FreeThe story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Rubutu wata hanya ce ta isar da sako ga al'umma. Allah ka ba mu ikon rubutu alkhairi ka sa mu amfani al'umma
Sample · Chapter one
___Cincirindon mutane ne cike a wani waje ana ta jimami da al'ajabi, in banda salati da hailala babu abinda ke tashi a wajen.Innalillahi'wa'inna'ilaihirrajiun! yanzu ɗan mutum aka zo aka yasar anan wajen" wata tsohuwa ta faɗa tana tafa hannuwa gami da kama haɓa. Da sauri Malam Bala ya ɗauki jaririn da aka naɗe cikin zani, yana ta canyara kuka, cikin galabaita."Mace ce" cewar Malam Bala, gaba ɗaya manyan gurin suka ƙara ruɗewa, kasancewar safiya ce sosai gari bai gama haske ba, Inna da buhunta na shimfiɗar sallah da ke hannunta ya faɗi tace" Malam Bala ka tabbata mutum ce?" Malam Ashir ya ce" gashi kuwa kina gani Inna" take ta hau tsinuwa da la'antar wanda ya yarda jaririya a mararrarbar hanya cikin ciyayi, abin ka ga ƙaramin gari take maganar ta baza ko ina, guri ya kuma cika da mutane yara da manya.Ya kamata mu kaita gun Maigari, mutane sai faɗin kawota nan Allah sarki baiwar Allah s...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.