minute without talking to you every day i keep holding my pillow thinking about you nice you are so precious to me! you are my half i can't be happy without you message me now I really want to spend some beautiful moment together I WILL Really love you too*ESHERH KALTHOOM* I can't live without you and I have forgotten everything about me, including her mind, nafi kowa son ki a cikin WANNAN DUNIYAR Swee flower piey.....
Yay maganan tamkar wani zararre yana janye hannuwansa daka rumfar daya mata yana nuna mata zuciyarsa tare da faɗin. "Duk wani Namijin da yay ƙoƙarin keta min iyaka da soyayyata na rantse se na ga bayansa se na kashe shi ko waye domin ke ɗin you're mine!!! Ke ta wa ce har ƙarshen abada Esherhhhh....... Sosái jikinta ya fara rawan tsoro ganin yadda yake ta dukan ƙirjinsa seti da Heart nashi a can ƙasan zuciyanta ta (Shi ke nan allurar mahaukatan ta motsa ALLAH ka kawo min ɗauki) tayi maganan da iya zuciyanta tana sake yin baya da baya har ta saɗaɗe shi ta wani irin kwasa ana kare tana shigewa ɓangaren mohjaddan'ta....
"Subhanallah ke Eaesherh wai lafiyanki kuwa kike shigo min da irin wannan gudun dalilin ki ƙarasa kassaramin ƙafafu!" Zama tayi tana sauƙe ijiyan zuciya ta re da furta. "Jaddaty na wllh tsoron hanyar kawai na ke ji!,shi ne fa nayi gudun nan" kallon ban yarda dake ba tsohuwar ta mata tare kuma da cewa. "Duk uban securities ɗin dake ba je a gidan har ki wani ce kina jin tsoro? Sannan ganan haske kamar ka yada allura ka sunkuya ka ɗauka har ma ki ce kina jin tsoro kya ma faɗi gaskiya ne yarinya" tayi maganan tana ɗaukan ruwan rowa ta shanye duka. Ta buɗe baki da niyar magana kenan ya shigo ɗakin dan haka jikinta ya soma rawa maƙud ta haɗiye maganar da tayi niyar yi ɗin tana zamewa ta kwanta tare da kwantar da kanta saman ƙafafuwan jaddah'n Tata...
Zama yayi kan Sofa yana gaida tsohuwar kallo ɗaya ta masa me tafi da harara tare da cewa. "Duk da baka zo gaida nin ba seda kaga wannan faratun na nan, to ta shi kaje bana son haisuwar nata ja'iri kawai..... Sumar kansa ya ɗan shafa yana son bama kansa nutsuwar data kwace mishi yana sauƙe ijiyar zuciya haɗi da fesar da numfashi ya na cewa. "Babu laifi hakan ma jiddoh in dan itan ma nazo sabo da I LOVE YOU MORE THAN ANYTHING'S, gaba ɗaya nake son ta da zuciya da Ruhina ina son mallakar Esherh a matsayin Matar Aure na! Pls jiddoh ki sanya baki dan ALLAH ko su daddy zasu fi yarda ayi maza² ai bikin nan ko zuciya na zata fi samar nutsuwa plsssssss" ya wani karasa maganar yana janye sautinsa sosái idanunsa na shigewa ciki.
"Kai ALLAH Rabani! Ina ni ina sanya baki ai Wllh Esherh batay kala da matar Auren da zaka aura ba, In Sha ALLAH miji zata samu me sonta tare da dangin sa dan kullum cikin roƙar mata ALLAH nake kan ya ɗauki Raina ya mata mijin nunama tsara. Tun wuri ma kwanta ka fidda rai da ita wllh lateeb uwarka bata son ta kaga kenan ba amfanin hakan. Ni ban nuna mata ƙiyayya ba amma ita take numa gudan jinina kamar kuma a koda yaushe take son muzantamin ƳA da JIKA wllh ko Ni bazan bari Esherh ta Aureka ba LATEEB.......
Ta ƙara sa maganan hawaye na wanko mata fuska domin sosái take jin babu daɗi akan duk maganganun da Mummyn lateeb ɗin ke yaɓama Mammah'n da Esherh. Ita ce mutum ta farko data fara da sama Esherh mummunan ciwon da akaron farko ya kusan tafiya da numfashin ta. Kuma dan me zata bari ɗan ta ya auri yarinyar da a kullum kwanan duniyar velinbing na rayuwarta take yi. In sha ALLAH zatyi duk iyaka bakin ƙoƙarin ta na ganin lateeb ɗin be mallaki Esherh'n ba, kai dama kowa dake cikin Family'n. Domin kuwa kowa yana da nashi matsalan akan hakan. Shi Omer Matar sa basma,shi ku ma Fawaz mahaifiyarsa, shi ɗin ma dai lateeb uwar ta shi matsalar sedai tashi matsalar tafi ta kowa yawa, domin su sauran ba koda yaushe ma suke nuna wani abu game da Esherh'n ba. Kuma ko auren ne gwanda ta auri fawaz ɗin tun da duk yafi su cikakken hankali da nutsuwar da zai dinga nesanta lefen Esherh ɗin ga mahaifiyar nashi. Kuma da can baya kafin lalacewar komai da ita Mummyn fawaz ɗin da ita Mammah'n Esherh'n ƙawayene sosái....
Kuma har kwanan gobe sukan gaisa harma da ziyartar juna kasan cewar ita Maman Fawaz ɗin ita da daddy Majeed suna Lagos ne da zama. Wanda shi ne ɗa na biyu a JEDDY's FAMILY. Wata kakkaurar Ajiyan zuciya ta sauƙe daidai lateeb ɗin na ɗagowa ya kalla jaddah'n da idanunsa da har wasu ruwa ruwan bala'i da masifa suka tara ta cikinsu. "Kika ce ba zaki bari na mallaki ƙaunata ba jaddah? Kin kuwa san babban zunubin da kika bari bakinki ya furta? To ni kuma na miki alƙawarin indai ina numfashi a cikin WANNAN DUNIYAR sena mallaki ESHERH KALTHOOM JEDDY's ko da na dare ɗaya ne koda ace na Rana ɗaya I promise you Wannan ɗin alƙawari nane jaddah ina son ki Rubuta hakan ki ajje komin........
Sauƙar marin da yaji saman lafiyayyar fuskar shi ne ya sa shi tsayawa chakkk tare da haɗiye kalamansa na ƙarshen da yay niyar faɗin....
"Idan baka da hankali toni inada hanyoyin dawo da kai kan daidai ɗin ka lateeb, wllh kafff zuriyata ba'ay tantirin da ze zo har gabana kan ido na yana faɗamin muggwan kalamai irin haka ba!ko ita uwar taka ina rabuwa da ita ne kawai domin duk abinda kama wani kai ma In Sha ALLAH se an maka. Kuma daga yau ina son ka ɓace ɓatt gaba ɗaya daga cikin rayuwar Esherh, tamkar haɗuwar hadarin kaka da kuma bajewarsa do You understand?" Jaddah'n ta faɗi tana kama hannun Esherh suka shige cikin lafiyayyen bedroom nata suna barinsa tsaye riƙe da face zuciyarsa na wani irin ƙumbura, yau da ace bason Esherh yake ba wllh da se yay gade fyaiɗe a gaban idon jaddah'n kuma ya aure tan da take ikirarin ba zata bari hakan ya faru ba in yaso ai wannan shi ne ƙarshen fita a rayuwar,In yaso in ma bugawa zuciyarta zaiyi to ya jima beyi ba sedai ta buga ta faɗi ta mutu....
A mugun ƙufule yakai ma iska naushi haɗi da wani kalar furzar da iska yana lumshe idanunsa yana sanya hannunsa cikin aljihun wandon sa ya zaro cigarettes da leiter ya na kunna wuta. Wata irin muguwar suƙa yama cigarrate's ɗin tare da wani lumshe ido yana fita a Room cikin wani mugun fusata.....
ESHERH KALTHOOM
Suna shigewa bedroom ɗin ta zame tana turƙushewa a wurin idanunta na wani kalan kaɗawa yayi ja sosai na tsananin kewar koma waye mahaifinta da take ciki. Idanunta ya kaɗa yay jajir tana son tayi kuka amma ta gaza domin ji tayi zuciyarta ta mata wani irin nauyin da ko kukan ba zata iya ɗauka. Wanda idan har batayi wannan kukan ba ciwonta da dama yake gaff da tashi na iya tashi take a wurin.... Ganin yadda jikinta a lokaci guda ya fara rawane ya sanya hankalin jaddah'n tashi tana nufarta...
Zaune takai tana kamo kafadarta zuwa kan ƙafafunta tare da kife hannuwanta biyu saman face na Esherh'n, kafin cikin muryan da yafi kama dana tashin hankali ta shiga faɗin....
"Yi kuka! Kiyi kuka ESHERH yi kuka dan ALLAH!!!. Karki bari hakan ya taɓa BRAIN naki inason kema ki ɗauka duk wani damuwanki ki ajje gefe ki ɗauka komai kamar ba komai ba ki ɗauka hakan kamar haɗuwar hadarin kakane ya haɗa,kuma ya baje ya ɓace ɓatt kamar komai ba'aiba. Karki bari abinda yake faru da Rayuwar ki yayi tasiri a ranki dahar zai yi pinning ɗinki down. FIGHT SHALELEN JADDAH'N TA fight the feeling and move on maza plsss ESH KALTHOOM JEDDY's....
Chakkk kuma ta dakata dan ganin yadda Esherh'n tayi wani kalan yunƙuri kamar zata tashi se kuma ta koma yarabbb bata ko numfashi...
Idanunta taja tana lumshewa Sakamakon wani kalan bugun da zuciyarta ya mata, wani abu me kama da ƙa shi na cake makwallaton ta. Itan ma numfashinta taji Yana neman tafiya amma taƙi bama hakan dama se ma cikin wani kalan tashin hankali ta furta.
"ESHERH!!!......
Ihun ƙiran sunan daya karaɗe ko ina da ke gidan kasancewar lokacin dare ya soma wajajen sha ɗaya ne da rabi... Dan haka sucurites ɗin dake zagaye da gidan sune suka fara isowa ɓangaren JADDAH'N. Se dai basa da iko ko izinin shigar mata bedroom dan haka sukay cirko² tsaitsaye suna ma parlour'n ƙawanya da bashi garkuwan idan ma wani abu ne me cutuwa yake a ciki ta yanda yana fitowa zasu fasa kansa...
Daddy majeed shi ne ya fara isa bedroom ɗin, kafin Abban Omer Wanda kusan tare ma suka shigo da Mammah suma suna jan turgwasuwa a inda jaddah'n ke zaune dirsham tayi zaman ƴan ɓori ga Esherh kwance a jikinta babu rai ya tafi..
Wani irin rawa ƙafafun Maah suka fara kafin tamkar kiftar ido ta koma ta fita a guje tana komawa passes nata. Only 1 minute se kata ta dawo hannunta riƙe da car key. Daidai lokacin da daddy ke mata ɗaukan jarirai kawai sukayi waje suna faɗawa cikin car ɗin da Maah tayi Parking nata dap da ƙofar parlour'n....
Da wani irin mugun speed Omer daya amshi key na car ɗin daga hannun Mammah yaja motar yana ficewa daga baki ɗaya passes ɗin jaddah'n....
Kai tsaye wasu motocin su jaddah suna faɗa suma suna rufama motar data ɗauka Esherh baya. A harabar building ɗin clinic ɗin Manyan Mercedes Benz black biyun da suka rufama motar baya ko kyakkyawan parking basuyi ba sukai saurin fitowa Babu Wanda hankalinsa ba'a tashe ba sabo da tsananin tashin hankalin dake cikin zukatansu na ganin yadda Omer ɗin ya shiga da Esherh clinic ɗin, yayinda wasu ɓoyayyun zukatan suke jin Allah yasa nesace tazo kusa Ashshe ta gaida umma bi ma'ana ta mutu ma kenan....
Mutuwar data kasance riga ce ga kowa ko kayi fata ko karka fata dole dole dolen dole dole ne kasan zaka mutu kai ma dan ba gadin duniyar za'a bar maka ba, tun dai ita mutuwar nan ɗaya ce in akayita ba'a taɓa dawowa har gaban abada abadan, don me kuma zaka ma wanin ka fatan ya mutu ɗin...
Arikice nurse's tare da doctors kusan biyar sukayo kan Esherh ɗin kawai dake kula da ita suka ƙaraso suna amsarta. Cikin gaggawa su kayi ciki da ita domin ceto numfashin ta,Wani irin yarfar da hannuwansa Omer yayi yana jingina da jikin motan tare da kulle idonsa kansa na wani irin sara masa. Tabbas yana jin cewar Esherh ita ce duniyarsa itan babu ta shima yana jin babu shi. Cikin wani irin tashin hankali likitoci da nurses ɗin asibitin suka rufa kan Esherh'n dake cikin private aminity emergency, Can kuwa waje Wani irin kuka Mammah ta fasa na tsananin tashin hankalin da Esherh'nta ke ciki Esherh'n da take jin itace Rayuwarta kuma sabo da ita ne take Rayuwa.
Jaddah kuwa wani irin rawa Jikinta yake ganin yadda jikinta ke rawane ya sanya manyan zaratan yaranta maza kewayeta daddy majeed na riƙo hannunta cikin nashi ya matse da ƙarfin daya sanya jaddah'n ɗagowa.
Idanunta da suka jaaaa ta zubama yaran nata kafin cikin wani kalan mugun tausayin Maah ɗin data kanta ita kaɗai ta turƙushe babu kowa wurinta. Dan haka ta sanya left hand nata tana janye hannun daddyn cikin nata tare da nufar Maah ɗin. Hannunta ta kama tana ɗamkewa a nata wanda kai tsaye koba a faɗa wa mahh ɗin ba tasan wannan ɗin ɗumin hannun mahaifiyar ta ne. Hakan ya sanyata faɗawa jikinta tana me sake fashewa da wani irin cunkushashshen kukan da tun farko yaƙi zuwar mata me ciwo da ƙona zuciya se yanzun...
"Jaddah ki ce mata kada ta tafi ta barni ita ma, karta rabu dani kamar yanda mahaifin ta ya rabu dani. Ku ce mata zanci gaba da kulawa da ita da bata kariyar da duk ta rasa tmtsayin rayuwarta.jaddah idan bata tashi ba nima bazan tashi ba mutuwa zanyi mu duka mu huta da wannan 𝘿𝙐𝙉𝙄𝙔𝘼𝙍! 𝙈𝙚 𝙘𝙞𝙠𝙚 𝙙𝑎 𝙩𝑎𝙧𝙞𝙣 ƙ𝑎𝙡𝙪𝙗𝑎𝙡𝙚....... Kuka take sosái jikin mahaifiyar nata kukan da yake fitowa tun daga hasalin zuciya da Ruhinta,kukan da duk wanda zaiji to kuwa Tabbas dole ze tausayawa me yin sane. Wani irin kuka ne me karya zuciya da ƙonewa...
Isowar Doctor NAINERH ne tana ƙarasowa harabar inda duk suke tsaye babu wanda ya iya ko zama a cikinsu ne ya sanya jikin kowa sake yin sanyi. kallon Mammah'n dake jikin jaddah tayi sai kuma ta ɗan saki ijiyan zuciya tare da faɗin.
"Sorry ma'am you have to wait here and please calm your self IN SHA ALLAH she'll be fine we'll do our all best just pray for her! And dan ALLAH ma'am ki dena mata kuka adda'an ki ita ne abu na farko da Esherh zata fara bukata First!"
Tana faɗin hakan ta juya ta shige tana ɗauke guntuwar kwallar data tarummata tare da wasu nurses biyu da suka zo shigewa da gudu suma zuwa emagency room ɗin da Esherh'n ke ciki. Baya Maah dake jikin jaddah tayi cikin tsananin tashin hankalin daya sake riskarta tare da fashewa da wani sabon kukan ganin yadda likitoci ke gudu suna shiga ɗakin da Esherh'nta take. Daddy dake gefen su ne yayi saurin taro su su duka biyun kafin cikin ƙarfin hali ya buɗe bakinsa daƙyar shima yasamu iya furta ma Mammah'n cewa.
"Please Mommah ESH ki dena kuka only just pray for her kinji and kiyi ta mata du'a kuka baya taɓa maganin damuwa okay?"
Wani sabon kukan ta sake saki tare da rintse ido tana me furta.
"Yaya majeed na gaji! Wllh na gaji da Wannan rayuwar, na gaji da ganin Rayuwar Sweetie Kullum cikin mugun haɗari. Zuciya na! Ina jin zuciyata tamkar zata buga ne ko kuma ta faso ƙirjina ta fito ta dena aikinta kowa ma ya huta yaya.......
Saurin rufe mata baki majeed ɗin yayi da sauri yana kallonta da idanuwansa da suka kaɗa sukai jajir tsabar tashin hankalin da suke ciki ga wani mugun bugu da wani irin sanyin da yaji yana ratsa masa har cikin jikinsa. Shi kaɗai a cikin zuciyarsa yake furta ALLAH yasa wannan karon Mummyn lateeb bata da hannu cikin tashin jinyar Esherh'n.
Juyawa Maah tayi ahankali ta kalla gefenta daidai isowar wata nurse ɗin daban a arikice ko gani sosai batayi tsabar tashin hankali tana isowa ta tsaya cak tare dabin kowa na wurin da jajayen idonta.
Kallo ɗaya dr Nainerh tayiwa Maah ta ɗauke kanta wani hawayen da batasan sanda suka tarun mata ba na cika jajayen idanuwanta itama, domin itama a yanzun tazama tamkar family na JEDDY's ne duk wani harkan lafiyansu na rataye ne a wuyanta. Irin kallon da Maah taga Nainerh ta mata da yanda ƙwalla ta cika idinta ne yasa nan take taji gwiwowinta sun gaza ɗaukarta ta zame daga jikin jaddah ta na zubewa kan gwiwowinta tare da rufe fuskarta da tafukan hannayenta wasu balaƴay'un hawaye na tsinke mata masu zafi da ciwo... Ɗauke kanta jadda tayi daga kallon Maah ɗin tayi ganin halinda da take ciki zuciyarta na ƙara sa yin nauyi sosae itama. Har hawayen da take ta ƙoƙarin dannewa na neman gangaro mata daidai loƙacin da ta ɗago kanta tana ɗora idanuwanta kan Mah.
Kafin Ahankali idanuwanta suci gaba da sauƙa kan duka mutanen da suke tsaye cirko cirko har Idonta yakai karshen kan LATEEB dake tsaye hannuwansa goye da bayansa sai kaiwa da komawa yake ya haɗa wata uwar zuba ta tashin hankali....
"I'm so sorry ma'am! Munyi duk wani ƙoƙarin mu na ganin koda numfashin ta ne ya dawo se dai hakan is to late ALLAH be nufa ba, yanzu haka numfashin ta na a matakine na 0:015 wanda muka ƙara sa bugar da shi domin gudun shima kada ya gudu!.....
Se kuma ta dakata domin wannan kalmar ta nemar wannan kwararren likitan masanin cutar numfashin shi ne kusan karo na biyar kenan da suke ta fafutukar neman ko ganin sun sama koda sunan shi ne.... A mugun hankali Maganar ta na rarrabe wa ta sake furta....
"A...aaaa....wan..nan... Ka...karon... dole ne.. muna da buƙatar sa!!! Mu na da buƙatar taimakon sa.....domin babu wanda ze iya ceto rayuwarta In ba....shi...ba!"
Rinannun idanunta Maah ta ɗago tana sauƙewa akan Nainerh dr tare da fara magana cikin muryanta da itama yake numshin ke gab da barinta ta ce.....
"Ko a wacce duniya yake, ko nawa zan kashe! Ko da kuwa ace katafanin dukiyana zata ƙare kafff ban damu ba indai za'a samo likitan!! To kuwa ban damu ba kai ciki harda rasa tawa rayuwar Lallai nan da 24 ina bukatar ganin wannan likitan gabana ko da kuwa se kai ga ɗurkusa masa ne zanyi in dai har a wannan karon ze ceto min Rayuwa da Numfashin bugun zuciyata ban damu ba maza a baza nemansa ko da kuwa yana a birnin sin ne lallai akwai buƙatar ya bayyana a wannan karon kamm............
Cikin son bama Maah ɗin hope ta buɗe bakinta tare da cewa.
"Sunan sa *SAMEER OTHMAN KAMPALA's, samm ba mazaunin Nigeria bane aikinsa kawai yawon zaga duniya ne, kuma shi ne wannan shahararren MONSTER ɗin ɗan kasuwar da ambatar sunan sa kawai kan haukata zuciyoyin maƙiyansa THE Billionaire Sameer othman kamfala's, se dai bana da tabbacin yanzun haka yana ko yana a wacce duniyar neee....
Kanta Maah ta riƙe sunan na mata kama da wani wasu data taɓa ji kota taɓa gani, sunan da bata ƙara jin koda kalan sa bane se a Ranar da Eemaan Sufyan ta ambaceshi.... Wannan tunanin datay ya sanya brain nata fara loosing itama take dan haka tayi baya luuuuuu....................
BY NAINERH KD and AMMEY LAYLERH ✍️☑️💪
Via phone Only WhatsApp
***
***