TAEESH

CHAPTER THREE

by @zinariya0102

_________Fulani Rahama da ke ta faman salati tana ta ambaton Allah, duk addu'ar da tazo bakinta yi take.

Dr.Salim da nurse Kubra ne a kanta cike da nuna ƙwarewar aiki, yana ta taimako don ganin an haihu kamar gaske, sosai Fulani Rahama ke faman shan wahala, dubata ya yi yana faɗin " four cm fa, ranki ya daɗe sannu" Fulani Rahama ta ce" doctor yaushe zan haihu?" ya ce" soon za ki haihu ranki ya daɗe" Kubra ya kalla yana faɗin" a sa mata n/s infusion with ogxcitocine one ampule idan ta zo eight cm call me "ya fita cikin sauri.

Da sauri su Umma suka tare shi "likita ya ake ciki? "ya ce" ku kwantar da hankalin ku da saura tukunna yanzu ma bacci ta ɗan samu, za ku iya tafiya don sai cikin dare zata haihu" Hajiya Binta ta ce"to ai shikenan Allah ya raba lafiya,bari mu tafi" Jakadiya ce ta ce "nikam nan naga zama har sai Yarima ya iso" Dr.Salim ya ce" ba a zama anan Baba Muna da enough labourers no need anyone, amma ku da zaki zauna ki je da daddare sai ki dawo" Umma ta ce" ni kam ba zan je ko ina ba har sai naga ƴata ta sauka" Dr.Salim ya ce"okay akwai masallacin mata a can Baba za ku iya zuwa can ku zauna" "kai likita!!! ka iya bakin ka, kar harshenka ya kai ka ya baro, wannan ba a banza take ba, na rantse da As-samadu zaka sha ɗaurin da sai igiya ta yi saura a jikinka na faɗa maka" cewar Jakadiya tana mai gargaɗi ga Dr. Salim. Shigewa ya yi yana mai yin shiru da bakinsa.

Sis Abida ce ta tare shi da gudu. "Doctor wannan Matar har yanzu bata haihu ba, har ƙarfinsu ya ƙare" cikin sauri ya nufi wajen ana bashi hand gloves, safar ya sa, Matar Christian ce, babu abinda take iya faɗa sai Jesus Christ oh! Messiah help me please, a hankali, don ƙarfinta ya ƙare, dole aka shiga da ita theatre room (tiyata) nasarar ciro mata yara biyu aka yi mace da namiji duk babu rai, ita ma matar ta mutu don ko farkawa bata yi ba. Ya rufeta file ɗin da ke bedside drawer ɗin ya ɗauka ya yi rubuce-rubuce ya ajiye. Ya kalli Abida ya ce" kar wanda ya shigo ɗakin nan har sai an ɗauke wannan. Ya nuna gawarwarkin.

"okay Sir" ta faɗa da girmawawa.

Ɓangaren Maimartaba Sarki Suhaid ma hankalinsa ya ƙi kwanciya tunda Hajiya Binta ta dawo ta sanar da su sai dare Rahama zata haihu, haka ya shirya da kansa zuwa asibitin, anan ya tarar da su Umma, har ɗakin da Rahama take ciki ya shiga, ta na zaune ta na cin Banana, tamkar ba haihuwa zata yi ba, ganinta yasa hankalinsa kwanciya, Dr.Salim ne ya yi masa bayani yanda zai fahinta, har magriba ya na asibitin, sannan ya koma aka bar fadawa guda biyu domin ko za a nemi wani abu.

Su Fulani sai waya suke domin jin ya ake ciki, Dr.Salim ya ce" na ce ku kwantar da hankalinku wallahi ko ta haihu lafiya sai na sa ta jinya kuma sai na hallaka abinda aka haifa, idan ban cika muku aikin ku ba to ni ba ɗan halal ba ne" hahhh hahhh shiyasa na ke ƙara basu tabbaci akan ka doctor ni nasan ba za ka taɓa bamu kunya ba, yana wayar cikin ƙasa-ƙasa da murya, yana dube-dube na rashin gaskiya.

Misalin ƙarfe ɗaya na dare, ciwo ya tashi, Fulani Rahama kamar ba ita ba, Dr.Salim ya sa aka kaita theater room, ya hana kowacce nurse shiga, dake asibitin nasa ne, kuma shiɗin ne IC, daga shi sai Fulani Rahama sai wannan Mata da ta rasu tare da gawar yaranta biyu. Ana jiran ƴan uwanta su kawo kuɗin aiki, sannan su ɗauki gawarsu.

Cikin ikon Allah Fulani Rahama ta haihu da kanta, jin kukan jaririya yasa ta faɗin "alhamdulillah" Dr.Salim ganin ta na cikin hankalinta yasa ya fito da wata allura a aljihun labcourt ɗin shi, ya yi mata, wani jiri-jiri ne ya ɗauketa take ta daina gani, da hanzari ya ɗauke jaririyar ya sa cikin wani corridor da yake ɗakin cikin wani glass na jarirai wanda ake ajiye jariran da basu isa haihuwa a ciki ba, ya sanya jaririyar ya kunna mata haske domin ɗumama na'urar, take jaririya ta koma ta dunƙule tamkar tana cikin mahaifiyarta.

Gawar jaririyar Cristian ɗin nan ya ɗauko ya ajiye kusa da Fulani Rahama, sannan ya fito yana sharce gumi, da sauri Jakadiya ta ce" an sauka likita?" Dr.Salim ya ce" Alhamdulillah ta haihu da kanta, sai dai ku yi haƙuri abinda aka samu ya koma" innalillahi wa'inna'ilaihirrajiun lailahaillahu shikenan munga samu munga rashi" Jakadiya Tabawa ta hau kuka tana salati tamkar ta zauce.

Umma tace "ya ita uwar take likita?"doctor Salim ya ce "ta samu bacci ne yanzu za a mayar da ita ɗakinta kafin ta farka, da safe sai ku tafi, sai haƙuri" ya wuce office ɗinsa.

Tun daren zancen jaririya ta koma ya baza masarautar Hauren Giwa,tunda Fulani ta Gabas ta sanarwa da Sarki Suhaid ya ji wani abu ya tsira masa a ƙahon zuciya har sai da ya dafe in da zuciyarsa take, in banda ambaton Allah babu abinda yake yi, bai san hawaye ne ke zuba a idanunsa ba, sai da Fulani ta gabas ta ce" ranka ya daɗe kuka fa kake yi, hawaye fa nake gani a idanunka, haba, ka yi tawakkali mana, Allah'n da ya bayar shi ya karɓi abinsa, daman can Allah ya ƙaddara ba rayye ba ne" ta yi maganar cikin tsantsan jimami da nuna kulawa da tausayi.

Cikin hanzari ya sa tissue ya tsane hawayen ya na faɗin "Allah shike bawa wanda yaso ƴaƴa mata zallah, kuma ya bawa wanda ya so ƴaƴa maza zallah, kuma ya haɗawa wanda ya so maza da mata, kuma ganin damar sa ne ya hana wanda ya so, Alhamdulillah ala kullu halin, Allah ka ba ni ikon ɗaukar wannan jarabawa da ka yi min" Fulani ta ce"amin amin dai Allah ya baka nasara"

Da kuka Fulani Zaitun ta shigo "shikenan yanzu gimbiyar da muke sa ran samu ta koma wayyo Allah na shiga uku!" ta kuma rushewa da kuka, Mai martaba da idanunsa suka ƙara cika da ƙwallah ya ce "haba Zaitun meye haka kike yi kamar ba mai imani ba, Allah'n da ya bayar shi ya karɓi abinsa, sai mu yi haƙuri tare da addu'ar Allah ya bamu zuri'a ɗayyiba" Haba ranka ya daɗe kabarni na yi kuka ko na samu sauƙi a cikin zuciyata, mu uku ko ɓatan wata ba mu taɓa yi ba, ita da muke sa ran zamu tara ƴaƴa a gidan nan daga jikinta ga da abinda aka fara" cewar Zaitun.

Fulani kamata ku je, da alama mutuwar nan tana neman zauta ta" Ta gabas ta ce" dole ne ranka ya daɗe" ta sa bakin alkibbarta ta na share fuska, ta kama Zaitun suka bar turakar.

Ana ta kiran sallah alamar asuba ta kusa.

Heyheyheyyy!!!! Amma ke kan anyi makira, kuka fa kike da gaske" cewar ta gabas, "hum waya gaya masa Barno gabas take ai wallahi makirci kaɗan ma suka gani, ba dai mun yi sake har ta ɗauki ciki ba, to ita ma ta gama don wallahi sai dai kowa ya rasa a gidan nan, yanda kaf cikin mu ba mu haifi Magajin Sarki ba, to kuwa babu ƴar mutsiyatan da ta isa ta haifa mtsw ashe ma Mace ta haifa" hahh hahh suka sheƙe da dariya gami da tafawa" Fulani Amina da ke zaune tace" ni ai gobe da safe sai gadon asibiti akan wannan al'amari, bari ma ku gani" ta ɗauki waya ta hau kiran Dr.Salim.

Bayan an mayar da Fulani VIP room tare da gawar jaririya a cikin kwali, su Umma da suke jiran farkawar Rahama amma shiru sai bacci take yi, badon tana numfashi ba da sai su ce ita ma ta cika ne.

Jakadiya Tabawa da Umma sai sallah suke suna addu'ar Allah ya bawa Fulani Rahama lafiya.

Dr.Salim kuwa bayan an bada gawar Eromosele da jaririnta ga ƴan uwanta don ya nuna ɗaya aka haifa ba biyu ba sun tafi, sahu ya ɗauke a asibitin ya ɗauko jaririya ya naɗe a zanin wannan mata ya sa ta a motarsa ya bar asibitin a daren, haka nan ya tsinci kansa da kasa hallaka jaririyar, kawai ya miƙi titi, a 360 yake tuƙi, yana ji ana ta kiran salla huɗu na dare hankalinsa ya ƙara tashi gudun kar gari ya waye bai fita da wannan jaririya daga motarsa ba.

Gangarawa ya yi, ya yi parking babu kowa dake ana tsananin sanyi, ya ciro jaririya ya shiga cikin ɗan garin wanda bai san ma ina ne ba, kusan tafiyar awa uku yayi a mota kuma cikin tsananin gudu, sai da yaje mararrabar wata hanya ya shiga cikin ciyayi ya ajiye jaririyar ya tafi da sauri, ya hau mota ya bar garin da baima san ina ne ba.

,

Sai lokacin hankalinsa ya kwanta, kiran Fulani Amina ne ya shigo wayarsa a daidai lokacin da ya isa unguwarsu, ansan shi ɗin likita ne yana iya fita komai dare, kuma yana dawowa komai dare.

Ya ɗaga cike da karsashi "ranki ya daɗe" Fulani Amina ta ce" an gaishe da likita bukan turai, aikinka ya yi kyau, tun da muka samu kyakkyawan labari aka sa maka sauran Bill ɗinka 20millions Naira" cike da farinciki ya ce" Allah ya taimake ki nagani Allah ya saka da alheri zan zo har gida in yi godiya ai" ba wannan ne yasa na kira ka ba, za a kawo ni KMC hospital ina so ne ka ce jinina ne ya hau sanadin furgita da wani mummunan labari da na ji" ya ce "angama ranki ya daɗe" Fulani ta gabas ta jinjina mata hannu hakama Fulani Zaitun ta shiga jinjina kai.

Fulani Amina ta kashe wayar tana faɗin" ya kuka ga wasan?" ta gabas ta ce "kai gaskiya ina yaba wannan makirci naku ƴan uwana, bari na koma part ɗina kar mu zama abin zargi, kinsan yanzu dole muna yi muna kula, Fulani Amina tace "nima tafiya zan yi, daman zaman feedback na yi, don jin ya Fulani zata fito bayan ta je wajen Uban gimbiya hahhhh hahhh" ke wana irin gimbiya ai sai dai kice "princess ta turawa hahh hahhh" duk suka kuma sheƙewa da dariya.

Da safe Sarki Suhaid tare da ƙaninsa Ciroma Ubaid ne tsaye a gadon Fulani Rahama wacce ta farfaɗo tana kallon kowa, sarki Suhaid yace " sannu Fulani ya jikin naki" Ba magana sai kallo" Umma da ta fahimci Rahama ba a hankalinta take ba, ta ce"ranka ya daɗe, tunda aka fito da ita bata magana bata motsi sai yanzu da naga ta juya idonta ta na kallonka" ta fashe da kuka.

"Innalillahi wa'inna'ilaihirrajiun!!! Ina Salim ɗin me hakan ke nufi"

Nurses aka kira "ina doctors ɗin suke?" cewar Ubaid. Dr.Faisal da Umar suna office, Dr.Salim ya je gida amma ankira shi yana hanya" Dr.Salim ne ya shigo da sauri tare da sauran likitocin, suka zube a ƙasa don kai gaisuwa " tunda ta haihu ance bata motsi meyasa me ta?" Dr.Salim ya tashi yana ɗaukan Stethoscope ya shiga gwaje-gwaje, doctor Umar ya tashi ya na duba idanunta, "she's in Comer fa" Dr.Salim ya ce"I know doctor Umar" Sarki Suhaid ya ce"meke faruwa ne naji kuna faɗin Comer" Dr.Salim ya ce"ka kwantar da hankalinka ranka ya daɗe, sometimes ana samun haka dalilin damuwa da mai ciki take shiga, amma hakan ba komai ba ne in sha Allahu zuwa wani lokaci zata dawo normal" Umma ta ce"innalillahi wa'inna'ilaihirrajiun!!!" Sarki Suhaid ya ce" dole ne a shirya tafiya Saudiya domin nema mata lafiya" da sauri Dr.Salim ya ce" wallahi ranka ya daɗe zata samu lafiya ka ba ni nan da kwana biyu, daman ana haka ko doctors" Dr.Faisal ya ce" Ranka ya daɗe kamar yanda suka faɗa, ana samun haka ba matsala ba ce, ka bamu nan da wani lokaci in Allah ya yarda zata samu lafiya batare da an je wata ƙasa ba" yadda likitocin suke da tabbaci yasa suka ɗan ji relief.

Sai lokacin ya kalli kwalin da gawar jaririyar take, kwakkyawa ƙatuwa da ita, Dr.Salim ya ce" sai haƙuri Allah ya baka masara" Mai martaba ya ce"Allah ya sa mai ceton mu ce" ya juya don kar hawayen da ya taru a idanunsa su zubo gaban talakawansa, tare da gawar suka koma aka yi mata suttura aka binneta a cikin makabartarsu.

Bayan tafiyarsa aka kai Fulani Amina KMC hajaran majaran, drip aka sa mata, ana ta tausayin ahalin mai martaba jin wai jininta ne ya hau, jin labarin abinda aka samu ya koma, wasu har da hawayen tausayin matan maimartaba, sai dare aka sallami Fulani Amina, bayan taje ɗakin Fulani Rahama ta ganta kamar matacciya anan ma ta nuna tashin hankali, ta na neman suma, sai da nurses da kuyangunta suka fito da ita.

CIROMA UBAID FAM

Ubaid Abdallah wanda yake riƙe da sarautar Ciroma na garin Hauren Giwa yana da mata uku tare da ƴaƴa goma sha biyu, Hajiya Binta ita ce uwargida tana da ƴaƴa biyar maza huɗu mace ɗaya, kuma ita ke da manyan ƴaƴa Abdallah shine babba sai Abubakar, sai Umar, sai Suhaid(Ameer), da kuma autarta Abida, Hajiya Nafisa itace ta biyu tana da ƴaƴa uku Fa'iza, Dawud da kuma Aisha, sai Hajiya Sadiya wacce take ta uku kuma amarya tana da ƴaƴa guda huɗu Zainab, Khadija, Aliyu sai auta Usman, duk kansu sun taso cikin gata da sangarta irin na sarauta.

Burin Hajiya Fatima shine sarautar Hauren Giwa ta dawo hannun Mijinta wanda yake ƙani ga Sarki Suhaid, ganin hakan bai samu ba yasa ta ke fatan ta dawo hannun ƴaƴanta, sanin Sarki Suhaid ba shi ɗa bare jika.

Kishi suke sosai tsakaninsu babu wacce take ƙaunar ƴar'uwarta kowacce burin sarauta ta dawo ɗakinta take, lokacin da labarin cikin Fulani Rahama ya je musu, ba ƙaramin tashin hankali suka shiga ba, musamman Hajiya Binta, duk wani tuggu don ganin cikin bai zauna ba sun yi, amma Allah ya kare abin sa, hankalinsu bai kwanta ba sai da suka ji abinda aka haifa ya koma.

Zaune yake cikin damuwa yana jan casbahar da ke hannunsa. "Assalamu alaikum" Hajiya Sadiya ta shigo, a hankali ya amsa"wa'alekissalam" zama ta yi kusa da kujerar da yake kai ta ce" ranka ya daɗe, har yanzu baka ci abincin nan ba?" ɗagowa ya yi idanunsa jajir ya ce" ta ina zan iya sa wani abu a cikina, alhalin ɗan'uwana yana cikin damuwa, wallahi da ina da yadda zan yi da na samawa Mai martaba magaji sai dai kash!!! Allah kaɗai ke bawa wanda ya so haihuwa" dogon numfashi ta sauke tana faɗin "hakane, kai gashi ya baka yawan zuri'a shi kuma bai ba shi ba, kuma ba wai don baya son sa ba a'a kawai saboda haka ya so kasan shi Allah babu mai masa dole" ya ce" astagafullah Allah ka azurta Maimartaba da samun magaji ta tsatsunsa" Hajiya Binta da ta shigo parlour'n ta amsa da "Ba amin ba" a zuciyarta sannan ta yi sallama, Sadiya ta shiga zuba masa dashishin da aka yi don Ubaid yana son abincin sosai, ganin Binta yasa ya ce" ya kika baro Fulanin?" Tace "ah jiki ya yi sauƙi don yanzu ma na ƙara kiran mahaifiyarta ta ce min da sauƙi har ta farka ta sha tea" take ya ji daɗi yana faɗin" Allah ya bata lafiya" galla masa harara ta yi ƙasan zuciyarta tana ganin shashanci da wauta irin na mijin nasu, da bai ɗauki sarautar da wani mahinmanci ba.

Wani saurayi ne ya shigo wanda shekarunsa ba su haura ashirin ba yana sanye da kayan sarauta, cikin nutsuwa ya gaishe da mahaifinsa, Abdallah kenan babban jika ga late Sarki Abdallah Ibn Zayeed mahaifin sarki Suhaid da Ubaid, cike da son ganin ɗan nata Hajiya Binta ta ce" ka dawo kenan" Abdallah ya ɗaga kai gami da faɗin "tun safe na dawo aka ce kuna hospital wajen Fulani" ta ce" wallahi kuwa ta haihu kuma abinda aka samu ya koma" Abdallah ya ce" eh da yake muna tare da su Ansar mun jima a wajen Mai martaba ai" ta ce" hum daɗin Abubakar kenan da shine da tuni ya neme ni" Ubaid ya ce" ina kwanciyar hankalin da zai yi haka ya dawo ƙasar gida a hargitse" tace" hakane kuma" Tashi ya yi ya nufi ciki don hutawa.

Abdallah Karatu yake a ƙasar Europe, shekara biyu kenan bai zo ba sai yanzu, mutum ne mara son hayaniya da duk wani Abu wanda danganci sarauta, duk da mahaifiyarsa na son sa masa son mulki tun yana ƙarami, amma shi ba shi da wannan ra'ayi.

An sauyawa Fulani ɗaki a KMC hospital sosai ake bata kulawa, tsawon kwana bakwai tana kwance, don duk lokacin da Dr.Salim ya faki ido sai ya yi mata allurar kashe jiki, Malam Rabi'u kuwa kullum cikin kawo rubutu yake ana shafa mata a jiki, duk sun faɗa daga shi har Umma, cikin dare Rahama ta farka, ɗauke da salati gami da miƙa, a furgice Umma ta farka daga baccin da ya ɗauketa bata shirya ba............

Anya kuwa kuna jin daɗin labarin nan kuwa???

***

Zinariya ce✍🏻