Chapter 1
*KARAGAR MULKI*
(Historical – Fictional – Magical – Heart-touching Love Story – Full of Confusion, Destiny & Betrayal)
***
For WhatsApp group👆👆👆👆👆👆
For WhatsApp Channel 👇👇👇👇👇👇
***
Wannan labarin k`irk`irarren labari ne duk abinda ki ka gani a cikin sa wanda yai dai-dai ko kamanceceniya da wani abu to bisa arashi ne,ban sa wata kalma da nufin cizgunawa ko munanawa wani ko wata ba.
STORY & WRITTEN BY :
(*Cwt~Sumiey*)
Marubuciyar littafin
MENE NE ABIN YI ?
JADEEDAH
And now...*KARAGAR MULKI*
❤ Wannan page naku ne massoya na ❤ Allah ya bar mu tare forever and ever
BOOK 1
♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
[01/07/2025]
PAGE 1
FREE PAGE
Bismillahi Rahamanir Rahim
"Ki yi haƙuri Malikat Juwairiyya amma ba zan iya bin ki ba,na riga da na saba da rayuwata anan,kuma ta fi ma'ana da alfanu a gare ni,kai bama a gare ni kaɗai ba har da ita kanta Sarauniyar, ke da ma mutanen gari baki ɗaya,"...." A'a kar ki ce haka Gimbiya Junainah domin a yanzu zamanki anan yana cikin haɗari,barazana,firgici harma da ɗimuwa","Ni kaina ai haɗarin ce wacce ke barazanar illata duk wanda yake kusa da ita ko ya raɓeta,to kinga in haka ne meye amfanin zamana da ku?,gara kawai ku bar ni in cigaba da zama na anan ,ko na ƙarasa sauran rayuwata a cikin wannan lambun da ke gefan gari,domin rayuwata da ku kasancewarta da kamar wuya Wai kiɗan ganga da lauje","Ba za ta sa`ɓuba wankan kuturu da sabulu domin a baya kin faɗi irin haka na amince amma a wannan karon ina mai tabbatar maki da yanzu ba za ki yi nasara ba,","Malikat Juwairiyya ki yi haƙuri amma bazan iya bin ki ba domin ina tsoro a koda yaushe zan iya rikiɗewa in zama halitta mafi tsoro da muni gaba ki ɗayana to in hakan ta faru ya zakuyi da ni,na daɗe da sanin Gurin kwanan balbela daban ya ke da na hankaka,ba abu ne mai kyau zai faru ba in su ka haɗu guri guda, ko kin manta ba ku da wani magani da za kuyi ko ku bani a kan haka ? ",Ba mu da shi amma hakan ba yana nufin zamu bar ki ki cigaba da zama anan daga ke sai dabbobi da namun daji anan ba,tunda daganan inda ki ke ba sauran gida gaba ko gida baya,me ya sa za ki tsorata gami da fidda rai dangane da samun lafiya a gare ki,ki ƙaurace wa mutane shin ki na tunanin hakan shine mafita,bari ki ji wani abu da a ce zaki ya ji tsoran mutane da tuni sun fara kiwata shi a gidajensu kamar yanda su ke kiwata Kare da sauran namun daji amma da ya jajurce gami da sa dakiya a zuciyarsa, kuma da bai tsorata ba sai ya juye gami da rikiɗewa zuwa Sarkin dawa,to me ya sa ba za ki kwatanta abinda ya aikata ba ?, ","Aikata hakan abu ne mai matuƙar wuya wai gurguwa da Auren nesa to meye aibun haka, ni ina jin daɗin rayuwata haka kuma Kiki tana ɗebe min kewa fiye da duk sauran mutanen da suke a tare da ni anan cikin masarautar tunda ina da tabbacin bazan cuceta ba haka itama ba zata cutar da ni ba,saboda ko da na rikiɗe zuwa wata halittar bazan cuceta ba tunda itama dabba ce kamar ni,in ma na cutar da ita za a ce duk ɗaya wai anyi ma tuwo barin miya","Wai Giwar ce ki ke ikirarin tafi mi ki daɗin rayuwa fiye da kowa da kowa ?,wannan da ace mutum ce sai in ce bita da ƙulli ta ke mi ki bugun kabarin kishiya,to sai dai an samu akasi ita ɗin dabba ce ,","Kwarai da gaske Malikat Juwairiyya,ita kaɗai ce wacce nake da ita a rayuwata ta yanzu wacce bata taɓa yunƙuri ko ƙoƙarin nisa gami da son rabuwa da ni ba,amma itafa Sarauniya da kanta ta zaɓa mana muyi rayuwa irin wannan da ta ke gudana a tsakanina da ita",...."To na gaji,dama can zura miki Ido nai taya za'ai mutum ya rayu a wuri daga shi sai itatuwa,dabbobi da kuma tsirai,to Wai ma daɗin me kuturu ya ji ga Allah da za ki ce kin fi san ki cigaba da rayuwa anan ?, bazan amince gami da lamuntar hakan ba,kuna bani mamaki da ga ke har Mahaifiyar taki,nice na haifeta ita kuma ta haife ki bisa hannuna kuma akan idona to amma ban taɓa ji ko gani makamancin yanda ku ke rayuwa ba,ke ko a hikaya,labari,tarihi da tarihihi har ma da tatsuniya ban taɓa ganin ko jin irin ta ku ba, ace ke da Mahaifiyar ki baku haɗa idanu ,ba ku ga maciji a tsakanin ku,balle a kai ga kun sha inuwa ɗaya da ita ,Kai abun da sake,Wai an ba me kaza Kai da ƙafa"," Ita ta zaɓa mana haka,kuma ke ia kin san halina da nata ba ɓaya ba ne,ba zamu taɓa iya zama wuri guda ba, bazan iya jure ko ɗaukar zalunci da mulkin kama karyar da take gudanarwa ba,kuma ma dai kowa da mazaunin sa wai an ɗaure mai dungu ya saɓule" ,"Wannan tsakanin ku ,kuma ma dai ai kinsan darajar kwarya ragaya in ta sau ƙasa ta sauya suna,duk daɗin da ki ke ji bai kai wanda za ki sama a cikin Masarautar ki ba kuma ma dai a yanzu zaman ki anan ba zai ɗore ba,sakamakon abinda ke shirin faruwa a wannan ƙasar tamu,bani da natsuwa,kuma ruhina ba zai taɓa samun salama ba matuƙar kina zaune anan ","Kamar ya wani abun ne ya ke shirin faruwa ?"," Tabbas wani abu ya faru ko yana gab da faruwa domin,Mahaifiyarki Sarauniya Junayyah ita da kanta ta ta fara buɗe ƙofar yaƙi tsakanin ta da ƙasar BIHINAR domin a makon da ya gabata an tsinci babban jirgin ruwa kwale-kwale a dai-dai bakin gaɓar kogin da yai mana iyaka da ƙasar BIHINAR ɗauke da mutane Ashirin sannan kuma da tarin makaman yaƙi a cikin sa,tasa an kama su gami da tuhumar abinda ya kawo su cikin ƙasar ta mu amma suka ce wai igiyar ruwa ce ta jawo su har suka tsinci kansu a wannan ƙasar,mu kuma ba mu amince gami da yarda da abinda su ka ce ba,saboda wannan dalilin ne yasa ba zan iya haƙuri ko barin cigaba da zamanki a cikin wannan dokar dajin ba,domin ba shakka ko makawa Sarkin BIHINAR ba zai taɓa zuba Ido ya na kallon mu ba , bayan mun kama ma sa mutanensa,shiyasa dole sai kin bar cikin jejinnan a wannan ranar ba sai gobe ba,tunda nasan duk kyan tafarnuwa bai yi ya albasa ba".
Sai da Gimbiya Junainah ta ja wani dogon numfashi daga bisani ta ɗora da cewa,"kin gani ko wannan shine dalili na farko da yasa bana son zama ko Rayuwa a cikin ku ko ba dan lalurar da Allah ya jarabce ni da ita ba,ta ya kuma a kan me zaisa bazata sa ke mu su mutanen su suyi tafiyar su ba, tunda sun gaya maku ba wajen ku su ka zo ba,yanzu dan Allah rayukan mutane nawa ku ke son jefawa cikin haɗari a kan hakan,ko da ya ke ni ba ruwana tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan doka".
Wata gigitacciyar tsawa Malikat Juwairiyya ta daka mata wacce har sai da Gimbiya Junainah ta miƙe tsaye tana mai fiddo da dara-daran idanunta waɗanda suke sakka da na maciji ko macijiya,ta ce da ita"Kome lalacewar masa ta fi ƙarfin kashin shanu,don haka ki shiga taitayinki haka kuma ki iya bakinki lalacewar mu bata kai har wani ya zo cikin ƙasarmu ya ci mu da yaƙi ba,domin ko jimina ta nutsa kanta a taɓo tafi ƙarfin a kirata da kaza,to ta ya ma wani sha-sha zai zo ya aikata mana abinda ya so ya fita ba tare da an hukuntasa ba,don haka dole ne su karɓi hukuncin zunubin da suka aikata,ni dai na san duk abinda ya samu shamuwa watan bakwai ne ya ja mata,dole ne mutanen ƙasar BIHINAR su san cewa ƙasar BAIBAH buhun ƙaya ce ba a cikata a danna".
"Haba Malikat Juwairiyya me ya kawo wannan fusatar har haka ?,idan har na faɗi wata kalma munmunan ki gafarce ni amma ba ina nufin haka ba ne har cikin zuciyata ba,ban ga dalilin da zai sa in ɗauki furan kan juji in martaba shi gami da killace sa fiye da wanda yai tsiro a farfajiyar Gidana ba".
" Jikata ki gafarce ni,domin ba furcin ki ne ya fusata ni kaɗai ba,A'a illa tunawa da nai yi da irin cin kashi da kuma cin zarafin da Masarautar BIHINAR tayi mana ne,an bige mu kuma a ka zo a ka hana mu kuka,haka jinanen ƴan'uwanmu suka riƙa gudana a ƙasa a ban za a wofi tamkar ambaliyar ruwa daga kogi ba tare da wani ya kawo mana ɗauki ba,a yanzu ƙaryar ware-ware ta ƙare tunda har ƴar fulani ta saida Gida,domin a halin yanzu manya-mayan Dakarun ƙasar BIHINAR su na hannunmu sai yanda mu ka gadama za mu yi da su ".
Jikin Gimbiya Junainah duk yayi sanyi harta kai ga fuskarta ta nuna hakan,"Ki gafarce ni ya shugabata amma ina son ki ba ni labarin asalin abinda ya faru a shekarun baya ,ba kamar yanda kika taɓa lasa min zuma a baki ba".
"Tsohuwar gaba kenan amma tabbas na na maki alƙwarin akan zan baki wannan labarin amma sai in mun koma masarauta tare da ke,"Tsohuwar gaba kuma tsakani masarautun biyu ?", Gimbiya Junainah ta sake tambayarta,"," A'a ba dai Masarauta biyu ba sai dai Masarauta uku","Har uku ya shugabata?"Tabbas kuwa amma ki bar komi sai mun Isa masarauta","Har yanzu zuciyata ta gaza amincewa gami da yarda akan in amince in bi ki ","Ya ke Jikata ki sa ni na shirya ma duk wani abu da kike jin tsoransa ".......ta katseta" Kamar ya ina son in san wanne irin shiri ki ka yima wannan rikitaccen al'amarin nawa da ya ke bibiyar rayuwata",sai da Malikat Juwairiyya ta jadogon numfashi kana ta bata amsa da cewa," Bokanya Azizah na kan haya tare da maƙarrabanta zata zauna da mu har zuwa sanda zata samo makarin jifan da aka yi miki","Ni fa kin ji matsala da ku,bayanda za'ai abu ya same ka sai kuce asiri ne ko jifa,ni ciwona jarrabtace daga wurin Allah,shine kuma kawai zai yaye min ",Haka kika sha yawan faɗi amma har kawo yau ban ga abinda ya sauya ba, duk miƙa lamarin naki a wurinsa da ki kai,"," Hmmmmm bawai ya manta da ni ne ba,A'a yana sane da ni,jinkirin ma na daga cikin ƙaddara da jarabawar da yayi min","Bana da wani lokaci isasshe balle har in tsaya sauraron wannan shaci faɗin na ki ,don haka ki tashi ki bi umarnin da na baki",Zan so ace zan iya abinda ki ka ce da ni to amma a gare ni ba wai iya lalurar da nake fama da ita ce damuwa ta ba,A'a har yanda zamana da ita zai kasance,ƙalubale ne gare ni babba","Hmmmmm kuna bani mamaki daga ke har ita,Wai yanzu Mahaifiyar ta ki ba za ki iya kiran sunanta ba sai dai ki ce mata ita,ke ko Sarauniya za ki iya kiranta da shi in ba za ki danganta kan ki da ita ba a matsayin wadda ta kawo ki duniya ba","kiyi hak`uri Malikat Juwairiyya amma a nan ban san me kuma zan ce da ke ba","Ina so ki sani kuma ki sa a ranki alaƙar jini ce tsakanin ki da ita,duk runtsi ko tsanani kar ki manta da hakan kuma da gaske nake na shirya ma komawar ki cikin Masarauta a wannan ƙadamin domin harda wannan matsalar sai da na nemo makarinta","Makarinta kuma mene ne makarinnata","In munje kya gani don haka ki tashi mu tafi domin ba mu zo da niyar daɗewa ba ko kuma mu yi dare"Amma ya shugabata ina neman wata alfarma idan har tafiyata ta zama dole to ina so da a barni in tafi da Kiki in da hali kuma da yiwuwar hakan,domin Kiki ce kaɗai halittar da na ke jin daɗin rayuwa da ita,in ki ka cire ke, Kawuna Ishmal da Kuyanga Jazila","Hmmmmm ki taho da ita domin Masarautar BAIBAH Gidan kowa da kowa ce ciki har da Kiki ",ta ƙare zancen nata fuskarta ɗauke da murmushi, ita kanta Gimbiya Junainah murmushin ne ɗauke a saman fuskarta wanda ta ɗauki lokaci me tsawo ba tai ba har tana mai cewa," Ko zaki naɗauka kenan za ki barni in tafi da shi","Kwarai ma da gaske ko da dukkanin namun daji da dabbobin cikin jejin kika nuna kina son tafiya da su Zan amince gami da baki damar tafiya da su saboda ke kanki kin San a cikin masarautartamu muna da inda zamu ajesu,kuma bugu da ƙari buƙatar ta fito da ga bakin Sarauniyar mu ta gobe Gimbiya Junainah ne,kin ga kuwa dole ne in amshe ta da hannu bibbiyu",ta ƙare zancen na ta ta na mai sakin wani murmushi sai dai akasin haka ne kwance a saman Fuskar Gimbiya Junainah, da haka suka tashi ba tare da sun ɗauki komi daga cikin muhallin da Gimbiya Junainah ke rayuwa ba,sai bayi biyu daga cikin bayin da suka taho da su suka kimtsa kayan gami da adana su inda ya dace ba tare da sun lalace ba
Samun wuri Gimbiya tai ta ja ta tsaya ba tare da da cigaba da tafiya ba,kusan bayi Ashirin ne tsaye suna jiransu, har sai da Malikat Juwairiyya ta ce da ita ,"Muje mana ya a kai ki ka tsaya?","Malikat Juwairiyya banga dokuna ba,ko kina nufin bayin sune zasu ɗaukemu a saman kafaɗunsu bayan mun shiga cikin wannan BIKAD ( mazauni ne da ake ƙirƙirasa domin sarakuna da attajirai, sukan zauna a kan sa sai bayi huɗu ko fiye da haka su d`auka,ita mahayar kala biyu ce 1.akwai wadda da ga sama a ke sa ganyayyaki ko sanho a yi rufin sama da ita a na yi ma runfar tokara a tsakiya,yanda runfar za ta tsaya dai-dai ko a sa lema,ga duk wanda ya taɓa ganin fim ɗin tarihin Annabi Yusuf to akwai sa a ciki(sanho na nufin buhu duk da dai a nayin na fata,kuma dai ya na ɗauke da ma'anoni guda biyu ne tunda akan zuba kaya a cikin sa)2.Ana amfani da katako ne ayisa kamar kejin kaji da ƙofofi guda biyu kuma ya na da ɗan girma tunda ya kan ɗauki Sama da mutum biyu ,har labule a na sa ma ƙofofin sa) ","Bahaushe yace idan ka daɗe ba ka ga mutum ba kar ka tambayi halinsa ka tambayi lafiyarsa kawai domin mai hali ba ya taɓa canja halinsa,ka na zaune da shi a hankali zai bayyanar ma ka da wannan halin na sa da ka san shi da shi a baya","Ba abinda ki ke nufi ne ya ke a raina ba,gani nai da kun zo da dokin ko Raƙumi da yanzu sai a ɗora BIKAD a saman dokin su ja ba sai mun ɗora ko wahalar da wani bawa ba ".........ta dakatar da ita"Ya Isa haka bana son cigaba da sauraren waɗannan zantuttukan naki,ko kin manta sunansa bawa ne kuma aikin sa kenan kai tsaye zan iya cewa an haifesa ne domin kawai yayi mana bauta ,don haka ki wuce ki hau mu tafi tun kafin ki ɓata min rai", haka tana ji tana gani ta sa ƙafarta ta shiga cikin BIKAD sannan bayi huɗu suka kama gefe da gefan suka ɗaga su tafi,sukuma sauran bayin suka bisu a baya bisa layi,Inda Kiki ce a gaba kafin bayi mata su biyo bayan ta ,daganan sai bayi maza da kuma dakaru.......