JIRWAYE

CHAPTER 12

by @deejasmah

JIRWAYE

Khadeejah Bint Ismail

Young talented writers association (YOTA)

In dedication to women in tech 💻

***

Wattpad: Deejasmah15

Arewabooks: Deejasmah

Tiktok: Deejasmah_writer

CHAPTER 12

DevFest na daɗa matsowa su Adeeyah ba zama sai shiri suke yi, ta gefen EMA ma dai ya amsa invitation ɗin su fisa tursasawar Snake don da ya so ya fasa su sake wani plan ɗin amma sai ya nuna masa za'a iya dacewa fiye ma da tunanin shi sai kawai ya yarje ya amince ba don yana so ba sai don ba a ƙin ta mutane wai an ce da ɓarawo ya gudu.

Sun saka shi cikin list É—in guest inda Æ´an team sai da suka yi magana kan shi don ba wai sun waye shi ba, amma a yanda ta musu bayanin abubuwan da yake yi da kuma yanda ya yi tagging Decembern shi as '' Let's make impact:giving back to the society'' wato dai ya shirya amfanar da al'ummar Kaduna daga abinda ya sani shi yasa take son su yi seizing opportunityn ya fara da su. Ai ko a take suka gamsu don sun san in dai har ya zo taron to tabbas za suyi kere a tsakiyar sa'annin su da ke wasu state É—in, DevFest na Kaduna sai ya zama abu na nunawa sa'a.

(Taron DevFest taro ne da ƙungiyar Google developers suke shiryawa a kowacce shekara, wacce kusan kowani state ana yi su kan gayyaci masana na'ura da yanar gizo don su shayar da al'umma ilimi a kuma haɗu ai networking a ƙulla alaƙa ta yau da kullum. Kuma kowani state burin su na su yafi na ƴan uwan shi so suna ganin dama ne suka samu wajen cin ma haka)

Kamar yanda ya faɗi a ran da kwana na ukun ya shiga 26th November na shekarar ya shigo ƙasar-a cewar shi kenan fa-hotuna masu yawa yayi a airport yayi posting a duk kafafen sada zumunta kama daga Facebook, X, IG da ma LinkedIn. Duka kuma sai da Adeeyah da ƴan team ɗin ta suka gani don yanzu sun dawo following ɗin shi sosai, sai dai ko shi bai sani ba don ba da official account ɗin ta take bin shi ba da na DevFest ɗin ne take amfani so ko da ya Scor ya duba bai gani ba tsaki ya kuma yi yana tsine mata a ƙasan zuciya.

Sai dai kamar yanda suka tsara haɗuwar EMA da TK sun ko haɗun on 24th a Boston a wani bar, sun tattauna sosai akan neman scorpion sai dai ya nuna masa zai je break gida zuwa jibi amma kuma ko yana daga can zai masa aiki. Jin ya ce zai je gida ya sanya shi tado da maganar yarinyar da aka gaya masa ita ta jaza masa masifa, jin sunan da ya kira ya sanya shi cewa ai shi ma ya san sunan don zai yi aiki da su a Kaduna in ya shigo. Bai nuna masa mamakin da yayi a waya ba sai ma cewa da yayi ya bincika masa ita wacece har ma da hotunan ta idan da dama ya tabbatar da ko itace ko kuma raina masa hankali ake yi, a gaban shi ya rubuta a plannern shi ya kuma tabbatar masa da zai yi duk abinda yace. Ya ji daɗi sosai don tunda tsautsayi ya haɗa shi da Scorpion bai ƙara samun natsuwa ba don duk wanda zai ba aiki a kan shi nuna masa yake yi ba zai iya ba don suna gudun taɓowa kan su matsala.

Ya na fita ya shiga rental car ɗin da ya tuƙo daga airport zuwa nan, wata farar envelope ya tarar akan dashboard tun kafin ya buɗe ya ga ƙatuwar tambarin kunama kan ta a take ƙirjin shi yayi mugun bugawa don ya san ba Alkhairi zai gani ba yana buɗewa ko ya ƙaramar note ne inda yake cewa '' You really ain't not gonna give a break about all this thing right? I won't warn or threat you but you ain't gonna like what you are getting yourself into SS 🦂'''.

A ruɗe ya fara kallon gefen shi sai dai babu kowa a underground packing lot ɗin sai shi ɗaya, ƙara duba takardar yayi yana mai jin tsoro a yau dai ya tabbatar mutumin nan ba mutum ba ne aljani ne in ba haka ba ya za'a yi ya kuma biyo shi Boston bayan daga inda yake zaune zuwa nan ɗin ba wai tafiya ƙarama ba ce ba. Tsayawa yayi cak da ƙarfi yake tambayar '' to a'ina ma yake da zama ne?'' tambayar dai ba ta da wani amfani tunda dai bai san ta ina zai fara neman inda yake ba abu ɗaya ne ya tabbatar a yau yana ƙarƙashin monitoring ɗin Scorpion kar fa yana zaune ya masa cinne wa FBI ya shiga uku ya lalace, kai ya girgiza yanzu ma da ƙarfi ya kuma furta '' No I'm not going down alone, we'd go down together!!".

Daga haka ya ja motar don barin wurin, duk abinda yake yi yana tsaye a rooftop ɗin barn yana kallon shi. Dariyar yanda ya ruɗen yayi a ƙasan maƙoshin shi ya furta '' wai wannan ne yake cewa zai ga bayana, ai ko bacci nake yi bai isa ba''. Ya ƙarashe yana cire mask ɗin fuskar shi wacce ita ce personan EMA yanzu haka ma an riga da an aikawa Sna ita don ya fara operation ɗin shi. Saukowa yayi shi ma ya shige ubern da ya kira wacce ta kai shi airport don komawa inda ya fito, ya gama aikin yau kuma sai wani jiƙon.

A zahiri dai ya shigo Kadunan daga Abuja har ma ya shirya wani tour a southern Kaduna na bin makarantu akan muhimmancin technology a rayuwar yau da kullum, wanda ba shi ya jagoranci hakan na wani ya samu a can wajen a Birnin Gwari ya haÉ—a da aikin wanda ya ji daÉ—i sosai don sun saki kuÉ—i. Hakan ya sa within one week da shigowar ta shi sai da social media ta É—in ke da maganar shi don sosai ake ta tattaunata a kowani shafi.

Bai tsaya iya nan ba saboda iya cusa kai sai ga shi yayi posting flyern Festival É—in yana gayyatar mutanen shi da su yi RSVP, ai ko sun yi registration kamar me hakan ya sa suka kuma jin tabbas ASH ba tayi mistake ba wajen gayyatar ta shi.

Ranar taron kam tun 8:30 aka fara check in, hakan yayi musu daɗi don sun san wannan karon ba African time tunda participants sun fara zuwa. Ita dai tana ciki sanye da kayanta na dindindin yau wata army green ɗin gown aka samu ta wani cashmere mara ƙyalli. Buɗaɗɗiya ce sosai ta sanya ash ɗin veil ta yi rolling da shi, da crocs ɗin ta na gado tana zaune ta gaba ta inda guests suke tana wa Ushern da zata kula da isowar guests bayanin yanda za ta shigo da su.

Cikin ƙanƙanin lokaci ko suka fara isowa wajen taron yanda aka tsara haka aka yi ƴan registration point ne suke fara ba su tag ɗin su suna shiga kuma ushers su yi directing ɗin su zuwa already reserved seats inda Adeeyah take tsaye. A tsakiyar isowar su EMA ya shigo wurin a registration point ya fara tsayawa, ya na zuwa check-in ne su oga Murtala suna isowa tashin farko suka gane shi nan tundaga nan ya fara samun treatment ɗin da ya kamata ai ko fuskar shi ta faɗada da fara'a su ka ba shi tag da soveniers ɗin shi kamar yanda yake a al'adance. Aunty Sumaiyah ce ta raka shi zuwa ciki ba wai usher ba, suna tafe tana ƙoƙarin engaging ɗin shi into conversations ba kuma laifi yana amsawa don Snake akwai good communication skills.

A haka har suka ƙaraso inda Dee take zaune ce masa ta yi '' and here's our guest management officer Adeeyah Shamaki''.

Zaro idanun shi yayi ya gaza ɓoye mamakin shi don bai yi zaton ganinta haka ba yarinya, ya zaci wata ƙatuwar mace za'a nuna masa. Kallon shi suka tsaya suna yi su biyun ganin haka ya sanya shi ɗan fuskewa yana cewa '' so this is ASH witchie? I've been looking forward to meeting you I'm Edward Micah Akoka'' ya ƙarashe yana miƙa mata hannun shi.

ÆŠan waving É—in shi ta yi don ba ta gaisawa da maza tace '' nice to meet you Mr. Edward''.

''You can call me EMA''.

''Ohh yeah EMA, I've been looking forward to meeting you too''.

''The pleasure is actually mine'' ya amsa da murmushi a kan fuskarshi wanda yake har zuciyarsa don sosai yarinyar ta ba shi mamaki ainun, ganin ba ta ita ake yi ba ya sanya Aunty Sumaiyah juyawa ta tafi ta bar su a wajen.

Seat ta nuna masa ya zauna yana fara jan ta da hira, sakewa tayi tana amsa masa musamman da ba wani labaran duniya yake mata ba a kan abinda ta fi ƙwarewa a kai ne. Cikin sanin kai take jan hirar wacce take sake fito da zallar kwarewar ta har sai da ya kai ga tambayarta hala PHd take yi ko? Dariya ta saki tana cewa '' I'm just an undergrad 200l going to 3''.

''I can't believe this, ki dai ce min wasa kike yi?" Ya furta da Hausar shi irin ta Æ´an southern Kaduna mix with American accent.

Kai ta girgiza tana mai cewa '' i mean it, you can ask around''.

Kai ya gyaÉ—a a ran shi yana cewa '' ashe ko Scor yau zai yi bala'i, ashe ma yarinyar duka ba ta da ko BSc shi ne har ta watsa masa aiki har haka lallai akwai talent a Nigeria sani ne kawai ba a yi ba''.

Kuma jan ta yayi deep cikin hirar inda take kuma gaya masa ai tayi classes ne kuma tun tana JSS 3 ta fara designing web, tambayar ta a wani Centre ta fara training tace masa '' Ihifix'' don a lokacin suna ƙasan Jabi Road kafin su koma inda suke yanzu. Kai ya gyaɗa don ya san su waye ƴan Ihifix ɗin Mr. Emma ya gina makarantar ya kuma baza ƙwararrun ma'aikata. Kiran Ridh ne ya shigo wayarta excusing kanta tayi ta fita waje don amsawa ba su wani daɗe ba don zai zo ne yake shaida mata da ya fito gida, ce masa tayi sai ya ƙaraso ta yanke wayar sai ma ba ta koma ciki ba don ta san nan da ƴan mintuna zai iya ƙarasowa tunda a Lamido crescent suke tsakanin nan da Arewahouse ko ba wani tafiya bane mai tsayi da ya fito daga Yakubu Avenue zai shiga ta Ahman pategi ya ɓullo ta Maska road daga nan ko minti biyu ya masa yawa ya iso ko kuma ya bi ta kan Isa Kaita ko kawai ya miƙo mafi sauƙin hanya ta kan titin coronation crescent ya bi ta luggard roundabout ya hau Ali Akilu.

Nan wurin su Aunty Sumaiyah ta zauna suna hira kan turnout ɗin da suka samu inda oga Murtala yake cewa yanzu ma zasu fara kawai tunda most of the guest sun halarta. Tana nan ko a wurin sai ga shi ya iso parking ya gyara ta tafi ta tarbo shi, ita ta masa komai kafin suka doshi hall ɗin. Sanda suka shiga samu tayi har Madalene Tanko ( shugaban women in tech na Kaduna South) ta zauna a inda ta tashi, gaisawa suka yi ta zauna a gefen ta Rhid kuma daga edge. Kallon gefen idanu Snake ya musu yana mamakin shi kuma waye, sai dai daga yanda suke magana ma ya gane akwai sanayya da shaƙuwa mai yawa a tsakanin su. Tail ne yayi beeping ɗin shi ya tashi ya fita a can gaban hall ɗin suka tsaya da shi yana ba shi labarin ƴar survey ɗin da ya saka shi inda ya shaida masa akwai mai bibiyar yarinyar don ya ga wani ya mata pictures da ta fito a ɓoye da ta shiga kuma ya bita ciki, hoton mutumin ya nuna masa kallon shi yayi yana cewa '' might be another trouble ɗin da ta kuma saka kan ta a ciki, well aikin su daban namu daban let's just focus on it shi wancan na DIAn ya iso ne?".

''Nope but soon zaka iya ganin shi''.

''Alright ka jira shi idan ya iso ku shiga tare,try to get as much information from him a zaman ku musamman kan yarinyar ''.

''Ok'' ya amsa juyawa yayi ya shige shi kuma Tail ya bishi da idanu bai san meyasa ya damu da lamarin yarinyar ba, ya san ta masa laifi amma kuma ai bai kai duk wainnan wahalhalun da yake yi kan ta ba. Abinda zasu iya yin duk abinda suka ga dama with just a snap of a finger amma yana bin the oldest way na bin mutum,yanzu fa an daina wahalar da kai komai kana zaune within the comfort of your home zaka yi komai a matsayin su na masu amfani da na'ura sun san haka kai ba ma su ba har mutanen da ba su san komai akai ba sun shigo gari bai ga amfanin maida su baya ba.

Taya ni gani dai makaho ya so tsegumi.

Deejasmah 🦂