7: Rake 3
by @mbello38
Daga kafan keda wuya, adeela ta kalla yanda ta dira a gabanta ta wuce. Phew! Ta sha an mirtsiketa tunda ita 'yar mitsilace wama yasan abinda ke faruwa a karkashi takalmansu.
Sauri tayi ta dosa titi. Wai! Wannan bakin abin. Wata kwaro ta taba bata labarinshi tace mata ga girma ga tsawo ga burji burji. Adeela ta shafa da hannunta sannan ta kallo gabanta.
Tafiyane gagarumi kuma ga kafafuwan mutane da motoci da bikes da kekuna, in batayi hankalinba seko a mirtsiketa. Gaskiya hanyan nemo raken nan akwai hatsari me girma.
Amma tunda tazo nan, to gaskiya seta cika aiki. Baza tabi wadannan mugun hatsarurrukanba don kawai tazo nan ta fasa. Aiko ta kalla hagu taga titinne a shimfide bila adadin, hakama dama.
Kafa ta saka ta harba a guje. Tabdi! Hatsari akan hatsari. Katuwan taya ta kusa latseta, ta kauce. Wani kara daga wata mota ya rikita mata kai, ta rikice. Kai, da kyar ta gudu da cin birki ta iya tsallake titin.
Murna, farin ciki da jin dadi ya bayyana a fuskanta. Ta tsallake titin kuma bata fada ko'inaba se cikin rake. Ta mulmula cikin raken, ga kamshi ga ruwa. Ta dandana raken, wani ruwan zaki me dadi ya dira a bakinta ta rufe idanu tana tsotsa.
Kai rake akwai dadi ga zaki. Tayi sauri ta mike tsaye tasa hannayenta hudu ta kwasa raken tasha bila adadin. Akwai ma'ajiya a cikinsu, nan take tara zakin in taje taba sarauniya.
Itama tasha nata zakin donko tasha wuya ya kamata ta farfado. Ta gama da raken ta kalla yanda wata wuka ke fille bayan raken, yanda wasu hakoran mutane ke tauna raken, ruwan raken na fesowa daga bakunan mutane.
Tsoro ya kama adeela ta ruga ta tsallaka titin. Yanzu kuma hanyan komawa tudunsu shima fa se a hankali. Bazata sake bin katangaba don tasha wuya wancan karon. Kuma wannan tasherance ta bada shawaran abishi. Ashe da kudurinta!
Haushi ya kama adeela. Taya za'ayi tashera taja musu bala'in da yayi sanadiyan rasa rayukan kiyashi da yawa?! Tana komawa seta kai karanta. Amma za'a yarda tunda ita kadai tasan kudurin tasheran?
Ta filin gidan gonan adeela tabi duk dade akwai wasu tudu da yawa ta wurin amma su ba ruwansu da ita. Harkokinsu kawai sukeyi sede su kalleta su cigabada aikinsu. Ta wuce filin ta hau kan siminti shima filin siminti se tsawon tsiya ta wuce sannan ta fara hango tudunsu.
Wani murna ya dira a fuskanta. Gida. Har wani karfima ta kara ji, tayi sauri ta dosa bishiyan tudunsu. Ji kawai tayi an nausota ta fadi ta mulmula kasan tudun ta watse a kasa.
Cikin jin haushi ta dago taga waye wannan daya bigeta haka. Ba kowa bace illa tashera da group dinta su hudu. Suka gangaro daga tudun suna kallon adeela. Daga kanta adeela tayi taga gumza, bompai, jera da tseela suna murmushin mugunta.
Mamaki ya kama adeela don tasha tashera ta sheka barzahu. Wato tana raye kuma harta dawo tudun. Tota samo raken ko dawowa tayi hannu baka? Ta mike tsaye da kyar ta kalla tashera.
"Mena miki da kika nausoni haka?"
Kallon rainin wayo gumza tayi mata, ta hannun daman tashera. "Wato kin rayu kuma kin dawo. Kina tunanin zamu miki da saukine?!"
Tashera ta iso ta damka wuyan adeela tana neman dagata sama da hannu daya amma ta kasa. Mamaki ya kama sauran don satin daya wuce tsaf tashera ke daga adeela da hannu daya.
Abin yaba tashera haushi sosai. Wai ace itace ta kasa daga adeela sama ta wuya! Ya akayi tayi nauyine haka? Me take cine da tashera bata amsheba harya kaiga tayi nauyi haka bata saniba?
Ta jawota kusada fuskarta. "Me kike cine haka kikayi nauyi?
"Abin.....abinda.....kowane....kowane lebura ke....keci." tace a wahale saboda shake wuyanta da tashera tayi.
"Karya kikeyi. Ainaga kin isa filin rake kinsha rake sosai saboda haka amayoshi zakiyi ki bani in kaima sarauniya."
Gumza tazo kusada adeela. "Sannan kuma mu kai karan cewa kece sanadiyan rasa rayuwan kiyashinda kika fita taredasu!"
Kambu! Adeela taji wani makakin haushi ya shake wuyanta. Banda son amshe wahalanta da suke sonyi kuma harda kulla shairi!! Ta wulwula ta kucce daga shakan tashera, ta nunata.
"Bayan kece kika bada muguwan shawaran cewa abita katanga hanya tafi kyau! Wato baki iya samo komaiba shine kike son kwace min nawa."
Zuciya taci tashera ta wankama adeela mari seda ta kife a kasa. Tasa matanta su kamo adeela su matseta seta amayo ruwan raken. Suka rike hannayenta tana ihu tana birgima. Bompai ta matse kasan cikinta wurinda idan aka taba dole ta amayo abincin dake wurin ajiyanta a cikin cikinta.
Kwallon ruwan rake ya fito daga bakin adeela tana gani ba yanda ta iya. Tashera na murmushi gefen baki ta dauka kwallon ruwan tana kallon idanun adeela ta shanye. Tasa matanta su tafi da adeela a kulleta a kejin masu laifi. Haka suka jata sukayi gaba suna dariya.
Bada saninsuba ashe jafu da bilba suna kallon duk abin dake faruwa tun dawowan adeela. Sintura ta iso taja yaran tana musu fadama be kamata su fito kusada wajen tuduba infa fara tayi awon gaba dasu. Ta kalla bataga abinda yaja hankalinsuba tayi gaba. Suka bi bayanta.
Dakin sarauniya tashera ta dosa, sojojin bakin kofan suka kalleta ta gaya musu tazo ba sarauniya zakinda ta bukata. Ta shiga ta iske sarauniya hubba a kishingide tana sheki ga tululen ciki ta kallo tashera.
Leburorinda suke kulada sarauniyar sukama tashera iso. Tazo ta amayo kwallon ruwan rake ta mikama wata lebura. Leburan ta karba taba sarauniyar. Murmushin dadi ya sauka a fuskan sarauniyar ta kalleta ta gane wacece sojan.
"Tashera zaki samu duk abinda kike bukata."
Amma bukatanta abu daya, taga an kore adeela daga tudun adama kawai. Batayi sanyi a gwiwa wurin gayama sarauniyar da mukarrabanta yanda wata lebura ta jawo musu hasaran kiyashinda suka tafi nemo ma sarauniya zaki.
Tayi sanadiyan rasa rayukansu gabadaya lokacin data tsokano jangwale gwada. Babu yanda ba'ayi da itaba karta jawo musu jangwale amma inaaa, takiji gashi kowa ya mutu amma ita ta tsira harda dawowa tudun.
Jin labarin nan ya konama sarauniya rai. Wata banzan lebura ta jawo rashin rayukan duka kiyashinda suka tafi nemo mata zakinta! Sannan har tanada kafafun dawo mata tudu!!
"Ina take?!"
"Garkame a keji, sarauniyata."
"Yayi kyau! Shugaban sojoji, iso da ita gabana!!"