HASKEN CIKIN DUHU

CHAPTER 07

by @nanameera08

HASKEN CIKIN DUHU

Chapter 07:  Endless Trials

Nanameera, YOTA/023.

Washegari wajejen ƙarfe 10:30am Salma na zaune kan kujera a tsakar gidansu tana ƙullin zoɓo Umma ta fito daga ɗakin, daga inda take ta kalleta ta ce“Amma dai kina ganin yanda garin nan yake ko Salama? Ba zaki yi da jiki ba ki gama ki zo ki shige” Salma wadda zuciyarta ke wani gurin ta ɗago ta kalleta, a sanyaye ta ce“Umma daman cewa nayi ko zan je makaranta naga abin da ake yi” riƙe haɓa Umma ta yi ta ce“Au ashe daman baki cire maganar wannan gantalalliyar makarantar daga zuciyarki ba? To sai kin dawo tunda kyauta zasu miki karatun, shi kansa uban naki daya ɗoraki akan wannan turbar ya haƙura ya saki tunda dai bashida yanda zai yi, dangin naci da gaddama” ta ƙare maganar tana zabga mata uwar harara. Sunkuyar da kai Salma tayi hawaye ya shiga sakkowa kan fuskarta, daka mata tsawa Umma ta yi tana cewa

“Zakiyi ki gama ki tashi anan gurin ko sai ranki ya ɓaci”

Goge hawayen nata tayi ta cigaba da ƙulla zoɓon. Tsaki Umma ta yi ta koma ɗaki tana faman sababi, Malam Habu dake zaune kan tabarma yana sauraren duk abin da ke faruwa ya kalleta amma bai ce komai ba. Zama tayi ɗan nesa dashi tana cewa“Haba yarinya kamar mayya idan ta kama abu, wannan makarantar ko ta uwarta ce sai haka”

“Rahmatu!”

Abba ya kira sunanta cikin ɗaga murya. Kallonsa ta yi ya ce“Kiyi duk abin da zaki yi amma karki sake taɓo mahaifiyarta, domin bata duniyar” a fusace ta ce“Au ashe? Sai kace min kishin matacciyar matarka kake, tsintacciya matarka” tuni jijiyoyin kansa suka mimmiƙe idanunsa ya yi wani irin kaɗawa ya kalleta ya ce“Ki iya bakinki, domin wannan furucin naki zai iya kai ki ga halakar da baki taɓa tsammani ba!” ganin yanda ya yi maganar in a serious tone ya sanya Umma Rahmatu yin shiru. Tashi ta yi ta fice daga ɗakin a fusace, tsaye ta samu Salma ta jingina da bangon ɗakin hawaye sai shatata yake akan kuncinta. Umma ta ce“Kin bar wajen nan kin je kin shirya ko dai ranki ya ɓaci?” Salma wadda ta tsaya tana jiran fitowarta ta shige ɗakinta. Wata doguwar rigar yadi ta saka dan daman tuni tayi wanka, ta sanya hijabi ruwan ƙasa wanda ya tsaya iya gwuiwarta, fuskarta ta fito sosai cikin hijabin. Goge idanunta ta sake yi sannan ta fito daga ɗakin kai tsaye ta nufi inda coolern lemon nata yake, daidai nan kuma yaron dake ɗaukar mata lemon ya shigo. Ɗauka ya yi sannan tabi bayansa suka fita daga gidan, Umma ta bita da harara.

Tafiya suke amma idanunta a rufe dan kuka take, sai da suka zo bakin titi sannan ta buɗe idanunta tana goge hawayen daya gama ɓata mata fuska. Tsaye yake jikin motarsa Accord yana sanye da wasu sport wear blue ƙafarsa sanye da sneaker black sai safar ƙafa fara, daga ganinsa kasan daga wani wajen yake. Ganin tana goge hawaye ya sanya shi tsallako titin ya zo gabanta, Salma ta kalleshi a lokacin da take ƙoƙarin sake rufe fuskarta,

“Hi dear”

Shiru yaji tayi masa ya sake maimatawa kuma bata amsa ba, girgiza kansa ya yi ya ce“Ayyah meya faru? Me aka yi miki?”

“Babu komai”

Tafaɗa tana yin gaba, da idanu kawai Al-ameen ya bita har ta tsallaka titin ta nufi hanyar Orange market ɗin. Numfasawa ya yi sannan ya koma inda motarsa take ya shiga kai tsaye kuma hanyar gida ya nufa.

Maitama, Abuja.

Turo ƙofar ɗakin tayi ta shigo, zaune yake kan sofa idanunsa kan system ɗin gabansa yana dannawa cike da nutsuwa. Sanye take da wata Abaya maroon colour ta ɗaure kanta da veil ɗin Abayar. Fuskarta fresh babu kwalliya sai lip gloss data sanya. Zama tayi kan kujera tana kallonsa ta ce“Yau ba zaka fita aiki ba?” yana cigaba da danna system ɗin ya ce“Uhn, ba zan je ba, akwai inda zan je ne” shiru tayi can kuma ta ce“Anjima around 2 inason zan fita, akwai wani get together da zamu yi da old friends ɗina” rufe system ɗin Farooq ya yi ya ɗago yana kallonta, murmushi taga ya yi ya ce“Alright Allah ya kaimu” “Ameen” Nimrah Said, sai kuma tafara danna wayarta. Shiru parlon ya ɗauka na wasu mintuna kafin Farooq ya ce

“Nimrah”

“Na'am”

“Inason magana dake, ki ajiye wayar hannunki” ɗago dara daran idanunta ta yi ta kalleshi sai kuma ta ce“But I'm hearing you ai”  Farooq ya ce“Eh nasani, amma inason ki bani hankalinki ne ba wai kawai ki saurareni ba” Tayi shiru sai kuma ta ce“Okay then, Ina ji” ta ajiye wayar akan table. Numfasawa Farooq ya yi kafin calmly ya ce“Kinsan dai irin abubuwan dake faruwa a cikin gidan nan, ba sai na tsaya ina sake faɗa ba. Duk da daman zaman aure ya gaji haka, amma abubuwan yanzu they're getting worth, I can't endure it, saboda haka na yanke shawarar na ƙara aura, kinga kema kya samu lokacin kanki kuma na daina shiga rayuwarki kamar yanda ki ke yawan faɗi. So that's it, in sha Allah nan bada nisa ban zan sake aure”

Tsaye yaga Nimrah akansa, tana yi masa wani irin shegen kallo, ta girgiza kanta tana dariya kuma tana cije baki at the same time. Tafa hannayenta ta yi sai kuma ta ce a fusace

“Aure! Aure? Aure kake cemin zaka yi Farooq? Kana ganin har ka isa kayi aure? Ni zaka ƙarama kishiya. Na rantse da girman Allah baka isaba. Kayi kaɗan Farooq kai ɗin banza, wlh baka isa kayi aure ba as far as Ina numfashi. To kai awa kuma? Wato ka mayar da Nimrah yar iska wadda batasan me take ba, sai na bari kayi aure. Hmmmm...!” Nimrah ta ƙare maganar tana wani irin huci, Farooq kuwa kallonta yake da mamaki dan bai yi tunanin haka daga gareta ba. Zagaye ɗakin ta shiga yi tana gyaɗa kai tana sauke numfashi. Can kuma ta sake dawowa gabansa a fusace ta ce

“Kai wlh ma kayi kaɗan kazo gabana kana faɗamin zaka ƙara aure. Wlh Farooq ka gama samun farin ciki a gidan nan, sai na tayar maka da hankalin da baka taɓa tsammani ni, I'll make u regret what you have said now” Daga haka tayi hanyar fita daga ɗakin, sai kuma ta dawo, dube dube ta shiga yi amma bata samu komai ba, idanunta ya kai kan system ɗinsa dake ajiye kan kujera. Wawurarta tayi ta buga da ƙasa tana wari irin huci, tashi tsaye Farooq ya yi yana bin ta da wani irin kallo. Ganin ta nufi hanyar kitchen ya sanya ya bita da sauri kafin ta shiga ya sha gabanta.

“Ka matsa min hanya na shige ko kuma nayi maka abin da ba zaka taɓa mantawa dani ba” girgiza kai Farooq ya yi ya jawota jikinsa yana faɗin

“Nimrah are you okay?”

Ture shi tayi tana masa wani irin kallo idanunta har rufewa yake ta ce“are you asking me? To ban sani ba! Nace ban sani ba Farooq! Kuma na rantse sai na zame maka masifar da bazaka iya da ita ba, sai na zame maka duhun da zaka gagara gano haske. Sai na balbala maka wutar masifa acikin gidan nan. Kuma zaka gani” ta ƙare maganar tana nuna shi da yatsa, kafin ta juya ta fice daga ɗakin kamar zata tashi zama. Furzar da numfashi Farooq ya yi dan koda wasa bai yi tunanin haka daga gareta. Me hakan ke nufi? Kenan tana sonsa? Ya girgiza kansa lokaci guda a fili kuma ya ce

“Impossible”

Nimrah na fita ɗakinta ta shiga, car key kawai ta ɗauka ta juya tayi waje. A corridor suka kusa cin karo, ta zabga masa wata uwar harara sannan tayi hanyar fita daga parlon. Da idanu kawai ya bita ganin ko mayafi bata ɗauka ba, Allah ne kaɗai yasan inda ta nufa yanzu.


Abacha road, Mararaba.
12:24pm

Tsaye take a parlon tana sanye da wata rigar atampa ɗinkin doguwar riga, ta ɗora veil wanda ya yi matching da atampar a kafaɗarta. Ƙarasowa wajen Fatiha tayi tana kallonta “I'm gonna to miss you sis” rungumeta Nayla ta yi tana faɗin “Same to me. Yaushe zaki zo Abuja?” waro idanu Fatiha tayi ta ce“Gidanku securities sun yi yawa, duk inda ka gilma sai kaga soja” harararta Nayla ta yi tana murmushi ta ce“To ai babu abin da zasu maki, Ni dai ki saka rana ki zo sai kiyi mana ko 2weeks ne” taɓe baki Fatiha tayi ta ce“Naji, amma sai dai idan zaki zauna anan kema kiyi 2weeks ɗin” Ta langwaɓar da kai tana faɗin “Yaya ne ba zai barni ba, beside ma inada lecture yau kin ga nayi missing” jinjina kai Fatiha tayi daidai nan suka sakko daga upstairs ɗin. Sanye yake wasu ƙananun kaya, t-shirt fara sai trouser blue colour, ya yi kyau abinsa. Mami na murmushi ta ce“Fatan dai kaji abin da nafaɗa maka?” jinjina kai Zayyad ya yi ya ce“Naji Mami, kuma in sha Allah zan yi. Sai mun sake zuwa” taɓe baki Mami tayi tana faɗin “Till next year kenan” girgiza kai ya yi yana murmushi ya ce“A'a Mami, in sha Allah zuwa next week ma zaki iya ganina” “Allah yasa” ta ce tana maida idanunta kan Nayla.

“Auta sai yaushe kuma?” Nayla da idanunta ya fara kawo kwalla ta tawo da sauri ta shige jikin Mami tana sakin kuka, shafa kanta tayi tana cewa“Ya isa, zan zo da kaina har Abuja na ɗaukoki, daina kukan” ta ƙarashe maganar tana goge mata hawayen. Zayyad taɓe baki ya yi ya ce“Idan taɓarar zaki cigaba dayi zan kama gabana” tura baki tayi tana sakin hannun Mami ta ce“Zan yi missing naki Mamina” jan kumatunta tayi ta ce“Nima haka Auta” daga haka ta kalli Zayyad ta ce“Yaya mu je to” gaba ya yi Ahmad yabi bayansa, ta riƙo hannun Fatiha wadda taja gefe tana hawaye ta ce“Muje ki rakani sis” daga haka suka yi hanyar fita daga parlon. Kuka sosai Fatiha tayi ganin da gaske tafiya Nayla zata yi, kai kace ta shekara ne a gidan, Itama Naylan sai faman koke-koken take. Tsaki Zayyad ya yi ya shiga motarsa ba tare da ya cewa kowa komai ba suka ga ya tashi motar, da wani irin Speed ya bar gidan dan daman mai gadi ya daɗe da buɗe ƙofar. A tare duk suka kalli inda ya bari, Ahmad daya san hali ya yi murmushi ya ce“Yayi tafiyarsa kin san baya jira” goge hawayen Nayla tayi tana kallon Mami ta ce“To yanzu wane zai kai ni gida Mami?” Fatiha ta ce da sauri“Sai ki sake kwana abin ki, idan ya so ranar Saturday sai Yaya Ahmad ya tafi dake” shiru Nayla tayi, tanason ta sake kwana amma kuma tana gudun faɗan Daddy, domin idan har ya ji bata je school ba for the whole week sai ranta ya ɓaci” langwaɓar da kai tayi Mami ta ce“A'a ki bari ranar Friday banida aiki dayawa a office idan nadawo sai na kai ki da kaina” Gyaɗa kai Nayla tayi, Fatiha ta ja hannunta tana faɗin “Muje ciki” . Da idanu kawai Mami ta bisu tana murmushi, ta kalli Ahmad ta ce“Wai ina Al-ameen tun safe daya fita ban ganshi ba”

“Maybe ya tsaya wani wajen, amma bai dawo ba” Girgiza kai ta yi ta ce“Allah ya shirya” Ameen Ahmad ya ce sannan ya yi hanyar entrance ɗin gidan.

Tafiya yake yana tsaki shi kaɗai, gabaɗaya traffic ɗin Mararaba ɓata masa rai yake. Ganin babu alamar sauƙin abun ya sanya ya ɗauki hanyar orange market kawai ya bi ta cikin kasuwa. Tafiya mintuna biyar ya yi cikin kasuwar nan ma ya tarar da wani traffic ɗin, Dukan sitiyarin motar ya yi yana faɗin

“Oh god!”

Jingina ya yi da kujerar motar yana kallon yanda titin yake a haɗe. Gajiya ya yi da zama a motar ya zaro kwalin cigarette ya zari guda ɗaya. Ya kunna da lighter ya fara busar da hayaƙi, nan da nan motar ta cika da hayaƙin tabar. Zuge glass ɗin motar ya yi ta inda hayaƙin zai samu damar fita, kamar an ce ya ɗago suka yi ido biyu da ita, tana zaune kan benci ta zuba uban tagumi, sake kallonta ya yi sai kuma ya ɗauke kansa ya cigaba da zuƙar tabar hannunsa. Salma kuwa girgiza kai tayi, aranta tana tunanin wannan wane irin mutum ne. Sai da ya shanye tsinke biyu sannan ya bari haka, ya feshe motar da air freshener nan da nan ta ɗauke ƙamshi kamar ba ita ce wadda ke warin taba ba. Mouth listener ya ɗauka ya feshe bakinsa ƙamshi mai daɗe ya game ko'ina. Ganin kamar ba zai samu tafiya ba har wajen ƙarfe 1 na rana ya sanya ya buɗe motar ya fito. Cikin tafiyarsa ta izza ya ƙarasa gabanta hannayensa zube cikin aljihun trouser ɗin jikinsa, kamar ba zai magana ba sai kuma ya ce

“Ina zan iya samun eatery nan?”

Ɗago dara daran idanunta ta yi ta kalleshi sai kuma ta ɗauke idanun ta ce“Nima ban sani ba, babu ma” Kallonta kawai Zayyad ya yi can kuma ya ce“Duk cikin kasuwar nan babu inda zan iya samun abinci mai tsafta?”

“Ni ban sani ba ko akwai ko kuma babu, ga masu abinci can ni su nasani” ta ƙare maganar tana kallonsa. Kallon inda ta nuna masa ya yi sai kuma ya girgiza kansa yana taɓe baki ya ce“Bazan iya cin wannan abincin ba” kallonsa kawai Salma ta yi sai kuma ta ce“To sai ka haƙura” daga haka ta ɗauke idanunta daga kansa ta maida hankalinta wajen titi. Ganin yanda tayi masa ya sanya abun ya so bashi haushi a ɗan fusace ya ce“Amsa kike bani wannan ko kuma rashin kunya kike yimin?” da mamaki Salma ta sake kallon shi, me tayi masa? Ta tambayi kanta. Ganin bata bashi amsa ba ya sake ƙular dashi ya ce

“Heyyy Yar tallah, har ni zan dinga miki magana kina ɗaukemin kai?” Salma da ranta ya fara ɓaci ta kalleshi ta ce“Eh naji ni yar tallah ce, amma ba wadda batasan darajar kanta ba take shaye-shaye ba” ta ƙare maganar tana galla masa harara. Baki buɗe Zayyad ke Kallonta ganin yanda yar ƙaramar yarinya ke gasa masa magana. Ya ce“Ke ni kike faɗawa wannan maganar?” Salma ta ce“Nafaɗa maka ɗin, kai wane?” ta ƙare maganar tana tashi tsaye, ta riƙe ƙugunta tana kallonsa. Zayyad da ya ji kamar ya maketa ya sake cewa“Wato na fuskanci baki da tarbiyya, iyayenki basu nuna miki yanda ake girmama na gaba ba ko?” da hannunta ta nuna shi tana faɗin “Kar ka kuskura ka sake sako iyayena babu abin da ya haɗaka dasu, da ni kake maganarka ka tsaya anan idan ba haka ba...”

“Me zaki yi?” kafin tayi magana mai kantin dake wajen ya kalleta ya ce“Haba Salma wannan ba halinki bane, ana miki kallon mutuniyar kirki?” a sanyaye ta ce“Baba kawai zuwa ya yi yana zagin iyayena, to me nayi masa?” Kallon Zayyad ya yi ganin yanda ya wani haɗe rai, mutumin ya ce“Haba Alhaji, daga ganinka baka yi kama da wanda zaka tsaya kana sa insa da yarinya irin wannan ba, kayi haƙuri dan Allah” Jinjina kai Zayyad ya yi yana ɗan murmushi ya kalleta ya ce“Okay, idan kina da rabon wahala watarana zamu sake haɗuwa. A sannan zan nuna miki ko wanene ni” daga haka ya juya ya bar wajen yana tafiya a zafafe. Da idanu kawai suka bi shi har ya shige mota, Mai kantin ya girgiza kansa yana kallonta ya ce“Kiyi a hankali Salma, irin waɗannan mazan haɗari gare su. Sunada ɗaurin gindi a ko'ina” hawayen daya zubo kan fuskarta ta goge tana cewa“In sha Allah Baba, ni daman tunda naganshi naji tsoro wlh” girgiza kai ya yi ya koma shagonsa yana cewa “Allah dai ya kyauta” Salma ta koma ta zauna ta sake zuba tagumi.


****
Zaune suke kan royal sofa ɗin dake zagaye da ƙaton parlon, Daddy ne da kuma wani abokinsa General Kabeer daya zo gidan suna magana, turo ƙofar parlon aka yi suka ɗaga kai a tare suka kalleshi. Da sauri ya tawo yana zuwa ya rungume Daddy yana murmushi ya ce“Sai yau ka dawo?” Girgiza kai Daddy ya yi yana shafa kansa ya ce“Tun jiya nadawo Zayyad, an cemin kun je Mararaba, banason na takura maka shiyasa ban kiraka ba” janye jikinsa Zayyad ya yi yana cewa“Okay, I see. Yanzu nadawo nima lemme take shower” Sai a sannan ya kalli abokin Baban nasa yana murmushi ya ce“Good afternoon sir” murmushin shima ya yi ya ce“Afternoon dear, Ya kake?” “Alhamdulillah” Zayyad said, jinjina kai ya yi ya ce“Masha Allah, Allah ya yi albarka” Ameen kawai ya ce sannan ya juya ya fita daga parlon. Numfashi Daddy ya sauke sai kuma ya kalli General ya ce“As a said before”

“Zayyad ne ya girma haka?” Jinjina kai Daddy ya yi yana murmushi ya ce“Yeh, shine, kaga ya girma sosai ko?” gyaɗa kai General ya yi ya ce“Gaskiya dai, ya kamata ace kun haɗa shi da mata ya yi aure” shiru Daddy ya yi can kuma ya ce“I think so general, but kasan halin yara, i didn't know weather he prepare or not” girgiza kai General ya yi yana cewa“Ya kamata a masa,  idan ma bai shirya ba sai yanzu ya shirya. Idan babu damuwa Daughter ta dawo daga USA last week sai ya je ya ganta, idan sun daidaita sai a yi auren a shige gurin” Murmushi fal fuskar Daddy ya ce“Wow,Masha Allah, aikuwa in sha Allah anjima zan yi masa magana, kuma zai je ya ganta” Jinjina kai General ya yi ya ce“Tom Allah ya bada iko”.

Zayyad na fita ɗakin Mommah ya shiga, bai ganta ba sai ƙarar plate daya jiyo a kitchen hakan yasa ya ƙarasa ciki, tura ƙofar ya yi ta juyo tana kallonsa.

“Zayyad kun dawo?”

Jingina ya yi da jikin bangon kitchen ɗin ya gyaɗa mata kai kafin ya ce“Eh Mommah, nadawo” shiru tai can kuma ta ce“Ina Nayla?”

“Tana can” ya ce a takaice, da mamaki Mommah ta ce“Bangane tana can ba, mun yi waya da Adda da safe tace min zaku tawo tare anjima, to me ya hanata dawowa?” Zayyad ya ce“Bataso ta tawo ne, tana ɓatamin lokaci nd kinsan Momma bazan iya jiranta ba, so shiyasa nayi tawowa ta, idan taga dama a kawota” Girgiza kai Mommah ta yi ta ce“Tana son ubanta ya ɗagamin hankali ne ya sanya bata tawo ba ko? Bari zan kira Yayar”bai ce mata komai ba ya juya zai bar kitchen ɗin

“Zayyad”

Juyowa ya yi yana kallonta ya ce“Na'am”

“Zamu yi magana da kai anjima, akwai abin da nakeson mu tattauna” shiru ya yi sai kuma ya ce“Okay Allah ya kaimu” daga haka ya fice daga kitchen ɗin. Ajiyar zuciya Mommah ta sauke aranta tana tunanin ko zai yarda??.

****Ko gama parking ɗin motar bata yi ba, ta buɗe ta fito tana tafe tana kuka, a babban parlon ta samu Daddy wanda ya dawo daga raka abokinsa, sai Mommah da Mommy dake zaune kan kujera, Mufeeda na tsaye jikin stairs tana danna wayarta. Kai tsaye wajen Daddy ta nufa tana sake fashewa da wani sabon kukan, da mamaki yake kallonta kafin ya ce“Ke lafiyarki? Me aka yi miki” durƙushewa tayi a wajen madadin ta bashi amsa ta cigaba da rera kukanta. Daddy da bayason ya yi magana ayi masa shiru ya ce a tsawace

“Baki ji ina miki magana ne?” cikin shassheƙar kuka ta ce“Daddy nagaji, nagaji da zama gidan Farooq, I'm so tired wlh. Daddy Aure zai ƙara, Daddy Aure zai yi fa” da mamaki ya kalleta sai kuma ya ce“Shi Farooq ɗin ne ya ce miki zai ƙara aure?” tana rage sautin kukanta ta ce“Eh Daddy, yanzu abin da ya gama cemin kenan, kuma ya ce ban isa na hana shi ba, nace zan faɗa maka ya ce wai ka wanene, ko nafaɗa maka sai ya aikata har cewa ya yi ko B. Musa ne zai dawo duniya ya hana shi ba zai fasa ba kuma...” Dakatar da ita Daddy ya yi ta hanyar ɗaga mata hannu, ya fara zagaye cikin parlon, jijiyoyin kansa suka mimmiƙe, ya jinjina kansa. Aƙalla ya ɗauki ya kusa 5mins kafin ya ce

“Then definitely I'll show him my true colour, zai gane wanene Idris B. Musa, ba shi kaɗai ba har ubanshi ya saka a matsala!” daga haka ya fice daga parlon da sauri kamar zai tashi sama. Nimrah goge hawayenta ta shiga yi dan ko babu komai tasan Daddy ba zai bar shi ya yi auren ba. Mommah ta kalleta ta ce“Nimrah! Nimrah!” Kallon Mommah ta yi sai kuma ta sunkuyar da kanta. Girgiza kai Mommah ta yi ta ce“Ki cigaba, wato saboda kinsan halin mahaifinku ya sanya ki ka zo da wannan maganar ko? Kina tunanin idan aurenki ya mutu wani ya yi asara?” Cikin shassheƙar kuka ta ce“Wlh Mommah ba ƙarya nake ba, haka ya ce min, kuma har zagina ya yi. Mommy dan Allah ƙarya nayi?” ɗan murmushi Mommy ta yi ta ce“How could i know? Amma dai nasan halin Farooq” Goge hawayenta tayi ta tashi tana cewa“Wlh ba sharri nayi masa ba” daga haka tayi hanyar upstairs abinta. Mufeeda dake tsaye ta bita da kallo, sai da taga ta bar wajen, sannan ta dawo parlon tana kallon Mommah ta ce“Wlh Mommah sharri take masa, Farooq ba zai zagi Daddy ba” girgiza kai Mommah ta yi ta ce“Nasani Mufeeda, Nimrah bata jin magana, duk abubuwan da nake faɗa mata basa shiga kunnenta”. Numfasawa Mommy ta yi ta ce“Rannan fa da tazo sai da muka yi magana, amma shima Farooq ɗin da laifinsa”

“Koma da laifinsa ai itama da laifinta, ya za'a yi kina zaune gidan miji baki masa biyayya? Haka taga mu muna yi? Da haka muke ai da ma kai labari? Amma zata ci ubanta wlh” Daga haka Mommah ta tashi ta haye sama. Da idanu kawai Mommy ta bita sai kuma ta ce“Allah ya kyauta”.

****
Tafiya take tana jan ƙafarta dan ba ƙaramin gajiya tayi ba, lokacin kusan ƙarfe shidda na yamma ne, hayaniya tayi yawa a hanya, yara sai kai komo suke wasu da uniform na islamiyya wasu kuma da kayan gida. A haka har ta ƙaraso ƙofar gidansu, burki taja ta tsaya tana binsa da kallo, fuskarta ɗauke da mabayyanin mamaki. Tasowa ya yi daga kan dakalin da yake ya ƙaraso gabanta yana murmushi.

“Hi dear”

Ta tsinkayi muryarsa. Shiru ta masa tana binsa da kallo har sannan, shafa kansa ya yi yana murmushi ya ce“Sorry baki sanni ba ko? I'm Al-ameen Jameel Giwa, I'm a physician doctor, ina aiki a clinic ɗin Mom ɗina, Dad ɗinmu ya rasu at least 10yrs yanzun, Ina zaune a Abacha road, Shikenan” yanda ya ƙare maganar yana watsa hannu ya sanyata ɗan murmushi, Kallonta Al-ameen ya yi sai kuma ya ce“And baki faɗamin ko ke wace ba, ko sunanki ma bansani ba” Salma shiru tayi masa can kuma ta ce“I'm Salma Abubakar, ina zaune da Abbana da Ummana, Ammina ta rasu tun ina ƙarama” girgiza kansa ya yi cike da tausayi ya ce“Allah sarki, Abun tausayi, Allah ya jiƙanta” Salma da idanunta suka fara kawo ruwa ta ce“Ameen Nagode” agogon hannunsa ya kalla sai kuma ya ce“Magrib ya kusa Salma, kuma naga kamar daga wani wajen ki ke, tunda naga gidanku shikenan bye” shiru tayi sai kuma ta kama hanyar gida, juyowa ta yi taga har sannan yana tsaye yana kallonta

“Sake zuwa zaka yi?” Ta tambaye shi. Gyaɗa mata kai ya yi yana murmushi, ta juya ta shige gida abin ta. Ajiyar zuciya Al-ameen ya sauke sannan ya fara tafiya toward direction ɗin motarsa yana jin wani irin sanyi a ranshi. Da sallama ta shiga gidansu, ta ƙarasa kan tabarmar da sauri ganin yanda yake ƙoƙarin gyara ƙafartasa..

“Abba...” ta faɗa a raunace. Shafa kanta Malam Habu ya yi hannunsa na rawa, hawayen azaba na zuba daga cikin idanunsa. Magana yake son ya yi amma ya kasa, tashi Salma tayi ta yaye labulen ɗaki tana kiran sunan Umma, sai dai shiru taji da alama ma Ummar bata cikin gidan. Dawowa tayi ta zauna tana kallon ƙafar tasa wadda duk ta kwaɓe sai ruwa take, hawaye na zuba kan fuskarta. Cikin kuka ta riƙe rigarsa tana faɗin “Sannu Abbana, Allah ya baka lafiya Abba, Allah ya rabaka da wannan ciwon, innalil lahi wa ina ilayhi raji'un, Astagfirullaha wa'a tubu ilayk” Tana nan zaune tana wannan kukan Umma Rahmatu tayi sallama ta shigo gidan, da mamaki take Kallonta ta ajiye ledar hannunta tana rataye mayafinta kan igiya ta ce“Yau kuma wani sabon kinibibin kika samu na koke koke? Ba zaki bar shi ya ji da abin da yake damunsa ba?” Ɗago kanta tayi tana kallonta ta ce“Umma mu kai Abba asibiti ƙafarsa ruwa yake Umma, ina ga mai gyaran nan bai gyara ya yi ba, zo kiga Umma”

“Iko sai Allah, ke a rayuwarki baki son kiga mun zauna lafiya? Wato ɗan kuɗaɗen da muke samu yanzu shine sai kin san yanda ki ka yi aka kashewa ubanki su ko? To wlh kin ji kaɗan, naji wani iskancin banza. Duk wadanda suke karyewa yake gyara basu ce bai iya ba sai ke gwana” Girgiza kai Salma tayi ta ce“A'a Umma wlh wannan daga gani da zafi, kuma ya ɗaure ciwon ya kamata a kwance aga yanda yake” a fusace Umma ta ce“Ke wace irin shashasha ce? Kin taɓa ganin inda aka kwance karaya a gida? To ba'a yi kai tsaye sai dai a kira mai gyaran ya kwance” tashi tsaye Salma dan daman da hijabinta a jikinta, ta ce“To Umma bari naje na kira shi” Taka mata tsawa Umma ta yi ta ce“Kaga yarinya? Dawo ki kunna min wuta na ɗora abinci ni, ki barwa safiya a kira mai gyaran” Jiki a sanyaye Salma ta tsaya, ta saci kallon Abbanta taga idanunsa a lumshe sai kuma ta ɗauki ledar gawayin tayi hanyar inda suke girki.

****Da gudu ta fito daga ɗakin, tana ihu ta buɗe dakin da take kwance tana kiran

“Salma! Salma! Ummusalma, fito kiga, innalil lahi wa ina ilayhi raji'un” Salma da batada nauyin bacci ta buɗe idanunta tana kallon Ummarta ta ce a kiɗime“Umma meya faru ki ke kirani da tsohon daren nan?” Kamo hannunta Umma tayi suka fito daga ɗakin tana kuka ta ce“Muje kiga Salma, min shiga uku” ban da faduwa babu inda ƙirji Salma ke yi, har suka shiga ɗakin. Ganin Abbanta a zaune yasa ta sauke wata ɓoyyayiyar ajiyar zuciya, Umma ta ƙarasa inda yake tana kallonsa ta ce“Salama kalli, Ƙafar Mahaifinki tsuntsa take Salama,Wlh tsutsotsine a ƙafarsa, inaga ta ruɓe Salama!”

# HCD
# Light within the darkness
# Nanameera.
***