FANSAR MACE
by @mrsisham12
11 & 12_*🦋FANSAR MACE🦋*_
Story & written
By
MRS ISHAM
~The writer of ~
NIDA PATIENT DINA
ASHE ZAMUGA JUNA
ƊAYA CIKIN BIYU
MAKIRIN IKO
and now
🦋FANSAR MACE🦋
JARUMAI
WRITERS ASSOCIATION
📚📚📚🖋️🤩
11 & 12
Wanke-wanke suke yi amma kamar kara yawan kwanukan ake yi kwanuka ne himili ga manyan kuloli da manyan tukwaye,gaba daya ta ji ta galabaita ba ƙaramin gajiya tayi ba ga yunwan da take ji. Suna cikin aiki wasu yara suka zo hannun su ɗauke da plate din glass da gudu. daya daga cikin sune ya faɗi plate din hannun sa ya fashe ya yi raga-raga a gurin da sauri ta miƙe dan ɗaga yaron, amma cikin rashin sanı tana zuwa batare da ta san akwai fasassun plate din agurin ba ta taka ya yanka mata tafin kafa, wani azaban raɗaɗin da ta ji ne ya sanyata sanya siririyar ƙara tana faɗuwa ƙasa. hawaye nan take ya fara zarya a idanunta saboda yankewan da tayi ba ƙaramin yankewa bane. Da sauri ƴar aikin da suke aiki tare tazo ta riƙe kafan tana mata sannu, sosai ta ji tsoro ganin irin yankan da tayi yasa da sauri ta bar backyard din tana cikin tafiya tama rasa wa zata kira kawai ta hango Adda da Haydar suna tsaye a compound alamun magana me muhimmanci suke yi ta nufesu da sauri
“Adda yarinyar ta ji ciwo sosai “
“Wata yarinya kenan Rashida ?” Adda ta tambayeta tana kallon ta
Cikin son tuna sunan Alisha ta ce “wannan da ki ka ce muyi wanke-wanke tare da ita Ameesha ne ko Aneesha ita ce kwalba ya yanketa sosai ne kuma”
Daga Adda har Haydar lokaci daya damuwa ƙarara ya nuna akan fuskokinsu hakan yasa basu tsaya bin ta kan Rashida ba suka nufi backyard din cikin gagagwa suna shiga suka sameta a zaune a ƙasa tana kuka ga kafarta dake ta zubar da jini
“Innalillahi Alisha garin ya haka ya faru ?“ Adda ta tambayeta hankali a tashe.
Gaban ta ya isa ya tsuguna yana riƙe kafar nata ko da idon sa ya sauka akan yankan se da ya runtse idanu saboda yanda ya ji tamkar yankan a jikinsa ne, be san dalili ba yaji ransa ya yi mugun ɓaci kallon fuskarta yai yaga kuka kawai take yi tana sauke ajiyar zuciya.
Duban Adda dake tsaye akan su fuska cike da damuwa yai ya ce “ fisabilillah Adda ya zaa yi yarinyar nan daga zuwa suna a sanyata wanke-wanke dan Allah dan annabi”
“Wallahi Haydar ni kaina ban so ba ita ce tace zata yi shisa na barta,dan Allah ɗauke ta mu je bangare na ta kofan baya bana son idon mutane ya dawo kan ta”
Tunani ya fara ta ya ze ɗauketa,tunda yake be taɓa sa hannu ya taɓa macen da ba muharramarsa ba, wannan dalili yasa ya gagara ɗaukanta se kallon yanda hawaye ke gangaro daga idanunta yake yi.
“Haydar me ka ke jira ne kam?” Ya ji muryar Adda tana masa magana saboda ta ga ya tsaya be ɗauke tan ba.
Bashi da wani zaɓi da ya wuce ya sa hannunsa duka biyu ya ɗauke ta cak kamar jaririya,Alisha da ta ji kamar zata zame ne yasa tayi saurin zagoya da hannunta a wuyansa batare da ta buɗe idanunta ba saboda bazata iya haɗa idanu dashi ba.
Bangaren Adda ya nufa da ita yakai ta wani extra room da ya kasance na saukan baki ne. kawai kwantar da ita yayi akan gado amma bata cire hannayenta da ta zagaye su a wuyansa ba, hakan yasa ya dubeta ya ga har time din idanunta a rufe suke ga hawaye da suka bushe a saman kumatunta ga wasu da suke kan saukowa.
“Alishaa bari in ɗauko First aid kit “ a hankali ta buɗe idanunta da har sun fara kumbara saboda kukan da tayi ta sauke su akan sa da sauri ta janye su sanda suka haɗa ido ta koma kallon ƙasa murya na rawa ta ce “ka yi hakuri uncle “ tana cire hannayenta a wuyansa.
“Never mind “ yace sannan ya fita a dakin, be jima da fita ba ya shigo da first aid kit ya zauna a kusa da kafarta. riƙe kafar yayi yana kallo yana jin kamar ya cire mata ciwon domin daga iya kallon kwayar idanunta ya fahimci irin azabar da take ji.
Cikin yanayı na rashin jin dadi ya ce”Amma dan Allah meyasa bazaki dena wayannan aiyuka masu wahalan ba? So ki ke ki lalace da kananun shekarunki? Manyan mata ma in suna aikin wahala basa Kyan gani balle ke yarinya dake”
Yana magana ne a yayinda yake goge jinin da ya ɓata mata kafar da cotton da spirit,yatsina fuska tayi tana bubbuga hannunta akan gadon tare da jujjuya kai cikin jin zafi saboda motsa kafar ma idan yana yi har cikin ranta take jin zafi.
“Sorry Alisha” ya faɗa a tausashe a haka tana kuka din ya mata dressing din kafan nata se de kam tasha kuka sosai da se da ta ji kanta ya fara mata ciwo,fahimtar hakan da ya yi ne yasa ya bata magani ta sha,zama yayi akan kujera yana dubanta da kyau gaba daya tayi lakwas se ajiyar zuciya da take saukewa lokaci-lokaci.
“Alishaaaa” ya kira sunan ta a sanyaye
Da shanyayyun idanunta ta kalle sa jin yanda ya kira sunan nata.
“Shin bakya da yan uwane ? I mean dangin mahaifiyar ki ko na mahaifin ki,meyasa bazaki koma wajen su ba ki ka zaɓi ki zo kiyi ta wahala?”
Shuru tayi tana lalubo karyar da yakamata ta yi masa wanda ze amince da ita dari bisa dari batare da ya yi tunanin komai ba.
Marairaicewa ta yi ta share hawayen da ya gangaro daga idon ta
“uncle Haydar lokacin da iyayena su ka mutu nima na ɗauka yan uwansu zasu share min hawayena,zasu ɗauke ni tamkar yar su ashe nayi gurguwar tunani domin ba haka yake a gurin su ba. Nasha wahala sosai a hannun su duka da zagi se da yasa na ji nima da mutuwa nayi na bi iyayena,tsangoma kuwa baa cewa komai wannan dalilin yasa na tsame kaina a cikin su na gwammaci in nemawa kai na mafita wannan dalilin yasa na nemi aiki.”
Haydar zuba mata ido yayi har ta karishe magana be iya ɗauke idanunsa a kanta ba,ya jima be ji labari da ya sosa masa zuciya irin labarin da ta basa ba,hakan yasa ya ƙuduri a niyar taimaka mata ta hanya mafi sauki.
“Shin zaki zauna tare da mu anan?”
Duk da wannan shine burinta samun gurin zama a gidan Ɗan gaske amma se ta ji tambayar ta sa ya zo mata a bankwarakwai da yasa bata san lokacin da ta furta
“Ban fahimce ka ba”
Se da ya lumshe idanunsa na yan sekonni ya buɗe sannan yace “ina nufin zaki zauna anan gidan mu?”
“Uncle to mezancewa Hajja Hauwa? Ita nake yi wa aiki,haka kwatsam in ce mata ni na dawo nan na san zata ji ba dadi sosai “ girgiza mata kai yayi yana kokarin magana Adda ta shigo ta zauna kusa da Alisha tana me ɗan rungumeta
“ Na ji komai duk maganar da ku ke yi da Haydar na saurara batare da kusan ina bayan ku ba,Alisha tabbas kin ga rayuwa bana fatan kuma a ce Allah ya bamu yanda zamu taimake ki amma mu kasa. Za ki iya zama a wannan gida namu har iya lokacin da ki ke so sannan batun Hajja Hauwa kuma na san abinda zan faɗa mata “
Sosai ya ji dadin maganar mahaifiyarta sa saboda yayi niyar yaje ya same ta ne da zancen se ga shi cikin ruwan sanyi Allah yasa ta ji su. dama ya san ba ze samu matsala ta bangarenta ba saboda Adda macece me son mutane da tausayi. “Nagode Adda Allah ya biyaki “ ta fada hawaye na sintiri a fuskanta wanda a cikin zuciyarta kuma farin ciki ne ya dabaibayeta yanzu ta samu abinda take so ta samu dalilin zama a cikin gidan Ɗan gaske.
“Haydar zancewa mahaifinka Alisha dangina ce iyayen ta sun rasu shisa ta zo ta zauna damu”
Kai ya gyada mata kafin ya fita a dakin, zama Adda tayi da Alisha tana mata hira sama-sama har bacci ya ɗauke ta. ganin tayi bacci ne yasa Adda ta gyara mata kwanciya sannan ta fita tana ja mata kofa. Tunda ta fara bacci ba ita ta farka ba se goshin mangriba ta sha mamakin irin baccin da tayi domin kuwa ta jima bata yi irin wannan bacci ba. So take yi ta fita a dakin amma ba hali bazata iya takawa ba, ta rasa yanda zatayi tai ga shi sallah take son yi amma ba damar tashi. Buɗe kofar aka yi Zainab da Ameera suka shigo a tare
“Sannu da jiki Alisha “
Suka faɗa a tare tana buɗe idonta dan dama sun kasance a lumshe ta ce “nagode dan Allah ina Hajja Hauwa?”
Ameera ce ta riƙe haɓa tana zama kusa da ita “Tabb tsohon zance ai Hajja Hauwa takai awa daya da tafiya,ta shigo miki ya jiki ta tarar kina bacci shine ta tafi”
A marairaice ta furta “na so in ganta kafin ta tafi” tayi maganar kamar zatayi kuka
“Kar ki damu inde Hajja Hauwa ce very soon za ki ganta ai, tana zuwa gidan nan da anty maryam ta koma gunta ne ma yasa ta rage zuwa” cewar Zainab. Kai ta gyada musu sannan ta roƙesu da su taimaka mata tayi alwala.
Bayan ta yi alwala, sallah daga zaune tayi sa Adda da kanta takawo mata abinci se da ta tabbatar da taci ta kuma sha magani sannan ta fita ta barta da su Ameera suna tayata hira.
Haydar tunda ya fita ya wuce office aikin binciken da ya ke yi yana zaune yana kallon CCTV footage na gidan Hashim zakewa na wannan ranan da aka yi kisan amma ya kalla yafi sau biyar be ga komai na zargi ba, hakan yasa ya fahimci cewa tabbas wannan makashin yana da wayo domin se da ya lalata cctv kafin ya shiga gidan,ɗan dukan table yayi da pen din hannun sa yana furta “shitt “ hade da shafa sajen sa. gaba daya abin ya ɗaure masa kai yau kwana bakwai da fara wannan binciken amma har yanzu ko shaida kwakwara guda daya be samu ba. abin na matukar damunsa domin tunda yake be taɓa cin karo da binciken da ya wahalar dashi irin wannan ba. saboda duk binciken da ya sa a gaba baya ɗaukan lokaci yake gama wa amma wannan babu shaida ko daya.
“Yallabai DCS zamu iya shigowa ne ko kuma mu tsaya daga waje?” Suka yi maganar suna tsaye daga bakin kofa wurga musu harara yayi ya ce “ ku tabbata a gurin “ dariya suka yi suka tafa sannan suka shigo. Auwal ne da Sadeeq sun kasance aminan Haydar ne su tun na yarinta dukkan su biyu likitoci ne.
Zama suka yi suna ƙare masa kallo kamar wayanda suka ga wani abu a jikin sa kafin suka kalli juna suka tuntsire da dariya. Shi de ido ya zuba musu yana jan siririn tsaki saboda yasan dalilin da yasa suke masa wannan kallon da dariya.
Auwal ne soma magana “Maza ka gan ka kuwa? Gaba daya a firgice ka ke,a firgice kuma a razane” Wani dariyar suka sake tuntsirewa dashi suna tafawa. Shi de girgiza kai kawai ya yi be ce dasu komai ba domin in da sabo ya saba da wannan iskancin na su tunda suka yi aure suka sa rayuwar sa a gaba, haka zasu zo office din sa su yi ta masa shakiyanci.
“ Wallahi Haydar ka gaggauta yin aure ko zaka samu nutsuwa dube ka dan Allah duk wanda ya gan ka yanzu ya san kana cikin tension “ wannan lokacin Sadeeq ne yayi magana.
Shi de kallo kawai yake bin su dashi “Dole duk wanda ya gan ni ya san ina cikin tension mana tunda binciken da nake yi yana kokarin tsotsemin ruwan kai”
Yayi maganar yana kwantar da bayansa a kujera
“To yanzu da a ce ka yi aure cikin sauki za ka dinga solving din case din ka, amma har yanzu kana nan a tuzuru ya zaa yi basirarka baze soma toshewa ba ai kawai Alhaji ka yi aure “
Duban Sadeeq da yai maganar yayi “wai dan Allah me yasa ku ka sako ni a gaba ne kam? Shikenan saboda kun yi aure se aka ce muku ni lokacin yin nawa auren ya yi? abeg you guys should let me breathe in peace “
“Mu fa gaskiya mu ke faɗa maka, amma tunda baka so a bar maganar se mun sake zuwa zaa yi sa yanzu ya ka ke ya Adda”
“Lafiya lau Auwal. Gaba daya ina cikin busy ne yan kwanakin nan shisa ko ta kan ku bana bi”
With a serious face suke kallon sa saboda sun hango damuwa da bakon yanayin da ya kasa ɓoyuwa a tattare dashi
Sadeeq ne ya gyara zamar sa yana mayar da dukkan hankalin sa gaba daya akan Haydar cikin sassauta murya ya ce “wacece ita? Faɗa mana wacece ita?”
Daga Auwal har Haydar kallon sa suka yi in a confused way,Haydar ne ya soma duba bayan sa kamar me neman wani abu ya ce “kai da waye ka ke yi? ”
Wurga mai goran ruwan hannun sa da ya shigo dashi yayi “Ban son iskanci da wa nake kuwa da ya wuce kai, Haydar wannan damuwar da ka ke ciki ba iya na stress din aiki bane definitely there’s a girl behind it,kar ka min karya daga kallon cikin kwayar idanun ka na fahimci haka”
Se da ya kalle su na tsawon minti daya batare da ya ce komai ba sannan ya sa hannu yana shafa kansa,ganin haka da suka yi be musa ba ya tabbatar musu da tabbas maganar Sadeeq gaskiya ne.
Furzar da iska yayi yana sauke numfashi a hankali “Yarinya ce ƙarama da ta rasa kowa na ta a kananun shekaru,ina tausayinta sosai. Can you imagine yarinyar nan aiki take yi kamar babbar mace? kallo daya za ka mata ka fahimci she is not use to it ”
“Amma ka na son ta ne da yasa hakan ya dameka?” Auwal ya wurga masa tambaya
“No no no Auwal! babu wani zancen soyayya kawai tausayinta nake ji,besides ai ba se dole kana son mutum ne za ka ji tausayin sa ba. The gurl is so innocent in na ga tana aikin wahala har raina bana jin dadin haka, saboda na san da ace daya daga cikin kanne na ne bazan taɓa bari su yi ba”
Dafa kafaɗarsa Sadeeq yayi yana tapping “Abokina in har kana tausayinta har haka why not kawai ka aureta?”
Kallon bakwai saura ya masa kafin yace “Damn it… Sadeeq are you okay? Yarinyar da ban jima da sanin ta ba zaka ce in aure ta,maybe tana da wanda take so besides ni bana fatan in yi auren da babu soyayyah a cikin sa. Kawai tausayin ta nake ji bayan haka kuma babu komai”
Taɓe baki yayi yace “shikenan kai ka sani,a juri zuwa rafi wata rana tulo se ya fashe.wata rana da kan ka za ka ce min ka faɗa soyayya da ita”
Kallon sa shi de kawai yake yana tunanin meye yake damun Sadeeq da wayannan maganganun,ganin in suka ci gaba da zama a haka to fa zasu ta jero masa tambayoyi ne Kamar wasu yan jarida. hakan yasa ya ɗauki car key din sa da files din da yake bukata ya nufi hanyar barin office din yana me cewa “to in kun gama shakiyancin na ku se ku fito min a office nide na yi gida”
Dariya suka yi Auwal yace “ au mu zaka tafi ka bari a office din ka? To ai baka isa ba malam kawai ka tsaya mu yi sallah sannan kowa ya wuce gidan sa mu masu mata”
Ya san neman sa da magana yake yi yasa be ko juyo ba balle ya amsa shi ya fice su kuma su ka bi bayan sa.
A can gida kuwa baƙi kaff an watse an bar maryam da su Adda kowa na sashin sa,Alisha kam tana naɗe bisa kan gado se su Ameera ne suke tare da ita.
Parking din motar sa yayi a farfajiyar gidan yana kokarin fitowa yaga an wangale gate motoci uku suka shigo, ya fahimci Dangaske ne da Sameer suka dawo gida. Ɗaukan abubuwansa ya yi ya fito daga cikin motar yana kokarin wucewa tamkar be hango su ba kenan ya ji muryar Ɗan gaske
“Aliyu Haydar”cak ya tsaya yana me jin haushin kan sa akan rashin dawuwa da wuri da be yi ba, domin da ya dawo da wuri yau sam baze bari ya haɗu da Ɗan gaske ba. saboda ya san se ya masa tambaya dangane da binciken mutuwar amininsa zakewa.
Shi da Sameer suka iso wajen sa “Baba barka da dawuwa”
Fuska a haɗe yace “aha… wato in na lura ni da kai wasan mage da ɓera muka fara a cikin gidan nan? Yau kwana uku kenan kana ɓuya ka ƙi mu haɗu dan kar in tambayeka ya case din da ka ke yi yake tafiya right?”
Sosa kunnensa yai bece komai ba yana kalle-kalle kamar be ji abinda ya faɗa ba.
“Aliyu Haydar? Ba ka ji ina maka magana bane?” Ɗan gaske ya faɗa yana duban Haydar din da kyau.
“Baba na ji ka kawai ban san amsan da zan baka bane,wannan binciken da nake yi bawai abu ne na gaggawa ba dole ina bukatar lokaci domin in haɗa duk wasu information da na samu a tsanake, aman kai kullum se ka ta maimaita min magana daya shisa kawai nake ɓoye maka”
Dariya irin na su na manya Ɗan gaske ya hau yi yana dafo kafaɗar Haydar suka soma tafiya kamar wasu abokai se da ya tsagaita dariyar kana ya ce “ abinda yasa zaka ga ina damunka ba komai bane face na ji shuru, daga kai har commissioner ba mu ji komai daga gare ku ba,kai da mu ke gida daya ai ya dace ka tsaya ka min bayani ko ba haka ba Sameer?” Yayi tambayar yana juyo ɓarin da Sameer yake.
“Hakane Baba “yai maganar yana yin gaba ya bar su a baya.
A haka suka shigo cikin falo bayan Haydar ya sanar dashi nan ba da jimawa ba ze gama binciken kuma ya faɗa masa hakan ne dan ya samu ya bar sa ya huta da yawan tambayoyin nan na sa.
Sama ya haura har ze nufi bangarensa se ya tuna da ita hakan yasa ya fasa shiga nasa ya shiga na Adda yana me shiga dakin da ta ke,can ƙasan maƙoshi ya yi sallama yana shigowa kan sa tsaye. tana zaune a bakin gado ta ga shigowarsa amma ta ƙi amsa masa saboda yanda ya yi sallaman can cikin maƙoshi kamar an masa dole wanda in mutum bawai ya kasa kunne ba tofa baze taɓa jin sa ba.
Zura hannayensa yai cikin aljihun wandon jeans din da yake sanye dashi yana jingina rabin jikinsa a jikin kofa ya tsura mata ido, yanda ya ga ko ɗago kai bata yi ba tamkar bata san da wanzuwarsa ba ya ba sa mamaki domin ko kaffara ba ze yi ba in ya ce ta san da shigowarsa
“Alisha..”
Se a sannan ne ta ɗago wayannan mayun idanunta ta ɗaura su akan sa da shima ita din yake kallo “Naam barka da dawuwa uncle Haydar” girgiza kai ya yi domin ɗan sanin da ya mata ya gane akwai ta da izza,wanda ba kowa ne ze fahimci hakan ba se me lura.
Rage murya yayi ya ce “barkan ki ya kafar ta ki ?”
Kallon kafar ta yi “Dasauki “
Be kuma cewa komai ba ya shigo yana isa inda take ya dubi kafan nata da ta ajiye sa akan pillow “in sha Allah nan da kwana biyu zuwa uku ze warke ki kiyaye kar ruwa ya taɓa sa”
“İn sha Allah zan kiyaye“ tayi maganar tana sunkuyar da kanta ƙasa. Shuru ne ya biyo baya babu wanda ya sake cewa komai.
Satan kallonsa ta yi jin sa shuru bece komai ba ta ga ya tafi duniyar tunani,wani tunani tayi sannan ta yi gyaran murya da siririryar muryarta
“Uncle Haydar tunanin me ka ke yi haka?”
“Bakomai me ki ka gani?” Yayi tambayar yana miƙewa tsaye da niyar tafiya
“Uhmm naga kamar ka faɗa duniyar tunani ne. shin ko akwai abinda yake damunka,” cikin zolaya ya kankance idanunsa akan ta “ko zaki min maganin damuwar tawa? “ ganin yanda ya zuba mata sexy eyes din sa ne yasa ta saurin janye idanun ta akan sa jin irin amsar da ya bata
Cikin kame-kame ta ce “sorry for asking “ ta ci gaba da wasa da hannun hijab din jikinta,ganin kamar bata ji dadin amsar da ya bata bane yasa shi sakin murmushi. domin shi cikin zolaya ya faɗi haka kuma ba da wata manufa ba amma ya ga kamar ita tayi wa maganar sa wata fahimta
“Alisha wani bincike nake yi da har yanzu na gagara kawo karshen sa if you can include me in your prayers I’ll really appreciate “
Dariya tayi a cikin ranta jin abinda ya faɗa dangane da binciken da yake yi a fili kuma cike da kulawa ta ce “in sha Allah uncle” sallama ya mata ya fita bin bayan sa da Kallo tayi yanda yake tafiya take kallo har ya ɓacewa ganin ta.
“Hmmmm Haydar Modibbo Ɗan gaske ai cases din da suke zuwa nan gaba da za ka yi binciken su Allah ya musu yawa a ciki kuwa har da wanda ka ke kira baba”
yawan comment da sharing da like din da zaku yi shi ze tabbatar min da kuna jin dadin wannan littafi,your comments really mean a lot to me ☺️❤️
Don’t forget to comment,share and like 👍