TAEESH

CHAPTER NINE

by @zinariya0102

_____Sharewa ta yi tamkar bata ji abin da Wasila ta ce ba, " barkan ki da zuwa, wai amma gaskiya kin ɗauko rana" Buhun kayan ta sauke, tana faɗin " lallaima A'i ke kuwa akan ba ki haihuwa shi ne kike riƙon ƴar tsuntuwa, ai kamata ya yi ki nusar da mijinki ya gane illar hakan, amma abin mamaki ki ka karɓa" A'i ta ce" ɗa ai na kowa ne Wasila, bari in shigar miki da kayan sannu" Buhun ta kama ta kai spare room, babu komai a ɗakin sai ɗan shirginta da ke gefe, Wasila dai sai taɓe baki take ta zauna a ƙasa ta na cin gyaɗarta, da sauri A'i ta goye TAEESH ta ɗauko tabarma ta shimfiɗa mata a falonta wanda yake tsaf da shi, sai dai babu kujeru daga labule sai wata tsohuwar t.v ƴar ƙarama da radio a kan wani tsohon table, Wasila ki shigo ciki mana, kin zauna a ƙasa sai ka ce wata baƙuwa" ce war A'i.

"Hum ko baki faɗa ba zan higo ai matar Yaya Ali" sannan ta miƙe ta hau karkaɗe ɗuwaiwanta ta shiga, jaɓar ta zauna tana miƙe ƙafa, " wai Allah alkur'an na gaji, bari na ɗan huta sai na tahi na yi sallah" ta faɗa tana kishin giɗa, farar shinkafa da manja A'i ta zubo a kwanon langa irin ta daa, ta zuba yaji da manjan, " ga abinci" ta ajiye mata, Wasila ta gyara zama, ta buɗe kwano, yawun tane ya tsinke ganin shinkafa, "lah hahhh alkur'an hiyasa nake son auren Ali gidanhi(shi) akwai hinkaha(shinkafa), ta faɗa a hankali sannan ta duma hannu ta juya ta du, ta hau zuba luma, A'i ta kuma shigowa ɗauke da ruwa a kwano ta ajiye mata, sannan ta zauna tana faɗin " ko gaisawa ba mu yi ba, ina wuni" Wasila da ta cika baki da abinci, ta hau faɗin " lafiya lumul" A'i ta ce" ya su Kawu fatan kowa lafiya" lafiya" ta faɗa a taƙaice tana ɗaukar kwanon ruwa ta kafa a baki, ƙwat-ƙwat kawai ka ke ji, sannan ta ajiye ta cigaba da cin shinkafa, tas ta tashi da abincin da zai ishe su da daddare ita da Ali da ƴarsu TAEESH, ƙaaaaahhhh ta saki uwar gyatsa, ta goge hannun a jikin zani, sannan ta haɗe da na hagun ta mutssukesu, duk hannun ya gauraye da nason manja.

"Yayan baya nan kenan" ce war Wasila, A'i ta ce" eh ai sai yamma zai dawo" Wasila ta ce"au to na hya (sha) ya yi balaguro ne ahe yana gari" A'i ta ce " yana nan, na ji an kira la'asar ba ri in zuba miki ruwa mu yi sallah" Wasila ta ce "uhum tom" har A'i ta kwantar da TAEESH da ta yi bacci ta yi alwala ta yi sallah, Wasila bata fito ba, ɗakin ta koma tana faɗin " ki fito ga ruwa..." maganar ce ta tsaya ganin Wasila ta baje tana bacci, komawa ta yi ta shiga aikin yamma, kafin mijinta ya dawo.

Sai biyar da mintina sannan Wasila ta tashi ta fito, tana hamma da miƙa ta gantsare, babu bra a jikinta, nunuwanta a tale suna reto, buguzun-buguzun ta ɗauki buta ta yi banɗaki, shaaaa ƙarar fitsarinta har tsakar gida, tamkar an kunna famfo, Ai ta zabga tagumi tana tsoron Wasila, tasan ƴar tijara ce, don akwai lokacin da suka je garin na Dumama, a gaban kowa Wasila ta dinga faɗar "ai da tuni ni ce matar Ali, rabon sai na haifi ƴaƴa biyar da ke wani baya haifar ɗan wani" babu wanda ya hanata, tunda A'i ta ji, tasan tantirancin Wasila ya shahara.

Alwala ta yi son ranta, " ina kika samin kayan nawa?" A'i da ke gyaran wake ta ce" yana ɗakin can, akwai sallaya a ciki" ɗakin ta nufa, taga tabarma a shimfiɗe har da filo da mayafin rufa, duk da tsoho ne amma a wanke yake fes, sai mafici a gefe. Gyalen da ta zo da shi, ta sa ta yi sallar Azahar da la'asar, sannan ta fito, ta hau kan turmi tana kallon A'i TAEESH na gefenta tana wasa da kayan wasa irinsu gwangwani ƴar tsanar roba, da abin kacau-kacau na roba.

"Har kin idar?" ce war A'i, Wasila ta ce" iyi mana, wai har yanzu bai dawo ba ne, ni fa na matsu na gan hi?" A'i ta ce" yana hanya ba kwana za ki yi ba ne?" Wasila ta zari tsinsiyar kwakwa ta hau sakace haƙora ta ce" kwana har da kwanaki ma, ai zan ɗan daɗe anan" A'i ta yi shiru tana ci gaba da gyaran shinkafa.

"Ni wai A'i in tambaye ki mana?" ce war Wasila, " ina jin ki" don Allah meyasa kike hana matan Yaya Ali zama ne?" murmushi A'i ta yi tana faɗin " ai ba ni nake hanasu ba, ai kamata ya yi ki je da kanki ki tambayi dalilin da ya sa suke barin gidan" Wasila ta ce" tab yo dalili ai kowa yasan dalili kin kafa kin tsare kin hana kowa higowa gidanki ke kaɗai kike sha'aninki yo wa ya isa ya higo" A'i ta ce" hmmm haka dai ake ce wa, amma idan malam zai aure ni ai ban isa in hana shi ba" da sauri Wasila ta ce " woooo tabdijan ai kowa yasan kin isa don kin fi ƙarfin hi, amma kowa yasan Yaya yana buƙatar ƙarin aure ko dan ya sami haihuwa" A'i ta ce" meyasa kuke mantawa da ce wa haihuwa ta Allah ce, ku dangin miji sai ku ɗauki laifi ku ɗorawa mace ku ka sani ma ko matsalar daga shi ne" a'a tuf-tuf a tufar da mugun miyau, Yaya Ali ai ansan irin haihuwa ne alkur'an, ki bahi dama ya auri wata ki gani, ina mai tabbatar miki a wata guda, sai kinga matarsa da ɗan kunhi" ta ce" sau nawa ya yi auren, har su shekara babu abin da ya yi kama da kun shin da kike faɗa" Wasila ta ce" a dai ji tsoron Allah" ran A'i ne ya fara ɓaci, tashi ta yi ta shige ɗakinta.

Kuka ta sa tana jin ciwo da baƙin ciki mara misaltuwa a zuciyarta.

"kenan an turo ta ne ta zo ta hanani sakat a gidana, wannan wace irin ƙiyayya ce sama da shekara sha ban huta ba" ta faɗa tana kifa kanta kan gado, sosai take kuka dan kalaman Wasila sun taɓata sosai.

Kukan TAEESH ta jiyo, da sauri ta gyara fuskarta ta fito. Wasila na zaune ta ce" ke dalla yi mana shiru, hegiya mara asali" A'i ta ɗauketa ta yi zaure, Hassana ta hango kiranta ta yi ta miƙa mata TAEESH ta ce" ki kaiwa Lami ita ki ce ta zo ta gaishe ta" Hassana ta kai hannu zata karɓeta, TAEESH ta ƙi yarda, A'i ta ce" ku je maza ku siyo mai daɗi" tana ɓanɓare TAEESH ɗin, ganin yawo za a fita yasa ta yarda da Hassana suka tafi.

Ta dawo ta ci gaba da aikinta, Wasila na kallonta, sallamar Malam Ali suka ji, ya shigo da kekensa, da sauri Wasila ta miƙe tana washe baki, hannu(sannu) da zuwa Yaya" Malam Ali ya ce" yauwa baƙuwa muka yi kenan" A'i na yunƙurin yin sannu da zuwa, Wasila ta karɓe ledar da ya shigo da ita ta ajiye tana ƙoƙarin zare masa fatanyar da ke kafaɗarsa, gocewa ya yi yana faɗin" sannu da ƙoƙori na gode, ya mutanen gidan" ta hau sosa kai tana faɗin " duk lahiya lumu, ai sun ce a gaiheka" ya ce" ma sha Allah, ina amsawa, ina Uwata ne ban ji taba?" ya juya maganar kan A'i sai lokacin ta samu damar magana " sannu da zuwa malam, yanzu nan suka tafi gidan Lami ita da Hassana" Ali ya ce" ba na son ta dinga nisa da gida, ga magriba ta kusa" shiru A'i ta yi tana ɗaukar ledar da Wasila ta ajiye, ɗanyen Nama ne sai kayan miya har da mai da maggi, ya ce" ki ɗan ɓararraka mana mu ci, Alhaji Musa ne ya zo duba aikin gonarsa shi ne ya bamu kuɗi, na biya kasuwa na siyo mana" ta ce" kai amma ya kyauta, daman kwana biyu ba mu ci nama ba" Wasila na jin ance nama ta hau faɗin "kawo in dafa" A'i ta ce " a'a barshi ki huta"

Ba ta so ba dai ta haƙura, satar kallon Ali ta hau yi, kyau ya ƙara yi mata, gashi ɗan cas da shi, kamar bai haura shekara arba'in ba.

Ya ce " ya su Kawu Wasila?" ta ce" kowa yana lahiya Yaya, ai Kawu ma ya yi jinya sosai, kusan wata shida akwance, yanzu ma da ƙyar ya bar ni na zo, ya ce ya yafe ka a dangi muddin ba kai abin da ya ce maka ba, ni ce ma nake ta tausarsa, ta faɗa tana rausayar da kai tana sa ɗankwalinta a baki alamar ta yi abin kirki, ya kamata a yaba mata, Malam Ali ya ce" Allah ya ba shi lafiya, ai bansani ba na so zuwa can Dumaman Allah ne bai nufa ba" ta ce" a'a fa Yaya Ali ba fa kason zuwa danginka kowa ya sani" haɗe rai ya yi, ya shige ɗakinsa.

A'i dai ido kawai ta zuba musu, tana ji tana gani an hanata hira da mijinta, Wasila ta koma ƙofar ɗakin nasa ta yi zamanta, ƙiri-ƙiri an hana ta bin bayansa.

Daga ɗakin ya kira ta "Aisha" "na'am" ta amsa tana tsame hannunta daga cikin ruwan wankin kayan miya, ta nufi ɗakin, matsawa kawai Wasila ta yi, A'i ta shiga, ita kuma ta kasa kunne don jin abin da zai ce.

" kawo min ruwa na sha, ina so zan yi wanka" ta ce" to" ta fito don zuba ruwan Wasila ta ce" kawo na zuba masa ruwan wankan, ki kai masa na shan kawai" A'i ta ce" to sannu na saki aiki" Wasila ta ce" a'a babu komai" ruwan takai masa ya sha, sannan ya fito ya shiga wanka, yana fitowa ana kiran sallar magriba, ya durƙusa ya fara alwala, Wasila ce ta ɗauki ɗaya butar ta yi banɗaki, sai shaaaaa ƙarar fitsarinta har kunnensa, wani takaici ne ya turniƙe zuciyar A'i, yana idarwa ya bar wajen, masallaci ya nufa, Wasila na fitowa A'i ta ce" haba Wasila wannan wana irin fitsari ne haka" ajiye butar ta yi tana faɗin me na yi?" A'i ta ce "ki dinga haɗe jikin ki mana ai hakan bai kamata ba" Wasila ta ce" heyy hye lallai matar yaya Ali, ƴaƴa biyar fa ba wasa ba ne, kinga alamar ina da abin haihuwa lafiyayye ato kinji" Wasila tunda kika zo, kike gaya min magana banaso mu samu saɓani da ke" tooooh daga faɗar gaskiya " Allah ya baki haƙuri ni ba baƙuwar zafi ba ce" ta hau alwalarta, rasa abin da zata ce mata A'i ta yi, ruwa da omo ta ɗauka ta nufi bayin..

*****

Video call suke yi tana faɗin " yaushe za ku taso?" Umma ta ce" au so kike mu bar wannan ƙasar, ai Rahama ba don ba don ba, da na ce munga gurin zama, ba na son barin ka'aba, da da hali abar ni anan daga harami sai zuwa shabbaki har tsahon rayuwa" Fulani Rahama ta yi dariya tana faɗin " kai Umma lallai kin ji daɗin hajjin nan, to Allah ya amsa yasa maƙabuliya ce" ta ce" amin amin nan da kwana uku zamu taso in Allah ya kaimu" Rahama ta ce" to Allah ya kaimu, idan Baba ya dawo a gaishe min da shi. " to sai anjima ki kula da kanki ki gaishe da mai martaba" da haka su ka yi sallama.

Batula ta karɓi wayar tana faɗin " ranki ya daɗe ina son na ganki cikin farin ciki, Allah ya ƙara miki lafiya" murmushi Fulani Rahama ta yi tana faɗin " Batula ba ki da dama, ke dai idan ba ki yi surutu ba ba kya jin daɗi" ɗaya baiwar ta ta Ruƙayya ta ce" ai ranki ya daɗe wallahi dama ta samu, ta yi a wani gurin mana hahhh" ta ƙara da dariya Fulani Rahama ta ce" ku dai idan aka daka ta taku sai kunsa cikin mutum ya yi ciwo" Fulani Rahama da kuyangunta akwai kyakkywar fahimta, duk sun girmeta, suna mutunta juna sosai, ga ta da alkhairi, iyayensu ma da suke bayi a gidan sun san uwar ɗakinsu ta dabance.

Misalin sha ɗaya na dare, sarki Suhaid yana tare da matansa, duk sun kanainaye shi, sun hana shi sakat, duk da sun san kwanar Fulani Rahama ne, kuma ba za ta taɓa yin magana ba, ta gabas ce ta ce" ranka ya daɗe ɗazu Mai girma Sultan Abu-Haisam ya kira ni, Mahaifinmu ba shi da lafiya ina so zan je na duba shi, Sarki Suhaid ya ce" subhanallah har yanzu Mai martaba mai murabus bai samu lafiya ba, ya salam, dole ne a shirya tafiyar gaggawa zuwa Sudan, tare da ni zamu je mu duba shi" daɗi ya kama Fulani Ta gabas, ta ce" godiya nake ranka ya daɗe" Zaitun ta ce" amma tare za mu je don mu ma ya kamata mu duba jikin nasa" Sarki Suhaid ya ce " a'a ba na buƙatar hakan, kowa ta tashi ta tafi ina so zan huta" a tare suka tashi suna yi masa sallama, Fulani Rahama ce kawai bata tashi ba.

Sai lokaci ta samu damar yin hira da mijin nata, don idan matansa suna nan to ba ta da kataɓus, idan ta cika magana sai ai ta yaɓa mata baƙar magana saboda ita ƴar talakan sarki ce, bayi masasƙanta.

Allah-Allah sarki Suhaid yake su fita ya samu ya huta da matarsa, haka nan ya ke masifar son Rahama da tausayinta, ko dan ita ce ta fara nuna masa hoton jininsa ɗa daga tsatsonsa, duk da abin da aka haifar ya koma, amma ta wanke masa miƙin da ke cikin zuciyarsa na kokwanton shi ɗin yana haihuwa ko a'a.

Ganin ya shiga tunani yasa Fulani Rahama taɓa ƙafarsa, fuskarta ɗauke da murmushi, kallo ta ya yi, yana mayar mata da nasa smile ɗin mai tsananin tsada, ta ce" tunanin me kake haka ranka ya daɗe?" showing ɗinta ya yi da nail ɗin shi, sannan ya ce" tunanin ki nake yi Gimbiya Rahama Suhaid" abin ne ya bata dariya aikuwa ta fashe da dariya, tamkar wani Wawa ya bita da kallo, mugun kyau ta yi masa, bai ƙi a ce su dauwama a haka ba, ganin ya kafeta da ido yasa ta je har kusan sa hura masa iskar bakinta a idanunsa, caraf ya cafketa, jikinsa ta faɗa ya shiga yi mata cakulkuli suna ta nishaɗi, ya manta shi ɗin sarki ne.

Sai da suka yi wasa sosai, ganin zai wuce gona da iri, yasa ta tashi tana faɗin " na manta, ɗazu mun yi waya da su Umma...." Shiiiii yanzu ba lokacin faɗar wani abu ne, soyayya zamu yi" ya faɗa cikin mayen so, kafin ta furta komai ta ji his soft lips in her mouth. Salon ne ya sauya, cak ya ɗauketa su ka yi cikin turakarsa.

Ɓangaren su Fulani Zaitun kuwa, kishi ne ya hanata sakat, duk rabar kwanan Rahama bata bacci, juyi kawai ta ke a gado sai jan tsaki.

Fulani Amina da Tagabas kuwa baccin su suke yi don buƙata ta biya, tunda sun sami doctor Salim a hannu.

Cikin bacci ta ji ringing wayarta, laluban wayar ta shiga yi, ganin new number ne yasa ta yi picking daga kwancen, "ke ce Barrister Zainab Aliyu Maitama?" Tar ta buɗe idonta tana faɗin " yes i'm?" tana sa recording, daga can aka ce " Ina so zan ja miki kunne da babbar murya akan case ɗin da kike a court, ki yi gaggawar janyewa" ta ce" ko kai wane ni, ko da me kake taƙama ba zan janye ba, har sai gaskiya ta yi halinta" daga can aka ce" to mu zuba mu da ke mu gani" ta ce" don't calling me again useless mtsww!!! Ta katse kiran.

Hantsilowa ta yi daga gadon ta nufi parlor Dr. Salim na zaune yasa system a gaba, yana ta research, "Dr. Har yanzu ba ka kwanta ba?" Ya ɗago yana faɗin " yanzu nake shirin tashi, bata nuna tsoro ko ta sanar da shi barazanar da aka yi mata ba, ta ɗauke system ɗin ta na kama shi, oya let's go" take ya kashe swatch ɗin, suka kwanta.

Da sassafe aka kira shi cikin tashin hankaki "hello, doctor Salim, kmc hospital ya kama da wuta........

Zinariya ce✍🏻