CHAPTER FIVE
TAEESH
(The child that Lived)
©Rahinat Hussein (R. Hussein Zinariya)
Marubuciyar
SILAR ƘANIN MIJI
IFFAH KO HIBBAH
AZIZAN BABA
SAKIN WAWA
ƘADDARATA CE
LUBE BODARA
MIJIN DARE
MASARAUTARMU
ƊAUKAR FANSA
NOW
TAEESH (The child that lived)
DIAMOND GLOW PEN'S💎🖊
```Haske a Rubutu Haske a Zuciya```
FREE PAGE 5
بسم الله الرحمن الرحيم
______Zaitun ce tare da rakiyar kuyangunta Indo da Atine "a fito lafiya ranki ya daɗe" suka tsaya daga bakin slither door ɗin, shiga ta yi da sallama, cike da girmamawa su Umma suka amsa gami da yi mata sannu da isowa, cikin shan ƙamshi ta kalle su, kallo irin na ƙasƙanci sannan ta zauna tana harɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya.
"Sannu Rahama ashe haka abu ya faru?" ta faɗa tana hura hanci, Fulani Rahama ta yi murmushi tace"haka Allah ya hukunta" ta ce "Allah ya ji ƙan Gambiyar Hauren Giwa yasa mai ceton mu ce" amin amin" Umma ta amsa.
Baba kuwa tunda suka gaisa da Fulani Zaitun ya nufi zaman Fada.
Miƙewa ta yi tana faɗin "Allah ya baki lafiya" ta nufi ƙofa don ficewa, cak ta tsaya ganin Umma bata taso don buɗe mata ƙofa ba, a fusace ta juyo.
"Ni fa ƴar sarki ce jikar sarki jinin sarauta ke yawo a jikina, kowa yasan sarkin Zazzau na yanzu yaya na ne uwa ɗaya uba ɗaya, tunda aka haife ni ban taɓa buɗe door da hannuwa na ba sai yanz....."Allah ya huci ziciyar ki ranki ya daɗe sha'afa na yi" cewar Umma tana buɗe mata ƙofar. "mtsww!!!" ta fita da hanzari, bayinta suka mara mata baya.
Haɓa Umma ta riƙe tana faɗin"toh ikon Allah" Fulani Rahama da ta ji babu daɗi tace" ki yi haƙuri Umma duk ni na janyo muku ƙasƙanci" Umma tace"kul kar ki ƙara ɗorawa kanki, hakan hukunci ne na Allah, shiya ƙaddara aure tsakanin ki da Mai martaba kuma ya sanya rabo don haka kar ki ɗauki wannan abun da Fulani ta yi wani abu, banda abin ki ma Rahama ai gaskiya ta faɗa ke da ita akwai bambanci" haka Umma ta dinga nuna mata hakan ba komai ba ne don wata rana sai labari.
Fulani ta Gabas kuwa da ta shigo, fuskarta cike da alhini, da kaɗan Umma zata girmeta, cike da girmamawa gudun kar a kwata Umma ta tareta, zama ta yi tana faɗin" sannu Fulani ƙarama, Allah ya baki lafiya, ba mu ji daɗin wannan al'amari ba, Ubangiji ya bamu haƙurin wannan rashi" cikin nuna jin daɗi suka amsa da amin, Umma ta ƙara da cewa"to ya za a yi sai haƙuri Allah ya sa hakane mafi alkhairi" Ta gabas tace"amin ya Allah, kina dai cin abinci sosai ko don kinga yanzu jikin ki ɗanye ne" Rahama ta ce" eh ranki ya daɗe" Ta gabas ta ce" don Allah a dinga kula da ita Umma don ta samu lafiya sosai, nan da wata tara mu sami wani" ta ƙarasa da shu'umin murmushi.
Dariya Umma ta yi tana faɗin" Ranki ya daɗe anya kuwa" Ta gabas ta yi murmushi tana ɗaukan Inibi ta miƙawa Fulani Rahama karɓa ta yi tana godiya, sannan ta ɗauki Banana ta ɓare da kanta ta shiga ci cikin nishaɗi, sosai ta saki ranta, babu wani alama da zai nuna tana kishi ko baƙinciki da auren Rahama.
Masu yi mata hidima ne suka shigo hannunsu ɗauke da wani baban faranti na azulfa, cike da kayan ado irin na matan Sarakuna, suka ajiye, tace" ga wannan daman na tanada ne saboda zuwan Yarima ko Gimbiya" godiya sosai Rahama ta yi, ta ji daɗi sosai da wannan karamci na Fulani ta Gabas, duk da tasan kansu a haɗe yake da sauran kishiyoyinta, amma bata nuna mata ƙiyayya kamar Fulani Zaitun da Fulani Amina ba.
Fulani Amina kuwa sai dare sannan ta zo tayi mata jaje, ita ma ta bata kyauta kamar yanda suka shirya ita da fulani ta gabas, Fulani Zaitun kuwa sai da ta tabbata sarki Suhaid ya shigo, sannan ta sa bayinta suka kawo ta ta kyautar ga Fulani Rahama, sosai Sarki Suhaid ya yi murna ganin yanda matan nasa suka nuna bajinta.
Bayan kwana arba'in da sallamo Fulani Rahama, ta warware sosai, Dr.Salim yana zuwa dubata kuma komai normal.
Bayan fitowar Dr.Salim daga ɓangaren Fulani Rahama, direct na Fulani Zaitun ya nufa, dalilin son ganinsa da take.
A shingiɗe take jikin tum-tum ana yi mata tausa ta sha ado da farar alkibbah, tana kallon Zee world, "ranki ya daɗe likita ya iso" cewar wata dattijuwa mai yi mata hidima, "ya shigo" ta faɗa tana komawa saman kujera.
"Assalamu alaikum" ya yi sallama, Atine da Indo suka amsa, suna barin parlon, "shigo mana doctor" ta faɗa tana nuna masa wajen zama "bisimillah" zama ya yi yana gyara coart ɗinsa.
"ranki ya daɗe yanzu Sallama yake sanar da ni kina son gani na" tace" hakane daman so nake ka ɗora waccen matar akan tsarin hana ɗaukan ciki" Dr.Salim yace" hmmm family planing kenan" tace" eh saboda ina gudun kar ta ƙara ɗaukan wani cikin a haifa mana masifa" Dr.Salim yace" an gama ranki ya daɗe, muna da hanyoyin tsarin iyali kala-kala akwai wanda ake allura, we have two types of injection it's nouris,and depor, su waɗan nan allurai ana yinsu ne bisa tsarin wata akwai wacce bayan wata biyu ake yinta ita ta ƙananan mata ce, waɗanda shekarunsu ba su jaba, sannan ana yin ta wata uku waɗanda shekarunsu sun ɗan ja, irin sun haihu da yawa kuma ana buƙatar hutu, sannan akwai roba da ake sawa suma iri biyu ne akwai implant and jardel, ita implant ita ce wacce ake sawa tsawon shekara uku, while jardel Kuma tana ɗaukan shekara biyar, sai kuma pills da muke da su, akwai na kullum wanda yake twenty four hours, ma a na kullum ana shan guda ɗaya, sai dai kowa da wanda ya karɓe shi,sannan ana ɗaure bakin mahaifa ma" Fulani Zaitun tace" to yanzu wanne tsarin kake ganin za a yi mata?" shiru ya yi na ɗan jim kaɗan sannan yace" gaskiya idan aka yi mata allura yanzu, nan da wata biyu kuma aka sake zata fahimta don kinga mutum yana da lafiya ai ba za a yi ta yi masa allura haka nan ba" tace" to a ɗorata akan maganin mana" yace" to garama shi ɗin, sai na fake da na gyaran mahaifa ne,amma shima naɗan lokaci ne idan ta daina zata iya ɗaukar ciki,ko kuma ta yi tsallaken rana, to idan aka yi rashin dace ta yi mu'amala nan ma zata iya ɗaukar ciki" fusata ta fara yi, "kai dalla malam idan ba za ka iya ba ka faɗa min in nemi wani" jiki na rawa yace" Allah ya huci zuciyarki ba wai bazan iya ba ne, ka da a samu matsala ne ace daga ni ne" babu wata matsala kawai ina so a yi mata allurar daga baya sai ka ɗorata akan magani, burina kawai a lalata mahaifarta" take yace"angama Allah ya baki nasara yaushe kike so a fara?" yanzun nan nake so, ka koma ka sanar da ita anjima zaka dawo ka ƙara dubata anan nake so ka aiwarta aikin" take yace"angama ba ki da matsala" sai lokacin ta saki murmushi, kuɗin da ke gefenta three rappers ne ƙimanin dubu ɗari uku ta miƙa masa, da hanzari ya karɓa yana godiya, ya buɗe brief case ɗinsa na kayan aiki ya saka,sannan ya tafi.
Wani daɗi ne ya ziyarci zuciyarta tana murmushi "idan kinsan wata ai baki san wata ba banza ƴar matsiyata" yana barin part ɗin ya bar gidan gaba ɗaya, gidansa ya koma.
Parker motarsa ya yi a waje, key da ke hannunsa ya sa ya buɗe ƙofa ya shige ciki, Zainab da suke ta hira da ƙanwarta Aisha wacce ta kai mata ziyara ta ɗago tare suka amsa sallamar doctor, cikin sabo Aisha ta ce"doctor ina kwana" yanda ya amsa "lafiya lau" babu walwala bare wasan barkwancin da yake mata, ko tsokanar mijinta da yake yi, kasancewar shi, ƙato mai jiki sosai, ita kuma ƴar ƙarama.
Wucewa ɗakinsa ya yi, kallon juna suka yi tsakaninsu Zainab tace"ina zuwa" ta bi bayansa, zaune ta same shi agefen gadonsa yana dannan waya."salama alaikum" ta faɗa ya ɗago yana amsawa, "lafiya kuwa doctor?" lafiya lau me kika gani?" to gani na yi ka shigo kamar akwai matsala" ta faɗa, yace"no babu wata matsala kawai yanayin aiki ne na gaji sosai" ayyah sorry my dear, ai kuna ƙoƙari ma, bari in haɗa maka ruwa ka ɗan watsa sai ka yi breakfast ka kwanta" yace"yau ba ki je aiki ba ne?" tace"eh ba ni da shari'a yau sai next week, da ke kasan muna kan haɗa evidence ne akan rapping ɗin da ɗan Alhaji Musa ya yi wa ƴar aikinsu, dake kasan abun na manya ne, har yanzu yaron ya ƙi amsa laifinsa hasalima cewa akai ranar da abin ya faru baya gari, duk sun toshewa sauran ma'aikatan baki da kuɗi" doctor Salim yace"oh my God wannan ƙasa ta mu sai addu'a an zalunci yarinya kuma an hana a ƙwatar mata ƴanci" tace" Allah yana bayan mai gaskiya" ta nufi toilet ta haɗa masa ruwa a bathtub sai ƙamshin turarukan wanka ruwan yake.
Sai da zai shiga tace" zan je in ɗauko Taj a school" yace" ina Ado ba shi yake ɗauko shi ba" tace" me ai tunda abin nan ya faru ni na ke ɗauko su da kaina, ai yanzu babu yarda a wannan duniyar" yace"okay ya yi" ya shige toilet.
"Lafiya kuwa" cewar Aisha wacce take ta zullumi akan mood ɗin da ta ga doctor " wai gajiyar aiki ce, har yama warware, key ɗin motarsa ta ɗauko "zo ki raka ni in ɗauko Taj a school" a'a ni tafiya zan yi, ki ajiye ni a bakin titi kawai" cewar Aisha.
Zainab ta ce" A'a kin manta uwar tafiya za ki yi, yaushe ma kika zo gidan nawa da za ki ce wani tafiya za ki yi" Aisha tace"doctor ya dawo zan zauna wallahi tafiya zan yi, haka kawai ku barni ni kaɗai kina can kuna shan soyayya hahhh" duka Zainab ta kai mata tana faɗin" Allah ya shirye ki Indo hahh" dariya suka yi, ta goya Ikram suka fita tare.
Har Saudat international academy suka je tare, ta ɗauko Taj yaron bai fi four years ba, Suhaima da ke da seven years ta zo tana faɗin"lah Mommy'n Ikram ina wuni" cike da murna, Aisha tace"Suhaima ƴan mata ya studies hope dai kina ƙoƙarin nan da na sanki da shi" eh ina yi ki tambayi Mami ma" Taj ta ɗauka, Suhaima na ɗaga musu hannu bye, don ita sai five thirty za su tashi.
Shima Taj ɗin dan a pre-nursery yake ne, da an shiga primary one sai yamma ake tashi, Saudat International academy babbar makaranta ce, don tun daga breakfast har lunch suke yiwa students, kuma sai abinda ɗalibi yake so zai ci. Suna da clinic a ciki don accident and emergency don kula da lafiyar yara.
Tunda ya fito ya ji karsashi a jikinsa dining area ya nufa duba abinda ta girka ya yi,chips and egg ne sai tea na na'a-na'a sai kuma kunun tsamiya da cowleg ɗin da ta yi warming. Sai da ya cika tumbinsa, sannan ya koma ya kwanta bacci Mai nauyi ya ɗauke shi.
Barrister Zainab na dawowa ganin ya na bacci ta hana Taj zuwa don kar ya tashe shi.
Barrister Zainab lawyer ce mai zaman kanta, shekara kusan goma tana aiki, don da aikinta suka haɗu da doctor Salim har suka yi aure, shekararsu takwas da aure a yanzu, suna zaman lafiya tasan yanayin aikin mijin nata don wani lokacin sai ya kwana biyu a KMC hospital ma.
Dr.Salim saboda lambobin yabo da yake samu har kungiyoyin duniya sai da suka yi awarding din sa irinsu UNICEF, WHO da sauransu. Around four o'clock ya tashi don ya ji daɗin bacci sosai, a gaggauce ya kimtsa ya nufi kmc hospital
Zaune take tare da Mai martaba a ɓangarensa, ta sha ado sosai duk inda ta motsa ƙarar warwaro ke ratsa kunnuwan sarki Suhaid, sanye take cikin abaya ƙirar Dubai, da ganinta kasan tsadaddata ce.
Cikin kulawa da so da ƙauna ta dubi Sarki Suhaid tace" ranka ya daɗe passports din su Umma ya fito banda bakin godiya sai dai fatan alkhairi, Allah ya saka da alkhairi ya jiƙan iyaye" murmushi ya yi yana ɗora hannunsa akan lip ɗin ta"shiiii banaso,addu'a kam na amsa amin, nima San Dawaki da Umma ai iyayena ne, ni dai fatana shine mu ci gaba da addu'a Allah ya kawo mana wani rabon mai amfani" kasa amsawa ta yi, sai ƙasa da ta yi da kanta.
Ɗago haɓarta ya yi, yana ɗaga mata gira da sigar tambaya, murmushi ta yi, kwantar da ita jikinsa ya yi, yana jin nishaɗi.
CIROMA FAM
Hajiya Zainab ce ke tafiya cikin wani ɗan ƙauye ƙafarta duk ta yi ƙura, wani gida mai kama da kufai ginin jar ƙasa ta shiga.
"Awohun ku dai masu gida" wasu mata da ke zaune akan duwatsu a tsakar gidan, suka amsa "awoho-awoho" wata mata ce zaune cikin shigar kayan Fulani na maza har da sandarta, tana wasu zantuttuka cikin harshen fillanci.
Ga magunguna kala-kala cikin kwaryaye, wani ihu tayi gami da ashariya sannan ta zube kumfa na fita daga bakinta.
"Sannu da zuwa arne uban arna sannu da zuwa lale lale, cewar Hajiya Zainab da wadadan nan matan.
Sai da aka fara ganin waɗanda suka riga sannan aka zo kan Hajiya Zainab matar Curoma, tamkar wacce take gaban Ubangijinta ta duƙa tana kai gaisuwa ta ajiye wasu kuɗi a gaban wannan bokanya mai suna Uwa-uwa.
"zuwa na yi godiya arne aiki ya yi yanda nakeso, ta haifi cikin babu rai" Zainab ta faɗa cike da farinciki " hahh hahh hahhh sai ni tsinanne uban tsinannu sai ni wakilin shaiɗan ɗan iblis kowa ya zo gare ni ya samu biyan buƙata a duniya, yanzu me kike so a yi?" gyara zama ta yi tace" yauwa Arne so nake a sawa mijina son sarautar garin ya ji indai bai hau mulki ba, ba zaman lafiya kuma a jefa gaba tsakaninsa da ɗan'uwansa, sannan ya dawo tafin hannuna sai abinda nace masa" dariya bokanya Uwa-uwa ta yi tana faɗin wasu surutai marasa ma'ana.
Wani ɗaurin magani ta ɗauko a ƙwarya ta miƙa mata, da biyayya ta sa hannu biyu ta karɓa.
"wannan magani ki ajiye shi, idan kina jinin haila ki ɗebi jinin ki zuba a kwalba ƙarama sannan ki zuba wannan garin maganin, ki samo makahon Damu ki sa wannan kwalba a bakinsa, ki bunne shi a maƙabarta, angama, don ko wuta kika ce ya shiga da gudu zai faɗa" Hajiya Zainab sai ta hau murna, tana faɗin " godiya nake Arne mai share mana hawaye" wani maganin ta ɗauko a ɗaure da tsumma kamar ganyen ciyawa, " wannan kuma a dake shi a haɗa da kashin Jaki a samu zuciyar rago da allura ɗari ba ɗaya a caccaka a jikin zuciyar a zuba maganin a samu likkafani a naɗe a ciki, sai a jefa a tsohuwar rijiya wacce bata taɓa ƙafewa ba, indai sarauta ce sai ta dawo hannunki" rasa inda zata sa kanta ta yi don murna.
Kirari ta shiga yi wa aljanin mai suna Arne, ta yi godiya ta tashi ta tafi.
Driver'nta amintaccenta Jazuli yana zaune a mota yana jiranta, ta fito daga cikin garin, cikin rawar jiki ya fito yana buɗe mata motar yana faɗin" barka da fitowa ranki ya daɗe" ta shiga tana faɗin" zo mu tafi kar magariba ta yi mana a waje" to ranki ya daɗe, a gurguje ya hau motar suka tafi..............
Zinariya ce ✍🏻