TUDUN ADAMA

5: Rake

by @mbello38

"Kash adeela, karfa kije! Filin rake nada nisa kuma hanyan akwai hatsari sosai." Pitinau ta kokama adeela.
Zaune take a dakin bacci kan makwancinta, adeela na tsaye tana shirya kayanta cikin dan sagale, jaka karama na sagalawa a baya.
Dazu da safe aka kasasu wurin samo samo abinci sai akace sarauniya ta bukaci zaki saboda haka se aka cire kwari goma suje samo rake. Adeela na daya daga cikinsu kuma tashera na daya daga cikin sojojinda zasu tare.
Pitinau ta kalle adeela cikin damuwa. "Adeela, tunda kikaga tashera tana daga cikin sojojinda zasu muku rakiya anya bada sa hannunta cikin hadawa dake a wannan tafiya me hatsariba?!"
Adeela tayi murmushi tana cigaba da tura guzurinta cikin dan sagalen. Ta tuna ana cikin zabansu taga tashera da group dinta sunzo sukama bireja me rarraba kwari magana.
Se kawai adeela taga bireja ta jawota ta hadata da masu nemo rake ta zama cikamakon na gomansu. Tashera tayi murmushi tana sanarda bireja tana daga cikin sojoji masu tafiya tareda kwarin. Tayi hakane don adeela taji kuma tasan bazata mata da saukiba.
"Dasa hannunta mana. Amma niba kwaro bace me ja baya a wurin nuna bajinta."
"Wane bajinta anaso ki hau sarauta. Infa wani abu ya sameki bazaki iyama yin takaranba balle hawa mulkin!"
In tashera tana tunanin ita adeela takeso ta cutar, to tayi kuskure. Se tayi nadaman tahowa tareda ita wannan tafiyan. Filin rake inda ma'aikatan gidan gonan ke siyan rakene.
A wajen gidan gonan ne, ketaren titi. Akwai me saida rake anan kiyashin ke samo raken. Tafiyan zata kaisu awa hudu shiyasa duk lokacinda sarauniya ta bukaci zaki, suke shiri na musamman.
Ba'a daukan kiyashi da yawa, kadan ya wadatar. Ana zaban masu kuzari kuma masu gudun tsiya domin akwai kwari da dabbobinda zasu iya lahantasu a kowane tako na tafiyan.
Adeela ta riga ta kafe setaje wannan tafiyan, kuma se tayi nasara dukda abubuwanda zeja mata cikas a cikin tafiyan. Ta kalla pitinau.
"Karki damu pitinau. Na san inda takeda rauni, kuma bazan bari taci galaba a kainaba."
Pitinau ta mata kallon anya. "Kefa ke kadaice, tashera kuma tanada jama'anta!" Pitinau ta hade gira.
Jajiria, me kulada dakin baccinsu adeela ta tsaya bakin kofan. "Adeela, ke ake jira duk sun shirya!" Ta daga murya don taji domin makwancinta yanada nisa da kofa.
Sagala jaka adeela tayi ta kalla pitinau. "Karki damu, ni karfece me wuyan lankwasawa." Ta fice.

Hanyan rake suka dauka, kiyashi goma da sojoji takwas. Ja gabansu itace ogansu paipai, suna sauka daga tudunsu ta fara zuba kamshin kwari sauranma suka zuba. Suna gangarowa kasa suka tsaya.
Paipai ta nuna wasu shukoki tace zefi sauki idan suka fita daga idanun mutane da dabbobi da kwari. Tashera itace ja gaban sojojin dake raka kwarin.
"Ta shukoki akwai hatsari saboda kwari masu fira dake harin kiyashi. Zefi kyau mubita fili ta gefen katangan can."
Hakane fa. Wani lokaci da paipai sukaje samo rake, a gaskiya ranan sunyi rashi sosai saboda wata fara tasasu gaba ta take wasu ta cinye wasu dake rikeda raken, wasu duk sukaji ciwo da rasa wasu sassa na jikinsu saboda gudu da tsira daga farar.
"Yanda tashera tace haka za'ayi. Mubita gefen katanga sannan kowa ya bude idanu don nan hanyan akwai hatsari."
Haka suka saka kafafuwansu suka jeru a layi suna tafiya suna fesa kamshin kwari kowa na zare ido yana kalle kalle kar suyi arba da wasu makiya daga kwari.
Adeela ta hango tudun shuri. Tudune na tururuwa dake kusada katanga amma ta bangeren hagu. Tudun yayi sama ya kusa kai tsawon katangan. Ganinta na karshe ma shurin lokacin tsawonshi na rabin bangon.
Amma yanzu ya kusa kaiwa saman bangon gashi ya kara girma da fadi. Ta hango tururuwa sunata harkokinsu a wajen tudun. Suna cikin tafiya, adeela ta lura tashera dake ja gaba ta fara komawa baya a hankali harta koma can karshe. To meyasa take.......
"Kadangare jangwale gwadaaaaa!!!" Paipai ta kwala ihu.
Wani katon jangwale ya hangosu ya tsaya yanakallonsu yana lashe baki. Tuni hankalin kowa ya tashi kowa ya rikece aka fara guje guje. Adeela taja wasu kiyashi zuwa wani lungu dake jikin bango amma seme. Jangwalen ya rugo a guje yayi kansu.
Suka watse wasu sukayi hagu suna ihu wasu sukayi dama. Adeela da wasu kiyashi biyu suka kara wuta suna dosan lungun katanganda adeela taso suje su boye da farko.
Aiko wannan jangwalen yace basu isaba. Yayi tsalle ya taro gabansu yanata kallonsu yana lashe baki.
"Ke kibita hagu ga wani karamin tsaga can ki shige. Ke kuma muje can kasa ga wani tsaga can mu......." Adeela ta fara bada shawara aka katseta.
"Kin haukacene? Wancan tsagan na kusada kafan jangwalen! So kike ki kaini ga mutuwata?!!!" Ta fizga ta ruga a guje tabi hannun hagun.
Jangwale ya tsallake adeela yabita a guje ya tareta tareda dayan kiyashin. Ya taketa sannan  ya lakumesu a baki. Gaban adeela ya fadi ta arta a guje ta shige lungun, zuciyarta na bugawa bila adadin.
Ta leka waje ta hango sauran kiyasan nata guje guje da labe labe, wasu ana cinyesu, wasu an takesu sannan aka cinyesu. Ta hango tashera na leke daga inda ta boye, idanunta na kalle kalle kaman tana neman wani abu.
Suna Ido hudu, jikin adeela yayi sanyi. Wani kallon mugunta tashera ta mata seda taji ilahirin jikinta ya fara rawa. Me tashera ta shirya? Shairin data saba? Lallai ko dole ta bar wurin inba hakaba zata tona mata asiri wurin jangwalen.
Aiko kaman ta karanta abinda ke fuskan tashera. Se gani tayi ta fito a guje tayi hanyanta. Mene?!!! Tazo wurinta shima fa wancan biyota zeyi yazo inbe cinye dukansuba ita ya cinyeta!!!! Aiko tuni ta fito ta lafta a guje tayi hanyan gate.
Kyallara idon jangwalen ya hango kiyashi biyu suna gudu. Daya katuwa wanda take kusadashi, dayan kuma karama amma bade guduba don harta kusa fita daga territory dinshi.
Yayi tsalle ya harba a guje yabi tashera. Ta juya taga yana binta tayi murmushi ta kara wuta tana doso adeela. Tuni adeela tayi kasan katangan ta hango wani tudun kiyashi. Aiko tayi wurin tana kallon baya taga jangwalen nata karasowa da zafi zafi.
Tashera ta lura taga adeela nayin hanyan tudun fira. Tudun sunada kwari masu fira, nan ya samu sunanshi kuma basu shiri da kiyashi. Tayi murmushi, in adeela ta tsira daga jangwalen ai bazata tsira daga tudun firaba.
Ta duba baya taga jangwalen na binta harya fita daga territory dinshi ta tsaya tana kallonshi. Adeela ta ruga ta shige tudun seta leko taga abinda ke faruwa.
Taga tashera na kallon jangwalen shi kuma ya dosota ya tsaya yana mata kallon mamaki. Se ganin yayi wani katon bakin jangwale ya diro gabanshi yana mishi kallon hari.
Nan ne ya lura ya fita daga territory dinshi kuma ma harya shiga territory din wani. Aiko tuni suka kaure da fada. Tashera ta kallon adeela me labe tayi murmushi ta ruga tabi wata hanya.
Haka bakin jangwalen ya kashe dayan jangwalen ya amshe territory dinshi. Zuciyar adeela ta kwanta amma seme? Wasu jajayen kiyashi masu fikafikai suka zagayeta sukayi awon gaba da ita.