FANSAR MACE

FANSAR MACE

by @mrsisham12

17 & 18_*🦋FANSAR MACE🦋*_

Story & written

By

MRS ISHAM

~The writer of ~

NIDA PATIENT DINA

ASHE ZAMUGA JUNA

ƊAYA CIKIN BIYU

MAKIRIN IKO

and now

🦋FANSAR MACE🦋

JARUMAI

WRITERS ASSOCIATION

📚📚📚🖋️🤩

17 & 18

“Mtssssw wannan gida na Ɗan gaske be haɗu ba, kowa da kalan iskancin sa aikin banza” yau ne karo na farko da ta yafa babban mayafi akan doguwar riga fitted gown da ta sanya, be wani kamata ba tayi ɗaurinta simple ta feshe jikinta da turare ko kallon kanta bata yi a mirror ba ta fita a dakin domin ita ba Ma’abociyar kwalliya bace ko kwalli bata sawa balle wani kwalliya. Dakin Adda ta je suna hira kamar wayanda suka jima da sanın juna.

Suna cikin hira bacci ya saci Adda wani tunani ne ya zo mata da sauri ta fita tunda ta sauko har ta fice a main falo bata haɗu da kowa ba, gun me gadi ta nufa.

“Adda ta aike ni karɓo mata saƙo a junction “ jin ta ambaci Adda ne yasa ya buɗe mata kofa yana kallon lokaci ya ga yanzu Karfe 8:20 yana mamakin to me zata karɓo a wannan lokacin. se da tayi ɗan nesa da gidan sannan ta samu abin hawa.

Inna na zaune ta ga shigowar ta kana ganin fuskarta ka san tana cikin damuwa amma lokacin da Alisha ta shigo se ta sauke numfashi tana faɗin “Alisha lafiya kuwa na jiyo ki shuru ?”

Zama tayi a kusan ta tana duban yanayinta “Inna meke damunki?”

“ Ƴar nan babu komai, kawai na shiga damuwa ne saboda shurun da na ji ki ina ta addua Allah yasa komai lafiya “

Yanda take son ta da kaunar ta ne yake bata tausayi bayan ita tasan bazata yi wani tsawon rai ba saboda ciwon zuciyar da take ɗauke dashi,bayan ahalinta inna ita ce macen da take matukar so domin ita ce ta zamo mata uwa bayan Mommah,hakan yasa take yi mata komai domin ta faranta mata,matar da ta riƙe ta, ta so ta lokacin da ta samu taɓin kwakwalwa ai dole ta so ta, domin ta zauna da ita tsakani da Allah ne bawai dan kudin da take dashi ba,slowly ta kwantar da kanta akan cinyar Inna ta yi shuru a yayinda Inna hannunta yake kan ta tana shafawa.

“Bazeyu in tafi da wayata can gidan ba da za mu dinga waya ai,amma bazeyu ba dole za ki yi hakuri na wasu kwanaki saboda yanzu ma dakyar na iya fitowa ina son in yi in koma gida ne kafin mazan gidan su dawo”

“Shikenan ki kiyaye don Allah dan wayannan mutanen ba abun yarda bane “

Kai ta gyada kana ta shiga dakin ta tana me jan kujerar table din ta zauna ta kunna system din ta da komai ta fara kallon gidan Peter da ta sanyawa karamar camera batare da sun sani ba saboda ta je gidan ne a matsayin an aikota man ta sa camera a bakin gate ta ciki. Duba abubuwan da take bukatar gani tai maganar da ta ji masu gadi suna yi ne yasa ta fahimci baya ƙasar kashe komai tayi ta tashi ta ɗau maker sannan ta canza masa date.

Haydar da ya fito daga gidan Sadeeq ya ɗau hanyar gida ne ya hango ta a junction din jeka da fari, tana tsaye ya gane motarta ne yasa mu matsala be yi niyar tsayawa ba ya murtuke fuska kamar be santa ba ita kuwa tana ganin motar sa ta tsaya a gaban sa tana roƙonsa da ya tsaya

se da ya ja tsaki kafin ya tsaya ya fito yana haɗe fuska.

“Haydar please can you help me fix my car?”

Wani uwar harara ya wurga mata “na miki Kama da machanic ne?”

Girgiza kai tayi alamar ah ah tana matso kusa dashi cikin tafiyar yanga ta ce “Tom ka taimaka ka kaini asibitin Zainab burkachuwa dan Allah "

Shi se yanzun da ta matso ya lura da irin kayan da yake jikinta riga da wando ne sun kamata se gyale da ta ɗaura akanta girgiza kai yayi takaici kamar ya yi yaya wai wannan ita ce ake so ya aura. Ko kaɗan be yi niyar tsayawa ba balle ya mata magana, kuma ba domin ta haɗa sa da Allah ba babu abinda ze sa ya taimaka mata.

Motarsa ya koma ya shiga yana matsa horn ba ɓata lokaci ta zo ta shiga gaban ta zauna tana masa murmushi “thanks my husband to be “ be kulata ba suka ɗauki hanyar asibitin Zainab burkachuwa suna isa ta kira waya “na iso kuna ciki ne?”

Be ji abinda aka sanar mata a wayar ba ya sake jin ta ce”okay kun koma gida Kenan to shikenan se gobe kawai zan zo gidan “ta katse kiran

“Honey wai sun koma gida. mu je gida kawai” se da ya watsa mata banzan kallo sannan ya soma driving.

Wani keke napep ne yazo kusa da motarsa kamar an ce ya ɗaga kai aikuwa idanunsa suka sauka kanta duk da ta sanya face mask amma seda ya gane ta. A can ƙasan maƙoshi ya kira sunan ta “Alisha “ya faɗa yana kallon time yanzu karfe tara ne da minti arba’in tunani ya fara me ta fito yi a wanann lokacin, se kallon ta kawai ya ke cike da mamaki amma ita bata gan sa ba saboda kanta ba ya setin inda motar nasa yatake

Yin gaba napep din yayi ba shiri ya bi bayan su yana me shan gaban napep din ganin abinda ya yi ne yasa ta kallan sa “honey lafiya “ko uffan be ce mata ba ya sauka a motar.

Sosai ta ji gaban ta ya faɗi lokacin da tayi arba da kyakyawar fuska Haydar da yake dunfaro su,ji tayi kamar ta zama tsuntsuwa ta fire, yanzu in ya tambaye ta wani irin karya za ta masa she’s so nervous but tried to calm her self down.

Leko kansa cikin napep din yayi a setin da take zaune har kamar fuskarta ze taɓo nasa kamshin turarensa yana me dukan hancinta bata san lokacin da ta shaka ba tana sauke ajiyar zuciya a ɓoye nan ta ji ta sake samun nutsuwa. Hannu yasa ya janye face mask din ƙasa yana duban yanda ta tsuke fuska cikin tsare gida dan kar ma ya zo mata da wasu tambayi da bazata iya amsa shi ba.

“Daga ina ki ka fito a irin wannan lokacin Alisha ?”

“Na je kwaso sauran abubuwa na ne a gidan kawu na amma sun hanani shiga gidan “ ta faɗa tana yin rau-rau da ido ga idon da yake sheki kamar ruwa ya taru a cikin su.

“ But why will you even go to them? mutanen da su ka nu na clearly ba sa san ki, fito mu tafi” ya faɗa yana riƙo hannun ta tafito,duk abinda suke yi tana zaune a motar tana ganin su ta cika tam kamar zata fashe ganin yanda Haydar yake wani nan nan da Alisha. Fito da 2k yayi ya miƙawa me napep din motar sa suka isa ya buɗe mata gidan baya ta shiga. kamshin turaren mace ne ya doki hancinta da sauri ta kai duban ta gaban motar sa ta ga macece a zaune bata yi tunanin komai ba ta gyara zamar ta.

Ta mirror ya kalle ta ya ga yanda ta ke ta lumshe ido cike da kulawa ya ce “Alisha are you okay?”

Da sauri ta dube sa kawai se ta gyada masa kai,a karo na biyu ya kuma cewa “are you sure “

Murya a marairaice ta ce “uncle Haydar ba komai fa “ kai ya gyada sannan ya soma driving da ga nan kuma ba wanda ya sake cewa komai a cikin motar, ita Alisha tana tunanin wannan din da take zaune gim gaban motar wacece,haka ita ma Meenal abinda ke ranta kenan sannan wani wutar kishi ne yake ta hayayyako mata a kirji ganin yanda Haydar yake yi mata.

“Ke ai na zan ajiye ki ni gida zamu wuce” ya yi magana idon sa na kan hanya.

Cike da kissa ta ce “Honey nima kawai mu wuce gidan, dama gobe zan zo ni amma yanzu tunda ga ni ga kai se mu tafi gidan “

Saboda baya son yawan magana se kawai ya ce “okay “ Alisha da ta ji ta kira Haydar da honey ne yasa ta fara tunanin ko de budurwarsa ce,hakan yasa ta ɗan leka fuskarta kafin ta taɓe baki ta kwantar da bayan ta tana jan tsaki ƙasa-ƙasa yanda babu wanda ze ji,duk abinda take yi idanun sa na kanta yana kallanta a mirror, dariya ta ba sa time din da ya ga tana lekan Meenal da kuma yanda ta taɓe baki ta ja tsaki murmusawa kawai yai.

“Honey yanzu yaushe Uncle ya ce zaa fara shirye-shiryen auren mu”

Ɗan satan kallan ta yai again ta mirror ya ga yanda ta saki ɗan ƙaramin bakinta tana sauraran Meenal,da be yi niyar amsa mata ba amma dan ya ga reaction na ta yasa shi cewa

“Meenal ban sani ba ki bari in mun je gidan se ki tambayesa kawai”

“Ohhh nagane ita ce Meenal din kenan yar Habibu katanga dakyau “ ta faɗa a ranta tana ɗan gyada kai.

Dariya tayi jin irin amsar da ya ba ta “shikenan ai ni zan tambayi uncle din gobe da safe,Honey wacece wannan ko yar uwar ku ce”

“Eh “ kawai ya faɗa yana tuki,side din Alisha ta juyo tana kallanta, se da gabanta ya faɗi ganin yanda take da tsananin kyau,, ta fita kyau nesa ba kusa ba, duk da ita farar fata ce Alisha kuma baƙa, amma ta mata fintinkau a kyau hakan yasa ta shan jinin jikinta “hi sunana Meenal fiancé uncle din ku“

“Ohhh sannun ki” ta faɗa a takaice dan wani haushin ta ne yakama ta ganin yanda take abu irin na cikakkun ƴan bariki ga wasu yan iskan eye lashes da ta saka sun tsaya tsage-tsage.

Yana jin su kuma yana kallon su ta mirror, yanda take tsumewa ne ya sa dariya kusan kufce masa amma ya yi kokarin dannewa.

“Kina bukatar wani abun ne ?” Da sauri ta ce “Noo honey babu abinda nake so” ɗan hararan ta yayi “ba dake nake yi ba,Alisha kina bukatar wani abu kafin mu isa gida?”

“Nothing uncle” a haka suka isa gida Meenal se jan Haydar da hira take yi shi kuma yana bata amsa sama-sama kamar wanda aka wa dole. Ita kuwa tana baya tana jin su idanun ta lumshe kamar wacce ta fara bacci. Yana yin fakin ta bude motar ta fita ta ba su guri,bin bayanta yayi ya bar Meenal ita kaɗai a motar.

Cin mata yai yana “Saurin kuma duk na meye ne?”

Cire facemask din da taji ya matse mata kunne ta yi “am just tired ina son in je in huta ne “

Gyara tsayuwar sa yayi yana kallan yanda fuskar ta har yanzu babu walwala “kina jin babu dadi ne?“

Bakatatan tambayar ya zo mata domin ba ta yi tsammanin sa ba “akan me fa?” Ita ma ta jefa mai tambaya a madadin bashi amsar tambayarsa.

Ɗaga kai yayi ya kalli sama yaga yanda sararin samaniyan yayi kyau ga taurari ko ta ina, batare da ya saukar da kan ba yace “kina son amsa tambaya da tambaya”

Za ta yi magana kenan Meenal ta iso inda suke zura hannunta tayi cikin tafin hannunsa ta riƙe gam tana murmushi,kallon ta yai ze yi magana ta yi saurin ɗaura hannun ta akan lips dinsa tana kashe mai ido daya “kar ka ce komai Honey”

Taɓe baki tai ta wuce ciki abun ta

Buge hannunta yai “ba ki da hankali ne? Kar ki sake taɓa ni kina ji ko?” Ya wucewa ciki bin sa tayi tana dariya tare da kiran “Honey” amma ko juyo wa be ba.

Su Yusra da suke zaune a main falo suna kallo ne suka ga shigowarta “Alisha ina ne ki ka je ki haka tun dazun mu ke ta dubak?” Ameera tayi maganar tana zuwa gurin ta tana riƙo ta suka zauna.

Yusra da tunda ta shigo take bin ta da ido ta kasa janye idanun ta akan ta tayi shuru tana jiran ta ji amsar da zat a bayar.

“Na je gidan kawu na ne kwaso wasu abubuwana amma suka hanani shiga gidan shine a hanyar dawuwa na haɗu da Uncle Haydar mu ka dawo tare”

Jikin su yayi sanyi matuka yanda take magana ya sa su jin ba dadi, domin yanda muryarta ke fita kamar zata yi kuka rungumeta Ameera tayi tana ba ta hakuri,cikin kula wa duk suka ta ce mata tayi hakuri wata rana su da kan su za su nemeta. A haka su Haydar suka shigo suka same su

Ba ƙaramin mamaki suka yi ba ganin sa da Meenal dan basu yi tsammanin hakan ba zama tayi a cikin su suka gaisa sama-sama dan duk ba wani yin ta suke yi ba musamman Yusra sam ta tsani Meenal hakan yasa ta jan tsaki ta bar falon.

Shima Haydar part din sa ya wuce Zainab ce tana yatsina fuska ta ce “amma me ya kawo ki gidan mutane da dare haka?”

A gadarance ta amsa “sooner or later In brother din ku ya aure ni gidan nan zan dawo dan haka i have the right to come anytime na ji ina son hakan” tayi maganar tana ɗaukan hand bag din ta ta nufi part din su Ameera din da banzan kallo suka bi ta “kai Subhanallahi yanzu me Baba ya gani a jikin wannan yar iskar da har yake son aurawa ɗean sa ita dan Allah “Zainab ta faɗa cike da takaici

Tsaki Ameera tayi “hmm kema de kya faɗa. wlh uncle Haydar sam be dace da irin wannan ba,mutum me hankali da kamala amma zaa haɗa sa da wannan abar”

Alisha da ta sako baki cikin hiran su din ne ta ce “ku dena aibatata se ku ga uncle Haydar ya zama silar shiryuwanta” duk zaro ido suka yi suna haɗa baki wajen faɗin “wannan din? lallai “

“Ke Alisha anya a cikin Gombe ki ke ma kuwa? Ke kin san hau din Meenal ? To babu wanda za ki faɗa masa sunan ta yace be san taba. Ke bara ki ji Meenal yar iska ce ta gaske shine kawai “ murmushi tayi ta girgiza kai domin yanda Ameera ke magana ne ya bata dariya

“Ameera Allah ya shirye ki” ta faɗa tana murmushi .

“Eh mana ai gaskiya ta faɗa Alisha,kin ga Yusra da Meenal ba sa jituwa. saboda wata ƙawar Meenal wai ta taɓa ce wa Yusra yar lesbian nan suka yi ta case dakyar maganar ya mutu, daga nan ne fa Yusra ta tsane ta” Zainab ta ba ta labari jinjina kai tayi a ranta ta ce “ai ba sharri ta mata ba yar less din ce “ a fili se cewa tayi “lallai kam ba su kyauta ba”

Tashi tsaye Zainab tai ta kashe TV ta dube su “ ku zo mu je mu kwanta “

“Alisha meyasa ba zamu dinga kwana a part din mu tare ba?”

Yaƙe ta yi itama ta miƙe ta riƙo hannun Ameera din “ sorry dear abinda yasa haka ni mutum ce me son privacy, I love my privacy shisa ka” sun fahimceta tunda kowa yanada raayin sa

“shikenan to mu yi bacci da wuri saboda mu tashi da wuri gobe sunday zamu je shopping in mun yi saa Uncle Haydar ya kai mu,dan ya Sameer na masa magana yace min gobe akwai in da ze he, kun ga kuma Uncle baya zuwa aiki a weekend “

“ to hajiya Ameera “

tare suka haura sama ita ta shiga part din Adda su kuma suka shiga na su,dakinta ta shiga ta sa key ta rage Kayan jikin ta riga mara nauyi ta sanya ta kwanta.

Yana tsaye a corridor ya hango shiganta part din Adda, kwafa yayi yana tuna dazun da ta watsa masa ruwan zafi “za ki san kin yi da Sameer Ɗan gaske se ne miki abinda ba ki yi tunani ba shegiya figaggiya “ ya wuce part din sa.

A bangaren Haydar kuwa tunda ya shigo yayi wanka ya zauna yasa system a gaba ze fara aiki amma ya kasa tunanin ta gaba daya ya cika masa zuciya ko rufe ido ya yi ita yake gani a hankali ya mari kan sa da zummar ya dawo dede “menene abinda yake damunka ne Haydar,focus on your work “ ya faɗawa kan sa.

Washe gari bayan ta idar da sallah tayi azkar ne ta nufi bedroom din Adda suka gaisa fuska Adda da faraa ta ce “jiya yaushe ki ka tafi dakin ki?”

Dariya tayi “Adda mu na hira ki ka yi bacci abin ki shine na tafi”

“Ai haka na ke, daga zaran na miƙe kan gado shikenan bacci yake sace ni,yau ne Uncle din ku ze kai ku shopping ko? ”

Gyada kai tayi tace “ehh haka Ameera ta gaya mana jiya”

“Tom Masha Allah in kun je ki ɗauki duk abubuwan da ki ke bukata. kar ki tsaya kunya kin ji ko?zan gaya masa ya siya miki waya ma naga baki da waya “

“To Adda Allah yasa ka”

“Ameen” , “amma Adda meyasa ake ce masa uncle ?”

Ɗan dariya Adda ta yi “saboda shi takwaran kawu na ne to shine ne fa Hajja Hauwa take ce mai me sunan uncle lokacin da yake ƙarami, daga nan kawai sunan ya bi sa uncle Haydar,uncle Haydar” dama hakan na ranta ta rasa me yasa kaff yan familyn suke ce masa uncle bayan kamata ya yi su ce mai Yaya kamar yanda suke cewa Sameer yaya. Amma yanzu ta gane dalili.

“Oooh nagane bari in je in dubo su Ameera” part din su ta nufa da Meenal ta fara yin clear a falo tana video call daga ita se guntun wando da riga vest ko kallon ta bata yi ba ta shige bedroom inda take jin muryoyin su.

Wasan banza ta iske su suna yi kamar wasu yara se jefawa junan su pillow suke yi suna ihu da tsalle akan gado tsayawa tayi daga bakin kofa tana kallan su,tunawa tayi yanda suke wasa da Zaid da Aryan su yi ta zagaye gidan ko su yi ta wasan ruwa. Ganin su da tayi ya tuna mata da yan uwanta zuciyarta ne ta ji yana so ya fara yi mata zafi hakan yasa ta ɗaura hannun ta akai ta dafe setin gurin tana sauke numfashi .

Yusra ce ta fara lura da ita “ya ki ka tsaya daga bakin kofa ki shigo mana” duk sauran kallon ta suka yi murmushi yaƙe tayi ta shigo ta zauna.

“Ahh lallai baku da matsala na ɗauka zan shigo in same ku ko kuna bacci”

“To ai idon mu biyo tun 4 muke ta hira kin tashi lfy ?”

“Lafiya lau Zainab fatan kuma haka” Duk suka amsa da “Alhamdulillah “

“Kun san meye?” Yusra da tayi tambayan suka kalla suna jiran ji meye take son ce musu “se kin faɗa” “yau so nake yi bayan mun dawo daga shopping mu tafi yawo cikin gari tunda na dawo ban fita ba zaman gida is so boring” they all agree with her idea banda Alisha da bata sa musu ba ki ba.

“Zamu je ko Lisha “ tayi tambayar tana kashe mata ido daya

“ I don’t think so” tana faɗar haka ta kwanta a gadon tana jin su suna hira, amma ba ta tashi ba ita damuwar da take ciki a rayuwar nan ma kaɗai ya ishe ta. Ba domin ta zo gidan su da niyar ɗaukan fansa bane da ko murmushinta ba za su gani ba balle ta musu magana. Amma ba ta da zaɓi da ya wuce ta dinga pretending,dole ta saki ranta saboda ta samu shiga jikin su da kyau yanda zasu yarda da ita dakyau-dakyau amma in ba dan wannan ba da magana da murmushi sun jima da zama tarihi a gurinta.

Yau tsabar hiran da suke yi ko dinning din sun ki sauka su ɗauki breakfast. Ƙarshe ma sa me aikin su tayi aka kawo musu abincin dakin. suhudu su ka ci Meenal kuma na ta daban tana falo har yanzu video call din take yi.

Yau ma kamar jiya haka wannan saurayin ya dawo gidan amma kasancewar yau Sunday me gadi sam ya hanasa shiga babu irin magiyar da be masa ba amma yace ba ze yi kasada da aikin sa ba dan haka ya tafi. shi kuma yace yau in be ga Haydar Ɗan gaske ba tofa ba ze taɓa barın kofar gidan ba. Haka ya samu guri a bakin gate din ya zauna tare da cin alwashin ko kwana ze yi a gun yau se ya gana da Haydar.

Karfe sha daya su ka gama shirin su na zuwa kasuwa. ita de falazo ta saka da karamar riga ta ɗaura babban hijabi akai har yana sharan ƙasa, ta fito hannun ta riƙe da niqabi da za ta ɗaura. suna ganin ta da niqab suka kwace wai gaskiya bazata sa niqab ba, ta ƙi yin kwalliya sannan yanzu ta ce za ta sa niqab su ba su yarda ba, ba yanda ta iya haka ta hakura da sawa tunda sun kwace Adda dake zaune tana jin su se dariya take musu

“Yoooo ni na ga ikon Allah yarinya ta saba sa kayanta ku Kyale ta mana”

Adda ta faɗa tana riƙe haɓa,Yusra tace “ah ah Adda shopping fa zamu ba islamiyya ko kuma taron MSS ba “

Suna tsaye a falon Haydar ya sauko se baza kamshi yake yi ,yai kyau cikin shigan half jumfa sky blue da ya sanya duk gaishe sa suka yi cikin girmamawa

“Kun gama ko?” “Yes uncle “

“Adda mun tafi se mun dawo. yau yaran ki sun rantse ni zan zama driver su “

“Yooo ya za ka yi ku je kawai ku dawo uncle din yan mata “ gaba daya dariya suka yi harda Alisha dan itama abinda Adda ta c ya sanyata dariya sallama su ka mata su ka tafi banda Meenal da take can daki tana bacci.

Fitowa suka yi farfajiyar gidan already ya sa driver ya fitar masa da motar sa kirar Mercedes Benz wane. hakan yasa me gadi ya buɗe musu kofa duk suka fito ya yi saura Ameera da Alisha ne a ciki ba su fito ba tukun. Wani dadi ne ya ji ya kamasa tsabar farin ciki kamar ya zubar da hawaye lokacin da ya ga fitowar Haydar da sauri ya ƙaraso gun sa, time din yayi dede da ze shiga motar sa

“Sir Haydar dan Allah in ci arzikin fiyayyen halitta ka ba nı kaɗan daga cikin lokacin ka na zo maka da magana me muhimmanci” dakatawa yay ya juyo ya kalle sa amma se ya ga be gane sa ba cikin mutuntawa ya ce “saurayi faɗi ya aka yi “dede ta nutsuwar sa ya yi yace “ko zamu ɗan keɓance da kai ?”

Kallon su Yusra ya yi ya ce su shiga motar shi kuma ya jinginu da jikin motar yana harɗe hannun sa a kirji ya zuba mai ido.

“Sunana Muhajid Abbakar Sadeeq jiya nazo gurin ka an hana ni ganinka yallabai nazo maka da magana me muhimmanci “

“Ina jin ka Mujahid”

Ya ci gaba da faɗin “Taimakon ka nake nema akan ceton wani wanda yake cikin halin rayuwa ko mutuwa dan gidan s……..sa…..sa” sunan da yake so ambata ne ya sarƙe masa a baki ya fara in-ina jikinsa ya ɗau rawa, idanunsa suka fiffito kamar wanda ya ga mugun abu. ba komai ya gani ba face Alisha da ta fito yanzu ita da Ameera kallon direction da ya kafe da ido da har yasa ya shiga wannan hali na tashin hankalin Haydar yayi ya ga Alisha da Ameera tambayar kansa yayi to me yasa daga ganin su ya shiga wannan halin amma to meyasa.

“Lafiya ka ke kuwa” ya jefa masa tambaya se a sannan su ka kalli wanda Haydar din ya yi wa magana. lokacin da ta yi arba dashi wani irin bugawa gabanta yayi se da ta ji naman zuciyarta ya motsa sannan ya fara harbawa fat-fat-fat wanda mutum inde yana kusa da ita sosai to tabbas dole ne ya ji heartbeat na ta,amma duk da halin da ta shiga be hanata kamewa da kuma tsuke fuska ba tayi tamkar bata taɓa sanın sa a rayuwarta ba.

Gaba daya ya gagara magana ya san tabbas idanunsa ba karya suke yi masa ba kuma ba gizo ba, tabbas wannan ita ce amma ai ta mutu kenan wannan fatalwarta ce a gidan ko kuma de wata ce me kama da ita.

yawan comment da sharing da like din da zaku yi shi ze tabbatar min da kuna jin dadin wannan littafi,your comments really mean a lot to me ☺️❤️

Don’t forget to comment,share and like 👍

Today is Friday don’t forget to recite Suratul kahf, sannan a yi wa annabi salati. Allah ya sadamu da alkairin dake cikin wannan rana.