FANSAR MACE
by @mrsisham12
19 & 20_*🦋FANSAR MACE🦋*_
Story & written
By
MRS ISHAM
~The writer of ~
NIDA PATIENT DINA
ASHE ZAMUGA JUNA
ƊAYA CIKIN BIYU
MAKIRIN IKO
and now
🦋FANSAR MACE🦋
JARUMAI
WRITERS ASSOCIATION
📚📚📚🖋️🤩
19 & 20
Kallon Alisha yai ya ce “Alisha ku shiga motar ina zuwa” shiga tai batare da ta sa'ke kallon inda ya ke ba, a ran sa ya furta “tabbas ita ce,wallahi Alisha ce tunda ga shi ya kira sunan ta,to menene ya faru? “
“Mujahid shin ka san ta ne?” Haydar ya katse masa zancen zucin da ya ke yi, a sukwane ya kalle sa sannan ya kalli motar da ta shiga ya girgiza kai kamar wawa “ah ah ban san ta ba”
“Shikenan to ina jinka kana cewa meye ɗazun?”
“Sir abinda na ke son cewa na manta yanzu. hankali na ya koma kan gıda gobe zan zo se in faɗa maka” yana gama magana ya tafi ya bar Haydar tsaye cike da mamakin ɗabi’ar sa. da farko ya ce yana son magana dashi, yanzu kuma yace hankalin sa yayi gida, nan ya fara tunanin to meye dalilin haka ganin ze ɓata wa Kansa lokacine ya sa ya shiga motar.
Tunda ta zauna take jin ta tamkar a ƙaya ta zauna. gani ta ke yanzu asirinta ya gama tonuwa, domin ta na da yaƙinin Mujahid yana da alaƙa da gidan Ɗan gaske. me ze faru in ya faɗawa Haydar ita din wacece?hankalin ta gaba daya ya tashi. ganin Haydar ya shigo motar ne ya ɗan dube ta be ce komai ba yasa ta furta
“Is over for me. shikenan yanzu Haydar ya san gaskiya,yakamata mu na isa super market in samu in gudu tun kafin hankalin sa ya dawo kaina” wannan shine shawaran da ta gama yankewa saboda shine kawai mafita a gareta domin cikar muradinta, matukar tabar Haydar ya tsareta to fa shikenan wasanta ya zo ƙarshe, ita kuma baza ta so wasan ya ƙare ba har se ta ruguza ahalin Ɗan gaske da sauran su.
Su Ameera suna ta yi mata magana amma shuru ba amsa hankalin ta sam baya cikin motar yanda zata yi ta tsere kawai take tunani,yana driving yana kallonta ta mirror, jira ya ke su isa ya tambayeta meyake damunta.
Su na isa suka fita a motar za su shiga cikine Haydar ya ce “ina da magana da ke “ su Ameera suka shiga suka bar ta tsaye a gurin jin yace yana da magana da ita,kirjinta dukan tara-tara kawai yake yi, tsoron me ze faɗa mata take yi. amman sam a zahiri ba ta nu na ba ta iso gabansa ta tsaya ya buɗe baki ze mata magana kenan aka kira sa a waya hakan yasa yace mata “minti daya “ ya ɗaga wayar ya matsa gefe yana me juya mata baya.
Ta na ganin wannan opportunity din ta silale ta bar gurin ta nufi hanyar fita a super market din. tana tsaye a bakin hanya ta kare fuskarta da hijab dinta se kalle-kalle take tana roƙon Allah ya kawo mata abun hawa cikin gaggawa se ga napep ko ciniki ba su yi ba ta faɗa ciki tana sanar dashi in da ze kai ta. har ta shiga napep din hankalin ta bawai ya kwanta bane gani take Haydar ze biyo ta a baya se da suka yi nisa tukuna ta samu relief, dede hanyar da za'a shiga anguwa uku wajen titin jirgin ƙasa man napep ya ƙare. sauka tayi me napep yace ta ba sa kudin sa ta tari wani saboda babu inda ake saida mai nan kusa, amma naira daya babu a jikinta, ta rasa yanda zata yi dama niyar ta in sun İsa gida ne ta karɓi kudi a gun inna ta bashi, to ga yanzu yanda ta kasance.
“Alisha” ta ji an kira sunan ta gagara motsawa tayi saboda ba ta san wanene idon ta ze gane mata ba. Ganin ta ƙi waigowa ne yasa shi cewa me napep din “nawane kudin ka malam? ”
“Dari tara ne” hannu ya sa a aljihu ya fito da gudan 1k ya basa sannan ya zagayo ta gabanta suna kallon juna. me napep kuma ya tura napep din sa yayi gaba wajen ya yi saura su biyu kawai
“Alisha dama kina raye?ya aka yi ke ba ki mutu ba. Sannan me ki ka je yi a gidan Ɗan gaske? “
“Kai ne ya kamata in yi wa wannan tambayar mujahid, menene dangantakar da yake tsakanin ka da ahalin Ɗan gaske?. Meyasa dan ka gan ni za ka sanar da Haydar Modibbo Ɗan gaske asalina? shin ka san abinda wayannan mutanen suka yi min ?”
“Nooo Alisha ban sanar dashi komai ba lokacin da na gan ki kwakwalwata dakatawa yayi da aiki “
A fusace take kallan sa ta san karya ya ke yi mata, hannun ta duka biyu ta sa ta chakumi wuyar rigarsa “karya ka ke yi Mujahid ka yi kaɗan ka yaudare ni,babu mahalukin da ya isa ya dakatar da ni daga abinda na fara,da kai da kasan gaskiya da kuma su din duk ba ci gaba da rayuwa za ku yi ba”
Tayi maganar tana zaro ƴar ƙaramar wuka a kugunta ta sa mai a wuya,ganin dagaske illata sa zata yi ga layin shuru babu kowa yanzu saboda yanda ake zabga rana,murya na rawa ya hau faɗin “Alisha ki dakata ki saurare ni,na rantse ban sanar masa da komai ba wlh ki yarda da ni”
“Ba na taɓa yarda da duk wanda ya yi kokarin wargaza min shirina, motsi kaɗan ka sa'ke yi zan raba wuyanka da gangan jikinka.“ tayi maganar tana matso da wukar setin maƙoshinsa
“A…ali…..sha na je gurin sa ne domin magana akan abinda ya shafe ku ke da family din ki, na je neman taimakon sa ne da kuma sanar dashi rashin adalcin da aka mu ku”
Yanda ya ke magana ya tabbatar mata da ya san abinda ya faru dasu to amman ya aka yi ya sani ? Saboda babu wanda ya san abinda ya faru a wannan daren nan, daga ita, se su wayanda suka aikata musu hakan ,se kuma Allah da ya ke ganin komai amma se ga shi Mujahid ya san abinda ya faru to taya aka yi ya sani kenan?, waye ya sanar dashi wannan magana. Tsabar zuciyar ta a bushe ya ke ko tsoron yanda ya fita girma bata ji ba, saboda Mujahid din sa’an Zaid ne kuma babban abokin Zaid.
“Ya aka yi ka san wannan maganar Mujahid ?”
“To kin sa min wuka a wuya ta ya zan gaya miki gaskiya ? “
Ba ta cire wukar ba se da tace “don’t try to act smart, wlh ka yi kokarin yaudarana ba za ka tsira ba”
Yana in-ina ya ce “na amince” cire wukar ta yi,hannu yasa yana shafa wuyansa da ya kusan bakuntan lahira se da ya gama haki tukuna ya soma cewa
“Ban je gurin Haydar Ɗan gaske saboda ina da alaka dashi ba,se dan tattaunawa akan maganar kisan gillan da aka yi muku. Amma ganin ki ya matukar tsorata ni, na shiga firgici da tunanin me yake faruwa dani hakan yasa ban iya ce masa komai ba na tafi,ban bar cikin anguwar ba se da na ga kun tafi hakan yasa na tari mashin na bi bayan ku, amma bayan da ku ka isa se na ga kina neman abun hawa a bakin titi bayan ki na bi dan ganin ina za ki je “
“Duk na ji wannan,go straight to the point“
“Na san komai akan abinda aka yi muku duk wani bayani ina dashi. Wallahi Alisha kawai banda yanda zan yi ne amma na so ɗaukar mu ku fansa amma waye ze tsaya min ta ina zan fara?sannan kuma yanzu ƙasar nan ya zama abinda ya zama ina tsoron in kai ƙara wayanda suka aikatan su ji su fara farauta na”
“Amma Mujahid a gun waye ka ji wannan abun ?“
Ajiyar zuciya ya sauke “Alisha is a long story yau shekara daya ina neman mafita,ki biyo ni domin samun amsar ki”
Ya yi maganar yana riƙo hannun ta, zuwa yanzu bata da zaɓin da ya wuce ta bi sa din domin sanın yanda akai ya san gaskiya napep ya tara sannan yace “malam Taura za ka kai mu can ciki wajen transforma na biyu”suka shiga tunda suka fara tafiya daga ita har shi babu wanda ya sake cewa dan uwan sa wani abu har suka isa anguwar. tafiya suke tayi can cikin anguwar can ƙarshe-ƙarshe babu kowa se daji. se wani Ɗan ƙaramin gida nan ya cewa me napep din ya tsaya. sauka suka yi ya biyasa nan ma sake riƙe mata hannun yayi har bakin kofan gidan, ya sa key a ƴar ƙaramar kofar ya buɗe suka shiga.
Ƙarewa ko ina kallo ta ke yi gida ne ɗan ƙarami deden zaman mace daya a talauce,an de gama gini an yi plasta amma babu ko fenti kofar falon suka nufa nan ma ya murza key ya buɗe suka shiga katifa ce kaɗai a cikin falon se akwatin kaya daya. Kallansa ta yi ta ga shima ita yake kallo,haka kawai ta ringa jin wani irin yanayı me wuyar fassaruwa jikinta ya yi sanyi sosai idanunta suka fara kawo hawaye ita kan ta bazata ce ga dalilin hakan ba amma tana jin kusancinta da wani sashi na ta.
“Mujahid “ sunan sa kawai ta iya ambata dakyar girgiza mata kai yayi alamar kar ta ce komai sannan ya nuna mata kofar wani daki,kallon kofar ta yi da idanunta da suke tsiyayar da hawaye marasa dalili,dakyar ta iya taka kafarta ta isa bakin kofan ta buɗe ta shiga, lokacin da tayi arba dashi wani irin sarawa kanta yayi kamar ze tarwatse ga mummunar jiri da ya kwasheta da se da ta kusan zubewa a ƙasa,jikin ta ya ɗau kerma zuciyanta na bugawa da karfi kamar ze baso kirjinta ya fito. komai na dakin ya soma juya mata kasa riƙe hawayen ta tayi. Jiki na rawa ta soma isa inda yake, tsayawa tayi akan sa tana kallan sa sosai a hankali da dasasshiyar muryarta ta furta
“Zaid,Zaid da gaske kaine? Ya Zaid dina dama kana wannan duniyar ?” Zaid da ke kwance kamar gawa akan gado na asibiti be ma san tana yi ba fuskarsa manne da oxygen ga wasu igiyoyin na’urorin da suke manne a kirjinsa dakin ma ko ina na’ura ce, fuskarsa ya tara gashi Kamar ba ƙaramin matashi ba, jikinsa ba riga, se guntun wando, saboda daga abinda ya Kama daga tafin kafarsa har zuwa cinyarsa a kone yake gurin yayi wani iri babu dadin kallo. Gaba daya ya sauya kamar ba Zaid matashi ɗan son gayu da kwalisa ba wanda yan matan TikTok da IG suke crushing ba. Hannunta na rawa ta sa ta shafa fuskarsa tabbas Ya Zaid din ta ne wanda take matukar so da kauna, ɗan uwanta da ya ke ji da ita kamar kwai. zuɓewa tayi a gaban gadon ta fashe da marayan kukan da tunda ta dawo hayyacinta bata yi sa ba. kuka take yi sosai tana tuna abubuwan da suka faru dasu cikin kukan ne take cewa
“Ashe akwai ahali na daya yake raye a wannan duniyar? ashe ba marainiya bace gaba daya, ɗan uwana na jini yana wannan duniyar,Ya Zaid ya aka yi ban san da kana raye ba meyasa?meyasa,meyasa? ” ta ƙarishe maganar tana dukan ƙasa sosai take kuka kamar za ta shiɗe, Mujahid dake tsaye a bakin kofa shi kansa hawaye yake yi cike da tausayinsu, mutanen da suke rayuwar su cikin farin ciki da kwanciyar hankali sune yanzu suka zama abun tausayi cikin mutum biyar biyu ne kawai suka tsira nan ma daya na halin rayuwa ko mutuwa.
Miƙewa tayi ta zauna a gefen gadon sannan ta kwantar da kanta a wuyansa tana ci gaba da kukan ta amma ta sassauta muryar ta.
A can super market kuwa bayan Haydar ya gama wayan ne ya juyo gare ta se de wayam ba ita a gurin da ya barta, dudduba ta yayi a farfajiyar amma babu ita hakan yasa be kawo komai a ran sa ba yai tunanin ta shiga ciki gurin su Yusra hakan yasa ya shiga cikin shima, samun su ya yi suna ta shopping suna ganin sa shi kaɗai kuma tare suka bar su a waje Yusra ne ta soma magana “Uncle Haydar ina Alisha din?”
Kallon me ki ke nufi ya aika mata “kamar ya ina Alisha ba ta shigo gurin ku bane ? " Kallon junan su suka fara yi suna girgiza kai su de ba su ga Alisha a cikin nan ba, saboda a waje su ka bar ta dashi yanzu kuma yana tambayar su ina take
“Meye ku ka tsaya kuna girgiza kai kamar wasu kaɗangaru kun min shuru ina tambayar ku?”
“Uncle Haydar ba ta shigo nan ba fa, ai a waje mu ka bar ku tare. amma gaskiya ba ta zo cikin nan ba dan da ta shigo za mu ganta tunda ta baki-baki mu ke ko Zainab? “ da sauri ta gyada wa Ameeran kai.
“To ina waya na juyo ban ganta ba shine nayi tunanin tana gurin ku” ya faɗa yana danna kiran layin Adda yana so ya ji ko de gida ta dawo, suna waya da Adda ne yake tambayar ta ko Alisha ta dawo amma tace masa ah ah bata dawo ba,, tana kokarin tambayar sa meyafaru ya kashe wayar. Da gaggawa suka fara neman ta a cikin San Hussain super market din amma fa babu ita babu dalilin ta. Zainab ce ta ce “ abun takaici ga shi babu waya a hannunta balle mutum ya kira ya ji lafiya”
Se a sannan Haydar ya san bata ma da waya ya ji haushi sosai dan da ya sani da ya jima da siya mata saboda rana irin haka yanzu ba su san inda ta yi ba.
“Amma mu koma gida kawai ni ina tunanin ko ta je gidan wannan kawun na ta ne da ta je jiya “
Sun yarda da maganar ta dan se yanzu hakan ya faɗo musu amma to meye dalilinta na tafiya ba tare da ta sanarwa kowa ba duk ta daga musu hankali. a haka suka shiga motar, kasuwan waya ya shiga ya siya mata waya iPhone 12 normal irin na hannun Zainab da sim ya koma motar yayi driving na su zuwa gida. A falo suka samu Adda,Meenal,Maryam da jaririnta Aryan suna zaune kana ganin su ka ga damuwa a tattare da su domin tunda ya kira su yake tambayar Alisha suka san something is not right
“Haydar ina ne inda Alisha ta je ta?”
Tambayar da Adda ta fara wurga masa Kenan
Se da ya zauna jiki a mace yace “Wallahi Adda duk bamu sani ba saboda ina fa tsaye da ita a bakin motar aka kirani na juya ina waya, na gama kenan na ga babu ita, kuma ko cikin San Hussain din ba ta shiga ba”
Tafa hannu Adda ta yi ta soma sallallami “ohhh ni Zuwaira ina yarinyar nan ta je to? Allah yasa de kafanta ne ya ja ta ba janta aka yi ba”cikin damuwa duk suka amsa da ameen banda Meenal da ta taɓe baki.
Maryam dake bawa yaronta madara a feeder ne ta ce “kun san fa Alisha ƴar dakin Hajja Hauwa ce ko de ta bi gidan ta ne? ku gwada kira ku tambaya”
“Maryam Hajja Hauwa ba ta gari ,yanzu muka kira ta ma ɗaga mata hankali kawai zamu yi,su Ameera de sun ce ƙila gidan kawunta ta je mu jira zuwa anjuma mu gani in ba ta dawo ba nasan abinda zan yi “ya faɗa yana miƙe wa tsaye da niyar zuwa part din sa,duk sun yarda da maganar sa, hakan yasa suka yi jugum ko siyayyan abinda suka je yi ma basu samu sun yi sa a tsanake ba suka dawo.
“Kun wani ɗaga hankalin ku akan wata banza mara asali,kila saurayinta ta bi kun wani damu kan ku” da zallan mamaki duk suka kalli Meenal da tayi maganar hankalin ta kwance.
Yusra da ta ke bin ta da banzan kallo ne ta ce “waya gaya mi ki kowa ma irin ki ne me shegen biye-biyen maza?ke har kina da bakin magana tsabar mutuwar zuciya kin tattaro kin dawo gidan su saurayi”
Murmushi Maryam,Ameera da Zainab suka yi domin kuwa amsar da Yusra ta bawa Meenal ya musu dadi,Meenal da maganar ya mata zafi ne ta ce “to ai gwara ni, ke fa me neman…”
“Ya isa dallah kar ku cika wa mutane kunne da haukan ku” Haydar ya faɗa a tsawace wanda ya dakatar da Meenal daga ƙarasa maganar ta. aikuwa mit tayi da bakin ta domin duk barikinta tana shakkan Haydar nesa ba kusa ba.
Part din sa ya wuce yana tunanin yaushe ne Alisha zata dawo gida.
Se da ta sha kukan ta sosai ta koshi kafin tayi shuru har zuwa yanzu tana kwance a jikin Zaid jin ta take tamkar ba'a duniyar take ba, farin ciki da bakin ciki ne suka haɗu mata a lokaci daya. tana kwance se sauke numfashi take saboda yanda zuciyarta yake tsananta bugawa
“A daren da wannan abu ya faru Allah ya ƙaddara Zaid yana da dogon kwana, wutar ya faracin jikinsa da kayansa wanda hakan shine ya farfado dashi daga doguwar suman da yayi,a gaggauce ya cire Kayan jikin sa sannan ya je dakin sa dakyar ya lalubo jallabiya ko da ya sa shi ma jiƙewa da jini ya fara yi. Kallon ku yayi ya ga duk babu wanda yake raye hakan yasa ya fice ya bar gidan ya kai kansa karamar asibitin Miyetti dake kusa da ku. An yi sa'a likitocin sun karɓesa suka basa taimakon gaggawa saboda in ba su taimaka ba ze iya mutuwa sakamakon harbi da buguwa da yayi akai ga kuma kunnan wuta. Bayan ya farfado ne suka tambayesa ina ahalinsa yace basa nan amma su bashi waya akwai wanda ze kira. nayi mamaki ganin kira karfe uku da rabin dare kuma da bakuwar number da kamar bazan ɗaga ba se kuma nayi tunanin ko wani daga gida ne yake kiran na. ko da na ji muryar Zaid hankalina ya tashi nan doctor din ya ce min in zo asibitin miyetti a cikin daren na fita,ko da ganin halin da Zaid yake ciki se da nayi kuka kamar raina ze fita. Zama nayi kusa dashi ina tambayar sa me yafaru nan ne ya kwashe komai ya faɗa min harda yanda ya zo asibitin duka yana gama sanar dani kenan ya suma. Likitan ne ya kira ni ya bani result din hoton da suka yi masa akai, ya samu buguwa ba na wasa ba wanda in ba'a ɗau mataki ba ze janyo masa cutar mantuwa ko kuma de ya shiga coma na tsawon lokaci, sannan duka da aka masa sun karya masa ƙashin baya,ga kuma mummunar kunan da yayi duka aiki zaa yi masa kuma baa nan Nigeria ba, in ana so ya warke sumul tofa dole a fita dashi India a yi masa aiki gaba daya. wannan shine kawai mafitar da likitan ya bani,tambayar sa nayi da kudin aikin da expensives din tafiyar mu ze kai nawa budan bakin sa yace min ze kai million ashirin da biyar zuwa talatin. hankalina ya matukar tashi, domin ko mahafina bashi da wannan kudin balle ni komai tsaya min yai cak , lokaci daya masassara ya sauko min abun ya haɗu min biyu ga abinda Zaid ya gaya min ga kuma kudin aikin sa,haka har garı ya waye ina asibiti amma har time din Zaid be farka ba, karfe sha daya na ga ko ina a social media platform maganar ku ake yi kan cewa gidan ku yayi gobara duk kun mutu. ji nayi ina ma ina da power da zan fito in sanar da duniya gaskiya. A haka na kwashe sati biyu a asibiti da Zaid amma fa babu labari,doctor ne ya sanar dani ya shiga coma kuma baze farka ba se an yi masa aiki. Duk wasu kuɗaɗe na nayi amfani dasu wajen yi masa treatment daga karshe ba yanda na iya haka na kawo sa wannan gida shima haya na kama shine aka zo aka shirya dakin nan aka sa masa wayannan na’urorin da ki ke gani”
Share hawayen fuskar ta tayi sannan ta miƙe zaune ta na me kallon Mujahid “nawa ne kace ze iya a yi masa aikin komai da ze warke Mujahid?”
“25 million ze yi komai kamar yanda doctor can ya faɗa min” jinjina kai ta yi ta kuma faɗin “amma ya zaa yi a fitar dashi ba tare da an samu mishkila ba? saboda ba na son duniya ta san muna raye yanzu “
Numfashi ya sauke ya shigo dakin “wannan duk ba me wahala bane samuwar kudin ne wahala Alisha,samun 25 million shine babba “
“Ko nawa ne zan kashe saboda ɗan uwa na. daga yau ka fara shirye-shiryen tafiya ni zan tafi yanzu in ɗauko maka ATM kai se ka san yanda za ka yi dashi “
Be taɓa tsammanin za'a samu kudi har haka a gurin Alisha ba saboda yanda komai nasu ya kone ,amma se gashi tana da wayannan makudan kudaden mamaki yayi ba ɗan kaɗan ba. amma yayi farin ciki da jin haka ko ba komai yanzu abokin sa ze samu lafiya,yana cikin wannan ya ji ta tana mai magana amma da yake hankalin sa na wata duniya be ma ji abinda ta faɗa ba.
“Me ki ka ce?”
“Ina son in ba ka hakuri sannan kuma in gode maka na kokarin da ka yi da ɗan uwana har na tsawon shekara guda, nagode sosai. tabbas kai din abokine na kwarai, aboki da ya riƙe amanar abokantaka, ba kowa ne irin ka ba”
Dafa kafaɗar ta yai “Noo need for this Alisha,ni da Zaid tamkar uwa daya uba daya haka muka ɗauki junan mu. kuma na tabbatar da a ce ni ne a wannan condition din Zaid ze min fiye da haka so please stop thanking me “
Murmushi ta yi hakikanin gaskiya Mujahid yayi gaining respect a gurin ta saboda yanda ya kula mata da jinin ta “ni zan je gidan Inna ta ,zan ɗauko maka komai in ya so se mu haɗu a junction na by pass ko ta gurin kasuwan tare."
A tare suka fito kowa ya hau abun hawan sa daban tana isa gida ta sanar wa Inna sosai ta tayata murna. se da ta watsa ruwa sannan ta ɗauki abinda ya kawo ta sannan tai mata sallama lokacin ana gabannin kiran mangriba,yanda suka yi a bakin tare suka haɗu nan ya sanar da ita nan da kwana uku zasu tafi. Sanar da ita yayi Peter ze shigo gobe kuma ya ɗau aniyar taimaka mata domin ɗaukan fansar ta akan sa.
Bayan ta basa ATM ne ta soma tunanin yanzu ya zaa yi ta koma Ɗan gaske family ? wani tunani ta yi na gobe ne za ta fuskanci Peter kuma in de ta koma gidan Ɗan gaske ba lallai ne ta samu daman fita a lokacin da ta so ba. Gidan Inna ta koma kawai saboda shine kawai solution
yawan comment da sharing da like din da zaku yi shi ze tabbatar min da kuna jin dadin wannan littafi,your comments really mean a lot to me ☺️❤️
Don’t forget to comment,share and like 👍